Idon Naira 16


 *_Arewabooks@Mamuhgee_*

16

Haj Maryamah na tsaye na kallonta cikeda zafi da dacin zuciya da wani mummunan nauyi a zuciyarta zainab din ta fice daga gidan rungume da yarta,


Babah dake gefen Haj Maryamah tsaye cikin shirinta tsaf na tafiya Cameroon duk jikinta neman mutuwa yakeyi da ganin samu da Rashi Dan kuwa da anbata 'yar saita Gama biye biyenta inda takeson zuwa kafin ta Isa Cameroon din.


Masu gadin gidan dasuka San zainab tun kuruciya da girma suna kallon wannan tashin hankalin zuciyoyinsu na kunci ta tafiyarta da 'yarta,


Babban tashin hankali da tsoronsu har ita Haj Maryamah din dawowar Aqeel ba zainab babu 'yarta Amma Kuma zuciyarta ta rinjayeta komai ya lalace tsakaninta da qanwarta.



Zainab kuwa tafiya kadan tayi aka fara Kiran sallar asuba Duk da hakan bata tsayaba tafiya takeyi batareda tasan inda take jefa qafafuntaba sbd rufewar ido Dana zuciya.


MARYAMAH dake goye bayanta tanajinta ba bacci takeyiba sbd tashin hankalin tuni ya tadata bacci gashi babah tsabar son tafiyar yasa Ana fara  rikicin ta dauketa ta tsala Mata wanka da ruwan sanyi.


Har akai sallar asuba aka fito gari yafara haske tafiya takeyi batareda tasan inane gurin zuwantaba

Idanuwanta kuwa sun kada sunyi jajir sun bushe Dan kuwa kukanta tuni ya tsaya harna zuci.


Tafiya taci gaba da Yi har asalin anguwarsu na gidan ubansu Wanda daqyar takawo kanta harta gane saidai tana shogowa layinsu Bata hango alamar gidansuba Dan kuwa wani mahaukacin gida take hangowa Mai girman gaske dayake nuni da gidan manya ne,


Anguwar gabaki daya ta canza tazama kamar anguwar Yan shiyasa sbd kalar samari da mutanen datake gani marasa kamun Kai sai Yan siye da siyarwa dasukai yawa.


Kofar qaton gida data tabbatarda Nan ne gidan ubanta harma da kusan gidajen hudu da aka hade akai gida daya dasu take kallo da idanuwanta dasuke qara rinewa da tsananin qunci da radadin zuciya.



Batada komai batada kowa sai wannan gidan na ubanta Wanda takeda gado acikinsa,

Saidai Kuma wannan tsarin data tadda yasa tarasa Duk wani Dan kuzarin datake ganin ta hangowa kanta.


Guri tasamu daga gefen gidan ta zame ta zauna tareda rintse idanuwanta wani zazzabin sabon tashin hankaline  yarufeta.


Agurin ta zauna tana Jin jikinta na rawar tashin hankali,


Wa zata tinkara da zancen Ina aka Kai gidan ubansu?

Wayema ya santa?

Maryamah da umma Kawai aka sani barema duka gidajen data sani na maqotansu babu gabaki daya anguwar ta zama kamar kasuwa kamar dandalin siyasa, ta Ina zata Samu mutumin arzkin da zata tambaya???


Shiru tayi tareda sunkuyar da Kai tana rasa tunanin kamawa,


MARYAMAH dake bayanta lafewa tayi a bayan nata sbd zazzabin wanka ruwan sanyin da babah tayi Mata tun kafin asuba hakama tagansu a inda Bata taba ganin sunzo ba Dan kusan MARYAMAH din Bata taba fitaba kullum suna gida Kamar mayu.


Ta Jima agurin zaune har Saida ta Dan dawo hayyacinta kadan kafin tafara kokarin miqewa sai kawai taji ihu da hayaniya ya gauraye koina

 anguwar take ta dauki ihu anata gudu....


A tsorace take kallon mutane dake gudu ta miqe tana neman hanyar tsira saidai tuni anguwar ta dauki wani irin yamutsin fada na Yan ta'addar siyasa harda makamai dasu tiya gas.


Jefarda kayanta tayi tana neman hanyar gudu Amma babu Dan kuwa sare sare akeyi sosai 

A rikice tasamu ta fada gidan dake kusada babban gidan masu gidan na neman tufewa ta fado suka rufe sunata masifa da zage zagen wannan masifa dataqi qarewa kullum haka suke a anguwar.


Itadai shirun tayi bayan babbar kofar jikinta babu inda Baya rawa sbd tashin hankali da quncin wannan rayuwar data samu kanta aciki Kuma.


Tana tsaye agurin itada wasu da yawa wainda da alama baqi ne a anguwar suma Dan hankalinsu duka a tashe yake saidai su dukkaninsu daga cikin gidan suka fito sabanin ita da shogowa tayi.


Harbe harben bindigar da akeyine yasa zuciyarta qarasa daskarewa sukuwa sauran sake shiga tsoron suka sbd tsoron kada ayi Kamen harna cikin gida tunda hukuma ce tazo ake harba bindigar.



"Allah dai ya tsinewa wainnan yayan banzan da Allah bai saka musu hakuri ba,

Ana abu daya duk zasubi su ishemu da kayan hayaniya,

Ina ramuwar baccin da banyiba sbd kasuwar Daren jiya shine zasu ishemu harda harbe harbe.""""



Daga bayansu zancen ke fitowa Dan haka dukkanin Maza da matan gurin tsoro da fargabansu yafara raguwa Dan kuwa LULU ce da kanta tafito take magana wato shahararren 'dan daudun daya Gama riquwa a bariki tareda gogewa a harkar duniyanci.


Fari ne tas dashi kyakkyawa Amma babu wani Abu daya nuna tsoro ko fargaban halinda suke ciki.


Kofar ya nufo Kai tsaye ya bude Yana cewa"


Kuzo ku fice qartin banza da wofi wlh sai antafi daku ai Dama na Hana kowace shegiya kawomun Maza a gida ku wuce.


Bude kofar yai gabaki daya ya fito batareda tsoro ba ko shakkar abinda yake faruwa a wajen.


Take kuwa yayiwa mazan cune aka shigo aka kamesu duka cikin tsautsayi aka hada harda zainab wadda kwata kwata takasa gane meke faruwa Dan hankalinta ya Jima da barin jikinta.


Har ansakata a mota ganinta da goyo Kuma kamar Bata hayyacinta yasa LULU cewa Banda ita.


Ba musu aka sauko da zainab Yan sandan suka wuce bayan sun cika mota uku da Yan ta'addar dasuka tada fadan Dama kwartayen dasuka kwana gidan karuwan LULU.


Bayan Kamen Yan sandan sun wuce anguwar ta lafa aka fara firfitowa kowa naci gaba da harkar gabansa..


Zainab kafafuwanta dake rawa takasa dagawa sbd tashiga babbar firgici na abinda yafaru din kamar kyaftawar ido.


Rasa nutsuwarta take neman Yi 

Tafara rarraba ido tana neman daurin kayanta tabar anguwar..


A dage Lulu ya kalli zainab din cikin gatse yace"


Ke Kuma daga Ina haka?

Da Alama baquwar zuwa anguwar ce

To maza kija qafafunki kibar anguwar Dan ba gurin zuwan irinki bane..


Da sauri zainab tayi gaba har tana tuntube zata Fadi...


"Ke dawo, zo

Shege kikai Kika baro gidane??


Kasa magana zainab tayi sai tayi gaba tana fasa neman kayanta duk da taso Kayan Dan basuda wasu saina jikinsu daga ita har MARYAMAH.


Ganin yanda take a kamar Mata hankali tana kallon babban gidan da gadonta yake ciki yasa LULU biyota ya kirata zaiyi magana yaransa suka iso mota kusan biyu suna masa kirarin,


"sai hajiya LULU"


Washe Baki yahau Yi Yana kallonsu sbd sune abin Alfaharinsa

Dan kuwa sune masu cire Masa baqin cikin aike kowane irine.


Kallon wadda ta iso gefensa yayi yace"


Siddi ki kaimun baquwar Nan ciki Ina tafe.


Kallon zainab yayi yace,


"Kibita Ina zuwa zamuyi magana.


Qin binta zainab tayi saidai Kuma ganin shine maqocin babban gidan yasata tunanin jiran ko zata Samu bayanin dazai isar da ita inda gidan mahaifinsu yayi.


Shikuwa Lulu ganin yanda take kallon babban gidan makocinsa Kuma maqiyinsa yasashi son tsayar da ita yaji 

Babbar fatarsa ace MANDE DS ne yayiwa matar wani abun yayi amfani da hakan ya lalata Masa suna da komai ya nuna Masa iyakarsa.



LUKMAN AHMED Wanda ake duniya ta sani da Lulu Asalin Dan anguwar ne Wanda mahaifinsa shima rasuwa yayi tun Yana qanqani,

Shi kadaine agun mahaifiyarsa namiji  sai qanwarsa mace wadda ta rasu sanadiyar fyade da akai Mata da qananun shekaru,


Rasuwar qanwarsa ita tayi sanadiyar ta mahaifiyarsa wadda ta rasu bayan sunyi yawon Sharia Har qarfinsu yaqare babu nasara sbd Dan manya ne yayi Mata fyaden bayan yayi shaye shaye.


Lulu yayi gwagwarmayar rayuwa bayan rasuwar mahaifiyarsa ya dauki fansar abinda akaiwa qanwarsa da hannayensa ta hanyar saka mugun itace yaron da yayi barnar dukan da yayi sanadin daya rasa idonsa daya da qafafunsa duka biyun tareda hakoransa na Hana guda shida.


Hakan yajawa Lulu masifa Mai tsanani aka aikasa gidan yari tsawon shekaru goma Sha daya

Yana fitowa yashiga harkar siyasa inda yasamu shahara amatsayinsa na 'dan daudun daya Gama cire tsoro da shakkar kowa.


Lulu yasamu shiga da suna sosai duniyar Yan siyasa da Yan duniya,


Gidan abinci ya bude babba Mai kyau da tsada,.

Ana haka aka Kuma yiwa yarinyar datake Masa aikin abinci a restaurant dinsa fyade Wanda yaja aka rufe restaurant din nasa yayi hasarar duka Dan arzikinsa..


Lulu yasha gwagwarmaya da wahalar rayuwa matuqa kafin yasamu yadawo gidan ubansa ya gyara..


Tun bai Gama gyaranba alhaji MANDE DS mahaifin Yaron dayayiwa kanwarsa fyade ya siye gidajen layin kusan guda hudu a jere ya bugesu yayi babban gidansa agurin batarda ya dubi lalacewar da anguwar tayiba tareda ga Kuma qarin Shi din Dan siyasa ne take jamaarsa suka sake maida anguwar ta yan siyasa.


Alokacinda mande ds ya siye gidajen yasone ya siye harda gidan Lulu sbd abinda yayiwa dansa yaketa sakawawa Ana lalata komai na lulun,


Rikicin siyan gidan lulun dayaqi saidawa ne yasa yane mande ds ne ke lalata Masa komai na rayuwa Dan haka yaqi saidawa qarshe ya maida gidan nasa na karuwai Dan kuwa gidan babbane dakuna birjik.


Mugun zama sukeyi da junansu sbd babu Mai kaunar wani tsakanin Lulu da alhaji mande ds din,


Lulu siyasar dayasan baa kaunar mande ko kadan ita yakeyi bakin Rai Dan haka yasa anguwar kullum cikin fadan sare sare akeyi na siyasa ga Kuma qaramar kasuwa a gurin,

Ga gidan Lulu daya shahara na karuwai,

Ga babban gidan abinci daya Kuma budewa anan Dan haka dai anguwar ta lalace gabaki dayanta babu mutumin kirkin dake zuwa,


Lulu da qarfin iko da lalacewarsa da karuwansa yayi amfani ya lalata suna anguwar kwata kwata sbd kawai duk lokacinda aka ambaci anan gidan Alhaji mande ds yake mutuncinsa ya zube a idon mutane.



*****Zainab ya kalla bayan yashigo palonsa ya zauna a daya daga cikin kujerun palon Yana kallon zainab data kasa zama tana tsaye tana jiransa itama.


Cikin sakewarsa irin ta Wanda baida damuwa yace"


Kece zakiyi magana ko nine zanyi???


Batareda tayi Masa kallon duka idoba ahankali tayi Masa bayanin gidan mahaifinta tazo nema.


Da mamaki ya tambayeta gidan datake nufi Dan duka gidajen yasansu tunda shima anan ya tashi.


Bayanin gidansu da mahaifinta tayi Masa take yaganeta Dan shekarunsu daya.


Cikin danne dacin Ransa na shekaru dasuka wuce ya sanar da ita Shi Dan Iya Fatu ne wadda ta reneta bayan rasuwar mahaifiyarta.


Da mamaki ya tambayi yanda ta haifi Yar dake bayanta Amma takasa sanar dashi komai sbd tasake shiga tsoro da firgicin rayuwa Kuma bayan Jin abinda ya samu iya Fatu dashi lulun.


Zaman Dole yasata sbd kukan da MARYAMAH ta fara 

Ta sauketa

Yasa aka kawo Mata abinci Mai kyau daga shagon kicin din restaurant dinsa tabawa MARYAMAH Dan ita bazata iya cin komaiba 

Duniyarta da komai nata ya tsaya.


Sallar asuba da tashin hankali yasa bataiba tayi a Rana tsaka kafin taci Dan sauran abincin da MARYAMAH din ta rage bayan ta yagalgala.


Da fari hanata tafiya yai sbd zai bincika Mata tagurin wa mande ds ya siye gidan nasu.


Batada zabi batada mafita tunda ko ta fita batada gurin zuwa Dan haka ta zauna a gurin Lulu din Wanda kaf gidan dakinsane kawai yakeda Palo da dakuna biyu aciki kowane da toilet sbd shine Mai gidan Kuma shugaban gidan.

##MAMUH#

#IDON NERA

#AQEEL ASAD

#HOTLOVE/MARRIAGE




*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.