Min Qalb 1-5


1

Bismillahir-rahamanir Raheem.


Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo ya zubar a babbar bolar bakin anguwar wadda za'a Kira da qaramar kasuwa sbd hargitsi da cunkushewar anguwar da manya da qananan kwatocinda suke cike taf da ruwa da ledoji tareda qananan abinci na wanke wanke dasuke biyowa,

Daukar biredin tayi tana kakkabewa tareda kaiwa bakinta daya gama bushewa yayi fari fat harya Fara yayyankewa alamar ko yawun bakinta sun gama bushewa ta gutsura kadan ta Dan tauna taji zai shiga 
Da sauri ta qarasa turasa cikin bakin tana taunawa da sauri jikinta na rawa tareda hanjinta dasuke qugin jin wani abu ya saukar musu bayan kwanaki dasuka Dan dauka a na'de.

Ganin wani almajiri yayo gurin Yana kallon biredin a yunwace Shima Dan ko gabansa baya kallo idonsa nakan biredin ko kyaftawa bayayi yasa tayi saurin miqewa tana qara tura biredin cikin bakinta da sauri sauri tana kallon almajirin karya iso gurinta Bata cinyeba ya kwace sbd wannan shine Abinda yake faruwa a bolar qwacewa daga marasa qarfi Wanda a duniyarma hakane duk me qarfi shike qwace Abinda yakeso gurin masashi,

Batada uwa batada uba,
Batasan kowa aduniyaba Wanda zata ce nata ne,
Ita aduniyarma gaba daya batasan komaiba face yawon bola da tsince tsince.

Almajirin na isowa gurinta yayi wuf da qarfi ya qwace biredin hannuwansa na rawa Shima yakai bakinsa yanaci da sauri sauri Yana hadiyewa ko taunawa bayayi sbd sauri yakai bakinsa.

Kallonsa takeyi tana hawaye tana lashe sauran Dan gari garin biredin dake hannunta tareda uwar dau'dar dake tafin hannuwan nata dasuka sauya kala sbd dau'da.

Tana kallo ya cinye biredin ya dago Yana kallon hannuwanta ko zaiga wani abin naci sbd yunwar dakeci hanjinsa yakai ko numfashi baya iyayi ko mushe yagani zai iya ci sbd qarfinsa daya gama qarewa gurin yawon bara.

Ganin yanawa hannuwanta kallon yunwa yasa ta juya ta tafiyarta zuwa tsakiyar bolar tana bincikawa ko zata Kuma samun wani abin.

Yarinyace qarama sosai Yar kimanin shekaru bakwai saidai yunwa da wahala Sunsa ta matse sosai kamar Yar shekaru shida,

Dau'da tasa fatarta takoma baqiqirin ko tantance asalin kalar fatarta ba'ayi 
Ga gashin kanta daya gama tsinkewa sbd dau'da da zamansa a bude.

Gangarawa tayi yafito cikin bolar tana qoqarin bude gwangwanin data samu cikin bolar fuskarta na nuna 'dokin son ganin me tasamo.

Bakin shagon alhajiyat me abincin bakin titin ta zauna daga can gefe inda ake Mata wanke wanke ta faki idanuwansu ta dauki wata matacciyar butar tsarkinsu ta Dora baki tafara kwankwadar ruwan da sauri sauri wani sanyin rahama na sauka cikin hanjinta ita batamasan wani abu qazantar ruwanba burinta dai su sauka a cikinta.

Fizge butar akayi da qarfi tareda jefarwa cikin masifa matar tasaka qafa ta tureta gefe tana cewa'"

Wannan yarinya wlh anyi muguwar mayya,
Yarinya saikace kafira ayita korarki Amma kullum saikin zo.

Kallon matar takeyi tanason yin kuka Amma Sam takasa sbd tunda ta taso batasan wani abu waishi so,qauna,kulawa ba ko gata bare tasan zafin rashinsu hartayi kuka.

Tunda tafara wayo daga ita sai kakarta kurma suke rayuwa a wani mataccen kangon shaguna wadda ita a wayonta batasan shin kakartace kokuma mahaifiyarta
Itadai tasan itace komanta gashi kurma ce bataji Bata iya mgn ga tsufa ahaka suke rayuwar Bara da yawon bola neman rubabben abincinda zasuci idan dare yayi sukoma shagunan dasuke kwana su kwanta duk da Basu kadai bane shagunan duk mabaratane da nakasashshi,

Koda iya tsohuwa tayi kwanaki kusan ashirin a kwance batada lfy tana gani tana kalla 'yarinyar ke fita yawon bola da bara tana ciyo abinci dame kyau da Mara kyau,
Wani lokacin ma idan ta ciyo Mara lafiya tana gani zatazo tayita amai da zawo Amma ahaka take sake fitarta tasake samowa Koda a bolar ne taci abinta,
Ciwo da yunwa da tausayin ganinsu ahaka yasa jikinta yin tsanani matuqa ahaka ta rasu batareda jamaa suna ankaraba ita Kuma batada wayon dazatasan meke faruwaba ahaka gawar tayi kwana biyu da yini take layin yafara daukar wani mugun wari wanda yasa sukasan akwai gawa.

ahaka kullum da daddare itakam take zuwa ta kwanta gefen gawar tayi kwanciyarta tayi bacci gari ya waye ta fita.

Koda aka gano gawar take suka Kira Yan sanda akazo aka bincika gawar suka tabbatarda rasuwa tayi ba wani alamar kasheta akayi suka kwashi gawar akai daji da ita acan aka binne a wata qaramar baqabarta.

Tundaga lokacin rayuwarta tasake gararewa sbd ankorosu daga waincan shagunan yanxu duk inda dare yamata acan take kwana saidai kasancewar shagon abincin alhajiyat na sabuwar anguwar data fado masu dafa Mata abinci anan suke kwana shago yasa itama ta fake anan bayan shagon take kwanciyarta tayi baccinta. 

Bayan qawace butarda matar tayi komawa tayi gefen shagon daga inda suke watso ruwa ta zauna tafara qoqarin bude gwangwanin Amma Bata iyaba takasa.

Kokuwa takeyi da gwangwanin tana saka farcenta tana budewa da qarfi Amma takasa sai jin tayi ankwace ta dago da sauri taga almajirin daya qwace Mata biredi ne da sauri ta miqe tana kallon gwangwanin hawaye na cikowa idonta tace"

Abuna ne kabani inaso"ta qarasa tana Kai hannu zata karba ya tureta ya juya da gudu Yana qoqarin budewa Shima.

Zaunawa tayi agurin tana hawaye daganan bacci yayi gaba da ita dama gashi yamma tafarayi.

Cikin bacci tasaki fitsafinta Wanda tsumman kayan jikinta suka shanyesa ko gangarowa beyiba.

Mangariba bayi ta farka tazo ta zauna gefen qofar shagon tana rarraba idanun samun Abinda zaa jeho waje.

Ahaka har akayi ishai qarfe Tara tayi Bata samu komaiba ta miqe tana Sosa kanta dake danqare da dau'da Takoma bayan shagon tayi kwanciyarta.

Gari ba wayewa ta miqe ta kama hanya neman Abinda zataci.


Yauma duk Abinda tasamu almajirin jiyane ya qwace Mata ya cinye Kuma duk inda tayi kusan Yana biyeda ita sbd ga dukkan alamu shi sabon zuwa ne kamar baisan ko inaba kamarma baisan ya ake hakurin yunwaba sbd shi komaima yasamu ci yakeyi gashidai Shima zasuzo sa'a daya danshima bazai wuce shekaru bakwai dinba.

Abun mamaki almajirin Nan saigashi gurinda take kwana Shima anan yake kwana idan gari ya waye tatafi duk inda tayi Yana biyeda ita.

Ganin haka yasa yanxu tana samun Abu take rabawa biyu tabasa Rabin tun bai qwaceba ya cinye.

Ahaka harsuka Saba sosai lokaci yaza sosai duk inda zasu tare suke zuwa harsuka samu wata roba a wata babbar bola da ita suke zuwa bara.

Yau Kam ranar babu wata sa'a acikinta sbd ko ruwan dazasu sakawa cikinsu Basu samuba duk inda sukace korarsu da hantararsu akeyi sbd bayan wari da zarnin fitsarin tareda tsamin dau'da babu Abinda sukeyi.

Kwanciya sukayi cikin bacci tafara jiyo sheshekar kukansa tayi saurin tashi zaune cikin tsoro ta kallesa tagansa zaune riqeda cikinsa.

USMAN?????? takira sunansa cikin sanyin maryar dake bayyanarda itama a galabaice take sbd yunwa.

Dagowa yayi ya kalleta da ido sharkaf da hawaye yace"

Amah cikina ciwo sosai.

Tashi tayi tareda kallonsa kafin ta juya tana cewa'"

Zansamo ruwa saimu sha.

Tana juyawa wasu manyan samari su biyu dake boye suka fito tareda toshe Masa baki suka dagasa cak suka wuce dashi suna zuwa motarsu suka bude da sauri suka jefasa da gudu suka bar gurin.


Cikin sanda ta Isa qofarsu alhajiyat ta dauko butarsu dake cikeda ruwa ta sidado ta dawo da sauri saidai tana zuwa taga babu usaman din cikin sauri ta ajiye butar tafara duddubasa koina tana Kiran sunansa.

Har kusan asuba Bata gansaba tadawo ta zauna shiru tareda qurawa robarsu ido,
Akaro na farko arayuwarta bayan iya tsohuwarta data samu wani arayuwarta Wanda taji ayau tanason karya tafi koina ya tsaya gurinta suyita yawon neman abinci atare,
Tasaba da usman sosai sbd a yanzu Koda Basu samu Abinda zasuciba sunada junansu damuwarsu kadance tunda suna debewa juna kewa.

Har gari ya waye Rana ta fito Bata gansaba tayi yawon duk inda suke zuwa bara tare Amma Bata gansaba ga yunwa ga gajiya ga qishirwa ga Rana haka ta dawo agajiye da daddare ta kwanta bayan Tasha ruwan butarsu alhajiyat.

Cikin bacci gaji motsin mutane tana bude ido taga wasu su biyu sunzo gefenta sun anjiye Usman din sun jiya da sauri sun tafiyarsu.

Da sauri ta tashi tana cewa''
Usman Ina kaje??

Bai motsaba sbd ko numfashi baya fitarwa
Ta juyoda fuskarsa tadan bubbuga tana sake Kiran sunansa har lokacin bai motsaba.

Ganin kamar bacci yakeyi yasa ta gyara Masa kwanciya tareda juyawa ta kwanta tanajin Dadi akaroro na farko a rayuwarta sbd usaman yadawo.

Koda gari yayi haske ta tashi har lokacin usman be tashiba ta dawo gabansa tana Kiran sunansa ya bude ido ya kalleta idanuwansa jawur jikinsa nata wani irin rawa atake taji tsoron ganinsa cikin yanayi da sauri tace' 
Usman menene? Kanajin yunwane haryanxu? Cikinka na ciwone haryanxu ma??

Ahankali ya nuna Mata duwawunsa Yana hawaye da dasasshiyar murya yace"

Sunmin wani abu anan zafi yakemin sosai''sai kawai ya fashe da wani irin kuka Yana dafe gurin sbd tsananin azabar dayasha agurin dasuka dannesa sukai amfani dashi.

Ganin irin kukan azabar daya keyi yasa itama tafashe da kukan ahankali musamman dataga jini a wandonsa tasan ciwone suka jimasa duk da basanma menene Abinda sukayiba.

Wasa wasa sai zazzabi ya rufe usaman sosai har jikinsa na wani irin mazari duk saita rude takamasa suka kutsa cikin kasuwa neman bara.

Suna shiga kasuwar taji wani me magani da lasifika Yana cewa'

Idan duwawunka ba ciwo baka iya miqewa bayan bahaya to kazo Muna mafaninka,
Idan kanajin fitsari baya fita sosai Shima kazo munada maganinka.

Da sauri taja hannun Usman dake tafiya a duduqe sbd ciwo da zazzabi sukazo gaban mutumin ta kalli maganinsa tana nunawa tace'"

Wannan zaka bawa Usman yaji ciwo a duwawu.

Kallonta me maganin yayi kafin ya kalli Usman da kyau Yana tauna goro da jajayen haqoransa ya washe baki tace'"

Ku kawo kudi' yana miqa musu hannu.

Kallon hannunsa sukayi kafin ta dago ta kallesa ta girgiza Kai alamar ita batamasan meyene ba.


Dari diyar ya fidda tareda nera dubu daya ya budesu ya nuna musu Yana cewa"

Kuje ku samo wannan ko wannan ku kawo nabaku magani yanasha zai warke.

Kallonsa tayi tana sake kallon kudin hannunsa kafin suka juya jikinsu a sanyaye sukabar kasuwar.

Kwana biyu jikin Usman babu wani sauqi gashi itama qarfinta yafara qarewa dole ta fakaici idon mutane da daddare tashiga shagon alhajiyat ta sato irin kudinda me magani ya nuna musu har guda uku.

Tana fitowa suka boye tunda safe suka shiga kasuwar neman me magani cikin saa suka Ganshi tabashi kudin duka tsabar zalinci saiya karbe duka dubu ukun yabasu canjin dari biyu tareda maganin Dan kanoma yafada musu su siya Koko susha dashi.

Kokon duka Darin biyu tasiya musu Usman yasha maganin ta shanye sauran kokon jikinta na rawa.

Dayake Shima Usman din harda yunwa dake cinsa yasa jikin tsananin 
Saigashi sun samu qarfin jiki bayan sun shanye kokon take suka kutsa kasuwa bara.

Da daddare yauma batada zabi bayan sake sato kudin 
Tunda safe suka sake siyan Koko yau harda qosai.

Sannu ahankali sata tashiga jikinsu 
Tun alhajiyat Bata ganewa ana Mata sata harta gane tafara saka ido sosai akan son kama barawon.

Cikin saa takamasu aikuwa tasa akayi musu mugun dukanda Saida suka fita hayyacinsu Kuma tasa aka koresu daga anguwar gaba dayama.

Wata sabuwar anguwa suka fada wadda tafi wadda suka baro hargitsi saidai wannan din 'yan ta'addane sukafi yawa acikinta sbd gasunan koina suna shaye shaye.

Cikin saa nanma suka samu wata tsohuwar makaranta suna kwana aciki sauqinsu daya makarantar nada megadi shiyasa sukejin saukin kwana.

Ranarda suka cika kwana shida a sabon gurin cikin dare suna dawowa wasu maza biyu suka taresu.

Saurin riqe hannun juna sukayi suna ja da baya sbd yanzu sunfara wayo sosai.

Damqo amatu dayan yayi da qarfi Yana cewa'"

Kai saketa ka ware daga Nan gun.

Dayan hannunsa yasa yaqara riqeta Yana girgiza Kai alamar aa.

Wani wawan Mari dayan ya sakar Masa Wanda yasashi ihu. 

Suka toshe masa baki tareda matsesa 
Shikuma dayan ya fizge amatu tareda kwantarda ita qasa da qarfi.

Kuka tasaki tana miqawa Usman hannu tana Kiran sunansa itama da sauri dayan ya rufe Mata baki Yana qoqarin cire wandonsa.


Kuka sukeyi duk su duka musamman Usman dayaga irin Abinda akai masane zaayiwa amatu Kuma ya dandani tsananin azabar hakan bazai Bari amatu ta dandana ba.
#mamuh.


#Zafafa biyar#

Saran boye
Billyn Abdul

Abin dake zuciyata
Hafsat rano

Kibiyar AJALI
Miss xoxo

Siradin rayuwa
Safiyya huguma

Min qalb
mamuhgee

Pay@
09033181070
Or 
09032345899
[3/2, 2:25 PM] Zafafa: _*MIN QALB*_
_Mamuhgee_

2

Bazai iya ganiba 
sunaji suna gani qaton saurayin yake kokarin keta rayuwarta dabata gama sanin ciwon kantaba,
Ita kukan datakeyi dannewar dayayi Mata akan duwatsu suna cin jikinta
Shikuma Usman kukan zabar dayasha yake tunowa itace zaayiwa amatu Wanda sanadin hakan sunzama 6arayi dole da qarfi da yaji.

Qoqrin bude qafafuwanta qaton keyi 
Usman yayi wani yunkuri tareda kama hannun Wanda ke maqure dashi ya sakar Masa mugun cizo Mai qarfi da haqoransa dasuka gama bushewa da dau'da.

A gigice yasakesa Yana yarfe hannu sbd azabar cizon.

Wani qaton dustsi Usman din yadauka baiyi wata wata ba ya buga akan qaton dake kan amatu 
Take ya sulale gefe kansa na tartsin jini sosai ko ihu daya beyiba ya zube agurin Yana wani irin Shure Shure.

Suna ganin hakan wani irin tsoro yashigesu da gudu ya kamo hannun amatu Yana cewa'"

Zo mu gudu amatu.

A firgice dayan ya riqesu Yana cewa'"

Kun kasheshi....a kidime yake fadar hakan cikin tsananin tsoron ganin abokinsa na Shure shuren mutuwa.

Qoqarin jansu yakeyi Yana cewa'"

Wlh police zan kaiku Kun kashesa,
Bazaki guduba ku barni cikin masifa akamani.

Jansu yakeyi da qarfi cikin firgici da tashin hankali suna kuka sosai suna rokonsa ya sakesu Amma Shima a rude yake kansa zai wanke kota halin Yaya.

Irin kukan dasukeyi Basu taba yinsaba arayuwarsu sbd jin wani ya mutu sbd su Kuma Suma kashesu dayan sukaji yanacewa zaayi.

Sosai suke kuka suna rokonsa ya sakesu Amma ko jinsu bayayi Dan Shima kusan kukan yakeyi na tsoro da firgici.

Wata qatuwar gora daga bayansu aka kwadawa qaton a tsakiyar Kai 
Ya tsaya cak tareda sakin hannuwansu Yana qoqarin juyawa yaga ko waye ya yanke jiki yafadi jini nafita a qeyar kansa.

Jikinsu na rawa cikin tsananin tsoro da firgici suka juyo suna qanqame hannuwan junansu tareda ja baya suna kallon qaton dashima yake Shure Shure.

Cikin sauri megadin makarantar ya matso gabansu tareda riqo hannuwansu yasaka musu kudi Yana waige waige Yace"

Kuyi gudu sosai kuje can qasan layin gaban kasuwar baya akwai makarantar almajirai ku shige cikinsu ku kwanta ku boye zanzo idan ankwana biyu
Kuyi sauri karku taba dawowa tanan 
Kuyi sauri kuje..

Kallonsa sukeyi suna sake sakin sabon kuka sbd sunqara firgicewa da Abinda yake fada,

Yaturasu Yana cewa'"

Kuje kuje kuyi sauri karku dawo.

Gudu suka Fara suna waiwayensa sbd akaro na farko da wani ya taimakesu arayuwarsu.

Tun suna waiwayensa harsuka bace suna gudu cikin Daren gashi yace karsu hau titi subi kwana kwana.

Koda suka Kai makarantar almajiran dare yayi sosai gashi karnika sai haushi suke musu duk inda sukabi.

Suna kaiwa bakin makarantar suka tsaya suna rarraba idon Ina zasu boye sbd almajiran gasunan kwance birjik a fili kowa da matacciyar tabarmarsa wasu Kuma da kwalaye wasuma hakanan suke kwance a qasa ga cinnakai da qwari da komai Amma ba ruwansu kwance suke abinsu suna bacci.

Hanunta usman yakama suka qarasa can qarshe yacire matacciyar rigar jikinsa data gama yagewa ta mutu ya shimfida musu suka kwanta kowannensu jikinsa na rawa numfashinsu na fita da sauri sbd tsananin tsoron dasuke ciki.

Asubar fari dukkanin almajiran aka tadasu suyi sallah 
Wanda wannan shine karo na farko dasuka tabayin sallah Shima Suma dai sunyi yanda sukaga kowa nayi gurin bin Abinda malam yayi.

Ana gama sallah kowa yadauko allonsa Yana bita.

Gari yafara haske sai sukaga almajiran na kallon amatu cikin mamaki suna kallon kanta Wanda gashinta ke butu butu da dau'da da qazanta Wanda yake son nuna ita mace ce.

Daga dama sukaji wani almajiri yace"

Kai wallahi idan malam yazo yaga mace dukanku zaiyi wayace mace tana zuwa Nan?hmm
Korarki ma malam zaiyi yanzu Yana fitowa.

Usman najin kora ya kama hannunta suka miqe anabinsu da kallo suka fice  a sanyaye.

Harsunyi nisa kadan yatuno da maganar kawu megadi na cewa karsu koma yayi saurin juyawa da ita Yana kalle kallen inda zasu fake Kuma.

Ganin har yamma tayi suna gararin gurin zuwa yasa ya lalubo kudinda kawun yabasu yaje shagon dake kallon inda suke yasiyo Rezar nera ashirin yadawo yajata suka zagaya bayan wani gida Yana cewa'"

Amatu zo muyi aski irin nasu almajiran malam saimu koma cikinsu tunda bamuda wani gurin.

Haka ta zauna yahau yimata aski
Saida ya aske kan tas Wanda duk kusan Rabin kan ya yayyakenta sai jini ke fita kadan kadan Amma Sam Basu damuba Shima sama sama yayi nasa askin rabi yayi rabi beyiba suka dunkule Rezar sbd gaba suka koma makarantar dama kayan jikinsu duk riga da wandone dasuka gama yayyagewa suka sauya kamanni.

Dayake makarantar ba qa'ida sukebi ba take malam ya kaebesu yaga sabbin alamjirai aka Basu tsoffin allon karatu take suka shiga sahun almajirai batareda kowa yasan cewa amatun mace ceba Koda malam ya tambayi sunayensu sukace Usman da amadu.

Ahankali suka Saba da rayuwar almajiranci duk da akwai wuya Amma tafi musu rayuwarsu ta baya dansu yanzu ganin sukeyi sunyi gata.

Akai akai Usman kemata aski sbd kar gashinta yafito musamman sbd tanada saurin tsirowar gashin,

Sunsaba idan sungama ayyukan gidan malam akayi karatu aka gama su fita yawon bara sai yamma sudawo karatun yamma sannan sufita barar dare daga Nan Kuma dare nayi zuzo su kwanta.

Yanzu suna samun yin wanka a sati ko so dayane shiyasa suka Dan Fara canzawa.

Tun suna qirgen kwanakin zuwan kawu megadi harsuka daina suka koma qirgen kwanakin zuwansu har lissafi ya batar musu.

Ko ayanxu dasuke cikin inuwar almajiranci abun dai 'dayane shine idan baka tsayawa kankaba Kaine a qasa ko yaushe,

Sunsha gwagwarmaya zamansu makarantar malam din,

Idan anyi sata su ake maqalawa,
Barna sune,
Laifi sune,
Hatta laifin cikin gidan malam su ake maqalawa shiyasa sunfi kowa azabtuwa sbd irin dukan da malam da ya manyan yaransa suke musu,

Shatin buloli ajikinsu yazama tamkar zanen fatarda aka haliccesu da itane,

Tun suna kuka a almari harsun qame sun daina sbd ganin rayuwar ahaka take koina na sama ya danne na qasan.

Duk hutunda akeyi sukam basa zuwa koina sbd basuda gurin zuwa shiyasa rashin tausayinsu yafi yawa sbd ansan ko an zalincesu basuda me tsaya musu.

Ahaka dai rayuwa taja tsananin rayuwa Yana qara musu yawa musamman yanxu da amatu take Fara nonuwa kullum cikin boye boye suke gashi yanxu abubuwan naqara tsanantar musu ne gashi amatu ko mgn batayi sosai da qarfi da yaji suke boyon mganarta kar agano mace ce.

Yanxu dasukayj wayo Usman shine me wahalar Abinda zasu ci duk da tare suke zuwa duk inda zasu gashi baqin jini tamkar a jininsu yake sbd duk inda sukaje tsanarsu da kyararsu akeyi shiyasa suka riqe aransu duniya kowa kansa kawai yasani basuda Abinda yafi musu junansu.

Wani hutu da akayi kamar daga sama saiga kawu megadi Wanda tuni suka Fara mantawa da kamanninsa,

Farin ciki da murnar dasukayi kamar shine danginsu da basuda musamman dasukaga yazo musu da gari kusan kwano buyi jikinsu har rawa yakeyi gurin yimasa godiya.

Amatu ya qurawa ido musamman kanta dake aske tas Yana qyalli ga wasu qananun quraje a jikinsu zuciyarsa na susa yaji dukkanin kuzarinsa ya karye sbd tabbas duk da baitaba haihuwaba ita 'ya mace ce bazaa jima ana boyeta ba amatsayin namiji.

Dazai tafi yasiya musu gwanjo kowannensu riga da wando masu Dan dama dama.

Tun daga lokacin yake Dan zuwa akai akai Yana dubasu sai rayuwar tadan Fara yimusu sauqi.

Awani zuwa da yayi
Baizo da niyar tafiya dasuba Amma atake tunaninsa ya sauya akan amatu sbd girma daya Fara zuwar Mata gadan gadan Yana tsoron amatsayinta na mace ta abalage acikin maza.

kallonsu yayi bayan sun zagayo bayan makarantar cikin karyewar zuciya Yana jinjina rabasun dazaiyi yace"

Usman kaga amatu tafara girma akwai hadari abarta cikinku anan..

Kallonsa sukayi atare cikin rashin fahimta.

Gyara tsayuwa yayi yace zantafi da ita zan kaita gurin me 'dakina idan yaso Kai saika riqa zuwa Mana hutu.

Atare suka girgiza Kai itada Usman din suna kallon juna idanuwansu na cikowa da hawaye.

Nasan zaa rina yafada cikin ransa Yana kallonsu zuciya a karye.

Kamo hanun Usman yayi yajasa gefe ya fahimtar dashi sosai ta yanda zai gane Abinda yake nufi 
Harya gane Yakuma amince sbd har abada bazaiso Abinda zai samu amatu ba.

Daga haka suka hakura sunaji suna gani suka rabu da juna kawu yatafi da su kafin daga baya Usman yadawo makarantar malam.

Tunda amatu tadawo gidan kawu Bata taba haduwa da tsangwama ba saidai Kuma babuwa wani janta ajiki da iyami tayi.

Basuda qarfi sai rufin asiri da haka malam yasakata primary school dinda yake gadi wadda tuni aka maidata 'yar maigadi.

Usman shekara daya yayi batareda itaba ya tattara karatun yadawo gidan kawu Yana kwana a soro komai tsananin sanyi da zafi kuwa.

A haka kawu yasamar Masa aikin tsaron gidan wanka da bahaya a Tasha har Shima yashiga primary 2 
Yana shiga primary 5 ya tattara karatun ya ajiye sbd gwagwarmayar rayuwa.

Kawu da iyami sune gatansu na farko,
Kawu da iyami sune wainda suka cirosu daga bola suka basu sunanda ake kallonsu da daraja ayanzu.

Shekakarda tashiga js 2 a shekarar suka shiga wata sabuwar masifar da akayiwa kawu sharrin satar cire winduna da qofofin makaranta ya siyar.

Duk inda ake zuwa roqo da Kai kuka sunkai akan alamarin Amma Abu ya agagara qarshe dpo nunawa yayi sai idan ita amatu kokuma matar kawun zasu kwana dashi tukuna zai taimakesu.

Akaro na farko da amatu ta tsani maza da taimakonsu.

Ranar dukkaninsu kwana sukayi kukan baqin ciki sunaji suna gani akayi gidan yari da kawu hukuncin shekara biyu dama Kuma abin hadda gayya sbd Shima alqali yaso amatun tabasa hadin Kai sbd irin wankewa da jikinta yayi gashi fatarta Ashe me irin hasken Nan ce ga jikinta daya gama fitowa ana mace tsaf yanzu iyakaci qarasa balagewa ne dabatayiba a cikakkiyar mace.

Tunda akayi gidan yari da kawu alamarin duniya yasakosu gaba ko abincinda zasuci ya gagaresu dole Usman ne yanaji Yana gani yake fita gwagwarmaya Amma sai ahankali.

Wata bakwai da zuwan kawu gidan yari aka koresu daga gidan dasuke suka rasa gurin zuwa ga iyami Dan cikinsa take dauke dashi wahala tasaka ya bare ko kudin asibiti basuda.

Akaro na farko da Usman yakoma sata kenan arayuwarsa ya kama musu daki buyi a wani gidan haya me dakuna goma reras a jere kamar shaguna,
Gidanda ya hada mutane dabam dabam masu halaye dabam dabam.
#mamuh#

MIN QALB❤️
Mamuhgee

ZAFAFA BIAYAR

SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma

MIN QALB
mamuhgee

YANKAN BAYA
billyn Abdul

KIBIYAR AJALI
Miss xoxo 

ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano

Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/4, 12:14 AM] Zafafa: *_MIN QALB 3_*
_mamuhgee_


_Min qalb Na kudine_

Daki 'daya ya dauka iyami da amatu suka dauka daya
Sabuwar rayuwa suka Fara a gidan inda ake zaman rashin nasiha da ragawa juna,
Sam gidan kowa ta kansa yakeyi Babu Mai ta6uwa kowa ka taba Babu sauki sai masifa.,
Hakan yasa suma ahankali rayuwa ta koya musu yanda take,
Sunaji suna gani itama amatu ta ajiye karatu suka fada gwagwarmayar neman abin rufawa Kai asiri,

Amatu da iyami suka bazama neman ayuka
Ita iyami tasamu aikin abincin wata makaranta amatu Kuma tasamu aiki bookshop din wata iyamura.

Bata wani jima tana aiki gurinba saigashi Shima Usman aka kamasa aka rufe kusan wata biyu ga iyami ma tana fama da ciwon diabetes sai kawai tace Mata ta ajiye aikin abincin makarantar kada taji ciwo al'amarin yaqara lalace musu.

Hakan yasa nauyi yahau kanta na kulada iyami damuma nauyin ci da shansu.

Rayuwa da lokaci sune suka koyar da ita darussa da dama wanda ayanxu take musu kallon fahimta,

Tunda lalurar nauyin ahalinsu tadawo kanta Bata taba samun Wanda yadubeta da fuskar taimakawaba kowa da wata mummunar manufa yakeson taimaka mata,
Ansha niyar lalatar Mata da rayuwa tana tserata,
Ansha wulaqantata akan ana Mata kallon fandararriya Mara asali,

A ranarda wani yayi niyar lalatar Mata da rayuwa ta dole da niyar zai taimaka musu aranar ne zuciyarta ta gama qanqansewa da duk wani alamarin mutanen duniya
Shiyasa take Kiran kanta da furen kan juji.

Iyami ma hakan yasake busar Mata da zuciyar zata nemi kudi kota yayane Banda haram,

Babban Abinda ke qara kawo tabarbarewar zaman lafiyarmu shine hukunci akan Wanda hukuncin laifinsa bai Kai ba shike kawo sauyawar tunani da zuciya,

To kusan hakance tafaru da ahalin kawu,
Bayan fitowar Usman tuni zuciyarsa ta gama kangarewa sbd rufesan da akayi suncire Masa tsoron gidan yari Kuma,

Rayuwarsu tadawo sabuwa,
Burinsu shine kudi,
Farin cikinsu shine kudi,
Mafarkinsu shine kudi,
Mafarkinsu shine kudi
Idan har kudi suke Hana Dan Adam wulaqanta da tozarta tareda azabta Irin wadda suka taso suka rayu acikinta to tabbas sun shirya samun kudi Koda na wani ne.


Basu sake jinjinawa alamarin kudi ba Saida sukayi belin kawu da kudi naira dubu dari bayan yayi shekara daya da wata Tara gidan yari.

Babban al'amarinda ya shallake tunanin abokan zamansu na gidan hayan shine qarmashewar da zuciyar kawu tayi fiyeda ta kowa acikinsu game da kudi,

Yana fitowa gidan yari Abinda yafara fada afili shine'"

Idan har kudi sune maganin wulaqanci da toxarci tareda maganin wani baqin ciki to tabbas burina yanxu shine kudi,
Kudinma ba qananun ba manya nake buri.


Shekaru sunja sosai alamura sunyi haske sosai a rayuwarsu sbd kowa yanada hanyoyin samun kudinsa,

Acikin gidansu dake cike tab da 'yan haya to tabbas Babu me masifa da fitinar kawu,

Bayada sauki ko kadan Dan babu ubanda yake ragarwa a gidan ciki kuwa harda alhaji mande me gidan,
Duk masifaffun gidan suna shafawa kawu lafiya sbd fitinarsa Amma shikuma iyami ce kawai daidai dashi sbd ko atsakaninsu basawa juna nasiha ko sauqi.

Damuwa,kuka,kunci,baqin ciki,takaici,tuna baya
Wainnan duk wasu abubuwane dasuka binne a bayan rayuwarsu,
Sun koya su ciyar da kansu tun basusan kan nasuba,
Sun koya tsayawa da qafafunsu da junansu tun basusan meye duniyar ta qunsaba,
Sunyi yaqi da wahala da yunwa tareda azabta su kadai batareda wani ya tallafesuba,
Sun yakice tsoro tun basusan meye tsoronba
Dan haka su aduk yanda rayuwa tazo musu yanzu basuda damuwa da ita sbd sunsan babu wata gwagwarmayar data fi wannan din.

Wannan shine rayuwarsu,
Rayuwar 'yancin Kai rayuwarda baduda burin komai cikinta saina suji Dadi su dawwama da juna acikinsa.

AMATULLAH yanxu rayuwarta takeyi cikin jin Dadi da walwala,
Babu Abinda ya dameta face taji dadin rayuwa tareda ahalinta data keda burin su samu duniya suji dadinsu,

Duk inda tasamu aiki Bata jimawa ake watsewa sbd halayenta na Babu Abinda ya dameta bayan shiririta da yin duk Abinda taga dama 
Duk Wanda yayi gigin shiga huruminta kuwa Yara take sawa qanana su koyawa mutum hankali kokuma usi Wanda beda aikin yi yanxu sai yawon banza sai idan ansamu na sanfewa a sanfe.

Amatu kyakkyawar cikakkiyar budurwace yanxu wadda tagama hada komai musamman kyawun jiki da fuska.

Maza ko gigin zuwa nemanta basayi sbd a duniya idan akwai Abinda ta tsana fiyeda komai to mazane idan aka cire usi dinta da kawunta.

Kana cewa kana sonta zata saka ahada maka jini da majina Wanda usi ne me aikin shida wasu abokanansa.


Ayanxu Kam sunsan duniya sunkuma darassantu da iliminda tabasu shiyasa   akoda yaushe ashirye suke da duk sabon darasinda zata kawo.

AMATULLAH K SALEH shine cikakken sunanta Wanda kawu yabata aranar da yafara kaita makaranta,
Usman K saleh 'dan uwantane da aduniya babu Abinda takeso da qauna sama dashi,
Zata iya sadaukarda rayuwarta data Bari wani abu ya samesa,
Hakama zata iya sadaukarda komai sbd shi sbd sunawa juna kallon uwa daya uba daya suke ko kawu baitaba sanin ba uwa daya uba dayane ya haifesuba duk da Shima bakowane yasan cewa bashine mahaifinsu ba musamman da kusan halayen amatu duk nasa ne na rashin hakuri ko kadan,
Acikin su hudu kuwa baasan waye yafi wani son kudi da abun duniyaba shiyasa ake musu laqabi da dangin tsamiya.

Arayuwarta tayi aiki kala dabam dabam zai Kai goma koma fiye Wanda takeyi yanxu a restaurant shine kusan na sha daya 
Hakama kawu yayi sanaoin harya gaji Amma yaqi kudi shiyasa ya tattara ya watsar yakoma zaman saka ido da jiran Wanda tsautsayi zaisa ya tabasa yaga masifa tareda siyan radio yakoma Shan waqe waqen gargajiya wanda kowa naji ba halin mgn sbd Shima ubanda zai tanka dinyake nema Amma haka kowa ke dannewa sbd azauna lfy duk da gidan kullum cikin fada da hayaniya ake.


****
Qarar waqar sani sabulu ce ta _duniya wandon roba_ ta cika gidan ta karade  wane daki da saqo na gidan sbd qarar muryar radio din da aka Kai qarshe gaba daya.

Hankalinsa kwance yake yana Shan waqarsa Yana sakace haqoransa da tsinke
Daka gansa zakasan babu Abinda ya damesa.

Dukkanin mutanen gidan 'dai 'dai suka ringa fitowa rayukansu a 'bace da takaicinsa na kullum Wanda inda sabo sun Saba da dabi'arsa ta tayardasu kullum da sautin radionsa da muryarsa Bata qasa
Gashi bamai ikon mgn 'yar gaban goshinsa da shaqiyin dansa suce ba Wanda ya isa
Amma rshin arzikinsu babu kalar Wanda basa fafatawa dashi wanda kallo daya zakayi musu kasan su din abin mamaki ne,
Rayuwarsu abin kallo ce sbd sudin abin mamakine.

Yana ganin mutanen gidan sunfara fitowa ya sake dauke Kai sama Yana jiran yaji wani Mai shafaffun Mai akai ne zaiyi mgn ya sauke Masa masifar dake cinsa ta takaicin iyami daya kwana dashi na biya Masa bashin dabaiyi niyar biyaba yanzu da kudinda yaci burin canza radio dashi na AMATULLAH da USI.

Cikin bacci qarar radio din ke shigarta Yana damunta,
Juya kwanciyarta tayi tana toshe kunnuwanta da pillow Amma
Sam qarar Bata daina shiga kunnuwanta ba.
Tsoki tasaki ahankali tana cewa'

Kawuuuu.

Saidata sake rintsawa ta juya kwanciyarta tsawon minti goma Amma Sam baccin ya gagara sbd qarar radio din dole ta yaye lullubinta ta miqe zaune tana miqa tana cewa'

Allah yasa yanda natashi yau cikin qoshin lfy  yasa yau ranar sa'atace,
Allah yasa yauma na hadu da irin hajiyar Dana hadu da ita jiya nayi mata kukan tausayi tabani kudinda zanyo......

Kasa qarasawa tayi tareda zaro ido sbd USI data tuno 
Da sauri ta dauki hularta dake kan katifarta ta sanya akai tareda zura silifas cikin sauri tana fitowa kota kan kawun batabi ba sbd daga yanayin waqar dayake sha a radio din ta fahimci yau ba sauqi a qule yake Wanda zai saukewa haushin yake nema shiyasa ba Wanda yace Masa uffan gudun masifa.

Bokiti ta dauka ta nufi fanfon dake can kusada  qofar shigowa cikin gidan
Tana zuwa ta tararda wani bokitin yakusa cika 
Ta gefen ido ta kalli maman junior dake tsaye alamar natane take jiran yacika hancinta na asalin yorbawa sai cika yakeyi Yana fidda iska sbd ita kullum a shirye take da duk inda masifa zata fado ta hauyi.

Shahada tayi ta rintse ido cikin ranta tace'
Bayina bane Allah ne ya qaddaro bazanbi layin jiraba
Ta sunkucesa da gudu ta fada bayin gidan daidai salamatu zata fito bayin tsoron ganin mutum a fujajan yayo ciki yasa ta zame ta Fadi qofar bayin
Aikuwa itakam amah Bata tsaya wata wata ba ta rufo bayin tana cewa'

Haka Allah yaso anty salamatu bayina bane Allah ne ya qaddaro zaki Fadi,
Kema maman junior yi hkr Allah ne ya qaddara da ruwanki zanyi wanka bayina bane.

Cikin wani irin tsananin baqin ciki da takaici salamatu ke kallon kanta zaune cikin ruwan qazantar qofar bayin bayan tayo wanka.,

Wani irin tiririn masifa zuciyarta keyi ta miqe amatuqar zuciye daidai isowar maman junior itama jikinta harwani mazarin masifa yakeyi tana cewa'

Wlh yau gidan Nan saidai kowa alaji landlord yakore agidan Nan Amma sai anyi balain da ko kawu fatihu duk masifarsa bazai hanani yiwa yarinyar Nan dukan tashi Kisha ruwan gishiri ba.

Kallonta salamatu tayi a harziqe tana cewa'

Saiki sameta cikin bayin tunda akanki aka Fara sauke masifa duniya 
Kinzo kina qaramin haushi
Idan ke duka zaki mata wlh ni yau saina dauko motar Yan Banga a gidan Nan kowa yaci ubansa tunda Nagano kowane shege a gidan Nan ya rainani tunda anga Ina zaman kaina.

Kota kanta maman junior batabi ba tahau dukan qofar bayin tana fadin'

Yau wlh zakisan halina dabaki saniba tun kafin kizo duniya nasan rashin arziki bazakizo ki rainawa kowa hankaliba kullum komai kikayi kina Kiran sunan qaddara ne daga Allah wlh yau Ina roqan Allah yahadaki da qaddarar Nan da kike kirawa mutane bayan nagama Miki dukan tuwon qasa.

Alhaji mande dake jiyo yanda ake buga qofar bayin gidansa da qarfi ba arziki ya zubo babbar riga yafito ya zagayo gidan tun a soron gidan yake jiyo qarar radion kawu fatihu yaja tsokin takaici ko sallama baiyiba ya fado gidan Yana cewa'

Uban waye zamansa ya qare a gidan Nan yau yake gyangyademin qofar bayi??

Maman junior najin haka tayo gurinsa tana masifa tana zayyane Masa Abinda yafaru bakinta ta kumfar masifar customers dinta nata jiranta ruwan dafa musu doyane tazo diba.

Tanajinsu cikin bayin Amma ko ajikinta tayo wankan da sauri ta fito basuma ankaraba ta fada dakinta tahau shiri
cikin sauri ta shirya cikin doguwar riga baqa mara Fadi sosai ta sanya hijab iya wuyanta ash ta dauki Jakarta qarama ta rataya a wuya ta fice.

Gaban kawu tazo tana ciro qaramar wayarta jaka tace'

Kawu sannu da tashi.

Yi yayi kamar baijitaba Yana gyara zaman radionsa data ishi kowa gidan.
Qofar dakinsu ta kalla inda iyami ke zaune tana sakawa Koko sugar tace'

Iyami Ina kwana??

Lafiya kalau.''tace itama fuska a tsuke.

Murmushi tayi Wanda yasa kumatunta lotsawa haqoranta suka bayyana 
Sbd tagano fadansune dai Wanda basa rabuwa dashi itada kawun Kuma ta tabbatarda akan kudi ne..

Dariya tayi tana juyawa tace' 
Allah kasa muyi kudi kawu da iyami su daina fada.

Harta fito gidan alhaji mande da maman junior Basu daina fadaba sbd fadan tsakaninsu yakoma.

Titi ta nufa da sauri tana adduar samun kudinda zata bailing usi.

Tana isowa titin tasamu adaidaita ta tare ta fada cikin sauri tace' 

Blue fox zaka kaini.

Tafiyar mintuna gomace takaisu gurin cikin sauri ta biyasa ta nufi harabar gurin dake tsareda security masu baqaqen uniform ta shiga
tana kallon wasu motoci biyu dasuka dauki hankalinta sbd tsananin kyawunsu da sheqin dasukeyi Dan har kanka kake gani ta jikinsu
ta kalli sama tace'

Ya Allah kasa muyi kudinda zamu mallaki irinsu nida usi mu Hana su kawu fada.

Ciki ta qarasa da sauri tana adduar Allah yasa yau tasamu sa'ar wani a cikin restaurant din.

Tana shiga ta nufi dakinsu na staffs din gurin inda suke sauya Kaya zuwa uniform din aikinsu.

Kayanta ta sauya izuwa uniform din aikin waitress dogon wando baqi da riga riga ash saita bar qaramin ash hijab dinta na iya wuya.

So takeyi ta tafi da wuri yau sbd gabaki daya hankalinta nakan usi.
Ta tabbatarda yanacan cikin wahala da damuwa duk da dai alqawarinsu ne bazasu taba saka kansu cikin damuwaba duk halinda zasu shiga sbd damuwa ciwo ce a ganinsu idan kasone zaka sakawa kanka damuwa a almarin duniya.

Amah!!!

Naam"ta karba tana juyowa daga jera drinks datakeyi a fridge.

Manager dinsune sanye cikin black Suit da medical glass a fuskarsa cikin tsuke fuska yace"

Ki hada black coffee dinda ake karbarwa _MD ZABEERA_ kullum ana kaimasa yau yazo da kansa zaisha anan,
And ki tabbatarda kinyisa yanda koyaushe ake hadawa kar asamu matsala amah.

Yaqe baki tayi da murmushin qarya tace'"

Bazaa samu matsalab inshallah manager.

Juyawa yayi ya fice Yana cewa' Allah yasa. 

Kamar yanda tasan ana hadawa haka tafara hadawa cikin sauri sauri tana gama zubawa Yana sake shigowa yace"

Yawwa ki hada a tray ki Kai VIP 3 yagama Abinda zaiyi tafiya zaiyima.

Babu Abinda ta tsana kamar kai abinci a aikinnan nasu tafison abarta a hadawa suna dauka suna kaiwa sbd idan tana ganin masu kudi burinta sake hauhawa yakeyi.

Tsaki tasaki ta dauke baki ta dauka tana tafe tana qananun tsoki tana Harare harare.

VIP dinsu Yana can sama Saida tagama tsinewa manager ko kafin takai saman daukeda tray din.

Saida ta tsaya ta huta kafin ta nufi VIP 3 din tana isa security din dake gurin ya tura mata qofar gurin yana washe mata baki sbd mutuniyarsace ba ruwanta lafiyayyan takeaway take Masa idan zasu tashi shiyasa kowa gurin yake yinta Dan babu ruwanta bayarwa takeyi shiyasa lissafin nasu yanxu gurin kullum cikin rudarwa yake tunda aka dauketa aiki gurin.

Tana shiga ta tsaya cak tareda lumshe ido tasaki wata irin ajiyar zuciya afili tace'"

Hummmmm masu kudi turarensu ma qamshinsa na dabam ne,
Ya Allah ga amah da usi.

Bude ido tayi ahankali daidai wayarsa na daukar ringin batareda ya juyoba ya sanya dogon hannunsa da fatarsa ke sheqin hutu da haske ya dauki wayar tareda miqewa ya nufi window ya Dora wayar a kunne batareda yace komaiba.

Zare idanuwanta dake neman rufewa su suma tayi tana girgiza kanta ahankali tace'"

Ya Allah.

Table ta nufa ta ajiye tray din idanuwanta suka sauka kan wallet dinsa dake ajiye da kudi acike acikinta batasan lokacinda tayi saurin dire tray din ta dauki wallet din ta bude taba zaro ido tace"

Yau ranar sa'atace ya Allah nagode maka.

Kudin ta zaro gabaki daya tana musu kallon qurilla fuskarta cikeda farin ciki tace' 

Kayi hakuri Dan balarabe Amma nafika buqatan kudin Nan.

Aje wallet din tayi ta juya da sauri cikin farin ciki tana damqe kudin ta fice tana sauri Dan karya gama waya ya juyo yaga ba kudinsa ya biyota yace kudinsa zai qwata itakuma bazata bayarba.

Ta glass din window dayake tsaye yake kallonta cikeda tsananin mamaki da qyamar halinta daya sanyashi kasa juyowa akaro na farko dayaga mace da irin wannan halin mafi Muni agaresa Wanda hakan yasahi kashe wayar wadda tunda ya daga baice komai sai sauraren zancen da ake Masa tacan Wanda kusan hakan dabi'arsa ce.
#mamuh#

#MIN QALB❤️
Mamuhgee

ZAFAFA BIAYAR

SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma

MIN QALB
mamuhgee

YANKAN BAYA
billyn Abdul

KIBIYAR AJALI
Miss xoxo 

ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano

Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/6, 3:14 PM] Zafafa: *_MIN QALB 4_*
_Mamuhgee_


#ZAFAFA BIYAR#PAY@+234 903 234 5899 OR 09033181070 


Tana fitowa dakin ta washe baki tareda daga kudin ta kallesu tana fitar fuskarta dasu tace"

Hmmm amah zakiyi kudi ki mallaki uwayen wainnan kiyi rayuwa yanda kikeso ki juya Wanda kikeso hhhh.

Kallon hashimu me tsaron qofar tayi tareda sakar Masa murmushin iko na nuna Masa itace agabansa tunda ita ke riqeda kudi,

Sake juyasu tayi tareda zaro Yan naira dubu 'daya 'daya guda uku tabasa tana cewa'"

Kana fadar Abinda yafaru yanxu to sunan aurenka matacce dan wlh sainaje nasa anhana.

Damqar kudin yayi da sauri Yana turawa cikin aljihu tareda washe bakinsa har iyaka yace"

Haba Hajiya amah kema kinsan hakan bazaitaba faruwaba,
Ko bomb akamin belt dashi bazan fadaba.

Dariya tasaki cikin girmama alamari da mutunci irin na kudi Wanda yasa hashimu fadar haka akan dubu uku kacal ma,
Sake kallonsu tayi tana dagawa tace"

Allah sarki kudi,
Kudi muna sonku 
Bama gane kowane yare sai naku.

Juyawa tayi tana cusasu cikin wandon jeans dinta dake cikin doguwar jallabiyarta tana cewa'"

Hashimu bakinka qanin kafarka.

Kallon tray din tea dinda takawo yayi yanason kallonsa amatsayin tsarkakken Abu Amma apatite dinsa yakasa dauka take yaji gurin gabaki daya yafita aransa ya kwashi wayoyinsa da wallet dinsa ya fito ya fice batareda ya kalli ko gefenda Hashimu ke Masa asauka lafiya ba.

Tana saukowa ta sauya kayan aiki ta zari Jakarta ko sallama batayiwa manager ba sbd gabaki daya hankalinta yatafi a station sbd tasan usi nacan najiranta.

Adaidaita ta tsayar ta fada tana cemasa'

Central police station zaka kaini.

Bayan ta zauna cikin napep din ta zaro kudin daga aljihun jeans dinta ta qirgasu dubu ashirin da bakwai ne kenan hadida dubu ukun data bawa hashimu dubu talatin kenan,
Hmmm lallai wannan daga gani me kudine yau badan belin usi ba da kamawa kawu shago zatayi yafara Sanaa Koda ta awon su gero ne da gari.

Daidai gate din central din aka ajiyeta ta sallami me adaidaita din ta kalli gate din station din tana Jan siririn tsaki cikin quluwa tace'"

Tabbas da munada arziki da nafi qarfin zuwa gurin Nan Ina mace,
Amma haka qaddara tazomin inaga stations din jahar Nan Babu Wanda bana zuwa sbd irin haka.

Sauke numfashi ma qarfi tayi tareda Jan iska tana cewa'"

Amah bakida Wanda yadamu da mutuncinki Dan haka ki daina kawo tunanin komai bayan na maida hankali ki Gina rayuwarki cikin jin Dadi batareda kinsa damuwar komai ko kowaba arai.

Rataya qaramar Jakarta tayi tana nufar hanyar shiga tana karewa 'yan iskan kurtun police 'din dake binta da kallon qurulla saidai dayake sunfi kowa sanin waye ita yasa suka kama kansu sbd tsira da 'yan canjin dake aljihunansu sbd Suma a qone suke murus ba canji.

Kamar daga sama insfector Garba ya ganta tashigo fuskarta a daure.

Dan hadiye yawu yayi tareda shafa aljihunsa ya lalubo Yan kudadensa kusan dubu shida ya hadiye yawun qaqa nikayi sbd gskia yanason amah Amma Kuma duk lokacinda ya kusantota saita sanfesa tas har mamaki yakeyi yanda take zaresu bai saniba baikuma ganiba yanda kasan me aiki da aljanu haka take.

Togewa tayi bakin kanta tana sake tsuke fuska ta kalli wainda suke incharge tace"

Gurin USI nazo.

'Dayan dayake qule da ita tun wani zuwa datayi belin Dan uwanta ta samfe Masa dubu hudu yake haqe da ita Danma fitinanniyar Bata tabuwa sbd ogansu daya gama mutuwa kanta tana kassarasa Amma qaton banxan yakasa bude ido ya fahimci Babu Abinda amah keso arayuwarta idanba kudi da Dan uwanta usi ba sai kawu.

Saida suka gama harare hararen juna kafin aka fiddo da Usi din aka Fara rubuce rubuce akace dubu gama sha biyar zata bayar.

Bude jaka tayi taciro kudin batareda tace musu komaiba ta miqa musu tana yiwa kudin kallon bankwana cikin ranta tace'"

Insfector Garba Kaine wlh zaka biya tunda kanaji kana gani suka kama usi akan sunyi fada da wani Dan masu kudi shine shi USI aka kamasa.

Insfector Garba na ganin irin kallon datayi Masa ya fada office dinsa Yana zare dukkan kudadensa daga aljihunansa Yana turawa qarqashin lokar office dinsa Yana zazzare idanuwa sbd gskia yau bai shirya daukar asara ba.

Kallon usi tayi zuciyarta na qunar ganin yanayinsa daga gani uban duka suka Mai suka cire haushinta Dan tasan kowannensu a qule yake da ita.

Wata baqar €class0221 ce tashigo station din tayi parking atake duk suka ajiye Abinda sukeyi jikinsu na rawa suka miqe suna fadin' 
MD ZABEERA ya iso.

insfector Garba ne yafito Yana cewa'"

Sargent salisu kufito da yaron Nan Wanda MD ZABEERA yakira yayi mgn akai Wanda sukayi fada da USI.

Yes sir"

Da gudu suka fiddosa tsaf dashi ba alamar antabasa ko kayan jikinsa fes suke.

Kallonsa tayi cikin mamaki jin shine abokin fadan usi atake taji haushinsu duk ya kamata ta kalli usi dayasha mugun duka tace'"

Usi uban waye yayi maka wannan dukan?
Ga abokin fadanka nan Babu alamar ko hararsa anyi bare duka.,

Wlh yau saina daukaka qara a kotu akan wannan abin......

Saurin katseta insfector Garba yayi sbd shigowar MD ZABEERA din Wanda qamshinsa yagama kame iskar gurin gabaki daya.

Batareda tajuyoba tace"

Bazanyi shiruba kodai abi Mana haqqinmu kokuma naje kotu wlh bazan yardaba...

Murmushin yaqe insfector Garba yasaki Yana dan satar kallon gefen MD din yace"

Kinga Dan uwanki shine baida gskia shiyasa Kuma Kinga......

Waro manyan idanuwanta tayi akansa cikeda mamaki tana cewa'"

Ni kake fadawa usi ne baida gskia??
To wlh ma nafasa auren naka daga yau ko sunan anguwar mu kakira Garba Allah saina raba aurenka da matarka me kamada bokiti.

Shiru dukkaninsu gurin sukayi musamman insfector Garba din sbd dai duk tagama bude Masa yawa agaban MD ZABEERA Wanda babban mutum da kowa ke matuqar respecting da matuqar karramawa sbd arzikinsa da mugun Jan girma da ajinsa bawai Kuma Dan shekarunsaba  sbd duka duka shekarunsa bazasu fi talatin da buyar zuwa da shida ba aduniya,

Yarone Wanda ake Kira da abokin manya sbd dukkanin abokanan hurdarsa manyane wainda wasu sun haifesa,wasu sunyi jika dashi wasuma sun kusa haihuwar tasa,
A familyn daya fito su din wani babban family ne dasuke da girma da mutunci a idon duniya sbd kamannin kakaninsa da uwayensa Amma a yanzu kusan Rabin qarin girma da mutuntawar dasuke qara samu sbd shine shiyasa ko acikin familyn nasa wainda basa qaunarsa suka fi yawa.

Kasancewarsa baida hayaniya da son shiga sabgoginda Basu shafi Abinda yake gabansaba yasa yake qara shiga ran abokanan harqallarsa Kuma hakan naqara Masa girma shiyasa koina yashiga ake matuqar mutuntasa musamman dayake yana mallakar wata irin tarin dukiyarda ta tsolewa mutane da yawa ido.

Batareda yatsaya bi takan hayaniyarsuba ya kalli insfector Garba da idanuwansa dake cikeda da wani irin kwarjini 
Atake jiki na rawa insfector Garba yace"

Ranka ya Dade Bismillah muje daga cikin office din"  yaqarasa fada Yana basa hanyar shiga office din 
Su Sargent suka Mara masu baya tareda yaron dayazo belin.

Wannan shine karo na farko arayuwarsa daya taba zuwa police station Dan haka bai tsaya Bata lokaciba ya kalli insfector Garba akaro na biyu cikin qosawa da zamansa cikin station din dayakejin kansa harya Fara juyawa ya bude baki cikin nutsuwarsa da kamewarsa datasasu Suma duk shiga nutsuwa yace"

Meye procedures din????

Da sauri insfector Garba yace"

Ba wani procedure sir just take him with u dama mun kamasane abisa rashin sani yanzu da safen Nan labari yazo Mana aishi din yaron amintaccen direbankane Wanda ka dauka kamar uba,
Muma ai tamkar ubane agurinmu 
Ayi hakuri sir munsaka babban mutum kamarka zuwa Nan.

Zuba Masa fararen idanuwansa masu sake rikitarda Insfector Garba yayi Yana nazartar yanda mutanen duniya suke,
Wato Babu wata doka ko adalci shidai me kudi akoyaushe shine me gskia komai yayi daidai ne wat a life.

Miqewa yayi tareda kallon mal aminu dayake kallon 'dansa cikin rauni da takaicin yau sune sukayi sanadin zuwan mutum me matuqar girma da mutunci kamar MAHMOUD DAHEER ZABEERA a irin nan,
Shi mutum ne daya tsani mutanenda suka dauki kudi sune rayuwa
Saigashi a hukuma ma kudin sune dai aka fifita.

Ganin duk sun shige office din insfector Garba dayake shine DPO din Nan dama ana kiransane insfector sbd sunan yabisa tuntuni,
Ta kalli usi da isonsa daya harya kusa liqewa sbd kumburin duka tace'"

To da mutum ya mutu dai gwara yazama biri
Dan haka da Babu gwara ba Dadi tunda sum ringa sun maka wannan dukan gurinsu zamu samu na siyan magani" ta qarasa fada tana zagayowa inda suka saka kudinda suka karba hannunta aikuwa cikin saa taga kudin aikin ranar gaba daya
 wani mugun murmushi tasaki tareda Kai hannu ta kwashe kudin gaba daya Wanda yayi daidai da fitowor MD zabeera cikin office din dpo Garba.
#mamuh#

Pay@
+234 903 234 5899
Or 
09033181070[3/8, 1:22 PM] Zafafa: *_MIN QALB 5_*
_Mamuhgee_


##Zafafa biyar#pay@ 09033181070 or 09032345899 

Usi ne yafara ankarewa dashi yaga yanda qarara idanuwansa da fuskarsa suka nuna tsananin qyama da takaicin Abinda idanuwansa suka gane Masa Nan ya fahimci cewar yarigada ya ganta yayi saurin dauke idanuwansa dga kallonsa yayi sbd tsananin kwarjini da cika masa ido da  yayi yai saurin yin qasa da murya Yana cewa'"

Amah kiyi saurin barin Nan kokuma ki maida kudin.

Batareda ta fahimci Abinda yafadaba ta kallesa tana cewa'' oya yi sauri mutafi nagama ramawa kura aniyarta  anan,
Insfector Garba Kuma zaizo yasameni a gida nasani acan zan fanshe wannan tozarcin dayamin agaban baqonsu da ko kallo bai isheniba bare na tsaya harsu gama kulasaba kafin su dawo kanmu.

Gaba tayi tana zuge zip din Jakarta data saka kudin usi na biyeda ita Yana satar waiwayen baqon dake bayansu fuskarsa a hade ko inda suke bai kallaba ua nufi motarsa Yana duba agogonsa dake nuna Masa lokacin ganawarsa da mahaifinsu yayi gashi shi mutum ne dayake aiki da lokaci komai lokacinsa yake ware Masa sbd tsari dayayiwa rayuwarsa.

Amah ko takan babbar motarsa batabi ba sbd gama quluwa datayi da Abinda Garba yayi Mata.

Usman kuwa suna fitowa tafiya kadan sukayi yaja ya tsaya jikin wata bishiya Yana sauke ajiyar zuciya ya zauna Yana jingina kansa jikin icen ya sake sauke numfashi ya kalleta yana sakin 'yar dariya kamar Babu rauni da tsamin duka a jikinsa yace"

Amah kina ganin akwai ranarda zamuyi rayuwa kamar sauran mutane masu daraja???

murmushi itama ta saki tana kallonsa cikin kulawa da rashin nuna damuwa kafin ta bude Jakarta ta shafo kudin dake ciki tana kallonsu tace"

Bama buqatar wani rayuwa ko gatan daya wuce muyi rayuwarmu ayanda take,
Karka saka wani Rai a wani rayuwan bayan kasan mu din asalin 'yayan bola ne,
Bamuda wani rayuwa bayan Wanda muke ciki a yanxu.

dariya Usi yayi hadi da miqewa tsaye yafara tafiya yana Dan dingyashi  saboda raunin da akai masa a kafa sosai yake masa zugi
 cikin sake quluwa Amah tabi shi da idanuwa tana tunano irin kalar rashin arzikinda zatayiwa Garba.
 
Tafiya sukeyi suna firarsu cikin nishadi sbd su Sam Babu Abinda suke ajiyewa arai ya damesu.


Suna shiga gidan da Aunty Salamatu suka fara cin karo aikuwa ta soma sakin numfarfashin masifa dan Sam bata manta dibar albarkan da Aman tayi Mata ba kafin fitarta,

 Amah na ganin hakan ta fuske ko kallonta batayi ba ma tai wucewarta zuwa dakinsu jakarta ta ajiye hadi da cire karamin hijab dinta ta fito ta nufi qofar dakinsu kawu ta tararda 
 Usi zaune tare da Kawu wanda ke tambayar Usin" wane shegen kurtun Dan sandan ne yayi maka wannan ta'asar???
 
Qwafa yayi Yana taba qafarsa dake Masa zogi yace"

Ai kawu idona idon Sargent salisu saina saka anyi Masa zanen yarbawa har a goshi da qeya,

Shikuma insfector Garba duk Yakuma zuwa gidan Nan gurin amah saina Masa askin kwalba.

Cikin takaici kawu yace"

Shi garban me kama da an sulala naman Kai shine yasa aka maka wannan dukan?  Kokuwa shi Sargent salisu din dayafi kama da danyar alala yayi gaban kansa yayima wannan dukan kamar wanda yayi kisa¿

Maman basiru dake kusa dasu tana aikin wanke rishonta ta tabe baki tana cewa'"

To meya raba dambe da fada¿

Tsuke fuska kawu yayi Yana kallon iyami dake fitowa daki daukeda robar garin tuwo dazata gyara yace"

Iyami kinajin matar nan nafadamin mgn bazakiyi Mata dukanda mijinta ba mijintaba ko yayanta bazasu ganetaba,
Waini iyami kodai auren dole ne mukayi?da kike wulaqantani ne kokuwa talauci haukane?

Dariya usi yasaki Yana cewa'"

Wlh kawu talauci haukane tunda gashinan duk bamuda hankali....

Butarda dake gefenda ya dauka a hasale 
Usin na ganin hakan ya tashi da sauri 
Kawun ya jefasa Masa Bata tsaya koina ba butar sai kan galan din kalanxir din maman basiru Wanda zata zubawa rishon take ya kwanta tana tsiyayewa dama kawun can yayi niyar jefawar ya tsuke fuska yahau masifar usi ya rainasa.

Usu kuwa dariya yake Yana kallon maman basiru dake kallon kalanxir dinta cikin tuquqin zuciya Tama rasa Abinda zata ce musamman ganin fuskar kawun tasan yanxu tana mgn zai Kira mijinta yace suje police ayi musu iyaka Dan aikinsa kenan cewa aje police ayi Masa iyaka da mutum.

Allah ya isana tace cikin ranta tana cewa bakinta yaja Mata saka baki cikin maganar Wanda Basu barin kowa da Allah.

Amah dake kawowa ta kalli maman basiru da idanuwanta sukai rau kamar ta saki ihu sbd takaici ta saki dariya tana cewa'

Iyami wlh karki Bari usi ya rainaki kaman yanda ya Rena kawu.

Kallon Usin iyami tayi tace'"
Kaje ka kimtsa idan kungama Abinda kukeyi kaida kawun,
Wlh usman ka daina biyewa wata fitinar.....

Iyami ki fito fili kice ni basai kin tsaya layi ba.

Nidai yanxu bance kaiba..

Iyami Anya kinason shiga aljanna kuwa?

Amah na ganin haka tasan fadan zasu Fara tayi saurin fiddo da kudin Jakarta take kalmar dake bakin kawu ta katse Yana qoqarin hadata.

Iyami ma aje robar hannunta tayi tana matsowa
Kawu ya bita da harara da qananun idanuwansa masu kama Dana 'yan Korea yace"

Ke amatu maida kudin Nan jaka sai anjima zansan me zaayi dasu tashi tafi daki dasu ki aje.

Kawu albashina ne na karba gurin aiki da niyar belin usi saigashi Basu karba ba sbd rawar jikin sunga wani baqonsu.

Nasani ai dama kedai tashi dasu daga Nan kafin wani ya wafce su.

Fizge jakar iyami tayi tareda cire kudin tana cewa'"

Wlh Babu dakinda zata kaisu Dan nasan ba albashinta bane,
Amatu kifadamin gskia inda Kika samo kudin Nan??

Kallon kawu tayi daya qura Mata ido Yana jiran jin Abinda zata fada saidai yanda tayi da fuska yasa ya fahimci inda kudin suka fito ya gyara zama tareda murzawa idonsa toka ya matse fuska yace"

Iyami so nawa nake fada Miki kidainawa yarinyar Nan haka?
Addua akeyi Allah ya shiryamanasu yabasu abinyi,
Kinga banason kina irin haka saiki tozarta gaban maqiya ga gida cikeda da maqiya komai muke ciki kunnuwan munafukai akanmu.

Kallon takaici tamasa tareda tura kudin cikin zaninta tana cewa'"

Allah yasa kugane yakuma shiryaku ku duka.

Ganin maman junior shugaban munafukan gidan ta shigo yasa ya hadiye maganar dayayi niyyar yi tareda cewa amatu "jeki.

Tana juyowa Ido biyu tayi da maman Junior wacce da alama daga kasuwa take ko dan jakar dake jikinta da uban mayafin data yafo daya gama miqewa da zufa ta dauke Kai ta wuce tana tsokanar junior dake gefen maman daukeda leda dayake yaron mutumintane suna dasawa sosai 
Ko kallon maman taqiyi sbd ganin irin kallon masifar datake binta dashi tareda harara.



***
Bakin Babban gate din ZABEERA motarsa ta tsaya batareda yayi horn masu gadin suka bude Masa da sauri tsananin girmansa dasuke gani fiyeda kowa a gidan idan aka cire iyayen familyn.

Da kansa ya tuqo motar sbd yabar malam take gida da yaronsa suyi sorting matsalar data kaisa hannun 'yansanda harya kwana station.

Sake kallon agogonsa yayi bayan ya kashe motar kafin yafito a nitse ya rufe motar ya nufi doguwar hanyar dazata sadashi da sashen Modibbo wato mahaifinsu.

Tafiyar mintuna hudu ce takaisa shashen Yana tura babbar qofar palon  ummi na fitowa babbar 'yar gaban goshinta nuratu na gefenta kowannensu fuskarsa Babu alamar farin ciki Wanda daga gani ummin ce ke cikin baqin cikin nuratu ke tayata damuwa.

Dattijuwace saidai hutu da tsananin jin Dadi da ilimi tareda gayu yasa shekarun nata sun dai 6oye sbd jikinta dayakeda kyau sosai.

Kallon daya zakayi Mata kasan itace matar gaban goshin me mallakar gidan sbd tsananin Isa da ikon datake nunawa.

Cak ta tsaya bayan ganinsa zuciyarta na qara tafasa da takaici saidai tayi controlling fitowar fushin nata ta kallesa da fararen idanuwanta 

Batareda ya kalli fuskartaba Yana kallon qofa cikin nutsuwar muryarsa data sanya nuratu Dan matsawa gefe tana kama kanta sbd tsananin kwarjininsa yace"

Umme barka da yamma,
Kina lafiya??

Kamalalliyar fuskarsa dake daukeda wani sirrin kyau ta kalla tana danne bacon ranta tace"

KHALIL baya daukan maganata ka fahimtar dashi inason yayi aurene sbd lafiyarsa sbd mganarka kawai zai saurara sbd Kaine ubansa.

Tana fadar hakan ta wuce Bata tsaya jiran Abinda zaice ba sbd tasan ba maganar zaiyiba ko zasu shekara ahaka tasan dai yaji Kuma ya fahimta.

Wannan shine daya daga cikin Abinda ta tsana gamedashi shine tsabar miskilancinsa datake kallo amatsayin ji da Kai ganin yafi dukkanin 'yayan ZABEERA zama successful business tycoon Wanda yake muamala da manyan gwamnati da sarakuna.


Kai tsaye yashiga cikin palon na Modibbo bakinsa na fitarda sallamarda modibbon ne kawai yaji ya amsa sbd sanin yanda mgn ke fitowa abakin 'dan nasa.

Gaban Modibbo din ya zauna tareda dagowa cikin girmamawa yace"

Barka da yamma modibbo,
Ka yini lfy?

Alhmdlh MAHMOUD
Ya iyalin naka??

Alhmdlh"kawai yace tareda kallon 'dan uwansa dake gefensa zaune ya sakar Masa wani qayataccen murmushi Wanda duniya dashi kadaine zakaji yayi doguwar magana ta fira a kaf family haryayimasa murmushi Wanda ko mahaifinsu iyakacinsa dasu bin umarni da biyayya Amma Khalil ne kadai Wanda ke ganin sakewar Mahmud din ciki kuwa harda matarsa wadda iyakacinsa da ita zaman biyayyar aure da bin umarni tareda mutunta juna.

Cikin murmushi Khalil ya kallesa Yana cewa'"

Allah ya taimaki ZABEERA na hudu.

Batareda ya kallesa ba ya murmusa har fararen haqoransa suka bayyana sbd wannan wata zolayace da Khalil din yake Masa tun suna Yara sbd ya tsokanesa musamman yanxu dayasan karban wata sarauta shine Abu na qarshe dazaiyi arayuwarsa sbd ya tsaneta indai akansa ce.

Gyaran murya Modibbo yayi tareda kallonsu suka nutsu tareda maida hankalinsu akansa yasake gyara murya cikin bada umarni da hukuntarwa yace"

Mahmud safiyar yau ZABEERA ya aiko da saqon a sanar dakai waadin mallakar kujerarka ta ZABEERA na hudu Dana bayarda sunanka yacika
Zaka shirya komawa masarauta tareda iyalinka.

A matsayin mummanan sako ya dauki zancen sbd zuciyarsa da Bata karbi abinba ko da a mafarki  saidai Kuma Sam fuskarsa Bata nuna alamar gamsuwa ki rashinta Khalil kawai ne zai qarar da cewa wannan ba Abu bane me yiyuwa a rayuwar md zabeera din.

Cikin girmamawa yace"

Modibbo idan naje Naga ZABEERA akan wannan alamarin Ina fatan bazan 6ata maka ba???

Kallonsa Modibbo yayi na tsawon sakanni kafin yace"

Idan har kana tunanin sanarda mahaifina ne cewa baka karba saqonsa ba tabbas zaka Sa6a ne.

Cikin sake nuna biyayyarsa yace"

Inshallah ba hakan bane.

Karka damu zakaje Amma sai ranar tafiyarka gaba daya.

Shiru yayi na Dan lokaci kafin ya miqe tareda cewa'"

A yini lfy Modibbo.

Ficewa yayi Khalil na biye dashi suna fitowa ganin yanayinsa yasa Khalil barinsa yaje yasamu nutsuwa tukuna duk da Babu Abinda ya nuna na damuwa ataredashi.

Motarsa yaja ya qarasa sashen dayake can kusan qarshen babban gidan Wanda yake nasa yanayin parking yafito yashige.

ZARAH dake zaune palon tareda me aikinta ta dago Kai tana ganinsa ta ajiye wuqar datake yanka gwaiba da ita ta miqe tareda qarasowa gabansa tana Masa sannu da zuwa cikin nutsuwa daidai shigewarsa hanyar dazata sadashi da zuwa sama inda dakinda yake ya amsa Mata da madaidaicin sauti sbd Bata iya wulaqanta ta sbd darajar sure dakuma biyayyarta tareda darajar Modibbo daya aura Masa ita.

Ganin yanda ta taso din Dan kulawa yasa yadan tsaya tareda kallonta cikin Ido sosai Yana qoqarin Bata mahimmanci yace"

Ina buqatan light abinci Mara nauyi.

Murmushin qara ganin girmansa tasaki sbd yanda akoyaushe yake mutunta zamanta matarsa har kaqoranta suka bayyana ta matsosa sosai tareda kama hannun damansa ahankali ta riqe cikin nata ta dago ta kalli fuskarsa da ya juyo ya kalleta tace'"

Thank you MD ZABEERA.

Kallonta yayi yace"

Ina jira""ya haye saman tana binsa da kallon kauna fuskarta cikeda murmushi kafin tajuya ta nufi hanyar kicin tana cewa'"

Hafsat zo ki niqamun kayan Miya a blender.



**
Umme tunda Takoma palonta ta zauna tana sauke numfashi tanason saukar da zuciyarta ga wannan al'amarinda yake faruwa da ita ako yaushe.,
'yayanta kusan sune koma baya a cikin familyn ZABEERA,
Dukkanin 'yayan Modibbo matane su goma sha shida Khalil da Mahmud ne kawai maza Kuma sune dukkanin wani burin Modibbo ya Dora akansu sai gashi ita nata 'dan shine wani iri Sam ko kyashin 'dan uwansa bayayi duk da Shima Barr ne babba me zaman kansa Kuma yanada nasa arzikin daya Tara bana mahaifinsu ba Amma Sam bai kamo MAHMOUD ba Wanda duniya shi kowa yafi sani a familyn ZABEERA yanzu.

Burinta idan har MAHMOUD yafi Khalil ta wani bangaren to shi zai karbi zabeera na hudu ta yanda zai take MAHMOUD din ta fagen suna,arziki,mulki,dakuma martaba a idanun mutane saigashi Rana tsaka su Modibbo da zabeera sun zaba MAHMOUD Wanda Sam bazata yardaba.

Kamar daga sama taji daga bayanta ance"

Aisha wannan karon damar kice ta qarshe kisa Khalil yayi aure ko su  Modibbo zasu sauya shawara su zabesa sbd shi wancan miskilin baya buqatar kujerar zabeera,
Duk wani suna ko arziki ko girmanda ake buqata ya samu abinsa da kansa amatsayinsa na Architecture MD ZABEERA so yanzu zabi ya rage naki na kisan yanda zakiyi.

MD bayada uwa a duniya bayada dangin uwa a duniya to kina tunanin idan yazamo zabeera na hudu waye zai nuna Miki iyakarki idanba zainab uwar matarsa ba wadda ko kadan kinsan Bata qaunarki.

Rintse ido ummen tayi tana jinjina 'dacin da zuciyarta keyi da zafi tace'"

Babu Abinda yakai ciwon hassada zafi a zuciya wlh Maryam,
Tun kafin MAHMOUD yazo duniya bandamu da uwarsa ba harta haifesa ga bar duniya bantaba kulawa dashiba duk da tsananin biyayyar dayakemin Amma tunda yafara zama wani abu a rayuwa Abu yazo ya dameni wannan masifa dame tayi Kama wlh zuciyata takasa samun nutsuwa shawon shekarun cigabansa
Amma wannan karon zanyi Abinda bantaba yiba.

Dawowa gabanta haj Maryam tayi tareda zama kusada kejerar dake kallonta tace'"

Me kenan???

Miqewa tayi tsaye tana takawa ahankali tace'"

A duniya Babu Abinda Modibbo da zabeera suka tsana irin cin Amana da zubarda mutunci,
Zansa su tsanesa tsana mafi Muni wadda zatasa sunansa yafita daga cikin zabeera bama zabeera kawaiba duk duniya ma saisunji yafita ransu sundaina ganin mutuncinsa.

Murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana cewa'"

Wane laifi?
Wane cin Amana Kuma???

Laifin ciki
Da laifin zubarda mutunci ta hanyar aikata 6anna.

Wani murmushin haj Maryam tasaki tana cewa'"

To waye yayiwa cikin ni ki fahimtar Dani yanda zangane.

Baiyiwa kowa cikiba Amma kudi zasusa ace yayi cikin.


Aisha kina tunanin akwai Wanda kudi zasusa tace MD yamata ciki karki manta MD mutuminda kowa ke mutuntawane wannan maganar bamai karbuwa bace mu canza shawara.

Maryam kudi duk inda kike tunanin su sun wuce Nan,
Akwai mutane birjik a duniyar Nan dazasuyi aikin komai sbd kudi musamman kudi irin wainda zan zubar akan wannan aikin.






No comments

Powered by Blogger.