Abokin Aikina Book 1 Page 12
LAMBA SHA BIYU.*
_Da safe ma haka muka tashi yana haɗe fuska, shirin fita ofis ya yi yana ƙoƙarin ficewa na sha gaban shi tare da riƙo hannun shi. Cikin damuwar da ta bayyana kanta a saman fuskata na ce da shi,_
"Wai me hakan yake nufi ne? Ban san me na yi maka ba jiya daga magana ka yi fushi da ni. Yanzu ma ga shi kana ƙoƙarin ficewa babu walwala. Don haka don Allah ka yi haƙuri idan har akwai abin da na yi maka ban sani ba"
_Bai ce da ni komai ba, ya zare hannuna daga riƙon da na yi masa ya fice. Zama na yi cikin sanyin jiki tare da yin tagumi hannu biyu ina tunani, da zancen zucin da na shiga yi ni kaɗai ina bai wa kaina amsa. Domin jikina ya ba ni kamar akwai wata matsala dangane da lefen, shi ya sa ba ya son maganar kuma ba ya son tattauna maganar da ni. Ajiyar zuciya na sauke tare da cin alwashi a raina, ba zan sake yi masa maganar lefen ba._
_Domin matuƙar tayar da zancen zai kawo mana rashin jituwa to babu amfanin dawo da hannun agogo baya.Tun daga lokacin ban sake yi masa maganar ba, shi ma bai ce da ni komai a kan hakan ba. Ummata ma tun tana tambaya ta har ta daina, wataƙila kame-kamen da nake yi wurin kare Mukhtar, ya sa ta gano abin da nake ƙoƙarin ɓoye mata._
_Wata uku da aurenmu na samu ciki, wanda ni ban ma san da shi ba, har sai da Mamar shi ta turo mini abokiyar zamanta tana tambayar, yaushe rabon da na ga al'adata. Shiru kawai na yi ina tunani kafin na yi mata bayanin wata ɗaya ne kawai ban gani ba. Farinciki kwance a kan fuskarta ta fice, na bi ta da kallon mamaki domin kaina ya ƙulle da tambayar. Saboda na manta shaf da wani zancen ciki."
_A lokacin da Mukhtar ya dawo gidan da yamma, na fahimci kamar yana cikin damuwa duba da yadda ya yi zaune shiru yana tunani. Domin ko abincin da na kawo masa bai ci ba sai cizon haƙoran shi yake yi. Zama na yi kusa da shi cikin kulawa na ce da shi,_
"Fatan dai lafiya?"
_Shiru ya yi mini ba tare da ya ce da ni komai ba, ya duƙar da kan shi ƙasa yana kallon ledar da ke malale cikin falon nawa. Ni ma ganin haka ban sake cewa da shi komai ba na yi shiru ina tunanin wa ya taɓo shi._
"Yanzu ke kin shirya haihuwa a wannan lokacin da muke ciki?"
_Tambayar da ya jefo mini kenan cikin kaushin muryar da ta tona asirin ɓacin ran da yake ciki. Mamaki fal raina na bi shi da kallo cike da rashin fahimtar inda ya dosa._
"Haihuwa ai ba a shirya mata, domin idan lokacin yin ta ya zo ko ana so ko ba a so sai an..." Zancena kenan wanda bai bari na dire ba ya katse ni da cewa,
"Dakata Malama! Ba wa'azi na ce ki yi mini ba! Kawai amsa nake so ki ba ni."
"Idan har amsata kake son ji a nan, to ni ban da zaɓi ko jayayya da hukuncin Allah. Ko yanzu na samu ciki zan yi godiya ga Ubangiji, idan kuma ban samu ba zan jira lokacin da zai zo, ai abin farinciki ne gare mu duka." _Amsar da na ba shi kenan cikin ɓacin rai, domin na fara fuskantar abin da yake nufi da tambayar, wanda nake ji a raina ba zan lamunci hakan ba._
"To cikin ya zo, kuma ya ba ki ki yi ta farinciki."
_Yana gama faɗar maganar ya miƙe fuu ya fice falon, tare da shura takalmin shi ya bar gidan. Idanuwana a kan kulolin abincin da na kawo masa bai taɓa ba, haka kawai na ji hawaye yana bin kumatuna ba tare da na san lokacin da ya fito ba. Bayana na jingina da kujerar da nake zaune, kaina a sama ina tunanin daman haka auren yake. Domin zuwa lokacin na fara fahimtar farincikin da ke cikin aure kaɗan ne, saboda damuwar da na fuskanta a cikin shi ta fi jin daɗin shi yawa._
_Tun daga wannan maganar ya shiga fushi da ni tsawon kwanaki. Domin bayan abincin da ya daina ci har da ƙaurace mini ya yi a shimfiɗa. Amma damuwar rashin cin abincin da ya haifar wa zuciya, ya fi na haɗa shimfiɗar yawa. Saboda ko kaɗan wannan lamarin bai dame ni ba a lokacin, asali ma ji nake yi kamar an takura ni a duk lokacin da ya nemi haƙƙin shi wurina. Sai dai ba na musa masa balle na yi ƙorafin da zai gano ba na maraba da shi. Mun ja lokaci kafin ya saki fushin mu dawo kamar yadda muke, amma ko kaɗan ba ya zancen cikin. Ni ma ba na yi masa don na gama gano inda ya dosa._
_Na fara fuskantar matsalolin cikin tsakanin ƙyanƙyami da aman da nake sha, a wasu lokutan da idan na ci wani abu zuciyata ta kasa kwanciya. Alhmdulillah! Mahaifiyar shi da 'yan gidansu suna ba ni kulawa, domin duk abin da nake so ko ban nema ba za su kawo mini na ci ko na sha. Ɓangaren shi ne kawai babu gamsasshiyar kulawa, musamman irin wadda masu ciki suke buƙata a yayin laulayi. Duk da ina jin haushin ko-in-kular da yake yi wa cikin, amma ba na nuna masa saboda ko kaɗan ba na son abin da zai haɗa mu rikici._
_Cikina yana wata huɗu ya yi bulaguro zuwa Abuja, ya bar ni daga ni sai cikina sai Mahaifiyar shi da dangin shi. Waɗanda suke faɗi-tashi a kaina domin su ɗebe mini kewar shi, kuma su faranta mini. Takanas Yayar shi ta kawo mini babbar 'yarta domin ta taya ni zama har ya dawo. Duk da wani lokaci a cikin gidansu nake wuni sai dare ya yi na dawo gidan na kwanta._
_Sai da ya shafe sati biyu har da kwanaki sannan ya dawo. Duk da ina jin haushin daɗewar da ya yi, saboda babu wani uzurin dolen da ya kai shi, amma hakan bai hana ni nuna masa farincikin dawowar shi ba. A daren ranar ya kashe ƙwalamar shi a kaina, amma ni ya janyo mini amaye-amaye a tsakiyar daren zuwa safiya. Saboda turaren jikin shi kwata-kwata bai yi mini daɗi ba, haka ma warin tabar da na ji bakin shi yana yi ya saka ni aman dole. Sai dai tun da ya yi mini sannu sau ɗaya ya juya kwanciyar shi yana ta minshari, jiki na ja na yi falo. A kan kujera na kwana a ranar ina ta tofar da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji a duk lokacin da na tuna da warin tabar._
_A rayuwata na tsani taba, domin ko warinta na ji sai kaina ya juya. Dalilin hakan duk mutumin da na gani yana shan taba har raina nake jin ƙyamar shi, kuma ba na zuwa kusa da shi balle warin ya dame ni. Kwana na yi ina juyi da tunanin ina Mukhtar ya haɗu da taba har ya sha, saboda tun da nake da shi ban taɓa sanin yana shan taba ba balle na gani. Hakan ya sa na shiga kokwanto a kan ita ce ko dai ni ce kawai na ji kamar ita._
_A lokacin mun cinye abincin gara har mun fara aune, dalilin haka na fara shiga wata sabuwar matsala. Duba da yadda na saba dafa abinci wadatacce na kai gidansu, bayan wanda 'yan'uwan shi suke shigowa su ci ko kuma su tafi da shi. Ga shi idan ma na dafa ni ba na iya cin nawa sai na gidansu idan an ba ni. Haka zan dafa iya konon da ya kawo, idan na cire masa na shi sai na juye musu saura a kula na kai musu. Hakan ya janyo suka fara haure mini kai, tunanin su ni ce kawai na tsiro da abin don ba na son ba su._
_Saboda ba su san daga shi ne ba, idan ya shigo da konon shinkafar ya ga da mutane a gidan sai ya je Kitchen ko wani wuri ya ɓoye ta. Sai dai ya kira ni gefe ya sanar da ni ga inda ya ajiye idan na tashi dafawa._
_Sannu a hankali suka canza mini gabaɗaya, abincin da nake kai musu ma suka daina karɓa, ni ma wanda suke ba ni suka daina aiko mini. Na shiga damuwa da neman dalilin sauyin su, na samu amsar a bakin 'yar Yayar shi wadda ta yi taya ni bacci. A lokacin da ta ga na shiga damuwa, a kan na ba ta abincin ta kai musu suka dawo mini da kayana._
"Wallahi Aunty dama kin daina ba su, don na ji suna faɗar tun da ba ki yi niyyar ba su ba gara su hutar da ke. Domin wai a lokacin da kike son ba su sai kin cika kula ki kai musu, kuma duk wanda ya shigo kina ba shi saɓanin yanzu da kika daina."
"Ikon Allah!"
_Ita ce kalmar da ta fito bakina ban shirya ba, saboda mamakin zancen da kuma rashin adalcin da suke ƙoƙarin yi mini. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na ce,_
"To wallahi Sajida ba daga ni ba ne. Shi yake siyo shinkafar kaɗan shi ya sa nake ba su kaɗan. Amma da a ce zai siyo wadatacciya zan ba su kamar yadda na saba, wataƙila ma a fi haka musamman yanzu da ba komai nake iya ci ba." Na ƙare maganar cikin damuwar da ta bayyana kan fuskata.
"Ki ƙyale su Aunty kowa ya yi nagari don kan shi."
_Amsar da ta ba ni kenan a ƙoƙarin ta na kwantar mini da hankali, kuma sosai ta shiga jikina. Saboda zallar gaskiyar da ke ciki tare da jin daɗin fahimtar da ta yi mini._
_Da ya dawo ban ɓoye masa komai ba na sanar da shi, saboda ya yi wa abin tufƙar hanci ta hanyar sauya awon da yake yi domin a samu zaman lafiya. Amma fitittike wa ya yi ya shafa wa idonsa kwalli, a kan cewa; konon shinkafar shi ne daidai ƙarfin shi. Na yi ta so na nuna masa illar ƙaramin awon da matsalolin da zai haifar mana a nan gaba, amma ya nuna mini ya fi ni sanin komai da tsarin rayuwa. Dole na ƙyale shi a yadda yake so don ba ni da ikon saka shi dole, musamman da na ga ya fi ni son dangin shi amma bai ji kunyar yin abin da yake so ba._
_Haka muka ci gaba da tafiya babu jituwa tsakanina da mahaifiyar shi da ƙannen shi, har zuwa lokacin da cikina ya yi wata tara haihuwa yau ko gobe. Wanda a lokacin ya karta mini wani gagarumin laifin da ya so katse igiyoyin au..._
Zuuuu! Shi ne sautin virbration kiran da ke fitowa a cikin wayata saboda tana silent. Wanda ya dawo da mu daga duniyar waiwayen bayan da muka lula daga ni har Amina, wadda ta yi luf tana sauraro na ko motsin kirki ta kasa yi.
Da hanzari na ɗauki wayar saboda ganin sunan Baba Ali ɓaro-ɓaro a jikin fuskar wayar. Gaishe shi na fara yi cikin mutuwar jiki da sanyin murya, bayan fargaban da nake ciki a kan kiran na shi. Wanda ya haifar mini da bugun zuciya da sauri da sauri, kafin na fara jin maƙasudin kiran cikin faɗa da ɗaga murya.
"Mijinki ya kawo ƙarar ki wurina, a kan abubuwan da kike yi a wurin aiki. Waɗanda bai kamata gare ki ba, a matsayinki na matar au..."
"Wallahi Baba ƙazafin da ya saba ne kawai babu gaskiya a ciki. Burin shi kawai na daina aikin nan bayan kuma shi ma yana rufa masa asi..."
Amsar da na ba shi kenan cikin muryar kuka saboda tsabar jin haushin abin da Mukhtar yake yi mini. Shi ma ya tare hanzarina yana faɗin,
"Ko ma dai mene ne ki ji tsoron Allah a
matsayinki na matar aure. Don kin san hukuncin matar da ke cin amanar aure, don haka ki kiyaye. Allah ya ƙara miki haƙurin zama da shi tun da Habi ta zaɓar miki zaman. A tunaninta irin wannan zaman ya fi alheri da zaman ki bazawara."
Hawaye na goge a kan fuskata sannan na ce, "Don Allah Baba ka yi haƙuri. Wallahi ba na ƙaunar Mukhtar a rayuwata kuma na tsane shi."
"Ki yi haƙuri Allah yana tare da ke."
Daga wannan maganar da ya katse kiran, sauke wayar na yi daga kunnena ina zuƙar majinar kuka. Kayana kawai na haɗa a jaka na miƙe na fice daga offis ɗin, ba tare da na yi wa Amina sallama ba saboda ƙunar da zuciyata ke yi.
Leave a Comment