Abokin Aikina Book 1 Page 13

 


LAMBA SHA UKU.*


         Karaf na ci karo da mutum ba tare da na tantance wane ne ba. Amma duk da hakan ban jira komai ba na yi gaba, balle na bai wa wanda muka yi karon da shi haƙuri.

     Idona a rufe na fice ma'aikatar tamkar na kifa. Jefa ƙafafuwana kawai nake yi, a dalilin duhun baƙincikin da ya yi mini rumfar da ta lulluɓe mini zuciya.

     Ban yi tsayuwar jiran adaidaita ba na ci gaba da jefa ƙafafuwa cikin sauri, har na yi katarin ganin wata za ta wuce babu kowa a ciki na tare. Luf na yi bayan na zauna  ina sauraron waƙar da ke tashi a cikin daidaitar. Wadda nake jin ta har tsakiyar zuciyata, domin ta ƙara rura wutar tsanar Mukhtar a cikin zuciyata. Saboda duk wani  baiti da ke fita a cikin waƙar, ina alaƙanta shi da ni kuma ina ji a raina tamkar ni ce nake furzo su daga bakina zuwa kunnen Mukhtar. 

 

'Ka rusa soyayyar da zuciya ke ma.'

'Na daina ƙaunar ka zan iya rantse ma.'

'Ba wata alfarmar da za na iya yai ma.'

'Ka naɗe tabarmar kunya ka je Allah ya yafe ma.'


'Maƙaryaci babu ni babu shi.'

'Tuntuni mun raba hanya da shi.'

'Ko da tsautsayi ya gifta.' 'Ni ba ni so nai gamo da shi.'

        Waɗannan baitukan ba ƙaramin tasiri suka yi wa zuciyata ba, domin sun ƙara tunzura ni na kai maƙura a kan abin da na kitsa wa zuciyata.            

      Wanda na gama amanna da cewa shi ne abin da zai kawo ƙarshen zaman yaƙin da nake yi da Mukhtar. Har aka kai ni ƙofar gidan mai adaidaitan bai canza waƙar ZO MU SASANTA ba tamkar da gayya. 


    Jikina yana rawa na biya shi kuɗin shi na nufi ƙofar gidan, ganin shi a buɗe ya tabbatar mini da su Ummu Salma suna nan. Afujajan na faɗa falon da ƙudurin na aiwatar da nufina, sai ga shi na yi turus babu shiri saboda Ummata na gani zaune a falon cikin yarana.

      Har a raina ban ji daɗin ganin ta ba, ƙarin takaicin kuma ƙofar ɗakin Mukhtar a rufe alamun bai dawo daga aiki ba. Gani na ya sa su Ummu Salma suka yo kaina suna ihun murna tare da faɗin,

 "Oyoyo Mama!" 

Fuskata a haɗe na isa tsakiyar falon na zauna babu yabo babu fallasa na gayar da ita. 

       Ba ta amsa mini ba, sai kallon da na ga tana yi mini ta gefen idona, Domin na kasa haɗa ido da ita. Don ba na so ta katse mini hanzari dangane da abin da na kitsa wa zuciyata, ko da tsiya-tsiys ko ta halin ƙaƙa. 


      Ummu Salma ta kawo mini abinci na ce ta mayar da shi sai na tashi, sannan suka yi tsakiyar gidanmu suna wasa suka bar mu mu zanta. Kasancewar ba a zuwa makarantar islamiya a ranar.

     Ganin hakan ya sa na miƙe zan shige ɗakina da niyyar na yi sallah, saboda ƙarfe biyu da rabi har gota. Umma ta yi hanzarin faɗin "Wurinki na zo Zaituna."

      Cikin dakiya na ce "Sallah zan yi lokaci ya tafi."

      "Je ki dawo ina jiran ki, duk da ban so na daɗe ba." 

     Ban iya sake cewa komai ba na shige ɗakina, a gurguje na yi sallar ba tare da na tsawaita ba. 

     Dawowa na yi na zauna kan  kujerar da muke fuskantar juna ni da Umma, Gyaran murya ta yi sannan ta kira sunana har sau uku. 

"Zaituna!"

"Zaituna!"

"Zaituna!"

      Sai da ta ɗan tsahirta sannan ta ce, "Sau nawa na kira sunanki?"

      Cikin dakiya na ce "Sau uku." 

    

      "Idan har da gaske ni ce na haife ki kuma na isa da ke, to ki daina kula wannan mutumin daga yau har zuwa abada!"

       Shiru na yi ina maimata kashedin da take ƙoƙarin yi mini da MD a zuciyata, wanda nake ji gara ta ɗiga mini ruwan dalma a jiki da ta yi mini iyaka da shi. Zuciyata a soye na goge hawayen da ke kwarara daga idona zuwa dandamalin fuskarta. 

       "Ba zan iya daina kula shi ba, duk da babu komai tsakanina da shi. Amma a matsayin shi na babba a wurin aikinmu, akwai abubuwan da za su haɗa ni magana da shi ko ba na so. Matuƙar dai ina aiki wurin ba sauya mini wani aka yi ba."

     Amsar da na ba ta kenan kafin shiru ya ratsa tsakani, tsawon mintuna ba ta ce da ni komai. Wanda ba na raba ɗaya biyu a kan maganganun da na yi ne take juyawa a ranta.     

     Kuka na shiga yi marar sauti domin a lokacin ba na iya taɓuka komai idan ba shi ba. Cikin muryar kuka na ji sautinta yana fita daga bakinta zuwa kunnena.

      

       "Na san ina tauye ki Zaituna, amma ni Allah ya sani akwai tunanin da nake yi miki daban, dangane da tarbiyyar 'ya'yanki. Domin sun kai lokacin da suka fi buƙatarki, kuma sun kai lokacin da kike cin moriyar abinki. Ba na so ki bar yaranki a gantale domin kin fi kowa sanin ubansu ba zai iya kula da su kamar yadda kike yi ba. Abu na biyu babu inda za ki je da su matuƙar kina buƙatar zama lafiya a wani gidan auren. Sannan ni ba ni da muhallin kaina balle na kwashe su na riƙe a hannuna. Kuma kin san babu kyatawa idan kika tare gidan Alhaji Ali daga ke har su, saboda ɗawainiyar kan shi ma ta ishe shi balle a ƙara masa da wata, bayan ya gama taki tun ƙurciya har girma. Saboda gidan zumu ba kasuwa ba ce balle a shiga duk lokacin da aka ga dama. Ki yi nazari da kyau zawarci a wannan lokacin da muke ciki ba abu ne mai kyau ba. Idan kika saka wa kanki haƙuri a yadda kike yanzu, a gaba za ki tsinci ribar hakan a wurin 'ya'yanki, a lokacin da ƙafafuwansu za su tsayu."


        Ruwan hawayena ya ƙara ɓallewa, domin na san gaskiya ce take faɗa mini. Amma ta kasa gano har yanzu ban mori aure ba, ban san daɗin aure ba balle more wa saduwar aure tsawon shekara goma sha biyu da na yi a gidan Mukhtar. Wanda na canye lokutan ina bautar auren kuma ta sani amma take ta kawar da kai. 

      'Shin idan ban ƙwaci wuyan hannuna na samu 'yanci a yanzu ba, yaushe ne zan taimaki kaina domin na fita daga wannan bahaguwar rayuwar aure, marar fasalin da nake ciki?'

        

     Tambayar da na jefi kaina da ita kenan kafin na yi jarumtar furta mata cewa, "Ba zan iya ci gaba da wannan zaman ba, domin Allah ma bai ce na yi irin shi ba. Asali ma ya ba ni damar na kai kotu a raba mana auren matuƙar na ji ba zan iya jurewa ba."

       "Ana barin halas ko don kunya Zaituna, idan ba ki raga wa Mukhtar saboda yana aurenki ba, za ki raga masa ko don 'ya'yan da ke tsakaninki da shi. Ki yi haƙuri ki bar wa Allah lamarinki, da yardar Ubangiji sai ya kawo miki haske a cikin rayuwarki ta nan gaba. Matuƙar kika saka dauriya kuma kika iyar da ladarki domin ki kai matakin nasararki."

      Ban ce da ita komai ba, domin na sani duk yadda zan nuna mata abin da nake nufi, ba za ta fuskance ni ba, balle ta gamsu da ra'ayina mu daidaita. 

      Nasiha ta shiga yi mini wadda fiye da rabinta a kan na ji tsoron Allah ne, sannan da ƙoƙarin gina mini katangar ƙarfen da take yi a tsakanina da MD.


     Har ta yi ta gama ban sake cewa komai ba, raka ta na yi ƙofar gida ta tafi tana goge ƙwalla tare da saka mini albarka. Dawowa na yi na zauna, zuciyata a cunkushe ina tunanin me zan yi na raba kaina da auren Mukhtar.

     "Ki gudu kawai!"

Amsar da zuciyata ta ba ni kenan, na nutsu sosai ina nazarin hanyoyin da zan bi na gudun ba tare da wani tarnaƙi ba. 

      Ajiyar zuciya na sauke saboda kai wa matsaya ɗaya a kan wannan shawarar da zuciyata ta gama ba ni. Amma hakan ba zai yiwu ba har sai ya dawo na fara ta kan shi, idan ya ƙi bin ra'ayina sai na ɗaukar wa kaina matakin gaggawar da ya fi dacewa da ni.


     Ranar bai dawo ba sai da dare ya yi sosai sawu ya ɗauke. Ƙarfe ɗaya saura na ji yana rufe gida, na miƙe zumbur tamkar wadda aka tsikari da allura. Na buɗe ɗakina na fito a daidai lokacin da ya shigo falon, hanzarin shan gaban shi na yi ban yi jinkirin komai ba na ci kwalar shi. Cikin matsanancin fushi da kai wa ƙololuwar ɓacin rai na fara faɗin,

       "Idan ka haifu cikin uwarka da ubanka ka sake ni yanzun nan!"


     Ƙwace kan shi kawai ya shiga yi yana shegen murmushin shi, wanda a koyaushe yake tura mini haushi da shi idan irin haka ta kama. "Shin ba ka ji maganata ba ne? Ka sake ni na ce! Idan har ka haifu cikin uwarka da ubanka!"

        Fisge kwalar shi kawai ya yi, sannan ya bangaje ni ya shige ɗakin shi, ba tare da ya ce da ni komai ba balle na san matsayata. Kuka na fashe da shi mai sauti tare da fasa ihu cikin ƙaraji na zube ƙasa ina turmuza tamkar ƙaramar yarinya. 


     Ban san ya aka yi ba na ji muryar su Ummu Salma a kaina, suna kuka tare da rungumata suna faɗin don Allah na yi shiru. Tausayinsu ya sa na ƙara sautin kukana maimakon na rage kamar yadda suke da muradi. 

      Mun ɗauki lokaci muna kukan daga ni har su kafin ya fito ya janye su daga jikina, suna tirjiya ya tura su ɗakinsu ya rufe ƙofar ya zare key. Ko kallo na bai yi ba ya koma ɗakin shi ya rufe tare da saka masa key a lokaci ɗaya. 

      Idona a rufe na miƙe tamkar wata zakanya na yi ɗakina, kayana na shiga haɗawa a jaka maidaidaiciya. Wadda ke ɗaukar kala biyar da wasu tarkacen da ba a rasa ba, sannan na saka abubuwan da zan buƙata dole a jakar hannuna.

     Agogon da ke manne jikin bangon ɗakina na kalla, wanda ke bugawa yana nuna ƙarfe ɗaya da minti goma sha shida na dare. Amma ban ji ko ɗar ba wurin janyo jakata na rataya ta hannun a kafaɗata na fito. Cikin ƙunar rai da bushewar zuciya na durfafi ƙofar gidanmu na buɗe, kai-tsaye na fice ina jan jakata ba tare da na ji tsoron duhun daren ba, balle abin da zai same ni.



No comments

Powered by Blogger.