Daudar Gora Book 2 page 3
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (03)
......Kamar yanada Malikat Haseenat ta faɗa an sake tsaurara tsaro a ɗakin da Iffah take, bana dakaru kawai ba harda tarin jami'an tsaron da Shahan-shan kawai suke bama tsaro tako ina yayinda ta kasance cikin masu iya bibiyar komai kai tsaye. Shi kansa abincin da ake kai mata a yanzu ya kasance na musamman dake samun saka ido, dan a rana ta biyar da yunwa ta nema mata illa sai dai likita ya shiga ya dubata. Dan dole ta koma cin abincin sai dai bata wuce lauma uku ko kurɓa uku na madara take ta ajiyewa..
....A ɓangaren masu faɗa ajin masarauta ana ta cigaba da tattara bayanan da suka kamata ta hanyar bincike. Sai dai tsaiko na farko da aka fara samu shine rasa cctv footage na sashen Tajwar Eshaan da ga asubahin randa al'amarin zai faru har zuwa lokacin isar su Daneen Ammarah da su Miran Jasim sashen. Sai wayar Iffah da itama aka nema ƙasa da sama aka rasa da lap-top ɗinta. Wannan al'amari ma ya kawo ka-ce-na-ce bana wasa ba har takai jami'an tsaro cafke mai kula da ɗakin tsaron aka garƙame. Amma kuma juyin duniya yace bai san yanda akai ba. Hakama hadiman sashen Iffah kaf ɗinsu an tattare, suma kuma sun rantse sun kuma basu san yanda akai wayar Iffah da lap-top ɗin sukai ɓatan dabo ba. Ba kuma suga wani ya shigo sashen ba. Waɗan nan abubuwa na rashin makamar tabbatar da Iffah akan laifin da kowa keda yaƙinin ta aikata ya kawo rabuwar kai da rikici babban akan mata hukunci. Yayinda su Miran Jasim suka sha jinin jikinsu, dan haka suka zama ɓangaren masu nuna kawai a kashe Iffahn. Ɗayan sashen kuma da suka haɗa da zuri'ar Sayeed Khairul-Bashar suka bore akan bincike na har sai an tabbatar a kuma ji dalilinta dan in ma har ta aikata to dole akwai saka hannun wasu a masarautar.
Rikici ne bana wasa ba, dan har takai anyi wani zaman a karo na biyu amma sam babu masalaha daga kowane ɓangare. Ɓangaren kuma dake ganin kashe Iffahn shi yafi sauƙi sune ɓangare mafi ƙarfi dan da yawansu na jikin Tajwar Eshaan ɗin ne. Malikat Haseenat ce kawai ke nuna a dai cigaba da bincike kar a aikata aikin dana sani. Hakama Daneen Ammarah sam zuciyarta taƙi aminta Iffah zata aikata bisa raɗin kanta, idan ma har ita ta aikata ɗin kenan tunda har yanzu babu wata shaida dake nuna itace ɗin ta bashi madarar dan bayan ita suma masu dafa masa abinci da amintacen hadiminsa duk suna a rufe. Ƙulle-ƙullen su Miran Arshaan ne yasa dukan zargin yafi ƙarfi akan Iffah. A yanzu haka kuma sunyi kane-kane wajen sake rura al'amarin da nuna ɗaukar zafi fiye da kowa musamman Miran Jasim daya kasance mai riƙe da masarautar har zuwa samun lafiyar Tajwar Eshaan da ake fata...
★★.... ★.....
Har cikar kwanakin mako babu wani cikakken masalaha akan al'amarin, sai ma ɗaukar zafi da kowane ɓangare suka sake yi. Iffah kuma taƙi taɓuwa bisa jajircewar Malikat Haseenat na sai fa anyi bincike. Wannan kafiya ta saka Miran Jasim da Miran Arshaan kasa zaune da tsaye. Barbushi kuma ya tabbatar musu in har fa Malikat Haseenat na numfashi bazasu taɓa samun yanda suke so cikin sauƙi ba. Dan haka ya basu zaɓi biyu. Kodai su gaggauta kasheta da hanunsu, ko kuma suyi ƙoƙarin tunzura Malikat Bushirat dayin amfani da ita kamar yanda sukayi da Iffah ta kawar musu da ita. Hankalinsu ya tashi, dan kashe Malikat Haseenat abu ne ba ƙarami ba musamman a wannan gaɓar da take taka wata rawa mai banbanci da tasu duk da tafisu kusanci da Tajwar Eshaan. Duk yanda suka tattauna da aunawa sun gafa wannan hanyar mai wahala ce a gare su, dan haka suka zaɓi nufar sashen Malikat Bushirat ɗin domin fuskantar ta kai tsaye. Fatansu zaman ya zame musu jifan tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, dan tunda aka fara rikicin nan Malikat Bushirat taƙi tofa komai ma, ta tattare hankalinta kacokan akan ganin lafiyar Tajwar Eshaan da aka hana kowa gani a masarautar sai ita da Malikat Haseenat har zuwa yau da ake cika kwanaki tara da faruwar komai.......
★... MALIKAT BUSHIRAT ★...
Yanda take magana cikin fitar ɗacin sauti tana kaikawo a fusace zai tabbatar maka ranta a ɓace yake ƙololuwa. Malikat Bushirat kenan da tun faruwar al'amarin nan babu wanda zaice yaji bakinta duk wannan sa toka sa ƙatsin da akeyi. A yanzu babban burinta bai wuce samun lafiyar tilon ɗan nata ba, batun hukunta wadda ta zama sanadin komai wato Iffah kuwa duk faɗi tashin da ake komai tana sane, sai dai bata shirya saka baki ba a yanzu acewarta akwai lokaci. A tsahon kwanakin nan dukkan wani motsin masarautar ruman a cikin kunenta yake fiye da masu kai kawon. Hauhawa da bunƙasar ɓacin ranta na yanzu kam yana da alaƙa ne da tattaunawar ta da su Miran Jasim, zaman nasu kuma kacokan ya alaƙantu ne ga hana hukunta Iffah da Malikat Haseenat tayi kai tsaye har sai anyi binciken da ta sharɗanta.
Irin wannan fusatar ga Malikat Bushirat shine fatansu, dan haka suka dubi juna cikin son danne murmushin kan fuskokinsu. Zama suka gyara tare da sake buɗe sabon shafin abinda suka faro. Miran Arshaan ya sake marairaice fuska mai cike da tsantsar damuwa yana mai duban Malikat Bushirat..
“... Ni a ganina ɓacin rai ko damuwa bashi ne zai zame mana mafita ba. Mu zauna mu tattauna yanda abinda ya dace kafin lokaci ya ƙure. Ban san miyasa Mammah ta ɗauka al'amarin nan da rashin muhimmanci ba. A yanda nake ji a zuciyata da tuni labarin wata akeyi ba yarinyar nan ba. Dan banga dalilin da zaisa ace wai sai anyi bincike za'ai mata hukunci bayan komai data aikata a bayyane yake, wannan tamkar muna nuna rashin muhimmancin ran yaronmu ne ma ai.....”
“Gaskiya kam Arshaan Akhi”. Miran Jasim ya tari numfashinsa da sauri, cikin nuna ɓacin rai shima ya cigaba da faɗin, “Ni kaina komai na kasa fahimta musamman akan ra'ayin Mammah. Sai nake ganin bata damu bane? Ko kuwa tafi son yarinyar sama da gudan jininta? Inba hakaba minene na waɗan nan sharaɗin marasa tushe? Bayan komai a bayyane yake. To gashi tace sai anyi bincike, amma dai-dai da cctv footage an nema an rasa tabbacin komai shiri ne. Inada yaƙinin komai sai dai yarinyar nan ta shirya kafin ta shigo masarautar nan. Dan binciken mu ya nuna ta aurensa ne dama domin ɗaukar fansar ƴan uwanta guda biyu, shiyyasa ta kwantar da kai ta shiga jikinsu musamman Mammah da Akia Ammarah da a yanzu suke nuna goyon bayansu kan cigaba da rayuwarta sai kace sun manta matsayin wanda taso halakawa a gare su...”
Maganganunsu sake hargitsa Malikat Bushirat suke da tunzurata. Tuni jin zafin Malikat Haseenat da tsanar Daneen Ammarah ya sake bunƙasa a ranta. Dama kullum Jasrah cikin munana Daneen Ammarah ɗin take a wajenta yanzu bisa huɗubar Miran Arshaan, dan tafi kawo mata zancen duk motsinsu a masarautar fiye da kowa, musamman daya kasance ra'ayinsu ya babanta da nasu akan hukunta Iffah. Yanda take sake kumbura jira suke kawai suji tace wani abu, amma kasancewar ta mace mai bahagon hali dama fahimta ko uffan da suke so bata tofa ba, sai cika take dai tana batsewarta ita ɗaya. Duk yanda suka cigaba da fanfatan kuma batace ɗin ba har lokacin samun damar ganin Tajwar Eshaan yay a gareta, dan tunda abin ya faru suma ɗin basu samu ganinsa ba kasancewar akwai doka mai haɗe da babban tsaro akan ganin nasa ga duk wanda ya kwana ya tashi a daular ta ruman, su kansu bisa tsayawar Malikat Bushirat ɗinne da itama sau ɗaya take da hurumin ganinsa a rana zasu ganshi yau ɗin.
Duk wani motsi da shiga da fitar jama'a a ƙarƙashin saka idon masu tsaron sashen yake a yanzun. Tako ina ka waiga cctv camaras ne. Su kansu ma'aikatan cikin sanya ido suke a kowane motsin tsakaninsu dan a yanzu kowa bai yarda da kowa ba ake. Sun sami tarba daga ƙwararren likitansa daya kasa ya tsare, yana hakane kuma bisa umarnin Malikat Bushirat ɗin. Cikin girmamawa ya gaidasu, batare da damuwa da yanda suka amsa masa cike da isa da ƙasaita ba ya jagorancesu zuwa ɗakin da aka warewa Tajwar Eshaan ɗin domin jiyya. Ɗakine tamkar asibiti, dan komai zaka samesa na aiki ingantattu da kowace ƙasa zata iya alfahari da shi. Dan ƙasar ruman na ɗaya daga cikin ƙasashe masu ƙwararrun likitoci da duniya ke alfahari da su tako wane fanni. Hakan yasa hatta shi kansa Shahan-shan dan yana ciwo bai ƙetare ƙasar haihuwarsa, kai sai ma dai su azo tasu ƙasar neman lafiyar saboda ingancin su....
Zaune yake a gadon marasa lafiyar bayansa jingine da tausasan filo da jikin gado da aka ɗago, duk da ya ɗanyi rama ƙyawun haibarsa da kwarjini na manne da cikar kamalar fuskarsa. Yayi fayau da shi da ƙara hasken daya bayyana bakin kwantacciyar sumar kansa data kumatunsa zuwa haɓa, light blue ɗin kayan jiyyar da suma suka ƙara fitar hasken fatar tasa tar-tar ga mai kallo sun masa ƙyau kamar ya saka ne domin ado. Sai manyan idanunsa da har yanzu fatarsu ke a ɗan kumbure alamar dai yana cikin halin jinya. Duk da jin an shigo bai motsa ba idanunsa nakan lap-top ɗin da yake sarrafawa cike da nutsuwa da ƙasaita.
Daga Miran Arshaan har Miran Jasim sukai turus alamar mamaki, dan sam zukatansu basu ayyana musu samunsa a haka ba musamman yanda likitansa yaƙi cewa komai game da zungurar da ƴan jarida ke masa akan son sanin halin da Tajwar Eshaan ɗin yake a yanzu. Saboda tun washe garin da suka tattauna da ƴan jarida basu sake cewa komai ba akan yanayin jikin nasa. Malikat Bushirat da hankalinta gaba ɗaya ke akan gudan jinin nata ta ƙarasa garesa fuskarta ƙawace da murmushi. Sai da taja kujera ta zauna a gefensa kaɗan ya ɗan ɗago saboda shigar ƙamshin turarenta cikin hancinsa.....✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
Leave a Comment