Saran Boye 11-15

 

No. 11

________________________

*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* 


       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida

kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*


___________________


   ................Kamar bazata juyaba sai zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncine shiɗin, 

       Abun mamaki babu kowa a wajen,  sai dai an sauke glass ɗin motar kaɗan alamar tanan koma wanene ya isar da saƙon nashi. Jitai zuciyarta ta sake hawa sama fiye da da. Ta yunƙura da nufin nufar motar gayun nan suka sake mata zobe. Kallonsu tai sama da ƙasa a wulaƙance da faɗin, “Wlhy idan baku matsamin ba ɗaya bayan ɗaya saina muku fashin goshi da dutsen nan”.

    Babu wanda ya motsa a cikinsu, da alama ma basa fahimtar yaren datai maganar, dan kallonta kawai suke tamkar wasu zakaru. Dutsenta da har yanzu ke a hannu ta sake ɗagawa zata bugama wani again. Da sauri yay baya da ɗana kunamar bindigarsa yana huci. Nu'aymah ta taɓe baki tamkar bata fahimci abinda yake shirin yiba, ta sake ɗaga dutsenta ta makama na gefen hannun haggunta a goshi cikin rashin tsamanin hakan daga garesa.

     Ƙara ya saki da duƙewa ƙasa bindigarsa na faɗuwa dan abun yazo masa a bazata, babu yanda za'ay kai tunanin shiɗin zata bugamawa. Ƙafa ɗaya daga ciki ya saka ya taɗeta tai baya zata faɗi cikin security ɗin gidan marayun da suka iso yanzun wajen yay saurin tareta. Ai tanajin bata kai ƙasaba tai wani irin ɗagowa da sauri ta wulwula dutsin nata sai akan motarnan dai ta ɗazun data fasama glass, kuma a gaba ya sauka, dan haka glass ɗin ya ƙara tsatstsagewa fiye da ɗazun.

         A yanzunkam bodyguards ɗinsa sun tabbatar bazasu iya haƙura da tsagerancin yarinyarnanba, sai sun ɗauki mataki duk da ogansu bai basu damar yin hakan ba. Hannu ɗaya daga ciki ya ɗaga zai kwasheta da mari iya ƙarfinsa, sai dai ganin za'a buɗe ƙofar motar ne ya sakashi dakatawa da nufar motar da sauri ya ƙarasa buɗewa yana saurin cewa, “Sorry Sir”..

           Banji an amsashi ba, sai dai motsin da naga anyi daga cikin motar ya bani tabbacin wanda ke a ciki zai fitone. Ba Nu'aymah kaɗai ba, harsu Yusrah sun zuba idone suga mai fitowar.

        Ƙafarsa dake cikin baƙin takalmi mai shegen ƙyau ta fara bayyana, kafin farin wandonsa. A hankali ya dire sandarsa ƙasa itama tare da ɗayar ƙafarsa ya fito gaba ɗayansa. 

     Koni mai ɗaukar rahoto saida na furta ‘masha ALLAH’ a zuciyata. Zuƙar iskar yammaci data fara kaɗawa yay a hankali cikin hancinsa ya fesar yana sake tamke farar fuskarsa dake zagaye da baƙin gashin saje siɗik, dan a rayuwarsa ya tsani kallo. Baiko kalli ko sashen dasu Nu'aymah da guards ɗinsa sukeba ya nufi inda su Nanah suka rufu kan yaron tare da securitys ɗin gidan marayun. Hannun Malika dake a saitinsa ya kama ya matsar da ita gefe, hakanne ya sakasu farga da isowarsa duk suka dawo cikin hankalinsu daga kallon ƙurullar da suke masa. Baice dasu uffanba yay wani ɗan dirƙuson gayu gaban yaron tare da kai yatsunsa biyu saitin hancinsa, yakai kusan sakan goma kafin ya janye, sai kuma ya maida kan jijiyar wuyansa dake a saitin kunne. Nanma ya kwashe sakan goma da ɗoriya sannan ya ɗauke. Miƙewa yay tsaye, idanunsa dake cikin baƙin glasess akan ƙaton symbol ɗin da aka rubuta sunan gidan marayun, kafin ya janye ya maida dubansa ga guards ɗinsa da har yanzu suke zagaye da Nu'aymah kamar wata ɓarauniyarsu. Da hannu yay musu nunin su barta, tare da yin wani salo da yatsunsa biyu wanda shi da su ne kawai sukasan ma'anar yaran nasa.

    Cike da takaicin rashin ɗaukar mataki a kanta sukaja baya kowanne na zuba mata harara a ƙasan ido da huro hanci. Gaba ɗayansu garesa suka nufo. Ɗaya daga ciki ya matso sosai inda yake, A hankali ya furta maganar da babu wanda ya iya jinta a cikinsu Nu'aymah, dan kuwa jajayen laɓɓansa ne kawai suka motsa kaɗan.  Ganin haka ya saka Nu'aymah nufosu da sauri itama. Yana ɗaga ƙafarsa zai bar wajen tana isowa tasha gabansa.

      “Kai malam dakata mana! Shin babu zuciyane a ƙirjinka kokuwa kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?”.

        Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin glasess ɗinsa, batare da yama nuna alamar ya fahimci yaren da take maganar da shiba ya raɓata zai wuce abinsa. Hanzarin riƙo sandarsa tai ƙoƙarin yi Yusrah ta riƙeta. Cikin magana raɗa-raɗa tace, “Aymah calm down Please, kalla kiga”.

       Sai da ta zubama bayansa harara kafin ta kalli abinda Yusrah ke nuna mata. Securitys ɗin gidan marayun ne tare da guards ɗin nasa uku dasu Nanah ta hango harsun kusa shigewa cikin Orphanage ɗin ɗauke da yaron a hannun ɗaya daga cikin guards ɗinsa. Juyawa tai da sauri ta kalli inda yake shima sai ganin motocin uku tai har sunyi reverse suma da alama gidan marayun zasu shiga.

             “Zuciyarki tayi sanyi ko? Iya masifa! ALLAH wataran sai kinsa an maidamu kwalta Nu'aymah, jibesu tamkar wasu bajiman zakuna su da ogan nasu. Da ganinsu kasan ba hausawa baneba ma, ke koma tsoro baƙyaji”. 

        “Mtsoww! Ina ruwana da rashin kasancewarsu Hausawa, inda banyi musu hakanba ai guduwa zasuyi dan tsabar rashin sanin darajar ɗan adam. Ko dabba suka bige ai ta cancanci su fito suga lafiyarta balle mutum, shegu masu suffar baƙaƙen aljanu”.

      Dariya Yusrah ta kwashe da ita tana faɗin, “Amma dai banda wannan Handsome ogan nasu ko? Dan wlhy dai kam komai yaji zammm anan kema kin sani”.

        “Ke kikaga wannan”. Nu'aymah ta bata amsa tana fisge hannunta dake cikin na Yusrahn ta tsallaka titi ta barta tana dariya. Dan ta kula bori kawai Nu'aymah keyi itama tasan gayen ya haɗu masha ALLAH, sai dai yanayinsa sam bai mata kama dana Musulmai ba, dan askin kansa kawai da ƙaton sarƙan Cross na diamond dake a wuyansa, da ɗan kunne guda ɗaya manne a kunnensa ya isa amsar hakan a garesu.

      Hango Nu'aymah har zata shige cikin Orphanage ya sakata saurin tsallaka titin itama ganin babu mota tabi bayanta.


       Nu'aymah da har yanzu keta faman jan tsakin takaicin mutanen ta nufi clinic ɗin gidan kanta tsaye, tasan dai bazai wuce can suka nufa da yaron ba. Kasancewar tafiyar tata sai a hankali, ba wani sauri ta iyaba kuma akwai tazara tsakanin gate ɗinma da clinic ɗin saiga Yusrah harta isketa. A tare suka ƙarasa batare data kula Yusrah daketa son taga ta sakko ba. Tsaitsaye suka iske su Nanah a reception da guards ɗin mutumin, sai bah-bah hindatu ɗaya daga cikin masu kula da yaran, da kuma Abban Adawiya da ashe tun ɗazun yana a cikin gidan marayun su Nu'aymah basu saniba.

      Waige-waigen inda zataga gayen ta farayi, sai dai babu ko mai kama da shi a wajen. Wani takaicine ya sake dirar mata a zuciya, cikin ranta ta ayyana ‘Wato shi yamafi ƙarfin shigowa kenan? To ai idan yasan wata baisan wataba’. Ta nufi hanyar fita tana surutunta a zuciya.

     Yusrah da tunaninta ya bata Nu'aymah zata iya zuwa ta sakemusu ɓarna a motoci tai saurin riƙo hannunta tana faɗin, “Ina kuma zakije?”.

          “Yusrah sakeni, bakiga wannan mai shegen taurin kan bai biyosu ba”. “Oh ALLAH, to minene idan bai shigo ɗinba, baga guards ɗinsaba, nasan ai zasu wakilcesa. Ki tunafa ba shine ya buge yaron ba ma, cikin guards ɗin nasane tunda shi yana a motar tsakkiyane, sannan ba shinefa ke tuƙinba”.

         “Wannan matsalarsace kuma, ai wanda ya bige ɗin dai yaronsane ko? To ya zama dole shina ya kasance a wajen wlhy dan ya ja masa matsala”.

       Kafin Yusrah ta samu damar mata magana sai gashi ya fito daga ɗaya a cikin ɗakunan clinic ɗin, Dr Safwan biye da shi a baya, taku yake cike da nutsuwa irinta zaratan samari masuji da lokacin ƙuruciya da kwanciyar hankali. Handglop ɗin dake a hannunsa taga yana zarewa ya jefa cikin shara. Har yanzun dai idanun nasa a toshe suke da Google ɗin, kuma fuskar a tamke, tana ƙoƙarin janye idanunta daga kallon nasa caraf suka sauka bisa kan ƙatuwar sarƙar Cross ɗinsa da aɗazun masifa baisa ta ganta ba.

      Cikin suɓutar baki tace, “Ashe Arne ne shiyyasa baida imani”. 

     Karaf wannan magana a kunnensa. Sai dai yanza yazo ya gittata ya barta da ƙamshin turarensa mai sanyin daɗi batarr da ko kallon inda takeba ne, zaka fahimci da wahala ace yamaji mitace, maybe ma bayajin hausar sam. 

          Wajen Abbah dake zaune ya ƙarasa, suna ɗan nesa dasu kaɗan shiyyasa bazasu iya jin mi suke faɗa ba. Ta taɓe baki da nufar Dr Safwan tana tambayarsa yaya jikin yaron?.

       “Jikinsa Alhmdllh, ai bama wani ciwo yaji sosai ba, yadai bugune a kansa da hannunsa na haggu, insha ALLAH kuma fatan komai zaiyi normal da wuri”.

      Duk da taji daɗin hakan sai bataji ranta ya huce daga haushin mutuminda ita kanta shaidace tasan ba shine ya aikata laifin ba. ‘Amma kuma ai ogan wanda ya aikata ɗinne’ ta raya a cikin ranta cike da gamsuwa da jawabin zuciyarta.

         Ɗakin da yaron yake kwance suka nufa suka dubashi duk da ansa masa ruwa barci ya ɗaukesa. Lokacin da suka fito basu iske mutanenba har motocinsu. Hakan ya bama Nu'aymah tabbacin sun wuce kenan.

         Suma nufar hostel ɗin yaran sukai suna sake tattauna abinda ya faru, tare da yin gulmar mutumin dako sunansa basu saniba. Nu'aymah dai uffan bata cewa, dan ita takaicima suke ƙara mata a kanshi kawai.

        

                 


_______________________


        Tunda suka baro cikin Orphanage ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yay shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe. Sai faman juya glasess ɗinsa dake a hannunsa na dama yake tamkar zai karyasa. Gaba ɗaya abinda ya farune ke dawo masa cikin zuciya daki-daki. Ya yarda yaran Arewan nan basajin magana tamkar yanda yakeji ana shan faɗa. Jibafa yanda ƴar yarinya ƙarama sa'ar ƙanwarsa Victoria ta tsaya agaban bindiga tana musu raini tamkar wasu sa'anninta. A karan farko yaja ƙaramin tsaki da furzar da iskar daya cika baki da ita yana maijin takaicin komai a ransa. A hankali ya buɗe idanunsa ya kai dubansa ga glass ɗin gaban motar tasa da Papansa yasa maƙudan kuɗi wajen siya masa. Yau shine hawansa na farko da motarma gaba ɗaya, dan sati biyu da suka wuce papa ya bashi ita a birthday ɗinsa matsayin gift. Amma sai gashi cikin sakanni an mata walmakalifatu, kamar Mom tasan hakan zai faru tace bata yarda yazo kano a mota ba daga Abuja, shi kuma gashi yanada uzirin da bazai yuwu ya fasa tafiyarba, dan dama zaibi jirgine kamar yanda ya saba sai akace jirgi bazai tashiba dan yanayi babu ƙyau yau. Shinefa ya zaɓi tahowa a mota duk da Mom bataso hakanba. Sake rumtse idanunsa yay da shegen ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa sosai tamkar zai hudashi da haƙori.

        Duk abinda ya keyi drivernsa na kula ta cikin mirror, hakanne ya saka zuciyarsa sake zafafa da abinda yarinyar tai musu shima, ya kai hannu ya shafa inda Nu'aymah tai masa rotse da dutse aka saka masa bandage, wlhy yau badan oga ya hanasu ba da yarinyarnan saidai uwarta ta haifa wata. Shiyyasa shifa a rayuwarsa yay mugun tsanar ƴan Arewa ɗin nan musamman hausawa, ƙauyawa dasu ko karatu basayi sai rashin mutunci. (Humm malam driver naka tunanin kenan, amma ƴan Arewa sun wuce da sanin duk wani gurɓataccen tunaninka ai🙄😏). Shi yanzu babban tashin hankalinsa ma mi zasuce da Madam ɗinsu akan wannan al'amarin daya faru?, dan kowa yasan yanda family ɗin gaba ɗaya ke masifar so da ƙaunar ogan nasu tamkar wani tsoka ɗaya a miya.

      Haka dai suka cigaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai. Gashi mahaukacin gudu sukeyi kai kace Lagos suka nufa ba Abuja ba.

       Tunda 6pm tayi kiran Mom ya fara shigowa a wayarsa, sai dai ko sau ɗaya bai amsa mataba ya share, sai ma kwanciya daya gyara cikin lallausar kujerar motar ya cigaba da latse-latsen laptop ɗinsa har yanzu da takaicin Nu'aymah a ransa.


*_ABUJA_*


          *_09:30pm_*  Dai-dai suka shiga garin Abuja saboda holdup daya riƙesu a madalla zuwa Kubwa expres, da ƙyar suka fita a jigace, dan kafin su iso Asokoro ji yay tamjar ya fasa ihu dan gajiya, shi dama can mutum ne da baida jimirin tafiya mai nisa a mota, duk da tafiye-tafiye sun kasance cikin ginshiƙin aikinsa kuwa.

         Anguwace da bata da maraba da a cikin turai saboda rashin hayaniya da haɗuwarta. Ko ina ƙwanyar yake da wutar nepa tamkar rana, duk da dare baiyi nisaba babu abinda kakeji sai haushin karnuka. Motocin uku suka tsaya dai-dai saitin wani ƙaton baƙin gate da zaka iya hango cikin gidan daga waje kasancewarsa tamkar net. Horn sukai, da gudu sai ga wani dake cikin Blue Uniform ya iso da sauri ya buɗe musu.

     Tunkan su gama dai-daita parking idanunsu suka sauka akan Madam Chioma dake ta faman kai kawo ta barandar saman bene. Sai dai ganin shigowar motocin tuni tabar wajen da alama zata fitone.

       Tuni Securitys ɗin gidan kusan su goma sha biyar suma sukayoma motar caaa. Buɗe masa akai da sauri, sai dai kafin ya fito Madam Chioma harta iso. Da kanta tasa hannu ta fiddosa a motar, tai saurin rungumesa tana magana cikin yarensu. “Yarona miya sameka? Ina kuka tsaya? Miyasa kaki ɗaga kiranmu?”. tashiga jero masa tambayoyin batare data bashi damar amsa ko guda ɗaya ba daga ciki. 

           “Relax Maa! i'm okay”. “Ka tabbatar?”. Ta faɗa tana ɗagosa daga jikinta hannayenta duka biyu akan kwantaccen sajensa tana shafawa, sai kuma tabi jikinsa da kallo daga sama har ƙasa. Ganinsa dai lafiya lau saita sake rungumesa tana faɗin, “Thanks God”.

           “Ɗan uwa sannu da zuwa”. Wata murya ta faɗa daga bayansu cikin harshen nasara. Sakinsa Madam Chioma tai suka juya suna kallon mai maganar. Matashin saurayine da bazai wuce 22years ba, sai kuma wasu dake bayansa su kusan bakwai. Kallonsu yay ɗaya bayan ɗaya kafin ya buɗe masu hannayensa sukazo duk suka rungumesa suma suna masa sannu da zuwan. Sai da duk suka gama sannan ya amsa musu da “Thanks you”. a jimlace.

      Har sun nufi babbar ƙofar shiga ainahin cikin gidan ɗaya daga cikin yaran cikin harshen turanci tace, “Jesus!! Miya faru da motarka Brother?!”.

     A tare duk suka juya suna kallon motar, amma banda shi dama yay gaba abinsa tamkar baiji mi Joy ɗin ta faɗa ba.

       Cike da firgici Madam Chioma ta shiga ƙwala kiran sunan guards ɗinsa ɗaya bayan ɗaya. Aiko jikinsu har rawa yake suka nufota ransu cike da tsoron amsar da zasu bata akan abinda sukasan dole su amsa tambayoyinsa dama.

          Aiko a jajjere ta shiga jero musu tambayoyin ko bari su bada amsa batayi. Sai da ɗaya a cikin yaran da zatama iya kai sa'ansa tace, “Mom ki shiru haka mana su bamu amsar miya faru?”. Zata sake magana budurwar tai saurin sake faɗin, “Please Mom”. Shiru tayi badan taso hakanba. Ta maida hankali ga guards ɗin da saima yanzune ta kula da masu fasashshen goshi biyu a cikinsu. Babban ne ya shiga mata bayanin duk abinda ya faru tsakanunsu dasu Nu'aymah daga farko har ƙarshe. A take takaici da baƙin ciki suka sake rufeta ta shiga zagin Hausawa da kiransu da sunaye marasa daɗin ji. Sai da tayi iya iyawarta kafin ta bar wajen tabi bayansa. Suma sauran yaran bayan nata sukabi suna zagi.


        Shikam yana shiga ƙaton babban falon gidan dake ɗauke da set ɗin kujeru biyu mabanbanta kala baiko tsaya ba yay saurin hayewa sama inda sashensa yake. Baya buƙatar kowa ya biyosa, dan haka yay saurin maida ƙofar corridor ɗin sashen nasa ya rufe, sannan ya ƙarasa nasa madaidaicin falon daya gama haɗuwa, yanata wani tattausan ƙamshi mai daɗin shaƙa da kwantar da zuciya. murza ma ƙifar falon key yayi sau biyu sannan ya shige. dispencer dake acan gefen dining mai ɗauke da madaidaicin d/table ya nufa, ya ɗauki glass cup dake cikin wani showglass mai ƙyau da ɗaukar hankali ya matsi ruwa. Tas ya shanye wanda ya ɗiban, ya ajiye kofin saman d/table ɗin ya baro wajen zuwa wata ƙofa dake a cikin falon. Nan ɗinma dai corridor ne, sai dai ƙofa biyu ce kawai a cikinsa, ƙofar ƙarshe ya nufa yana zame baƙar jacket ɗin jinsa tunkan ya buɗe. Ya riƙeta a hannu ɗaya sannan ya ƙarasa ya murda handle ɗin ƙofar ya tura ya shiga.

       Fes ɗakin yake shima, yanata tashin ƙamshin fresheners data haɗe da turaren da yake amfani da shi. Jefa jacket ɗin yay saman gadon ya ƙarasa gaban mirror yana ƙoƙarin cire sarƙar cross ɗin wuyansa. Ya ratayeta jikin wani ɗan hangar ƙarami mai ƙyau dake cike da sarƙoƙin kala-kala a  ajiye saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban madubin yanata faman yamutse fuska dan yunwa yakeji, sai da ya cire takalman ƙafarsa da safar, farar ƙafarsa dake fes ta bayyana kafin ya miƙe kansa tsaye ya nufi wata ƙofar da ko ba'a faɗaba kasan toilet ne.

     Yana shiga aka fara knocking ƙofar falonsa, amma sai ya share ya cigaba da abinda yake a ciki. Anyi kusan sau uku sannan aka bari. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe Milk color. Hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana tsane sumar kansa da kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tana masifar lasar kuɗaɗe kodan ƙyawun da take dashi ga mai kallo a ido balle kuma wanda ya taɓa.

         “Yoohan! Buɗe min ƙofa”. Ya tsinkayo muryar Mom tana faɗa cikin yarensu da ɗan buga ƙofar yanda tasan bazai takurasa ba. Gefe ya karyar da wuyansa yana yamutsa fuska da yarfar da hannayensa duka alamar shifa an takura masa. Fuskarsa cike da takaici yaje ya buɗe mata tare da juyowa a binsa batare da ya tsaya saurarenta ba.

     Ƴar dariya tayi abinta, dan ko kaɗan hakan bai dametaba, tasan ya gajine matuƙa, shikuma idan ya gaji to lallai sannan baƙin ransa ke ƙara hauhawa, kowa kuma yimawa yakeyi har ita da Papa. Ƙarasawa tai inda yake tsaye a gaban mirror yana cigaba da tsane kansa. Kama hannunsa tai ta zaunar, ta amshi towel ɗin ta cigaba da goge masa kan tana kallonsa ta cikin mirror fuskarta washe da murmushi.

     Shiko ya ciskule tasa kamar zai fasa ihu. Sai da ta tsane masa kan tas kafin tajawo hand dryer ta jona a jikin soket ta fara busar masa da shi. Ajiye dryer ɗin tayi da jan hancinsa tana faɗin, “Nasan wannan fushin bana komai bane sai yunwa da gajiya my boy. Taso kaje kaci abinci ka kwanta ka huta”. Tai maganar da turanci

          Yana shirin miƙewa danya shirya akai knocking ƙofar, jiyay tamkar ya fasa ihu dan takaici, shiyyasa sam bayason zaman gidan nan wani lokacin, dan ana hanama rayuwarsa shaƙatawa da hutawa. A hakanma gwara nan, abinda yafi tsana shine zuwa ƙauyensu, dan anfi cika masa ciki da takaici acan fiyema da nan Abuja. Mom ce tai magana, shiko tuni ya miƙe ya koma wajen kayansa. Ɗaya daga cikin ƙannensa ce mai suna Victoria. Tarkacen kayansa ne daya bari a mota cikin guards nasa ya kawo tun ɗazun, shine yayta masa knocking lokacin daya shiga bayi, da yaji ba'a buɗeba ya koma dasu ya bama yaran akan idan ya fito saisu kawo masa.

          Zubesu tai akan table ɗin gaban gadon, ta juya garesa zatai magana ya ɗaga mata hannu da sauri tare da nuna mata ƙofar fita. Baki ta kumbura ta juya ta kalli Mom nasu dake murmushi sannan ta fice tana buga ƙafafu da ƙananun kukan taɓara.

      Miƙewa Madam Chioma tayi itama tana faɗin, “Ina jiranka kai maza ka fito”. Kansa kawai ya ɗaga mata ya cigaba da abinda yakeyi...........✍



Read more har bakwai yau?.😳😵😓🚶🏻.


No. 12


________________________

*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* 


       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*


___________________


................Sai da ya kammala ƙalular shirinsa cikin kayan barci wando 3quarter da riga Armless sannan ya zura slippers masu taushi ya fita. Kusan su shidda ya iske a falon kowa da hidimar da yakeyi. Wasu kallo wasu danna waya wasu surutu.

     Da sauri Miracle ta ɗauki remote ta rage ƙarar television ɗin dan tasan ya tsani hakan. Shikam baimabi takan kowaba ya nufi d/table. Kafin ya ƙarasa Miracle ta rigashi isa, yana ɗaura hannunsa saman kujera zai jata baya ta ɗora nata akan nashi. A take fuskarsa ta sake tsukewa, ya ɗago fararen idanunsa ya zuba mata wani banzan kallo. Maimakon ta janye hannun saita kashe masa ido ɗaya tana murzawa a hankali. Kallon hannun yayi cike da tsantsar fushi. Duk da tsoronsa dana yanayinsa a yanzu ke ratsata bata fasaba, saima karta zaƙo-zaƙon faratan ta ta farayi tana matsawa da hannunta gaba akan nashin cike da salon iskanci.

          Ita da kujerar ya haɗa ya wancakalar gefe, kafin takai ƙasa ya bita da halbi, sai gata ƙasa wanwar. Ƙarar data firgita kowa a gidan ta ƙwalla tana faman ihu kamar wadda aka yanka. Dukansu kanta sukayo, yayinda Yoohan ya sake ɗaga hannu zai ƙwaɗa mata mari Gebrail ƙaninsa yay saurin riƙesa, fisgewa yay yayi ƙwallo da kujerar kusa da shi ta dining ɗin ya juya fuuu kamar wani kumurci ya nufi sama. Da sauri Mom data fito daga wani ƙofa yanzu saboda jiyo ihun Mira ta shiga ƙwala masa kira da turanci. “Yoohan! Yoohan!! Yi hakuri zo kaci abinci”.

      Baiko waiwayeba balle tai tunanin samun amsa. Da gudu ta bisa tana haɗa steps ɗin da bibbiyu. Kafin ta ƙarasa har ya tura ƙofar ya maida ya rufe. Bugawa Mom ta shigayi tana kiransa cike da lallashi “Yoohan! yi haƙuri kaji, kar kayi fushi zo kaci abinci Please”. Duk da yaransu take maganar, amma yaƙi buɗe mata. Shi tunima yabar jikin ƙofar harya shige bedroom ɗinsa.

        Zuciyarsa cike da matsanancin ƙunci ya faɗa saman gadonsa ya kwanta a rufda ciki. Ji yake gaba ɗaya duniyar ta masa masifar ɗaci, yaja filo ya danne kansa da shi da ƙarfi.


      A falo kam Mom data sakko a ranta a ƙuntace ta ƙarasa inda Mira ke faman kuka har yanzu, cikin faɗa tace, “Miracle bance ki fita hanyar Yoohan bane? Kin riga da kinsan halinsa baya son wannan banzan halayar amma ke kam bazaki kama kankiba. Ki cigaba, wataran idan ya karyaki ko ya miki mugun dukan da za'a gaza ganeki zaki kiyayesa ai”. Batare da ta saurari amsa daga Mira ba ta wuce ɗakinta cikin fushi itama, dan a rayuwarta ta mugun tsanar ganin an ɓatama Yoohan rai a gidan. Tana masifar son yaronta fiye da sauran ƴaƴanta.

          Kuka Mira ta sake ɓarkewa da shi iya ƙarfinta su Joy na lallashinta, da ƙyar suka iya ɗagata dan tanada jiki sosai bawai siririya bace, sannan a shekaru sai dai suyi sa'anni ma da Gebrail ƙanin Yoohan ɗin. 

      Da taimakon su Joy Miracle taje ɗakinta, sai da suka kwantar da ita a gado Gebrail ya kalleta shima cike da takaicinta. “Mira idan baki fita hanyar Brother ba na tabbatar shine zai maidaki gurguwa kafin ki koma gidanku, nasha faɗa miki shifa a rayuwarsa yanda ya tsani shan giya haka ya tsani harka da mata. Wanda yay kashi biyu cikin ukun rayuwarsa a turai matan can basu sakashi ya iskance ba ta yaya kike tunanin ke ƙaramar ƙwaruwar Najeriya zata iya sakashi aikatawa? Ƙilama dakin kama kankine zai soki kamar yanda kikai fata, amma a haka ina tabbatar miki tsanarki yake ƙarayi dan baya ɗaukar lamarin ta fuskar soyayya, idan kinji shawarata sai ki kiyaye”. Yana gama faɗa ya juya yay ficewarsa, kafin duk suma sauran su fito a barta daga ita sai Joy da take kusan sa'arta itama. Dan twins ne ita da Gebrail ɗin. Hawayenta ta share tana danna ƙafarta data buge, da yarensu tace, “Joy wai miyasa Brother ɗinku bashi da kirki?, gashi duk iskancin da wulaƙancin da yakema mutane su Mom sai sudinga goya masa baya basa son ɓacin ransa, kamar sunajin tsoronsa ma......” da sauri Joy ta rufema Miracle baki da hannu tana girgiza mata kai, sai da ta tabbatar tayi shiru kafin ta saketa, ƙofa ta nufa da sauri ta leƙa, ganin babu kowa saita maida ta rufe sannan ta dawo wajen Miracle ɗin. Daf da ita ta zauna cikin magana raɗa-raɗa tace, “Ni kaina na daɗe inason yin maganarnan da Wani Mira, kinga dai su Mom duk su suka haifemu, amma idan kika lura sunfi son Brother Yoohan, ko yaya suka gansa a damuwa sai kiga sun rikice, sannan duk abinda yakeso shi ake masa. Kiga dai yanda kike sonsa yana wulaƙantaki a gidan nan amma basu taɓa nuna masa rashin dai-dai akan hakan ba. Kowafa tsoronsa yakeji anan gidan har Mom ɗin”. Mira dake sauraren Joy kamar mai ɗaukar karatu tace, “Yayi kuɗi ne shiyyasa ai”. Kai Joy ta girgiza mata da faɗin, “Sam ba haka bane Mira, ki tuna tuntuni suke masa wannan gatan na fitar hankali, makaranta saida ya zaɓa ya darje mai mugun tsada a ƙasar waje, har sai da ya cika burinsa na zama babban likitan da yakema duniya aiki bama Najeriya kaɗaiba, amma kina gani ni da Gebrail a 9ja muka fara karatunmu, sai yanzune da shi yace zai fita damu sannanfa suka yarda”. “Hakane Joy. to ammafa kinsan Yoohan yanada bala'in ƙwaƙwalwa, dan sister Divine tace min sanda suna primary yafi kowa hazaƙa da ƙoƙari a ajinsu, yanzu za'a karanta masa yanzu zai ɗaukesa a kai. Ni yanda ya tsaya yay karatun ya birgeni, dan masu irin shegen kaifin ƙwaƙwalwar nan tasa basu da yawa a cikin mutane, zakiga kuma mafi yawansu sunfi yarda su zama mugaye fiye da mutanen kirki, balleshi daya tashi ɗan gata ma. Amma kigafa shi a ma tsarinsa baya shan komai har giya da ba komaiba, baya neman mata, abinda kawai ya sani a rayuwarsa shine aikinsa da Family ɗinsa. Gaskiya ina masifar son gayen nan Joy, komai nashi yana birgeni”. 

        Dariya Joy tayi sosai, ta wani juya idanunta cike da yanga, “Ai bake kaɗaiba Mira, koni da yake Brother ɗina sonsa nakeyi, haka ƴammata da yawa suke haukacewa a kansa, shiko babu wacca ta ishesa koda kallo ma, Mom tace tunda suke da shi bai taɓa ce musu ga budurwarsa ba. Ke nifa da ƙanwa zata iya auren yayanta da Brother Yoohan zan aura fa”. Baki Mira ta taɓe cike da kishi ta ɗauke kanta batare data bama Joy amsaba. 

     Joy data fahimci kishi Mira keyi saita kwashe da dariya ta miƙe, amma ita tasan har cikin ranta son Brother ɗinta take da gaske. Kuma harga ALLAH tana kishin ganinsa da wata mace har Mira ɗin, dan yau sosai taji daɗin mazgar da yayma Miracle.


🤣Joy kedai muguwace to.



               A tsarin gidan dolene duk safiyar duniya ka fito babban falo inda suke taruwa su duka har ma'aikatan gidan suyi addu'oinsu. Yoohan ne dama sai ya gadama randa ta raya masa yake fitowa idan har ya kwana a gida, dan yafi ganema yayi tasa a ɗaki shi kaɗai baisan hayaniya, garama idan Papa ya takura masa.

      Yauma kamar kullum duk sun hallara, har ƙananan yaran duk an tasosu, Papa da yay tafiya ne kawai babu sai Yoohan da kowa yasan yau bazai fitoba tunda jiya da haushin Miracle ya kwanta. Amma duk da haka sai da Mom taje ta buga masa ƙofa.

      Yana jinta sarai, dan tashinsa kenan yana zaune a kan gadonsa ido a rufe yana addu'ar shima. amma yay mata banza, sai da ta gaji dan kanta ta haƙura. Sauka yay a gadon fuskar nan kamar kullum a cinkushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da ALLAH ya azurtasa dashi bayyana ba (damma babu hasken bautar UBANGIJI a cikinsa Yoohan daya zarce hakan ga mai kallo😭).

        Slippers ya zura ya nufi toilet, ya kusa mintuna goma a ciki sannan ya fito, da alama dai ba wanka yayi ba, dan kayansane a jikinsa bai canja ba. Ficewa yay daga ɗakin gaba ɗaya ya fito falonsa, a mamakina sai naga ya ɗaga labulen bangon gabas, sai ga ƙofa a wajen ƙatuwa ta glass. Danna wani abu yay a bangon ta zuge da kanta ya shiga. Ƙaton ɗakine da aka cika da kayan motsa jiki kala-kala. Gaba ɗayansa kuma da glass aka yisa, ta ciki kana iya hango harabar gidan dama cikin anguwar gaba ɗayanta. Zama yay ya ɗaura takalma a ƙafarsa batare daya canja kaya ba ya fara motsa jiki a style kala-kala. Yana a kusan mintuna hamsin da farawa amintaccen yaronsa da Nu'aymah ta fasama kai jiya ya shigo ta wata ƙofa ba wadda shi ya shigoba. Madaidaicin tiren hannunsa ya ajiye kan wani table dake can gefe gaban kurera doguwa guda ɗaya kacal dake a ɗakin, sannan ya dawo inda Yoohan ke cigaba da ɗaga ƙarfe yace, “Good Morning sir”. Sai da ya furzar da zufan dake sakko masa har kan laɓɓa sannan yace, “Morning” a taƙaice. 

            Ajiye ƙarfen yay ya miƙe ya sake komawa kan wani machine ɗin, sai da ya fara batare daya kallesa ba yace, “Solo! Aikin dana saka ka fa?”. Kan Solo a ƙasa yace, “Sir komai ya kammala, yanzu haka ma nasan sun kama hanyar tafiya dan tunda daddaren na sanar masa, ya kuma tabbatar min za'a haɗa komai tun a daren, a yau su tafi kaiwa”.

       “Good” ya faɗa a taƙaice yana kallon agogon dake manne a bango ƙato. Lumshe idanunsa yay ya buɗe yanata faman fidda numfashi da sauri-sauri. Sajensa kansa ɗigar da zufa yakeyi balle murɗaɗɗen jikinsa dake sharkaf tamkar wanda yayi wanka. Sauka yay daga saman machine ɗin ya amshi ƙaramin towel dake a hannun Solomon ya fara goge fuskarsa zuwa wuya.

        Da sauri Solo ya ɗakko tiren daya shigo dashi shima. Iska Yoohan ya furzar kafin ya ɗauka babban kofin glass dake cike da tatattun kayan marmari da babu koda suga a ciki akan tiren dake hannun Solomon. Barin wajen yay da kai kofin bakinsa yana sha, ya ƙarasa kujerar nan ƙwara ɗaya ya zauna da ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya ya ɗauka remote ya kunna television dan akwai program ɗin da yake kallo a NTA kullum safiya a irin wannan lokacin a duk inda yake, inhar kaga bai kalli wannan shirinba to sai dai inda yake babu wutar nefa kuwa.

             Dawowa Solo yay gefensa ya tsaya suna kallo a tare, yana shan lemonsa suna magana jefi-jefi akan tafiyar da zasuyi yau har aka kammala shirin, dan minti ashirin ne dama. Ajiye kofin yayi ya miƙe bayan ya cire takalman yabar Solomon na gyara ɗakin da maida kowane abu inda yake.


      Kusan 9am ya fito daga ɗakinsa cikin gayunsa dake rikita ƴammata, sai baza ƙamshi yake kamar wani gonar turare. Sai dai tamkar kullum fuskar dai babu fara'a. Sajen nan da gashin sunsha uban gyara na ɗaukar hankali kamar dansu kawai aka yosa duniyar.

        Tunda ƙarar takunsa ta fara bayyana garesu falon yayi tsitt, kowa ya zubama hanyar benen idanu duk da sunsa wanene ɗin mai tahowar kuwa.

           Kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa yana sake tamke fuska musamman da yaga Miracle zaune. Mom ce cike da farin cikin ganinsa ta miƙe tsaye tana buɗe masa hannayenta alamar yazo. Fuskarsa ya ɗan saki amma ba murmushi ba, ya nufeta ya ɗan rungumeta a gefe saɓanin ita da ba haka take buƙatar yi masaba, ta fison ta jisa sosai a jikinta, sai shi kuma sam baiso. yace, “Good morning Mom”. “Good Morning my boy, ka tashi lafiya?”. Kansa kawai ya gyaɗa mata. Tai murmushin jin daɗi tana kama hannunsa cikin nata.

       “Good morning Brother”. Suka haɗa baki wajen faɗa yaran suma, amma banda Mira data haɗe rai wai ita a dole fushi take da shi. Kallonsu yay sosai da fararen idanunsa ɗaya bayan ɗaya kafin ya amsa musu da muryarsa mai amo. Ya ɗaura da tambayar lafiyarsu kamar yanda ya saba cike da kulawa da sonsu. Dukansu fuska a washe suke amsa masa, dan sunsan yana ƙaunarsu. Idan dai baƙin halinne ya motsa ba sani ba sabo yakema kowa a gidan.

        A tare suka ƙarasa d/table shi da Madan Chioma, ta zaunar dashi da kanta ta shiga zuba masa abincin da tasa akai masa na musamman. “Thanks” ya faɗa a saman laɓɓa ya ɗauka cokali ya fara ci. dai-dai misali yaci, dan badan ma tafiya da zaiyiba bazai karyaba a irin wannan lokacin. Dan shi mutum ne mai ƙa'ida da tsari. Komai nasa a tsare yake tamkar wani bature😜 (mudai munsan ALLAH shike tsara rayuwa ba mutum ba😁).

         Cikin damuwa Mom daketa kallonsa tace, “Badai ka ƙoshi ba?”. Idanunsa ya ɗan lumshe mata alamar amsawa. Tai saurin kamo hannunsa tana girgiza masa kanta. “Jiyafa bakaci abinciba ka kwanta, shine yanzu kuma......” “Shiiii!!” ya faɗa yana ɗora ɗan yatsansa akan bakinta, “Mom ya isheni haka”. Badan tasoba ta barsa. Yasa tissue ya goge bakinsa sannan ya miƙe, “Mom zan wuce Lagos, zata iya yuwuwa daga can bazan dawo nanba zanje ƙasar Kenya. Cike da damuwa take kallonsa, har yanzu ta kasa sabawa da waɗannan tafiye-tafiyen nasa, dan ko kaɗan batason yay nesa da ita, a koda yaushe tafison taita ganinsa tare da su.

        Kansa yaɗan girgiza dan yasan miyasa jikinta yay sanyi. Ya kama hannunta da yasha farce zaƙo-zaƙo, murya a tausashe yace, “Mom kimin addu'a mana, baƙyaso na cigaba da taimakon mutane ina samun lada?”. Da sauri tai murmushi, “Inaso sosai Yoohan, sai dai aikin nan ya maka yawa, gaba ɗaya baka da wani lokacin kanka kai saina wasu. ALLAH yasa kaje lafiya ka dawo lafiya”.

     “Amin” ya faɗa da yin kissing hannun nata.


      Gaba ɗayansa suka fito domin masa rakkiya har wajen da motar da zai shiga take, cikin girmamawa guards ɗinsa da securitys gidan suka iso ɗaya bayan ɗaya suna gaishesa. Kamar yanda ya saba musu alkairi idan zai yi tafiyar kwanaki haka yauma duk ya bisu da shi ta hanyar Solomon dake da kusan ci dashi fiye da kowa, dan duk inda zaije tare suke tafiya, sannan komai nasa shi yake sakawa. Dan haka yasan sirrinsa sosai da halayensa fiyema dasu iyayensa. A tare suka shiga masa addu'ar fatan alkairi, ƙannensa kowa na masa shagwaɓar zaiyi missing ɗinsa. Babu dai dariya a fuskarsa, amma duk yana binsu da kallon kulawa. Kafin ya bisu ɗai-ɗai yay kissing nasu a kumatu, banda Miracle dako kallon inda take bayayi. Gebrail ya buɗe masa mota ya shiga, shima ya zagaya ta ɗayan gefensa ya shiga dan zai masa rakkiya airport ne.

         Ɗaga fararen idanunsa yay ya kalli Mom da duk fuskarsa tai kalan damuwa. Yatsunsa biyu yasa a gefen bakinsa yay mata alamar *_Smile_*. Murmushin kuwa ta saki har haƙoranta na bayyana kafin ta ɗaga masa hannu. Shima yatsunsa biyu ya ɗaga mata daɗan motsa laɓɓansa kaɗan yay maganar da shi kaɗai yaji kayarsa. (Dan nidai banjiba🙄😏).

      

      Ganin motocin sun fice Madam Chioma ta sauke ajiyar zuya, yayinda Miracle ta share hawaye masu zafi da suka gangaro mata batare data shirya hakanba. 

     Juyawa sukai suka koma ciki, dama yaran sun wuce school su tun ɗazun.


__________________

*_NU'AYMAH_*

_________________


           Tunda garin ALLAH ya waye kaikawonsu suketayi na hidimar walima a cikin gidan marayun. Da safe kusan goma Hajjo ta iso tare dasu Hajarah. Su Umm kuma sai zuwa anjima.

         A babban harabar farkon shigowa cikin gidan marayun aka kafa manyan rumfuna tare da kujeru masu yawan gaske. Sai babban munbari da malamai zasu gabatar da lectures insha ALLAH.


     Nu'aymah harkokin gabanta take kawai, tama manta da wani faɗa da tayi da wasu jiya. Haka take, akwai saurin fushi da tsiwa akwai kuma saurin sauka da mantuwa. Itadai wuyarta ace ta rama kota maida murtani, daga haka kuma ta manta sai wata ta taso.

      Wajen misalin sha biyu saura ta kammala shirinta cikin baƙar jallabiya datasha adon manyan jajayen duwatsu masu ɗaukar ido. Itace shigar da gaba ɗaya ƙawayen amare zasuyi a wajen walimar. Tayi ƙyau sosai, ta sake gyara gashinta da saida akasha dagama kafin ta yarda aka tsefe aka wanke mata shi. Tanada gashi gwargwado dan yana sauka mata har kan kafaɗa, amma ta tsani kitso, gashi ta zama budurwa amma batabar kukan kitso ba har yanzu. Tsifar kai ma kuka take masa da wankewa balle kuma kitso.

      Jan veil ɗinta madaidaici ta naɗa, kalar saita sake bayyana ainahin hasken fatarta da kwarjininta da ƙuruciya. Ga jambakin data saka kaɗan a laɓɓa ya sake ƙawata madaidaiciyar kwalliyar tata. Sauri take taje kiran da baba malam ya aiko ai musu yanzun nan tana wanka. Tasa turare kaɗan ta fito da ɗan hanzarinta.

     Tare suka tafi ita da Amal da Yusrah, dan su ukun ya aiko kira. Suma sunsha ƙyau cikin kalar rigar da Nu'aymah tasa iri ɗaya komai da komai. Akwai tazara tsakanin office ɗin baba malam zuwa sashen gidajen yaran, amma haka suka taka cikin nutsuwarsu suna ƴar hira har suka isa. Sai da aka nemar musu iso sannan suka shiga.

      Baba malam ya ɗan kallesu ya ɗauke kansa, a ransa yanajin daɗi da godema UBANGIJI daya azurtasu da kamilan yara da yayi. Basu izinin zama yay kafin su gaidashi. Ya amsa musu kamar yanda ya saba. Sannan ya lissafa musu aikin da zasuyi a wajen walimar. Sai dai ba komai ya saka Yusrah a cikiba kasancewar tanada aure ita. 

     Suna shirin miƙewa zasu fita security yay knocking ƙofar office ɗin dayin sallama. Amsa masa sukayi, baba malam ya bashi iznin shigowa. Cike da girmamawa yace, “ALLAH gafarta malam saƙone wani bawan ALLAH ya aiko dashi”. Baba malam dake saurarensa yace, “To aike kuma Rufa'i. Nami kenan?”.

       “Kayan abincine dai mota guda gasu can a waje”. Baba malam bai sake cewa komaiba ya miƙe. Shi ya fara fitowa sannan su Nu'aymah a bayansa.

     Mota ce ta kamfani, dan haka baba malam ya ƙarasa suka gaisa da drivern cikin mutuntawa. “Malam ko zan iya sanin saƙo daga ina haka?”. Baba malam ya faɗa cikin fara'a da mutuntawa. Murmushi drivern yayi, shima cike da girmamawar yace, “Ranka ya daɗe wlhy nima bansan daga wa kayan sukeba, amma dai wani bawan ALLAH ne ya saya a kamfaninmu ya kuma bada wannan address ɗin a kawo tare da wannan”. Ya ƙare maganar da miƙa masa leda madaidaiciyar ruwan ƙasa.

       Sai da baba malam yay ɗan jimm kafin ya amsa, dan su gidan marayunsu nada tsari, ba komai suke amsa kai tsayeba babu bincike saboda gudun abinda zaije ya dawo. “Idan bazaka damuba ko zaka bani Number ɗin Manager ɗinku?”. “A babu damuwa ranka ya daɗe, dan dama shima yace na baka idan nazo”. “To Alhmdllh”.

      Wucewa sukai tare office ɗin baba malam ɗin, inda suka bar su Nu'aymah nan tsaye suna kallon kayan cike da jin daɗi da jan addu'ar alkairi ga wanda ya aiko ɗin. Suna a wajen tsaye baba malam da drivern nan suka sake figowa, a yanda sukaga fuskar baba malam ɗin yanzun sunsan ya amshi kayan shima. Umarni ya bama security ɗin nan akan a raka drivern har jikin store ɗin Orphanage ɗin a sauke kayan................✍

13

.................An gudanar da gagarumar walimar aure da saukar alkur'anin marayun ALLAH da waɗanda son zuciya ta saka iyayen nasu ajiyesu saboda gudun abin kunya. Sai kuma UBANGIJI mai rahama yay musu gata ta hanyar waɗanda basusanma sanda kikaje kika aikata ɓarnanrba.
     An sha wa'azi mai ratsa jiki ga manyan malamai, tare da addu'oi ga waɗan nan yara. Sai ƙyaututtuka daga manyan mutane ta hanyoyi da dama. Al'amarin dai sai muce Alhmdllh. Sosai su baba malam da ƙannensa da Hajjo harma da iyalansu suke cikin dunbin farinci da zagayowar wannan rana a garesu, dan kuwa ba itace ta farko ba, dan wannan shine karo na bakwai da zasu aurar da yara a cikin wannan gida. Al'amarin kam ya burge mutane matuƙa, inda wasu sukaji inama sune da wannan ƙyaƙyƙyawar zuciyar haka irin tasu baba malam. Yayinda wasu kuma suka ɗauki ɗammarar shigowa cikin tawagar a dama dasu da iya abinda ALLAH ya hore musu suma. Komai ya ƙaytar, dan ya tafi cikin nutsuwa, sarki ya bama waɗanan yara ƙyaututtuka, hakama Gwamna daya turo wakilinsa dan shi bai samu damar zuwaba ya dai bada tashi ƙyautar ga waɗannan angwaye da amare.
          Su Nu'aymah ansha kaikawo, dan kuwa sunyi tiɓis kamar sune amarorin. Bayan an tashi daga walimar da ƙyar suka rarrafa masaukinsu suna maida numfashin wahala. Su dai su Umm sunbi mazansu sun koma gida kamar yanda sukazo tare. Su Nu'aymah d Hajjo kuwa suna nan sai sunga ƙwal uwar daka.

________________________
  
           Bayan sallar isha'i baba malam ya tattara ƴan uwansa su duka uku a falonsa. A tare sukaci abincin dare, tare da tattauna yanda walima ta tafi cikin aminci da farin ciki babu wata matsala. Sunyi godiya ga UBANGIJI da ya zamemusu garkuwa, sannan baba malam dake tsaye akan komai.
     Ɗan murmushi kawai yayi batare da yace dasu komai akan hakanba. Kafin cikin nutsuwa ya nuna musu leda ruwan ƙasa da aka kawo ɗazun kafin walima tare da kayan abinci. Kasancewar bai samu zama dasu ba ɗazun sai bai sanar dasu komaiba ya bari sai sun dawo gida suyi maganar a tsanake sannan su duba abinda ke a ciki.
     Abba Musbahu da ya kasance ƙarami shi baba malam ya mikama ledan yana faɗin, “Musbahu buɗe muga minene a ciki, dan shi manager ɗin kamfanin da aka kawo kayan ta hanyarsu yace dukkan bayanan da muke bukata zamu samu anan. Amma mu kwantar da hankalinmu wanda ya bada ɗin baiyi da wata manufa ba, kuma shi yayine badan musan wanene shi ba, idanma muna tsoron wani abune to duk abinda mukaga be kwanta mana a raiba ko wata matsala ta biyo baya to mu nemesa shi, zai kaimu ga mai saƙon idan buƙatar hakan ta taso”.
      A tare sukace masha ALLAH, ALLAH ya sakanka masa da alkairi, ya biyasa da sakamakon abinda yafi wanda yayi. Shima ALLAH ya faranta masa fiye da yanda ya farantama mabukata.
      “Amin". baba malam ya amsa musu, yayinda Abba Musbahu ya fiddo abinda ke naɗe cikin leda mai ƙyalƙyali. Buɗe ledar yayi sai ga madaidaicin kwali ya bayyana. ya buɗe kwalin shima. Sun sami envelope guda biyu, ta farko check na kuɗi da suka basu mamaki fiye da zato. Dan a irin wannan halin da ake ciki mai bada ƙyautar irin waɗanan kuɗi masu yawa haka ai dole a jinjina masa. Sai zungureriyar wasiƙa, wadda bayanan cikinta ke magana akan su bada sunan yara talatin na gidan marayun da suka ƙare sakandire, ya ɗauki nauyin karatunsu na jami'a harsu ƙare, maza 15, mata 15. sai sunan kuma wasu ashirin din, maza 10 mata 10 sukuma waɗanda suka kare karatun zai nema musu aiki. Daga ƙarshe yace yana roƙonsu alfarmar sakashi cikin jerin mutane da zasu dinga hidima ga wannan gidan marayu gwargwadon ƙarfinsa.
         dukansu ajiyar zuciya suka shiga saukewa na mamaki da al'ajabin wannan mai saƙo. Kafin su shiga ja masa dogayen addu'oi, daga ƙarshe suka tattauna sosai akan lamarin. Sun yake shawarar faɗama UBANGIJI akan lamarin. Idan alkairine kuma mai wannan ƙudiri bada niyyar cuta musu ya zoba ALLAH yay riƙo da hannayensu gaba ɗaya. Idan kuma da wata manufa tattare da shi ALLAH yay musu maganinsa tunkan ya samu damar shiga jikinsu balle ya cutar da bayin ALLAH.
     Daga haka suka tashi akan zasu mikama UBANGIJI kukansu tsahon kwanaki uku, inda zuciyarsu ta karkata akan al'amarin zasu ɗaukesa a matsayin shine zaɓin da ALLAH yay musu, saisu yanke hukunci akan hakan. zasu cire kuɗaɗen daya rubuta ɗin a maidasu asusun gidan marayun.  bayan an gama ƙurar ɗaurin auren gobe idan ALLAH ya kaimu kuma saisu tantance yaran daya buƙata game da cigaban karatunsu da kuma waɗanda za'a nemarwa aiki.

*_ABUJA_*

               Bayan tafiyar Yoohan da kamar awa biyu sai ga papa da tawagarsa shi kuma ya dawo gida. Dama sunje taron manyan fastocine daya gudana a jihar Lagos, yau kwanansu biyar kenan a can. Ya samu tarba daga iyalansa da ma'aikatan gidansa, inda madam Chioma ke maƙale da shi har sashensa tai masa rakkiya.
       Bayan ya ƙimtsa ya fito sukai zaman yin lunch su duka a dining, sosai suka cika falon da surutu kamar ba abinci suke ciba, kowa na bama papa labarin abinda ya faru da baya gida. A cikin surutun nasu ne Abraham ke faɗama papansu an fasama Brother Yoohan motarsa a kano.
     Cak Papa ya tsaya daga cin abincin yana kallon Abraham ɗin, kafin ya maida kallonsa ga Madam Chioma da a lokaci guda ɓacin rai ya mamaye fuskarta. “Mi naji Abraham na faɗa Darling?”. Kanta ta jinjina masa tana ɗan karta cokalin hannunta akan filet ɗin abincinta, “Hakane Honey, jiya da yaje Kano abin ya faru, dama jira nake ka dawo asan matakin daya dace a ɗauka, shiyyasa bance masa komaiba dan karya ce bayaso ayi komai dan kasan halinsa dai”.
      Ɗan dukan table ɗin papa yayi da ture kofin da aka zuba masa lemo ya faɗi. A tare yaran duk suka zabura dan tsorota. Ya miƙe a fusace yana faɗin, “Miyasa tun a jiyan baki sanar minba, Gebrail ka tattaramin guards ɗin Yoohan gaba ɗayansu yanzun nan”.
            Cike da jin daɗi Gebrail ya amsa ma papa yana miƙewa. Dan shima burinsa a ɗauki matakin dama.

      Cikin mintuna ƙalilan guards ɗin Yoohan suka taru a falon, kallo guda zakai musu ka fahimci hankalinsu a matuƙar tashe yake. Musamman da suka shigo falon suka iske Papa nata kai kawo rai ɓace, kai kace gadin wani abu ya keyi. Sunkai tsayuwar mintuna goma kansu a ƙasa kafin ya kallesu da jajayen idanunsa.
         “Inaga baku da wani amfani game da tsare lafiyar Yoohan, zamu sallameku mu canzaku da waɗanda zasu iya, dan na inhar kune zaku cigaba da kulamin da yaro wataran sai an masa yankan rago kuna kallo baku iya yin komaiba akai”.
     Cikin ƙololuwar tashin hankali suke bashi haƙuri da roƙonsa. Suka ɗora da faɗin, ba laifinsu bane suma, boss ɗin nasune ya hanasu kowanne irin yunƙuri akan yarinyar. Kuma suna isowa sukaima Madam bayanin komai da ya faru....
      Tsawa papa ya daka musu wadda ta sakasu yin shiru lokaci guda. “Idan ya hanaku ɗaukar mataki miyasa bazaku kirani tun a lokacin ku sanar mini ba?! Tunkan ku fara aiki ban sanar muku duk randa kukayi kuskure wani abu ya faru da yarona abakin aikinku ba?”.
        Ka faɗa mana sir. Suka bashi amsa kowanne rai a dagule a tsorace kuma. 
     Hannu yasa ya bugi kujerar gabansa, “Oh shine kuma baku tuna wannan dokarba?!!”.
         Madam Chioma dake bayansa ta kama hannunsa ta riƙe cikin nata tana ɗan murzawa alamar lallashi, dan bata buƙatar a sallami guards ɗin, itama suna mata nata aikin ne daban. “Darling relax, kasan halin Yoohan ɗin namu ai, kai musu afuwa su kiyaye gaba kawai. Sai kuma musan abinda ya dace a ayi, idan aikawa za'ayi a kamo mana yarinyar shikenan, dan bana goyon bayan a barta”.
        Iska ya furzar daga bakinsa, ya zare hannunsa daga nata ya zagaya cikin falon sosai ya zauna a kujera. Kwalba dake a saman ƙaramin tray ya ɗauka ya tsiyaya abinda ke a cikinta a kofin glass ɗan ƙarami da shima yake a kan tray ɗin. Gaba ɗaya ya juye a baki yana ya mutsa fuska, kafin ya ajiye kofin ya kallesu ɗaya bayan ɗaya.
        “A ina abin ya faru?”.
“A ƙofar gate ɗin wani orphanage ne sir, kuma muna ƙyautata zaton yarinyar itama ƴar gidan ce, dan ciki boss yasa muka shiga akai treatment ɗin yaron”.
        “Daga nan zuwa safiyar gobe ku tabbatar wannan yarinyar tana nan cikin abuja, inba hakaba a bakin aikinku”.
        A tare suka saki murmushin jin daɗi, dan koba komai suma dama ƙulle suke da yarinyar, da kuma takaicin hanasu ɗaukar mataki da Yoohan yayi jiya. Yanzukan sun sami damar cin ubanta dai-dai gwargwado. Cike da girmamawa da alƙawarin yin abinda papan ya sakasu suka amsa. kafin ya basu izinin barin falon.

      Ko cikakken mintuna ashirin basu ƙaraba a gidan suka ɗakko hanyar kano duk da kuwa a lokacin ƙarfe ɗaya na rana ya gota. 

      Tofa, ana wata ga wata kenan😳😳 .

_____________________
*_NU'AYMAH_*

            A ɓangaren su Nu'aymah suma a washe garin wannan ranar bayan sakkowa sallar juma'a a massallacin aka ɗaura auren yara talatin da shida dake a gidan marayu na ƊAN JIBIYA FAMILY. Inda bayan kammala ɗaurin auren aka rakasu da addu'oin fatan alkairi kuma. 

         Da yamma su Nu'aymah suka ɗanyi shagalinsu iya mata a sashen matan, suma mazan anguna sukayi nasu a sashensu tare da sauran angunan da ba'a gidan marayun suke ba suma. Bayan sallar la'asar kusan ƙarfe biyar da tai dai-dai da isowar tawagar guards ɗin Yoohan gidan marayun aka kwashi amare gaba ɗayansu aka miƙasu ɗakunan mazansu, bisa rakkiyar iyayensu su baba malam. bayan doguwar nasiha da sukasha daga garesu tamkar yanda mahaifa kema ƴaƴansu idan zasu miƙasu gidan miji.
        Duk wani jan ido da barazanar Guards ɗin Yoohan securitys sun hanasu shiga cikin Orphanage ɗin, acewarsu sai dai su faɗi miya kawosu anan gate, idan sunga da damar barinsu su shiga shikenan, idan sunga babu damar hakan kuma sai dai su juya. Ran guards ɗin ya ɓaci matuƙa, sunji kamar su harbesu kowama ya huta. amma sai suka danne sukai musu bayani akan abinda ya kawosu, tare da tabbatar musu suna tare da ƴan sanda.
      Duk da securitys ɗin gidan marayun sun gane wa ake nufi da kuma miya faru jiya sai suka nuna bama su ganesuba, dan a ganinsu bai kamata su bada damar da za'aci zarafin ƴa ɗaya tilo ga wanda bai taɓa gajiyawa wajen musu hidimaba. Sun kaɗasu dambu taliya sunce basu gane Nu'aymah ba, su bama susan anyi wani abuba.
     Ran guards ɗin yayi ƙololuwar ɓaci, sai dai ɗaukar mataki ya gagaresu, dan suma securitys ɗin gidan marayun bawai kanwar lasa bane. Sun san taɓasu babban bala'ine ga ogan nasu papa balle su ɗin karan kaɗa miya. Dan haka suka bar orphanage ɗin ransu a ɓace, akan zasuje su sake shiri gobe su dawo.
     Hotel suka kama, kafin su kira papa su sanar masa da komai daya faru.

★★★★

         Su Nu'aymah da basusan wainar da ake toyawaba ana kammala miƙa amare baba malam yasa Yah Ahmad ya tattara masa su aka wuce dasu gida badan sunso hakanba. Dan so sukai sukam sai sunyi sati ɗai-ɗai a gidan kafin su koma gida. Sai dai baba malam ya ɓata musu shirinsu.
     Aiko koda suka koma gidan sai suka dinga fushi da kumbure-kumbure. Kayan biki da baba habi ta haɗa musu ma sunƙi kulawa. Babu wanda yabi takansu a gidan, saisu Kubrah ne ma ke musu dariyar tsokana suna sake ƙulal dasu dan duk suna sashen Hajjo ne da suka dawo tare.

____________________

     
         Gaba ɗaya ran guards ɗin Yoohan a ɓace yake, tunda suka iso hotel ɗin da suka kama basu zaunaba, sai faman ƙulle-ƙullen yanda zasu sami Nu'aymah da matakin da zasu ɗauka a kanta sukeyi. Kai kace wata babbar ƴar ta'adda suke bibiya.
      Sun ƙulla yafi sau hamsin suna warwarewa. Suna tsaka da sake ƙullawa saƙo ya iso garesu daga hannun ɗaya daga ma'aikatan hotel ɗin. Number wayace daga wani, ya basu damar su kirashi idan suna buƙatar sanin inda wadda suke nema take..  
             Da yake burinsu kenan jiki na ɓari suka kira kuwa. Ba'a ɗagaba har sai da ta kusan tsinkewa. Ƙinyin magana akayi. sai da ɗaya daga cikin guards ɗin ya fara magana. 
      “Duk da bamusan ko wanene ba, mun maka alƙawarin inhar ka sanar mana inda yarinyar take zamu biyaka da kuɗi masu nauyi, oganmu ma zai maka ƙyauta ta musamman”.
       Batare da an basu amsaba aka yanke wayar. Kallon juna suka shigayi tambayoyi fal ransu. Kafin ɗayansu ya iya furta wani abu sai ga saƙo ya shigo. Da sauri suka buɗe ganin Number da suka kira ɗince. Ba komai bane a saƙon face cikakken address ɗin gidansu Nu'aymah, da sunanta harma da hotonta.
    Daɗine yay mugun kamasu, dan kuwa sun sake tabbatar da itaɗince, dan haka jiki na rawa suka sake kiran wanda ya tura musu ɗin. Yanzun ma dai baiyi maganaba, sai sune suka buƙaci ya turo musu accaunt details nashi ko nata zasu tura masa ladan aikinsa. Ƙitt aka yanke wayar batare da ance komaiba. Mintuna kaɗan kuwa saiga accaunt Number an turo. A take suma sukaima papa massege bayan sun kirashi sun sanar masa komai. 
             
     Har a lokacin cike yake da ɓacin ran abinda ya faru, dan yaje yaga yanda akaima motar bugu na fitar hankali, shiyyasa ransa ya sake ɓaci, ya kuma tabbatarma kansa ko ɗiyar uban wacece yarinyar sai ta yabama aya zaƙinta.
           Babu ko tantama ana turo masa accaunt details ɗin ya antayama maishi kuɗi masu tsoka, dan a ganinsa bukatarsa ta biya. Mizaisa yaji ciwon biyan wanda ya taimakesu.

________________________________
*_NU'AYMAH_*

               Yau sama-sama Nu'aymah ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon ƙafa alamar zuwan period ɗinta. Ita dama takan fara da ciwon ƙafane, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ƙwaɗayi kamar taci mutum ɗanye.
      Tunda Umm ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Yusrah da Amal nata barcinsu a kan gadon su. Ita ta fara tadawa kafin su Amal, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Nu'aymahn data maida kanta ta kife tsakanin ƙafafunta.......
      “Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Nu'aymah ta ɗaga kai ta kalli Umm, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, “Umm lafiya lau, kawai gajiyace tasa ƙafafuna ciwo”.
      Ɗan ƙura mata idanu Umm tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Yusrah ce ta ƙaraso wajen Nu'aymah ɗin ta durƙusa. “Baby ƙarya kikaima Umm wlhy, daga gani baki da lafiya”.
    Yamutsa fuska Nu'aymah tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Ƙafafuna ke ciwo wlhy Yusrah, nasan kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko anjima”.
         Amal dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Yusrah data harbo jirgin Nu'aymah tai saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Amal. Nu'aymah kuma tai tsaki idonta cike da ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Yusrah ke mataba har yanzun.
  
       Bayan sun idar da salla Yusrah da Amal suka fice taya iyayensu aiki, Nu'aymah kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci yay gaba da ita.

     Umm da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast ita da ƴan aiki ta shirya na baba malam da sauran ƴan uwansa a falonsa da kanta kamar yanda ta saba inhar duk suna gari, dan tare sukecin abincin safe da dare. Na rana ne dai bai zama dole su dukansu suna a gidaba shiyyasa. Garama idan ta kama juma'a ace dan duk basa zuwa ko ina a wannan ranar sai massallaci.
        Sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta saka turaren wuta ta leƙa bedroom ɗinsa. Yana wanka, sai kawai ta buɗe Wadrobe ɗinsa ta zaɓo masa kayan da zai saka, saboda yau zasuje taron wani wa'azi a jihar katsina. Bayan ta ajiye masa duk abinda tasan zai buƙata ta fita zuwa ɗakin Muhammad danta taimaka masa yayi shirin makaranta shima.

*_08:15am_*

       Kusan takwas da kwata su baba malam suka hallara a falonsa shi da sauran ƴan uwansa domin karyawa. Sun sake gaisawa cikin girmamawa kamar yanda suka sabama kansu. Kafin su zauna su fara karyawa abin cike da birgewa.
     Sunyi nisa da cin abincinsu sukaji sallama. A tare suka amsa idonsu akan ƙofar. Ƙarasawa ciki falon Abbas da yay sallamar yayi. Ya durƙusa har ƙasa ya gaidasu. kafin cikin damuwa yace, “Abba ƴan sandane ke sallama”.
       “Ƴan sanda kuma Abbas? Lafiya dai ko?”. Baba malam dake kallon Abbas babu ko ƙyaftawa ya faɗa.
       “Abba ban saniba wlhy, amma sun nuna wai an turosu su tafi da Nu'aymah ne”. 
       Ran Abban Adawiya a ɓace yace, “Wace irin Nu'aymah kuma? Miya haɗata da ƴan sanda banda shashanci irin naka Abbas?”. “Wlhy Abba haka sukace, dan hotonta ma suka nuna”. Miƙewa sukai su duka huɗun, sai dai su uku suka fara fita, kafin baba malam yabi bayansu..............✍
14

.................A tare suka fito harabar gidan, inda suka iske matan gidan da sauran samarin da basu kai ga ficewa sabgoginsu ba duk sun fito suma. 
      Suna ƙarasawa ga ƴan sandan Nu'aymah da Amal taje ta kira itama sai gata ta fito tana ɗan ɗingisa ƙafa. Sanye take da siket da riga na atanfa, sai ƙaramin hijjab da Umm ta sabar mata da sakawa a cikin gidan saboda samarin gidan tunda ba muharramanta bane ba.
       Tunda su Baba malam suka fito jikin wasu a cikin police ɗin yayi sanyi ganin dai da gaske an turosune gida mai daraja kamar wannan dan suyi abinda basu da tabbacin faruwarsa tunda ba'a gabansu akaiba. To amma yaya zasuyi, d.p.o ne da kansa ya sakasu zuwa su kama Nu'aymah, ga kuma kuɗaɗe da sukaci har kashi biyu daga Papa da kuma guards ɗin Yoohan na toshiyar baki. (Ya rabbi ka tsaremu cin rashawa da bada ita. Amin🙏🏻😭).
        
     Sun gaisa dasu Abba cikin girmamawa, kafin su sanar musu daga station ɗin da aka turosu da kuma abinda zasuyi. Kusan a tare su Abbah duk suka juya suna kallon Nu'aymah. Baba malam ne kawai kansa a ƙasa yana ɗan murmushi. Batare da yace komaiba ya nufi inda jama'ar gidan ke tsaitsaye suma suna kallonsu hankali a tashe.
       Hannun Nu'aymah ya kama batare da yacema kowa uffanba. Itama kuma babu musu ta bisa har wajen ƴan sandan. Ya miƙama macen hannun Nu'aymah yana faɗin, “Itace wannan?”.
        Kallon hoton dake a waya babban nasu yayi, kafin ya kalli Nu'aymah. “Eh itace ALLAH ya gafarta malam”. Ya faɗa cike da girmamawa ga baba malam. Murmushi baba malam yay musu yana nuna masu Nu'aymah dake kallonsa kamar wata sokuwa. “Gata nan, zaku iya tafiya da ita”. Da sauri Abban su Abdallah ya yunƙuro zaiyi magana baba malam ya ɗaga masa hannu fuska a ɗaure. Cak ya tsaya hankalinsa a ƙololuwar tashe. Hakama su Abban Adawiya hankalin nasu a tashe yake da hukuncin da baba malam ya shirin yankewa. A ganinsu ai basai anje station ba, zasu iya tsayawa su tattauna anan, musamman ma shi Abban Adawiya da yana cikin Orphanage randa abin ya faru. Kuma an sanar masa komai akai.
        Godiya ƴan sanda sukai tare da juyawa da Nu'aymah zasu tafi. Tirjewa tai tana kallon Baba malam daya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garesu tamkar baisan mi akeyiba. Hannunta ta fara ƙoƙarin fisgewa idanunta na cika da ƙwalla. “Abba wlhy bansan mina musu ba”. Tai maganar muryarta na rawa. 
     Juyawa baba malam yayi zai bar wajen batare daya kula maganar Nu'aymah ba. Sai da yay taku biyu uku sannan ya tsaya tare da juyawa ya kalli ƴan sanda da Nu'aymah data fisge zata dawo. Cikin tsananin kaushin murya yace, “Idan bazata biku da arziƙiba ku ɗauketa!!”.  
     Tsayawa Nu'aymah tayi cak tana kallon baba malam ɗin. Sai kuma ta kalli inda su Umm suke. Sake dawo da idonta tayi kan ƴan sandan da suma ita suke kallo. kunyar baba malam ce kawai ta hanasu fara cin ƙaniyarta tun anan. Tsaf ta haɗiye kukanta. Ta juya cikin ɗingishi ta nufi ƴan sandan. Basuce mata komaiba suka tasa ƙeyarta gaba suka fita waje inda motarsu take.
      A gaban ƴan anguwa daketa kai kawo aka sakata a motar ƴan sanda. Gaba ɗaya hawayen da Nu'aymah ta fara ɗazun sun ƙame ƙaf. Ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tai shiru. Sai faman cije baki kawai take saboda zugi da ƙafarta ke mata. Har suka isa police station ɗin bata ɗagoba. Sai da ƴar sandar ma ta taɓata sannan ta san sun iso. Ɗago kanta tai a hankali ta kalli station ɗin, sai kuma ta juya ga ƴar sandar dake mata kallon tausayi. Dan ita yanda taga mutanen na hanƙoro akan yarinyar ta zata ma wata tsohuwar macece, ashe yarinyace ƙarama. Itace ta taimaka mata ta fito, ta kama hannunta ganin kamarma ta kasa tsaiwa. A haka suka shiga cikin station ɗin da taimakon ƴar sandar. 

  
         “Amma Yaya ka.......” hannu baba malam yay saurin ɗagama Abban su Adawiya dake son masa bayanin ainahin abinda ya faru. Ya kallesa fuskarsa babu wasa, “Banason jin komai akan hakan Mustapha. Kaje ka shirya mu wuce banason yazam mu ake jira”.
     Kai kawai Abban su Adawiya ya kaɗa masa. Kafin ya kalli su Abba Musbahu ya bar wajan jiki a sanyaye. Da sauri su Abban Abdallah suka nufi mota da nufin bin bayan su Nu'aymah, sai kawai a bazata suka tsinkayi muryar Baba malam na faɗin, “Na haramtawa kowa bin bayanta a cikin gidan nan, idan kuma wani ya aikata koda ban saniba zai fuskanci fushina”.
     Cak suka tsaya daga yunƙurin shiga motar, kowannensu goshinsa na tara zufa. Babu wanda ya iya sake cewa komai har Baba malam ya shiga sashensu ya fito cikin shirin fita. Ta gabansu ya wuce zuwa sashen Hajjo data sha maganin mura tun ɗazun ta kwanta. Duk wainar da ake toyawa bata saniba dan barci takeyi. Baifi mintuna biyarba sai gashi ya fito.  Yanzunma bai kalli sashen da kowa yake ba ya nufi inda motar da zasu tafi take, sauran motocin uku da ɗalibansu zasu shiga da ƴan agaji kuma duk suna a harabar massallaci. 
     Suna kallo motar ta fice batare da ko mutum ɗaya ya iya cemasa a dawo lafiya ba, shima kuma bai nuna ya damu da hakan ko jiran cewar tasu ba.

      Umm ce ta fara sulalewa ta koma ciki, kafin sauran suma su fara zare jiki ɗai-ɗai suna shigewa sashensu. Addah dai bayan Umm tabi tana share hawayen da ke sakko mata batare data farga da fitowarsu a cikin idanunta ba.

_____________
*_ABUJA_*

        Tunda labarin kama Nu'aymah ya isa kunne Papa farin ciki ya mamayesa shi da Madam Chioma, breakfast da suke shirin zamanyi ma su kasawa sukayi, sai kai kawo sukeyi zuciyoyinsu fes kamar an basu rabin duniya. 
    Dolene yasa a koyama yarinyar hausawan nan hankali, dan shi a rayuwarsa idan da abinda yafi tsana a rayuwarsa to ƴan yankinta ne. Ya tsani yarenta fiye da mutuwarsa, a cewarsa babu abinda suka iya sai haihuwa, ƴaƴan nasu kuma babu tarbiyya sam, daga ƴan bangar siyasa sai masu bara. Sam mutanen da yankinsu basu masaba, inda ace zai iya zama shugaba, sai ya shafe yankin ko tarihinsu baza'a sake aji ba. (hummm Papa, a ringa sara dai ana duban bakin gatari).
           Abinda papa ya keta faman rayawa a ransa kenan yana murmushi. Waya ya sake ɗagawa yay magana da d.p.o ɗin akan yanzunan a bama guards ɗin Nu'aymah su taho masa da ita Abuja. Shi kuma d.p.o ya turo da accaunt Number ɗinsa yanzu zaiji alert.
        Cike da farin ciki d.p.o ya amsama papa. Babu ko tunanin komai a ransa ya aika da accaunt details nashi, ya kumayi zaman shirya takardar ƙarya akan laifin da bashi Nu'aymah ta aikataba.

(Humm! Ya ALLAH ka shiryemu ka shiryi shuwagabannin mu da jami'anmu. Ka tsame bara gurbin cikinmu, idan masu shiryuwane ka shiryesu. Idan bazasu shiryuba UBANGIJI kafimu sanin miya dace dasu, mun barka dasu😭🙏🏻).

________________
*_LAGOS_*

         Fitowarsa kenan daga ɗakin theatre a matuƙar gajiye. yanda yake tafiya kawai zai baka wannan amsar. Tare yake da likitoci uku da suka tayasa aikin, sai Nurses suma guda uku. Dai-dai sun ƙaraso ƙofar wani office nurse ɗin dake a gefen damarsa ta miƙa masa tasar hannunta ya jefa hand gloves ɗin daya cire daga hannunsa ya jefa a ciki, hannu ya ɗaga musu kawai alamar su dakata anan ya tura ƙofar ya shige.
       Basu damu ba, dan kowa yasan Dr Yoohan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana, sannan baida fara'a. Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar kullum shi cikin ƙuncin rayuwa yake, kokuma girman kaine bisa ga ɗaukakar da ALLAH ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Yoohan sam ba haka baneba. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. Idan ya shiga cikin musulmi bazaka taɓa cewa shi ba musulmin bane, musamman daya ajiye ƙasunba da yanda yake gudanar da al'amuransa sak halayyar musulman ƙwarai. Sai dai fa idan kaci karoda sarƙar Cross a wuyansa da akoda yaushe baya fashin sakawa ne zaka gane daga ina ya fito. ALLAH ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan UBANGIJI shine mai komai da kowa.

         Office ne daya amsa sunansa office. Bakajin komai sai sassanyan ƙamshin turarensa dana ac. Wanda ke zaune a rikunin kujeru uku dake can gefen office ɗin yana aiki ya miƙe yana masa barka da fitowa cike da kukawa.
     Kansa ya ɗaga masa fuska a yamutse na alamar gajiya. kafin ya ƙarasa ga kujerar zamansa yaja wani file dake a jiye ya fara singing.
      Tasowa Richard yay da sauri garesa yana murmushi, ya ajiye files ɗin hannunsa gaban Dr Yoohan ɗin yana faɗin, “Doctor akwai mutane biyu da zaka ganifa yanzun kafin ka tafi hutun awa uku da rabi, idan lokaci ya cika zaka sake shiga theatre room, na mutane biyu da suka rage suma”. Da sauri Yoohan ya ɗago yana kallon Richard fuska a marairaice kamar zai fasa kuka. Richard yay saurin haɗiye dariyar dake neman kufce masa dan yasan shima da gaske Yoohan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace, “Da gaske nake Yoohan, gama files nasu na kammala dubawa”. 
          “Rich.. Please, wlhy na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa. 
      Murmushi Richard yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima.
         ALLAH ne ya haɗashi da Yoohan tun a secondary school, a farkon haɗuwarsu sam basa shiri, dan abokan faɗan junane a aji. Ba komai yasa rashin jituwa tsakaninsu ba sai kasancewar su duka sunada matuƙar ƙoƙari, kafin Yoohan yazo school ɗin shike ɗaukar na ɗaya a ajinsu, amma Yoohan na zuwa ya amshe wannan matsayin. Kafin zuwan Yoohan ɗin kuma kowa sonsa da girmamasa yake a ajin, hasalima shine Monitor, ƴammatan ajin ji suke tamkar su haɗiyesa kuma. Amma Yoohan na zuwa nanma komai ya canja, kan ƴan ajin ya rabu biyu, wasu na ɓangaren Yoohan wasu Richard. Dan haka aka zama abokan dabin juna, duk da sam Yoohan baya kula duk haukarsu. Rashin kulawar Yoohan ɗin tasa a koda yaushe shi da tawagarsa suke ɗauka Yoohan matsoracine, dan babu wanda ya taɓa ganin faɗansa. Sai fa wataran da suka kaishi bango yayma Rich dukan mutuwa, da ƙyar aka karɓesa a hannunsa dan Yoohan akwai zuciyar tsiya. Tun daga wannan duka da Yoohan ya masa suka koma abokan juna, tun sauran ɗalibai na ƙalubalantar abotar tasu har suka fahimci ta gaskiyace suma sukabi. Shi da Yoohan duk burinsu ɗaya ne akan karatu, dan haka haɗewarsu waje guda ta ƙara musu himma da ƙwazo. Koda suka kammala secondary kuma cikin amincin ALLAH iyayensu suka amince musu tafiya karatu tare. A gaba ɗaya rayuwarsu tare ta gudana, sai daga bayane Yoohan daya cigaba da wasu kwasakwasai (Courses) ne suka ɗan rabu, danshi ya amshi aikin da aka bashine a ƙasar London bayan zamowarsu cikakkun likitoci, saɓanin Yoohan daya ƙi amincewa.
     Daga baya Yoohan ya kuma samun ɗaukaka fiye da tashi, danshi ya ƙara faɗaɗa wasu karance-karancen daya bashi damar iya duba marasa lafiya ta kowane fanni, aikinsa ya zam zai iya yinsa a kowacce ƙasa kuma. 
       Bayan shekara ɗaya da fara wannan gwagwarmayar Yoohan ya fahimci bazai iya shi kaɗaiba sai da taimakon Richard, dan haka yaje ya dabaibayesa da daɗin baki har saida ya amince suka sake curewa waje guda suke gudanar da aikin a tare. Yanzu haka shekararsu ta biyu kenan da fara aiki, suna ɗaya daga cikin manyan matasan likitoci da duniya ke alfahari dasu bama ƙasarsu ko yankin Africa kawai ba.
    A yanzu haka dai shi Richard ana shirin aurensa ma da wata baturiya, shiko Yoohan yaƙi motsawa sam, a cewarsa shi bama zaiyi aure yanzuba sai nan da wasu shekarun daya tsara.

           Ɗakine madaidaici dake ɗauke da kayan ɗaki complete, shima sai ƙamshi yakeyi kamar ba'a cikin asibiti ba. Kansa tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matuƙar ji. Tunda ya iso Lagos a daren jiya bai hutaba, dan ya iske patients da yawa da sukai booking ɗin ganinsa. Tun a jiyan yay dauriyar zaman duba files ɗinsu, waɗanda yasan akwai mafita ya rubuta musu Doctors ɗin da zasuje su gani ya turama Rich. Waɗanda kuma yasan sai shine zai duba ya sanar da Richard ya sanar musu time ɗin da zasu gansa ta hanyar text messeges.
       A safiyar yau tun ƙarfe huɗu na asuba ya baro gida, tunda yazo kuma aiki yake bai hutaba. Bayan ya gama duba adadin daya ƙayyade ya shiga theatre akan matsaloli daban-daban kuma, yanzunma ba ya gama baneba, yanada loacin hutawa ne na awa uku da rabi kafin ya koma ɗakin theatre ya ƙarasama mutane biyu dake a ƙasa kamar yanda Rich ya faɗa. Bayan ya kammala dasu zai ƙara hutun awanni uku jirginsa ya ɗaga zuwa ƙasar Kenya inda wasu patients ɗin ke jiransa canma.
            Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Blue, sai hular wanka data kare gashinsa daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Solomon ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy.
        Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar. Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?.
       “Yoohan!” ya tsinkayi muryar Richard na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Rich ɗin yay maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da gaske ya gaji baison takura.
      Yana buɗe ƙofar yace, “Rich plea.....”
          Saurin katsesa Richard yay da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Yoohan, matar da kaima aiki a kano yanzun nan Doctor Sa'ad ke sanar min an samu matsala”.
       “What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Richard da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ɗakin yay da sauri, yama manta da wata gajiyarsa. Wayarsa ya ɗauka domin neman Dr Sa'ad. Ganin ashe shinema ya kirasa ɗazun lokacin da Richard ke knocking ya sakashi kiransa. Bugu ɗaya kuwa Dr Sa'ad ɗin ya ɗaga. 
       Ko gaisuwa basuyi zaman yiba Dr Sa'ad ya shiga masa bayanin dukan abinda ya faru, da halin da matar ke a ciki yanzun.
        Hannunsa dafe da kansa cikin tsagwaron damuwa yace,  “Dr Sa'ad ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a bata kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare maganar da ɗan kaushin murya.
        Dr Sa'ad da maganar Dr Yoohan tai masa zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa, amma sai Yoohan ɗin ya kuma dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please, zan turo maka hanyar da zakubi wajen fara bata taimako yanzun, nima ina hanyar tahowa”. 
       “Okay Sir” Dr Sa'ad ya amsa masa daga can cikin wata irin murya mai cike da ɗaci da takaici. Yaro ƙarami dashi yana juyasu dan kawai ALLAH ya basa baiwar da tafi tasu, tabbas idan ba kawar da Dr Yoohan sukaiba a duniya rayukansu da hanyar cin abinsu na a cikin garari. 
      (Ni dai nace Humm).

      Shi Yoohan baima saurari amsawar Dr Sa'ad ɗinba, dan tuni yayi wurgi da wayar saman gado cike da takaicin likitoci irin Dr Sa'ad, da a kullum basu da kishin ƙasarsu da jama'arsu, burinsu sudai kuɗi kawai da taƙama da aikinsu. Da hanzarinsa ya fito ainhin Office ɗin yana faɗin, “Rich Please ka bincika min idan akwai jirgi mai tafiya kano daga nan zuwa mintuna talatin”.
       Da sauri Richard ya fita daga office ɗin zuwa nasa, dan yabar wayarsa a canne. Shi kuma Dr Yoohan yaja Laptop ɗinsa dake saman tebirin daga tsaye ya shiga dannata da sauri sauri cikin ƙwarewa. A haka Solomon ya shigo ya samesa, batare daya tsayaba yay saurin shigewa bedroom ɗin domin fidda masa kayan da zai saka dan Richard ya sanar masa halin da ake ciki, kuma shi Dr Sa'ad ya fara samu a waya kafin Richard ma.
         Dr Yoohan na kammala tura abinda zai aikama Dr Sa'ad ya nufi ɗakin shima. bai wani damu da tsayawa duba kayan da Solomon ya ajiye masanba ya ɗauka ya fara ƙoƙarin sakawa, shi kuma Solomon ya fito ya bashi waje.
        Shirin yake ransa duk a jagule da takaici, yana kammalawa ya fito jacket ɗin suit ɗinsa a hannu, necktie ɗinma haka. Gashinsa kansa yau sama-sama ya samu gyara. Haka yake shi, a kullum matsalar al'umma itace tashin hankalinsa da damuwarsa. Da kaga damuwa a idanunsa to patient ɗinsa na cikin matsala ne. Baiko kalli inda Solomon ke tsaye da jikkarsa a hannuba ya nufi hanyar fita fuskarnan babu alamar wasa.
      Kusan cin karo sukai da Richard dake ƙoƙarin shigowa ya sanar masa an samu jirgi, kuma cikin amincin ALLAH zai tashi nan da mintuna goma sha bakwai ne, da ƙyar akama samu ticket ɗin guda biyu. A yanda Dr Yoohan yasan garin Lagos da yammaci irin haka yasan kafin su isa airport ma lokacin tashin jirgin ma ya wuce, dan haka ya yanke shawarar su tafi a Ambulance kawai zasufi samun hanya da sauri.
       Rich kansa yayi na'am da wannan tunanin na Yoohan, dan haka yama yanke shawarar kaisu da kansa ko Yoohan ɗin zai kuma samun nutsuwa.............✍

_____________________________
15

.................Kaɗan ya rage su makara a hanyar zuwa airport, ALLAH dai ya taimakesu suka isa gab. Sai da Richard ya ga tashin jirgin sannan ya bar Airport ɗin yana mai kiran Dr Sa'ad ya sanar masa ga Dr Yoohan nan ya taho su kwantar da hankalinsu.
      Duk da Dr Sa'ad baiso hakanba sai ya amsa masa harda addu'ar isowarsu lafiya. A ƙasan ransa kam ji yake kamar zuciyarsa zata babbake da wuta dan takaici da tsanar Dr Yoohan ɗin da bai taɓa tare masa komai a duniyaba bayan nusar dashi ya san kansa kawai.
     Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Madam Chioma na shigowa. Ɗagawa yay da hanzarinsa, dan yasan dai bai wuce ta kira Number Yoohan ɗin bata shigaba ko bai ɗagaba. Ya gaidata cikin girmamawa kamar yanda ya saba, kafin ya ɗora da faɗin, “Mom lafiya dai ko?”. Daga can tace, “Eh Richard, lafiya, amma na kira abokinka sau uku bai ɗagaba, nayi zaton ko yana akan aikine idan ya kammala zai kirani, sai dai har yanzu banga kiransaba. Na kuma nemesa yanzu da kaina wayarsa bai tafiya. Shine nace ko lafiya?”.
       Murmushi yay yana ƙara jinjina ƙaunar wannan uwa da ɗa a zuciyarsa. Cike da kulawa yay mata bayani yanda zata fahimta, sai dai yanda tai azamar katsesa jin ya ambaci kano sai abin ya nema firgitashi. Kafin ya samu damar tambayarta dalili harta yanke kiran.

*_ABUJA_*

       Hankalin Madam Chioma a tashe tai kiran Guards ɗin Yoohan dake shirin tahowa da Nu'aymah Abuja. Cikin azalzala ta sanar musu karsu taho su ajiye Nu'aymah a police station ɗin maza su nufi airport su tarbi Yoohan gashi nan ya taho da ga Lagos. Tai mugun basu gargaɗi akan inhar wani abu mara ƙyau suka bari ya faru da Yoohan ɗin yau to su tabbatar a bakin aikinsu kenan, bayan horo mai tsanani da zasu fuskanta kuma.
              Sanin Madam Chioma zata aikata fiye da abinda ta faɗa inhar akan Yoohan ne ya saka guards ɗin Yoohan bin dukkan umarninta. Har an fito da Nu'aymah da ko harara babu wanda yay mata a station ɗin, hasalima tana a office ɗin d.p.o tunda aka kawota suka sanarma d.p.o halin da ake ciki game da umarnin mahaifiyar uban gidansu.
       Babu musu ya amince da ajiye Nu'aymah har suje su dawo, su kuma suka shiga motocinsu suka bar station ɗin zuwa airport ɗakko Dr Yoohan da suka san nanda mintuna ƙalilan ne jirginsu zai sauka.

      Murmushi Nu'aymah tayi tana mai buɗe tafin hannunta ta kalli ƴar takardar da baba malam ya saka mata lokacin daya kamo hannunta. Takardar ta sake buɗewa ta karanta addu'ar dake ciki tana murmushi, wata irin ƙaunar mahaifinta da tausayinsa na ratsata a zuciya da ɓargo. A yau ta ƙarajin ƙwarin gwiwa akan shirin mahaifin nata. Wanda daga ita sai shi sai ALLAH daya hallicesu sukasan da shirin. Amma ko Umm yaja mata gargaɗi mai ƙarfi akan karta bari ta sani, bakomai yasashi yin hakanba sai wani dalilinsa da itama yace ba yanzu zai sanar mataba sai nan gaba.

   Gaba ɗaya Yoohan ji yake kamarma jirgin baya wani sauri, duk bayan mintuna sai ya kalli agogon hannunsa yayi ƙaramin tsaki da Solomon ne kawai ke jinsa, yay masifar ƙosawa yaga sun sauka. A yanda hankalinsa ke a tashe har sai da Solomon yaji tausayinsa ya kamasa. Yana mamakin yanda Dr Yoohan sam babu wani ƙyashi ko ƙabilanci a ransa, game da aikinsa bai taɓa banbanta kai ɗan wane addini bane ko kai ɗan wane yankine. Kansa tsaye yake ƙoƙarin sa, shiyyasa a kullum ALLAH ke sake ɗaukaka darajarsa, dan kullum bayin ALLAH cikin masa addu'oi suke a zahiri da baɗinin zuciya.
          Duk da burinsa nason jirgin yay saurin sauka ahakan bai hanashi fita cikin nutsuwa ba lokacin da jirgin ya taɓa ƙasa. Yanda yake tafiya kawai ya isa abin kallo ga mutane. Duk da fuskarsa kullum a cinkushe take hakan bai hana ya ɗauki hankalin masu kallonsa daga maza har mata ba.
         “Welcome sir”. Yaji an faɗa Lokacin da suke isowa wajen masu taxi shi da Solomon dake a bayansa. Kamar zai share sai kuma dai ya juya. A bazata idanunsa suka sauka akan guards ɗinsa waɗanda baiyi zato ko tsammanin ganiba.
     Da sauri suka ƙaraso gabansa zuciyarsu na dukan ɗari-ɗari ganin kallon da yake musu na tsagwaron mamaki da tuhuma, cike da girmamawa suka shiga gaishesa ɗaya bayan ɗaya, kafin su ɗora da masa bayanin Mom ce tace suzo su tarbesa.
      Duk da akwai magana a bakinsa game da ganin nasu a kano sai ya share bai yiba. Ya nufi inda ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa mota ya shiga.
       Sai da suka fito da ga airport ɗin gaba ɗaya suka hau kan titi sannan ya jefama driver da Solomon ke kusa da shi tambaya a bazata.
     Cikin harshen nasara yace, “Miya kawoku kano?”. Cikin faɗuwar gaba driver ya kallesa ta madubi. Sam bama kallonsu yake ba, hankalinsa nakan waya yana dannawa. Cikin ɗan rawan baki na rashin gaskiya driver ya bashi amsa da faɗin, “Sir M... Madam ce ta aikomu”. “Yin me?”.Yoohan ya faɗa da ɗago fararen idanunsa ya zubama drivern cike da nazari. Sosai kallon ya firgitashi, dan anyi sa'a lokacin da Yoohan ɗin ya ɗago idanu yayi dai-dai da ɗagowar driver shima ya kallesa. 
     Saurin riƙe sitiyarin yayi jin zai ƙwace masa, dan har motar sai da tayi ɗan tangaɗi kaɗan. “I am sorry sir” driver ya faɗa da sauri ƙirjinsa na dukan tara-tara ganin yana neman zubar dasu a ƙasa. Shiru Yoohan bai tanka ba, hasalima ya ɗauke kansa tamkar baiga wani abu daya faru ba. Sai ma ya ɗauka waya yay kiran Dr Sa'ad da kai hannu saman kunnensa ya gyara Bluetooth ɗinsa na fama dake a maƙale.

       Solomon da duk ya fahinci akwai wani abu dangane da zuwan ƴan uwanasa kanon ya haɗiye yawu da ƙyar shima yana satar kallon madubin, ganin hankalin Yoohan ɗin baya garesu sai yay saurin maidawa ga drivern. Ƙyaftama juna idanu sukai, alamar dai sun saba da yaran. Solomon ya ɗan gyaɗa kansa yana gyara zama.
     A haka suka isa asibitin batare da kowa ya sake magana ba. Tun kafin a buɗe masa shi harma ya buɗe ya fice abinsa. Da yake yau zuwan bazatane Dr Sa'ad kawai ya san zaizo sai Dr Aysha, sauran Doctors ɗin basu fito sun tarbesa ba kamar yanda suka saba.
    Sai dai tun shigowar motocinsa wasu daga ma'aikatan asibitin suka fahimci shine. Yayin da gefe guda kuma da ya zama abin kallo ga mutane. Musamman ma yanda yake tafiya Guards ɗinsa na take masa baya. Waɗanda suka sanshi nata faɗin, “Dr Yoohan yay zuwan bazata, yaukam za'asha masifa musamman akan ma'aikatan dakeda sakaci akan aikinsu. 
     Duk da ya fahimci yanda wasu a cikin ma'aikatan ke ta guje-gujen sanarma iyayen gidansu zuwansa basuko ishesa kalloba. dan abinda ya kawosa shine kawai a gabansa ba su da shirmensu ba.

     Tunda su Solomon sukaga shigewarsa sai yaja hannun ɗaya daga cikin Guards ɗin suka fito, sauran kuwa na tsaye ƙiƙam tamkar an dasasu gadin duniya🙄😏, sai zazzare idanu suke sun hana masu kai kawo ta wajen sukuni. Ba marasa lafiya da ƴan uwansu kawaiba, hatta ma'aikatan asibitin a takure suke. Masu sanya da aikinsu duka sun dage saboda jin zuwan Dr Yoohan. (ALLAH ya ƙyauta. Bazakaji tsoron UBANGIJIN daya halicceka ya baka amanar wannan aikin a ranka ba sai wani shasha mutum irinka, ba kuma komai ke kawo tsoronsa ba sai gudun karka rasa aikinka🤦🏻, ya salam. Musulmai ina muka ajiye gaskiyar tamu? Ina muka ajiye koyarwar addinin namu? Ina muka ajiye tausayi dajin ƙan da aka san mumini da shi?. Ku dubafa Dr Yoohan ba musulmi bane, baɗan yankinku bane, ba yarenku bane? Amma yana nuna fushinsa akan sakaci da cigabanku, yana nuna damuwarsa akan ƴan uwanku, yarenku addininku, yayinda ku son zuciya da burin tara duniya ya rufe jinku da ganinku. Kaje asibiti kaga ana wulaƙanta marasa ƙarfi dan kawai sunzo neman lafiya. Babban abin takaicinma yafi yawa a ɓangaren mata masu haihuwa. Kaga ma'aikatan asibiti nacin zarafinsu dan kawai sun kasance ƙauyawa ko talakawa. Haba ƴan uwana, wannan aikinfa da kike cin zarafin wasu dashi tamkar mabuɗine na gida guda biyu. Wuta ko aljannah, ya rage naki/nak ka zaɓama kanka wanda kafi buƙata. ALLAH ya shiryar damu dai, ya rabbi kai riƙo da hannun ma'aikatanmu masu ƙyawawan zukata domin rahamarka da alfarmarka🙏🏻😭).

__________________________

             Tunda Addah ta isko Umm a ɗaki basu iya cema juna uffan ba. Kowa ya zabga uban tagumi ne yana saƙa mai fishshesa. Sun kwashi tsahon mintuna sha biyar a haka kafin Addah ta katse shirun nasu da faɗin, “Ni nama rasa abin faɗa wlhy akan wannan al'amari, har nawa Nu'aymah take da ƴan sanda zasuzo su tafi da ita? Mi ma to tayi musu? Sannan miyasa yaya malam zai yanke wannan hukuncin mai tauri haka?”.
          “Wannan sune tambayoyin da nake taima zuciyata Addah, amma sam na gaza samo amsar ko guda a ciki. Ina ƙyautata zaton a tafiyarsu bikin nan koma miye ya faru acan ya faru, dan........”
           “Haba Umm miyasa zakice haka? Naga dai su a cikin Orphanage suke? To mima zata aikata da har ace mu bamujisa ba?”. 
      “Addah yaran nan kafa haifesu ne amma baka haifa halinsu ba, minenema bazasu aikataba tunda basa ganin idon kowa. Ballema Nu'aymah da batajin magana sam, wuyarta dai ta samu sakewa ne kawai, shiyyasa sam banason ko gidanmu tace zataje ta kwana ko wani waje wlhy, danni bansan ina ta ɗakko wannan halin nata na tsiwa da rashin kunyaba”. Yanda Umm tai maganar cikin ɓacin rai yasa Addah saurin faɗin. “Dan ALLAH karki tsaurara harshenki akan wannan abun, mudaibi komai a sannu muji inda matsalar take. Nu'aymah har yanzu yarinyace, kuma sanin kankine duk rashin ji da tsiwar Nu'aymah batayinsa ita kaɗai sai da gudunmawar su Adawiya dama, tunda halin nasu ai duk ɗaya ne.....”
       “Humm Addah kema kinsan indai gaskiya zaki faɗa Nu'aymah ta fisu kaifi, dan duk abinda zasu aikata itace jagora”. “To kowa ya zauna akan ra'ayinsa danni bawai yarda zanyi ba, inaga dai bara nakira su Yusrah muji minene ya faru?”. Umm dai batace komaiba, tanata kuma ƙoƙarin danne damuwar dake cizon ranta da kukan dake yunƙuro mata a rai. Duk da Alhmdllh zuwan Addah a gareta ya sanyaya mata fushinta bakamar sanda ta shigoba.

        Sallamar Yusrah da Amal ce ta saka Umm da Addah ɗagowa suna kallonsu. Basai an faɗaba, daga gani kukama sukeyi. Hakan da Umm ta gani sai ya sake karya mata zuciya, tai ƙasa da idanunta tana karanto7 addu'ar neman sauƙi da sassauci wajen UBANGIJI.
     Zama su Yusrah sukai kansu a ƙasa suna sharar ƙwalla. Addah tace, “Kuka ba shi bane mafita Amal da Yusrah, ku sanar mana mikuka sani game da hakan dan musan hanyar data dace mu kama wajen amso ƴar uwarku”.
      Share hawayensu duk sukai, cikin nutsuwa sukaima su Umm bayanin abinda ya faru aranar ƙunshi, sai dai sun ɓoye cewa Nu'aymah ta fasama guards ɗin kai, sundai ce ta wulwula dutse bisa tsutsayi ya daki glass ɗin motar. Hakan da tayine kuma ya saka mutanen tsayawa amma da guduwa zasuyi. 
      Shiru babu wanda ya iya cewa komai tsakanin Umm da Addah, sai da kusan mintuna uku Addah ta sallamesu suka tafi.

         “Umm! Inaga lokaci yayi da zamu fara aiwatar da shirinmu a gidan nan gameda waɗanan abubuwan. Na kula al'amarin ƙara zurfi yakeyi kullum”.
       Murmushi Umm tayi idanunta akan Addah, ta ce, “Addah wannan ai babu saka hannun kowa a ciki, itace ta jama kanta. Ni wlhy a yanzuma naji bana sha'awar sanin wanda ke aikatawar.........”
        “Me yasa?”
Addah ta faɗa da mamaki.
     Murmushi Umm ta sake yi har haƙoranta na bayyana, tace, “Addah to minene amfanin sanin? Babu abinda sanin zai amfanar sai fitina. Idan a gidan nan yake zai zama sanadin lalacewar zumincin da aka gina bisa haƙuri da juriya. Idan kuma a waje yake za'a jawo masa tsana daga mutane a tozarta iyalansa. Addah hakan baida wani amfani a gareni, dan wlhy bana fatan kwana da wani musulmi a cikin raina koda na kwana ɗaya ne, dan bani da tabbacin wayar gari. Koma wanene UBANGIJI ya rufa masa asiri na tsahon lokaci, ya kuma fimu sanin hikimar yin hakan. To mu haƙura kawai mu barsa da UBANGIJIN ya ishesa komai”.
     Ba ƙaramin ƙurama Umm ido Addah tayiba, har sai da takai Umm ɗin ta taɓata da faɗin, “Ina kika tafi kuma?”. Murmushi Addah tayi da sauke ajiyar zuciya. Tace na tafi duniyar mamaki ne da tsarkake sunan ALLAH, Umm ki godema ALLAH ya azurtaki da ƙyaƙyƙyawar zuciya wlhy........”
     “Kema ai ya azurtaki da ita Addah, dan ina koyi da wasu ƙyawawan halayene daga gareki. Hakan yasa ƙaunar da nake miki ta dabance a zuciyata wlhy, fatar bakima bazata iya kwatantawa ba, kun bani gudunmawa ke da Baba wadda har na koma ga ALLAH bazan gazaba wajen roƙa muku rahama da yardarsa”.
       Hawayene ya cikama Addah ido kamar yanda ya cikama Umm itama, suka kama hannun juna suna murmushi cike da ƙaunar juna da ta ginu tun ƙuruciya..............✍

No comments

Powered by Blogger.