Daudar Gora Book 2 page 7


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (07)




........Kwanaki biyu kenan ana jiran tsammanin farfaɗowarta amma shiru kake ji, tun likitocin na iya controlling ruɗanin su Daneen Ammarah su ma har karayarsu ta fara bayyana. Dukkan wasu salon dabaru irin nasu na ƙwararrun likitoci sunyi amma babu wani canji tattare da Iffah duk da bincikensu na baɗini ya tabbatar musu nasara. Zuwa dare da ke neman ƙulle adadin cikon

kwanaki na uku ruɗanin likitocin ya sake bayyana da shi kansa uban ginsamin duk da basarwar tasa a yau dai sai da ya magantu. Dan cikin tashin hankali lokacin da Daneen Ammarah ta ziyarcesa take sanar masa har da kukanta, saboda ita a nata tunanin ma yanzu ko bai ma san a halin da Iffah ke ciki ba ne dai shiyyasa baiyi mata magana a kanta ba, itama kuma bata masa ba. Shiru kamar bazai tanka ba duk da hawayen da take faman sharewa na tsikarar zuciyarsa. 

      “Calm dawn Mamy”.

  Ya faɗa cikin sanyinsa da ƙyar kai kacema ba daga bakinsa kalmomin uku suka fita ba.

    Daneen Ammarah da ke sharar hawaye ta shiga girgiza kanta kukan na sake ƙwace mata, “Abni ta ina hankali zai kwanta da wannan yanayin, ina tausayin yarinyar nan matuƙa. Ina tsoron wani ya sake samun damar cuta mata ta hanyar yahudawan nan da bamu da tabbacin riƙe amanarmu da ke hannunsu. Tana da ƙyawawan halaye ɓoyayyu da sai mai lura da nutsuwar fuskantar ta zai iya ganinsu a bayyane. Ita ɗin tamkar lu'u-lu'u ce a cikin zinare, Abni bana so mu rasata a gaɓar da ta cancanci a kalla a nuna tamkar jinjirin wata da kowa burinsa shine ganinsa. Bana son wasu suyi amfani da wannan damar wajen salwantar mana da ita a wannan gaɓar da idanunmu ba zasu kasance kanta na tsawon kowanne daƙiƙa ba....”

      Kansa ya ɗan kauda gefe kaɗan tare da lumshe idanunsa da wani irin salon ƙasaita irin na gawurtattun sarakunan da jinin mulki ke kaikawo a jininsu. A zahiri kam babu alamar wani yanayi a fuskarsa da zai iya bada wata ƙofar da wani zai iya fahimtar baɗininsa, hakama fuskarsa bata canja da ga yanda take ba. Babu alamar zai ce kamar yanda Daneen Ammarah tafi buƙata da ga garesa har tsahon wasu mintuna da ta gama fidda rai....

      “Mamy bana son kuka”.

   Ya sake faɗa a fisge a yanayin motsa pink lips ɗinsa kaɗan tare da dai-daita buɗe lumsassun idanunsa a kanta yana mai riƙo yatsun hannunta uku na tsakkiya kasancewar tana zaune ne a kujerar gaban gadon jiyyar tasa gab. Kai Daneen Ammarah ta jinjina masa cike da rauni tana ƙarasa share hawayenta. Yanada abin faɗa fiye da wanda ya faɗa a bakinsa amma furtawarce mafi girman aiki a garesa. Sai kawai ya zaɓi ɗan yin luuu da idanunsa tamkar zai lumshe sai kuma ya buɗe tare da motsa kumatunsa kaɗan alamar murmushi. Duk da a iyakar lips ɗinsa ya tsaya hakan bai hana Daneen Ammarah maida masa murtani ba cike da jin ƙaunarsa matsayinsa na ɗan ɗan uwanta mafi soyuwa a ranta kuma shugabanta.

         Ƙwayoyin idanunsa ya juya ga Doctor da ke daga gefe, tazbihi kawai yake ma UBANGIJI da girmama jini irin na masu mulki da ƙasaitar Shahan-shan ɗin na su, har zuciyarsa na raya masa anya kuwa akwai wani sarki mai mulki da ƙasaitarsa zata iya kamo ƙafar ta Shahan-shan ɗin nasu Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed?. Rashin mai tayasa ya sashi haɗiye tarin gulmar dake ran nasa ya saci kallonsa ta ƙasan ido, sai akai sa'a dai-dai saukar idon Tajwar Eshaan ɗin a kansa. Da sauri ya maida nasa ya rissinar yana mai jin kaifi da tasirin na Shahan-shan ɗin a kansa. 

     “ALLAH ya ƙara lafiya da tsohon rai mai albarka ko ana buƙatar wani abu ne?”. 

    Ya faɗa cikin rawar harshe da kaifafan idanun Tajwar Eshaan suka haddasa masa. Kallon nasa ya cigaba da yi har na wasu tsahon sakanni da suka kusa ƙulla mintuna biyu kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya faɗi abinda ya ke ta juyawa a ransa tun ɗazun.

          “Zata iya kasancewa tare da mu anan?”.

     Cikin gyaɗa kai da sake risinar da shi Doctor Afif yay saurin faɗin, “Idan hakan shine buƙatar adalin sarki shugaban sarakunan ƙasar ruman da al'ummar cikinta ya tabbata abu mafi sauƙin zartarwa a bisa umarninsa”.

         Kansa kawai ya ɗauke ba tare da ya sake magana ba har doctor ya fice. Daneen Ammarah da fuskarta ke faɗaɗa da murmushi ta buɗe baki zatai magana, sai hakan yay dai-dai da ɗagowarsa gareta, har cikin rai yaji daɗin ganin murmushin a fuskarta, amma bazaka taɓa gane hakan a tashi fuskarba. Ya dai ɗan sake ƙasa-ƙasa da idanunsa masu yalwar cikar gashi da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta...

      “Kinyi farin ciki?”.

   “Sosai sosai kuwa sweetheart. ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya cigaba da tsare min kai ga duk wani abin ƙi. Ya yalwata zuciyarka da imanin da baya yankewa da tsoron ALLAH. ALLAH ya ƙara maka lafiya adalin shugabanmu abin alfaharin ƙasar ruman da al'ummar cikinta....”

        “Mammyy!”.

    Ya faɗa da wani irin sanyi-sanyi da ke son bayyana shagwaɓarsa a fili duk da fuskarsa ta shanye komai ta ɓoye. Karan farko Daneen Ammarah ta saki ƴar siririyar dariya dan ganin Baby Eshaan ɗin ta na baya a zahiri. (Su baby Eshaan anji jiki😜🏃)...


       ★Cikin ƙankanin lokaci aka cika umarninsa ta hanyar saka gado a ɗakin dake jikin katafaren ɗakin jiyyar tasa da gilashi kawai ya rabasu da nashin da ya kasance na musamman a sashe na musamman tare da dukkanin kayan aikin kula da duk motsin mai jiyya da abinda irin tata jiyyar take buƙata. Yana zaune a irin zaman da yafi yi a gadon jiyyar tasa ƙafafu a miƙe an rufesu da farin lallausan duvet har zuwa ƙugunsa, bayansa jingine da filon daya zauna dai-dai yanda ake buƙatarsa da taimakon ɗaga gadon da akai irin na mai jiyya. Duk da yanayi na mai jiyya da fuskarsa ta nuna tana nan tar-tar da ita da hasken nan nasa mai ɗaukar ido kamar madara, hakama kwantaccen gashin daya zagaye fuskarsa baƙi siɗik na kwance a fuskar kai kace wani hamshaƙin gyara yake samu. Duk da kasancewarsa a asibiti mayataccen ƙamshinsa da nasa ne shi kaɗai babu wani mahaluki mai irinsa ya gama manne ɗakin da duk wani abu da ake sarrafawa. Alkur'ani ne a hannunsa yana karatu dan haka bai ko motsa ba har aka kammala gyara gadon da za'a ajiye Iffah itama aka gungurota a gado. Da taimakon likitoci biyu mata aka ɗagata daga gadon da suka turota suka maidata a gadon da aka kafa. Sharɓan take kwance idanu a rufe, ƙyaƙyƙyawar fuskarta ma'abociyar tsiwa da rashin barin sai ta kwana tayi wani fayau. Ta rame ga idon duk wanda ya santa duk da bata cikin hayyacinta, damma bargon da aka lulluɓeta da shi ya ɓoye ramar da tayi ta jiki. Har suka kammala komai suka fice bai motsa idanunsa da ga kan Alkur'anin ba, karatunsa yake a nutse cikin zuciya da tattara dukan hankalinsa kacokan.

     Sai da ya kai inda yake buƙatar kaiwar sannan ya dakata yana mai lumshe idanunsa da sakin jerarrun ajiyar zuciya, dan a duk sanda ya kusanci Alkur'ani ta hanyar karantasa ya kanjisa cikin wata tarin nutsuwa da mulki ko dukiya ko wata ɗaukakar duniya bata bama ɗan adam. Yakan shagaltu da wani sirri da mai karanta Alkur'ani ne kawai ke iya samunsa a duniya. Sannan dukan damuwa da nauyin zuciyarsa kan kwaranye ya dinga jinsa tamkar wani sabon mutum sabuwar haihuwa. Bayan jan tsahon mintinan da suka sake tabbatar da gamsuwar nutsuwar da gangar jikinsa da zuciyarsa ke buƙata ya sake sauke ajiyar zuciya da buɗe lumsassun idanun nasa inda zuciyarsa ke fisgarsa da umarnin da bazai iya bijirewa ba. Duk da gilashin da ya raba sun tsaf yake iya hangota kwance samɓal, illahirin jikinta da zahirinsa ke a bayyane zagaye da na'urori kala-kala da suka kasance sirrin aikin likitoci. Idanun ya sake lumshewa ya buɗe akan fuskarta dake fayau sai hasken data ƙara mai tsananin ɗaukar idon mai kallo. Tabbas akwai abin faɗa a lips ɗinsa, sai dai ƙasaita da ƙarfin jinin iko mai yawo a jijiyoyin jikinsa ya jagorancesa ga haɗiyesu kawai dan barin kaza cikin gashinta kamar yafi alkairi ga mai kiyo.


    ★.... ★★.... ★.....


       Tun isowar labarin abinda ya faru da Iffah a wancan daren take jin ranta fes, sai dai zuciyarta na son sanin wanda ya aikata koma miye dan ta tabbatar masoyinsu ne. Cikin zumuɗi tai yunƙurin kiran number ƴar uwarta domin ta sanar mata amma ta gagara samunta. Hakan bai mata daɗi ba, amma dai bata damu sosai ba dan tasan itama komai zaije gareta. Da wannan farin cikin ta kwana a wannan ranar har zuwa jiya da Iffah bata dawo hayyacinta ba.


      A yanzu kam cikin harzuƙa da ɓacin rai take neman Malikat Bushirat ɗin dalilin labarin sake zuwan Daneen Ammarah sashen Tajwar Eshaan a yau, amma babu alamar zata sameta, tana a cikin wannan ɓacin ran labarin maida Iffah sashen Tajwar Eshaan ya sake riskarta. Cikin tashin hankali ta wancakalar da wayar tayo waje, batare da jiran driver ba ta nufi sashen Malikat Bushirat ɗin..


       Hadima Banou dake tafe a ɗan gaggauce dan cika umarnin aiken da Malikat Haseenat tai mata tabi Jasrah da ke fitowa a mota rai ɓace da kallo. A hankali ta lashe laɓɓanta tana mai haɗiyar yawu. Ta jima tana kawaici akan cikin nan na Jasrah saboda shakkar Iffah, amma a yau kam ga dama ta samu. Sake haɗiye tsinkakken yawunta tayi tana gyara tsaiwa. Gabb sukai karo da Jasrah da alamu suka nuna idonta rufe suke da ɓacin rai, itako Hadima Banou duk da tayi ne ta biyu sai ta zube ƙasa cikin rawar jiki tana neman afuwa da rantsuwar bata lura da tahowarta ba har da ƙoƙarin dafa ƙafafun ta, Sake ɓaci ran Jasrah yayi, cikin rufewar idon ta ɗaga hannu ta sauke mata lafiyayyen marin da ya saka sauran hadiman dake ɗan kai kawo shiga razani. Maruwa dai kam Hadima Banou ta maru, dan har sai da tayi ƴar a dunguren da duk wanda ke a wajen yaji tausayinta. Amma a gareta hakan ma nasara ce dan ta samu abinda take so. Fuuu Jasrah ta tsallaketa ta wuce zuwa cikin sashen Malikat Bushirat rai a ɓacin, sai dai cikin girmamawa hadiman ƴar uwar tata suka sanar mata saƙon data bari na bata buƙatar ganin kowa. Watsa musu mummunan kallo tai taja tsaki da shigewarta.........✍️







   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.