Gidan Aro 3

 

 *03*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*


Ya d’auki mintoci yana tsaye kansu kafin ya duk’a a hankali ya zauna gefen majinyaciyar, yai amfani da hannunsa guda ya dafa matar dake duk’e tana sharb’an kuka “Hajara kukan nan ya isa haka, shi majinyaci ba kuka yake buk’ata daga wajenmu ba.. Abinda yafi buk’ata shine addu’o’inmu.. Kiyi hak’uri ki daina kukan nan kinji..”


Ta d’ago fuskarta da tuni hawaye ya wanke ta janyo tissue paper tana share majinan da yazo hancinta alamun taci kuka.

“Daddy gaba d’aya hankalina ya gaza kwanciya, ace ko yaushe ahalin nan cikin tashin hankali muke.. Babu k’asar da ba’a fita da Nuratu ba amma jikinta yak’i dad’i kullum ciwon nata ma kaman k’ara gaba yake.. An gama Bikin SAFEENAH da MU’AZZAM Ko tarewa basuyi ba wani tashin hankalin ya kunno aka tsinci gawan Ikram..” Ta kuma saka hannu tana share hawayen dake mak’ale cikin idanunta, a hankali takai hannunta ta dafa saman na majinyaciyar, cikin rawar murya take furta “Poor Nuratu, bata San da labarin mutuwar d’iyarta ba.. I’m sure duk randa ta farka daga wannan jinyar nata ta tadda wannan mummunan labarin zata shiga tashin hankali ne maras misaltuwa.. Na kasa daina tunani, mai Ikram tayima wannan mutumin ya kasheta , sannan Maiyasa shima ya kashe kansa.. Da ace shi D’an Garkuwa da mutane ne da ya nemi Ransom.. Ikram yarinyar kirki ce mai tsananin kamun Kai balle ace biye biyen maza take.. Ko shakka babu mutumin nan saceta yayi...Bazan tab’a mance rawar data taka a rayuwar D’amu Musaddiq ba.. Ikram Ta zamto tamkar wata fitila data haska rayuwar Musaddiq, bani mance lokacin da ya dawo daga k’asar England  bai dawo da takardan komai ba.. Baiyi karatun ba Sai yawo da abokan banza.. Bani mancewa har kusan koranshi kayi a gidan nan.. Amma Ikram da Mu’azzam basu cire rai akanshi ba.. Mu’azzam ya shawo kanka ka yafewa Musaddiq, sannan Ita kuma Ikram ta taimakawa Musaddiq wajen ganin rayuwarsa ta inganta.... And now that she’s gone.. I don’t know what’s going to happen to our son..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..


Alhaji Marwan Gamji ma hawayen da ya kasa rik’ewa ne ya sauk’o masa yana k’ok’arin dannewa..Ya rungume matarsa yana fad’in “Ya isa Hajara.. Allah yana nan da sannu zai daidaita mana al’amran ahalinmu kinji Ko.. Everything will go back to how it was before kinji koh..”


Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Ta yaya Al’amara zasu koma kaman yanda suke da bayan babu Ikram a halin yanzu, Ikram ta tafi yanda bazata sake dawowa ba. Al’amara bazasu kuma kasancewa kaman da ba.. Ikram Fitila ce a cikin gidan nan, kowa tasan yanda zata zauna dashi.. Na shak’u da yarinyar nan fiyeda yanda na shak’u da Karimatu da Meema, kusan kullum tare muke yini nida ita wajen jinyar mahaifiyarta.. I saw how dedicated she was to her ailing mother.. Yarinyar kirki wacce ko wace uwa zatayi fatan samun irinta.. Bata tab’a banbanceni da mahaifiyarta ba.. Ikram rashinta zai bar gib’i Babba a gidan nan...” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..


Hannu yasa yana mutsuke gajeren hawayen da ya mak’ale masa, lokaci guda yake furta “Wanda duk yayi ma Ikram wannan abun shine aiki yake gabansa domin kuwa itakam Ta sami shaida.. Sannan ita duniya dama takenta kenan GIDAN ARO, dik yanda ka kaiga sonta Ko k’inta wataran dole ka barta.. Yi k’ok’ari ka tanadi guziri mai kyau a GIDAN ARO domin ka inganta gidanka na lahira wacce itace tabbatacciyar GIDA...”


Mommy ta d’an dubesa kafin tace “Wai kaima baka yarda wannan mutumin da aka tsinci gawarsu tare shi ya kasheta ba.?”


D’an jan numfashi kad’an Daddy yayi yace “To be honest, I don’t know what to believe... Maiyasa mutumin nan zai kashe Ikram sannan ya kashe kansa..?”


Mommy tace “Maybe baiso a kamasa dan yasan dole a kamasa shiyasa da yayi garkuwa da Ita ya kasheta sannan ya kashe kansa..”


Daddy yai shiru kaman mai nazari sai kuma ya d’an girgiza kai yace “Still it doesn’t make any sense.. Maiyasa zai kashe kansa dan tsoron kar ya tafi gidan Yari..?”


Mommy tai shiru tana nazari itama..


Fasali ya d’anyi kafin yaci gaba da fad’in “Inada tabbacin Muazzam bazai huta ba har Sai ya zak’ulo su Wanene Keda alhakin mutuwar Ikram.. Sannan Ina fata kafin zuwa wannan lokaci Nuratu ta sami lafiya domin taga yanda za’a hukunta ko su wanene suka aikata ma d’iyarta haka..” 


Wani irin bugawa k’irjin Hajiya Hajara yai lokaci guda.. Ta d’ago tana duban mijin nata Wanda da gani har cikin zuciyarsa yayi maganar.. A hankali ta shiga jinjina kai tana furta “Wannan gaskiya ne.. Ko su wanene suka aikata ma Ikram haka sun cancanci a gurfanar dasu gaban shari’a..”


Ta d’an nusa kad’an kafin tace “Yau ‘yan Fufore Sun koma gidan Sai ya dad’a mana girma da shiru..”


Jin baice komai ba ya sanyata kuma gyara zama tace “Jiya muke magana da Shema’u akan ciwon Nuratu, take ce min har yanzu Aunty Nurah dai shiru jiki yak’i dad’i nace mata wllhi anyi magani k’asashe da dama amma Allah bai nufa an dace ba.. Toh shine take ce min an gwada na gida.? Nace mata Ai baka faye yarda da maganin gidan nan ba.. Tace min akwai wata mata datayi shigen irin ciwonta, maganin wata bafulatana aka gwada dake wata Ruga cen gaba da Fufore.. Shine take ce min Ko za’a gwada nace mata gaskiya saidai idan na maka magana naji abinda zakace.. Magani kuma dace ne ba’a San yanda maganinta yake ba..” Ta k’arashe tana mai tsaresa da idanu cikeda kulawa..


Knocking d’in da akai a k’ofar d’akin ne  ya katse masu tattaunawar tasu, Mommy Ta d’an janye jiki daga cikin nasa, tai k’ok’arin saita kanta kafin ta bada izinin shigowa.. 


Wata budurwar yarinya ce da bazata gaza shekaru 16 ba ta turo k’ofar ta shigo.. 


Yanayin da suka ganta ciki ya sanyasu zuba mata idanu suna jiran suji yau kuma menene ya faru a gidan


“Kiki lafiya..?” Mahaifiyar tata ta tambaya 


Alhaji Marwan Gamji kaw cewa yai “Come here baby.. Zo ki fad’a min mai ya faru..”


Cikin sanyi ta K’araso ga iyayen nata.. Ta dubi wannan ta dubi wannan..


Duban mahaifiyar tata tai tace “Mommy it’s Addah FEENAH.. Tace ita gidanta da Ya Mu’azzam zata tafi tinda ‘yan karb’an gaisuwar Ikram sun watse, ‘Yan Fufore sun koma itama zata tafi nata gidan..”


Ta juyo tana duban mahaifin nata “Daddy you need to stop her, nida Meema mun ce mata Bride bata Kai kanta gidan Groom shine tace zataje ta sami Inne ta kaita tinda ita bata koma Fufore ba..”


Mik’ewa yayi yana fad’in “Ina Safeenan take..?”


“She’s in her room, probably parking her stuff..” Kiki ta fad’i tana matsawa kusan mahaifiyarta dan bama mahaifin nata hanya..

Cikin sauri yasa kai ya fice..


Kiki ta dawo da dubantaga mahafiyarta tana yatsina fuska tana duban Aunty Nurah dake kwance..


“Wai Ke Mommy bazaki daina damuwa akan matar nan bane.. Matar nan fah kishiyarki ce amma ko asalin danginta iyakacin abinda zasu mata kenan.. Ni ban tab’a ganin kishiya irinki ba Mommy wacce take ma kishiyarta jinya. Ko a sch idan ina labarin Mommy ta ita take ma step mom d’ita jinya mamaki suke sha sai suce Lallai Ke ta daban ce..” Tai fasali tana mai zama gefen mahaifiyar tata kafin taci gaba da fad’in “And Mommy tun tasowarmu a haka muke ganin matar nan, ciwonta bai gaba bai baya Ke kuma sai faman wahala kike da ita dik tulun maids d’in dake gidan nan basu isa jinyar nata ba sai kin saka hannu..”


Murmusawa  Hajia Hajara tai tana duban d’iyar tata “Kareema kenan, yaro dai yaro ne.. Bazaki fahimci komai ba yanzu sai nan gaba.. Mamarki kirki ne da ita bazata iya ganin wasu suna shan wahala ta k’yalesu cikin wahala ba.. Nuratu da kike gani ba kishiyata bace kawai, tamkar ‘yaruwa haka na d’auketa domin kuwa idan baki mance ba a baya Yayan Babanki mai rasuwa take aure.. Kinga nida Ita mun jima da sanin juna tun kafin Daddynki ya aureta..”


Kiki Ta d’an turo baki tace “Amma Mommy Maiyasa da nata mijin ya mutu ta aure miki naki mijin..? Mommy nan gidanki ne bai kamata ta aure miki miji ba..”


Murmusawa Mommy ta kumayi kafin tace “Nurah batada kowa a k’asar nan, batada dangi a nan.. Mijinta ne kad’ai danginta sai kuma yaranta, shiyasa koda mijinta ya mutu nawa mijin ya aureta..”


Shiru Kiki tai tana sauraren mahaifiyar nata kafin ta tab’e baki tace “Even so Mommy, she shouldn’t have married your own husband.. Ita ta aure miki miji ga kuma d’anta Ya Mu’azzam ya aure Addah Safeenah.. Um nidai duk bana son irin wannan had’e had’en kusancin tai yawa... Shikenan namu family d’in sun k’are a cycle d’aya..Ni gwara ma da Addah Ikram Ta mutu nasan itama da yanzu an soma maganan nata auren da Ya Musaddiq.”


“Ke Karimatu..!” Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa wanda ya sanyata zabura babu shiri..


Mommy taci gaba da fad’in “Kina jina.. Koda wasa koda wasan wasa kar na kuskura na kuma jin wannan kalma ya fito daga bakinki balle har kiyi gangancin furtata cikin gidan nan kinji koh..!” Ta k’arashe tana mai nunata da ‘yar yatsa cikin tsananin b’acin rai..


Kiki baki a ture ta mik’e tana fad’in “Fine Mommy, kema kinfi son wannan matar da yaranta sama damu yaranki.. Kaman yanda Daddy yake nuna yafi sonsu.. This is not something new a gidan nan.. Dama Daddy ya saba nuna yafi sonsu tun kafin Ikram ta mutu..”


“Kimin shiru da maganar Ikram nace and kindly leave this room kafin na b’ata miki rai..”


Fuu ta fice fuska a kumbure kaman zata kurma ihu..


Tana ficewa Mommy ta dafe k’irjinta tana Sauk’e ajiyan zuciya.. Ta maidoda dubanta ga Nuratu da fuskarta ke duban wani b’angaren.. A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tasa kai ta fice...


Tana fitowa d’akin Safeenah ta nufa yanda ta tadda Safeenar duk’e saman carpet tana fuskantar Daddy dake zaune bakin gadonta,  kanta a k’asa da alama hawaye take..


“Daddy I’m sorry.. Kawai inaso na kasance da mijina ne.. Please understand me..” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..


Cikin kwantar da hankali yaci gaba da fad’in “Na fahimceki Safeenah.. But don’t you think yayi sauri ayiwa Mu’azzam maganar tariya yanzu..I mean, he recently lost his sister.. And he’s looking into the matter right now...Kuma  Kema ‘yaruwarki ce..”


Cikin muryar kuka Safeenah Ke fad’in “Daddy gani nake kaman Mu’azzam kufce min zaiyi.. Daddy kaga da k’yar ya yarda akayi aurenmu sabida jinyar Aunty Nurah toh mai kuma zai faru yanzu da Ikram ta rasu.. K’ila yace ya fasa auren ma gaba d’aya Daddy..” Ta k’arashe wani kukan na taso mata..


Cikeda tausayin d’iyar tasa yake dubanta dan yasan yanda take tsananin k’aunar Mu’azzam.. 


Hannunsa ya mik’o ya kamo nata kafin ya soma magana cikin kwantar da hankali “Safeenah an riga anyi aurenku da Mu’azzam kinji.. Shid’in mijinki ne, babu abinda zai rabaku ki kwantar da hankalinki kinji koh..”


Izuwa lokacin sosai take kuka tana fad’in “Daddy you don’t understand.. Daddy Mu’azzam ba kaman kowa bane. Bata soyayya yake ba balle aure, baida lokacinsu Daddy I’m sure of it, yafi bada mahimmanci ga jinyar mahaifiyarsa da kuma aikinsa na d’ansanda.. Ba don Inne ta dage sai anyi aurenmu ba nasan k’ila da ba’ayi ba.. And yanzu da ya sami dalilin da zaice ya fasa.. I know him zai iya cewa ya fasa auren.. Daddy please kar ka bari aurenmu da Mu’azzam ya sami matsala..” Yanda take maganar gaba d’aya tamkar mai son fad’in wani abu duk ta daburce tama rasa mai take fad’i.. Shi kansa Daddyn da mamaki ya soma dubanta..


Cikin sauri Hajiya Hajara ta k’arasa ta rungume Safeenah dake sharb’an kuka tana sunbatu..


Shigowar Meema a birkice tana fad’in “Mommy..! Mommy kizo ga cen Ya Mu’azzam ya dawo da Ya Musaddiq.. And... he looks high..” 


Wani irin zafi Alhaji Marwan yaji zuciyarsa na masa, take ya shiga  karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Yai saurin ficewa daga d’akin cikin tsananin damuwa...


Mommy Ta dubi Meema dake tsaye daga bakin k’ofa tana duban yanda Safeenah ke cazgan kuka ta bud’e murya tace “Fita ki bamu waje..”


Turo baki gaba Meema tai cikeda haushi kafin Ta juya tai ficewarta tana k’walla kira ma k’anwarta Kiki..


Cikin sauri Mommy ta isa rufe k’ofar had’ida danna mata lock..


Ta juyo tana duban Safeenah dake tak’ure waje guda tana cazgan kuka tana fad’in “I can’t lose him.. I love him so much.. No.. No I can’t lose him..”


Jijjiga Safeenah take tana fad’in “Safeenatu Safeenah..Ke ki natsu nace..!”


Safeenah kaw kaman cewa ake ta k’ara..


Mari maiji da lafiya Mommy ta d’auketa dashi Wanda ya sanyata yin tsit kaman an d’auke ruwa..


Tana sakin huci take duban Safeenar..


“Kina jina ki fad’a min mai kike son fad’awa mahaifinki.. Talk to me now..!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya tana mai firfito da idanu waje..


Safeenah dake rik’eda k’uncinta wajen da Mommy ta mareta bata daina kukan ba take fad’in “Mommy idan Mu’azzam ya sani he will hate him.. Zai tsaneni Mommy..  Or he might even send me to jail..”


Izuwa lokacin Hajiya Hajara ta fara daina gane mai Safeenah ke fad’i.. Cikin daburcewa ta shiga bud’e hannuna tana fad’in “Safeenah.. Ke Feenah mai kike fad’i.. Ban fahimceki ba..”


Safeenah na hawaye take fad’in “Mommy I feel guilty.. I feel responsible..”


Girgiza kai Mommy Ta kumayi tace “Har yanzu ban fahimceki ba Safeenah.. You feel responsible for what.?”


“For Ikram’s death Mommy..!” Ta fad’i mata cikin tsananin rawar murya....


Izuwa lokacin bibbiyu Mommy Ke gani.. Cikin sauri ta janyo hannun Safeenah suka zauna saman gado


Wannan karon cikin tsananin sanyin murya take magana 


“Safeenah.. Maiyasa kikace haka.. You did not kill Ikram, did you.?”


Cikin sauri Safeenah ta girgiza kai alamun a’a tana fad’in “No Mommy I didn’t..”


“Then how are you responsible..?”


Kallon mahaifiyar tata tai kafin tasa bayan hannu ta goge hawayenta. A hankali Ta soma fad’in “Mommy Ikram tana zargin ban daina aikata wasu d’abi’u da nake aikatawa a baya ba, Ta d’auki wayata ta karance Adress d’in a lokacin shagulgulan bikina..” Kuka sosai yazo ma Safeenah Mommy jikina sanyaye take dubanta,


Tai k’ok’arin saita kanta kad’an kafin taci gaba da fad’in “But Mommy abinda na sani shine I was to meet up with a client wllhi wllhi Mommy bansan Criminal bane... Bansan makashi bane..”


Girgiza kai Mommy tai tana fad’in “Ni duk nan wani fahimceki ba Safeenah “Toh Wai kan wani dalili Ikram zata zargeki..?” 


Saida ta share hawayen da ya kuma gangaro mata kafin taci gaba da fad’in 


“Kin tuna lokacin  da aka kaita University of Salford ina ajin k’arshe ne Ita kuma tana year one d’inta Musaddiq na aji uku.. Toh gida d’aya muka zauna nida Ikram, Mommy a nan Ikram tasan duk wasu abubuwa marassa kyau da nakeyi, Ina kawo maza su kwana a gidan..” Kuka ya sanyata katse maganar..


Mommy tace “Ina saurarenki Safeenah ..”


Safeenah ta goge hawayenta kafin taci gaba da fad’in “Ikram witnessed everything, akan idonta komai yake faruwa.. Muka sami matsala a lokacin tace zata fad’awa Daddy da Mu’azzam  duk abinda nakeyi.. Da k’yar na shawo kan Ikram nace mata friends d’Ina ne kawai and bama yin wani abu maras kyau.. Dukda haka Ikram bata yarda ba saida ta sanyani nai mata alk’awarin bazan sake yin abota da maza ba muddin Ina son kasancewa da Yayanta.. I promised her as she requested... And Mommy wllhi wllhi tin a Salford na daina bama Maza kaina..” 

Batakai aya ba Mommy Ta Kai mata mari tana hawaye take furta “Ashe duk tarbiyan dana baki kinje kin watsar a turai.. How could you..” Ta k’arashe tana mai kuma Kai mata mari..

Zata kuma Kai mata wani marin ne Safeenah tai saurin rik’e hannunta tana fad’in “What do you expect Mommy.. Kun tura budurwa k’asar waje.. K’asar da babu kowa nata.. Kun bata gida da ko wacce irin Gata.. Meye wannan budurwar bazatayi ba.. Mommy wannan kuskure ne da da yawan iyaye suke aikatawa.. Tura mace tayi karatu a k’asar da babu kowa nata ba birgewa bace Mommy.. Bance duka ba amma akasari lalacewa suke kafin su dawo.. Mommy ko a addini ma Babu kyau tura mace taje uwa duniya da sunan yin karatu ba tareda wani nata ba..”


Cikin kuka Mommy Ta katseta da fad’in “Ai an tura Musaddiq.. Kuma Musaddiq d’an uwanki ne..”


Cikin kuka itama tace “But kafin Musaddiq ya tafi Mommy I was all alone.. Har saida nayi shekaru biyu a UK kafin Musaddiq ya tafi.. Kuma Mommy Musaddiq shima nashi watsewar yake tareda ‘yanmatansa har saida Ikram ta taho Salford kafin ya rage wasu abubuwan da yakeyi sabida Ikram da nasihar da take masa... Mommy ki yarda akwai naku laifin daga ke har Daddy...”


Cikin kuka Mommy Ta katseta da fad’in “Ke ni Kimin shiru ba guntun wa’azi nace Kimin ba tinda kin riga kin gama watsewarki da mazan turawa a turai.. So nake ki fad’a min Ta yanda alhakin mutuwar Ikram ya rataya a wuyanki..”


Safeenah ta kuma k’unshe bakinta tana jin wani kukan na taso mata..

Daidai lokacin aka soma knocking..


Jin muryar mai k’wank’wasa k’ofar ya sanya Mommy da Safeenah ware idanu suna duban juna.. Cikin sauri Safeenah take k’ok’arin saita kanta Mommy na aika mata wane irin kallo.. Saitin kunnenta take rad’a mata “Kina jina..”

Safeenah tai saurin jinjina kai 


Mommy taci gaba da fad’in “Koda wasa kar giyan soyayya ya d’ibeki ki bud’e baki ki sanar da mijinki wani abu.. Ke bama shi kawai ko Daddy bazai sani ba, sannan babu wanda zai san wannan maganar.. Daga ni sai ke kin fahimta..?”


Nan ma saurin jinjina kai Safeenah tai kafin Mommy taci gaba da fad’in “Kisan yanda zakiyi ki b’oye wannan rawar jikin naki dan idan kika bari ya fahimci wani abu kashinki ya bushe Safeenah, Kinsan Wanene Mu’azzam kin fi kowa sanin zafin zuciyarsa.. Ba ke kad’aiba inaga har zuri’arki kaf Sai ya tura kurkuku muddin ya fahimci you’re somehow related to case d’in mutuwar ‘yaruwarsa..” Ta gyara tsayuwarta tana mai kuma yin k’asa da murya “ Kina jina..Zaki natsu kuma zaki nitsa kanki yanzu sannan kiyi abinda ya dace..” Ta k’arashe tana ware idanunta a fuskar Safeenar..


Cikin sauri Safeenah ke jinjina kai tana mai k’ok’arin saita bugun zuciyarta.. Lokaci guda ta koma kan Gado ta zauna tamkar marainiya...


Mommy ma ta saita kanta kafin ta dubi Safeenah tace “Nidake bamu gama magana ba, zaki sanar dani komai..” Tai maganar tana kad’a d’an yatsarta a Fuskar Safeenar..


Safeenah Ta lumshe idanunta tana jin sanda Mommy Ta isa ta bud’ewa Mu’azzam k’ofar..


Haka kurum yaji wani iri da yanayi da yaga Mommy ciki dikda k’ok’arin saita kanta da take.. Sai ya jingina hakan da iftila’in da ahalinsu ke fuskanta a d’an kwanakin..


Gaisawa sukai da Mommy kafin tace “Gwara daka k’araso.. Gata nan kowa yayi shiru ya daina kukan rashin Ikram amma ita bata daina ba.. Nayi nasihan nayi  lallashin duk tak’i dainawa nace k’ila sai kazo.”


Haka kurum yaji bai gamsu da abinda Mommy tace ba abinka da Detective dukda cewa tin a waje Meema ta sanar dashi Addah Feenah  nata kuka ta kulle kanta cikin d’aki, ya jinjina kai kad’an yace “Zan mata magana Mommy.. You can go now.. I think Musaddiq needs you..”


Mommy Ta jinjina kai kafin tace “Mu’azzam.. Thank you for bringing him home..”


Jinjina kai kurum yai ba tareda yace komai ba har Mommy Ta fice..


Cikin yanayin tafiyarsa yake takowa cikin d’akin, saida ya d’auki lokaci yana dubanta yanda ta tak’ure saman gado kanta kife saman gwiwa, a hankali yake takowa cikin d’akin.. Gefenta ya zauna har lokacin kanta na kife tana matsan hawaye..


Ya d’an fuzar huci yana shafe goshinsa kad’an, kana ganinsa kasan he must be completely stressed out.. Hannu yakai kaman zai tab’ata sai kuma ya janye hannun nasa yana mai d’an janye fuskarsa idanunsa a lumshe.. Jin alamun haka yasa Safeenah k’ara sautin kukanta..


Ya d’an rintse idanunsa kad’an kafin ya dad’a matsowa kusanta, hannayensa duka biyu yasa ya d’aura saman kafad’unta.. Kaman yace ta k’ara nan Ta kuma sake masa wani kukan..


D’an kauda kansa gefe yayi still yana rik’eda ita, kaman bazaice komai ba Sai kuma ya rungumota cikin jikinsa ga kukan nata dake k’aruwa “It’s okay Feenah.. Ya isa haka.. Ki daina kukan nan haka..” Yanda yake maganar tamkar wani d’an koyo sosai zai baka dariya..

Jin haka yasa Safeenah lafewa cikin k’irjinsa tana mai kuma sakin kuka.. Ba kukan tashin hankalin da take ciki takeyi ba.. A’a kukan Farin ciki da murna take yau Allah ya cika mata burinta Gata nan cikin jikin Mu’azzam d’inta kuma a matsayin matarsa.. Shid’in halaliyarta ne.. Cikin zuciyarta Ta furta _My Halaal_ .

Tina haka da tayi ya sanyata had’e hannunta ta rungumo bayansa sosai tana kuma kwantawa cikin jikinsa tana kuma sakin kuka...



No comments

Powered by Blogger.