Abokin Aikina Book 1 Page 28
ASHIRIN DA TAKWAS.*
Da sanyin jiki na wayi safiya, domin kuwa ban yi wani baccin kirki ba a daren ranar. Hakan ya janyo mini ciwon jiki da ciwon kan da na ji ba na ra'ayin fita ranar. Kai-tsaye na tura wa MD saƙon ba na samun damar zuwa offis.
Bayan mun karya ni da yaran muka fara ƙoƙarin fitar da kujeru a tsakar gida, kafin mai adaidaita ya zo ɗaukar su.
Muna tsaka da fito da su Mukhtar ya fito daga ɗakinsa yana waya.
"Ki kwantar da hankalinki, ba ni na ce zan ba ki ba? Zan ba ki... Yawwa! Ko ke fa! Ki jira ni anjima kaɗan zan aiko mi..."
Wani tuƙuƙin baƙinciki ya taso mini, nan take hawaye mai zafi ya cika mini ido. Na fakaici idon yaran na goge, sannan na bar tsakar gidan na koma ɗakina. Kwanciya ta kenan yaran suka shigo da gudu, suna sanar da ni ga Najib mai adaidaita ya zo ɗaukar mu, na ce su tafi kawai Allah ya tsare hanya.
Bayan fitar su na ji kuka mai ƙarfi ya suɓuce mini ba tare da na shirya wa zuwansa ba. Na jima ina kukan kafin na ji sassaucin nauyin da nake ji a cikin zuciyata. Na shiga tunane-tunanen matsayin aurena da kalar zaman da nake yi a gidan Mukhtar.
Ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba sai da na ji yana rafka mini sallama a saman kai. Firgigit na farka tare da zabura saboda ganin shi a saman kaina, da hanzari ya juya zai fice ɗakin yana cewa,
"Umma ce ta aiko da kaya, ki tashi ki je ke yaran suke jira tun ɗazu."
Na miƙe ƙasusuwan jikina suna ƙara na fito ɗakin jikina liƙis, taku nake yi babu kuzari na yi tsakar gidan. Inda na ga yaran tsaye cirko-cirko da sababbin kujerun da suka kawo a gabansu, waɗanda muka ajiye kuma har sun fitar da su waje ban sani ba.
Umurni na ba su a kan su shigo da kujerun, na nuna musu inda za su ajiye da yadda za su jera mini su. Yadda na faɗa haka suka yi, nan take wurin ya fito fes ma sha Allah gwanin burgewa. Musamman da suka maƙala mini sababbin labulan da suka zo da su masu matching da kalar kujerun.
Farinciki ya ziyarci zuciyata, a lokacin da suka tafi na zauna saman kujerun ina goge ruwan hawayena.
'Umma ta kasa fahimtar gundurar da na yi da rayuwar auren Mukhtar. Ta kasa gano inda matsalata ta fuskanta ba zama da shi ne damuwata ba. Yaushe zan fita daga ƙangin wannan aure na kama-karyar da nake yi?'
Shiru na yi daga zancen zucin saboda amsar da zuciyata ta ƙara kitsa mini wadda ta sa ƙirjina bugawa dam-dam!
'Sai kin tsufa yaranki za su yi miki amfani idan ciwon hawan jini ya kama ki, a lokacin za su dinga zaryar kai ki asibiti ana rubuto miki magunguna wani bayan wani.'
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"
Ita ce kalmar da ta fito daga bakina ban shirya ba,
'Idan kuwa har haka ƙarshen haƙurin da na yi zai kai ni. To rayuwar da nake yi a yanzu ba ta da wani amfani ko kaɗan, matuƙar ƙarshe na ya zo a ɗawainiyar kai ni asibiti. Domin a yi ta jera mini takardun maganin hawan jini, yarana su sha wahalar kai-da-komo da ni a tsakanin gida da asibiti.'
Amsar da na bai wa kaina kenan a zuciya kamar yadda zuciyar ce ta kitsa mini komai.
''Ya zama dole na yi wata hoɓɓasa, tun kafin wankin hula ya kai ni dare"
"Komai za ka yi yanzu, aikin gama ya gama sai haƙuri. Kuma zama da ni yanzu kika fara, don wallahi babu wata kotu ko alaƙalin da zai sakin ki ba tare da amincewa ta ba. Yadda muka fara rayuwa tare haka za mu ƙare ta, saboda babu ɗan iskan ƙaton da zan bari ya aure ki bayan ya gama bibiyarki da aurena, ba tare da ya yi duba da illar ɗaukar wa kansa kaya a dalilin auren da ke saman kanki ba."
Maganar Mukhtar kenan a kaina yana huci tamkar ya dake ni, da kallon mamaki na bi shi baki a sake. Saboda ƙoƙarin datse mini farincikin rayuwa da yake yi koyaushe. A bahagon tunaninsa wannan barazanar da yake yi ce take hana ni ɗaukar wa kaina matakin gaggawa.
Ajiyar zuciya na sauke sannan na yi dariya a matsayin tura masa haushi na ce,
"Maimakon tsoro ko fargaban da kake ƙoƙarin cusa mini a zuciya, sai maganganunka suka dawo ba ni dariya haiƙan. Wai kai a tunanin da kanka yake ba ka burgarka ce take riƙe da ni a gidanka? To ka yi kuskure kuma ka saɓa lamba. Kamar yadda na sha faɗa yanzu ma zan maimaita; neman gamawa lafiya da rabuwa da mahaifiyata cikin aminci; ya sa ba na zartar da hukuncin da nake yanke wa kuturun aurenka, a kowace daƙiƙa da bugun numfashina. Ka gode wa Allah ko lahira wani yana cin albarkacin wani; kamar yadda kake cin na 'ya'yanka a wurin Ummata yanzu, duk da kai ko kaɗan ba ka san zafinsu ba. Amma idan tani ake bi abin da ka sani ne zan maimata yanzu ka ji, idan ana saki dubu duka sai na katse igiyoyin har ma nemi ƙarin wasu na daddatsa."
A fusace ya yi kaina zai kai mini duka, na yi hanzarin ja baya tare da nuna shi da hannu ina cewa,
"Kul! Kada ka yi gangancin taɓa ni ka janyo na yi maka aika-aika yanzun nan. Na fi so na je gidan kaso da na bari ka dake ni ka hana ni kokawa, domin mari da tsinka jakar da kake yi mini kullum ba don ba na iya ramawa ba ne nake ƙyalewa. Idan ka kai ni bango kuma zan nuna maka na fi ka zama 'yar tarawi."
"Idan ma kin ce za ki rama ai ke ce a wahale, domin aurena ne ba kya so kuma ba zan taɓa sakinki ba."
Yana ƙare faɗar hakan a fusace ya bar wurin zai fice falon, na biyo shi a zafafe ina faɗin, "In dai wannan baƙin auren kake taƙama da shi ka faɗo. Don tuni ya lalace babu komai a cikinsa face kwasar zunubai."
"A hakan kuma za ki zauna ko kina so ko ba kya so!"
Abin da ya faɗa kenan ya fice gidan, tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da ƙirjina ya buga sanadin sautin ƙarar ƙofar,
'Garam!!!'
Dawowa na yi na zauna, zuciyata sai hawa da sauka take yi ina fisgar numfashina da ƙarfi. Na ɗauki lokaci a haka sannan na fara jin sallamar wasu mata a bakin ƙofar falon.
Na fito ina amsa sallamar idona a kansu, tunanin inda na san su a raina na yi amma na kasa.
"Dangin amarya ne, mun zo duba ɗaki."
"Allah Sarki to ku shigo mana!"
Na ƙare maganar cikin sakin fuska da murmushin yaƙe na yi gaba, suka bi ni a baya na ja na tsaya a bakin ƙofar ɗakin. Da fara'ata a kan fuska na ce da su,
"Ku jira na karɓo muku makullin ɗakin a wurinsa."
"Ai shi ya ce mu shigo, ga makullin a nan ya ba mu."
"Faɗuwa ta zo daidai da zama, yanzu yake sanar da ni zai ba ni na ajiye muku kafin ya fita."
Maganar da na yi kenan ina 'yar dariya, a ƙoƙarin kore damuwar da ke kan fuskata.
"An hutar da ke ai tun da ya ba mu!"
Wata matashiya daga cikinsu ta faɗa cikin haɗe rai tana ƙoƙarin buɗe ɗakin, ɗakina na nufa zuciyata tana tafasa saboda duka biyun da yake ƙoƙarin hawa kaina. Tsakanin rashin mutuncin da Mukhtar ya yi mini da rainin hankalin da dangin amaryarsa suke ƙoƙarin kawo mini.
Wanka na faɗa shaf-shaf na dirje jikina, cike da jin haushin bai sanar da ni zuwansu ba. Da ban bari suka same ni a yadda nake ban cancanɗa kwalliya ba.
Ƙwafa na yi kawai tare da cije leɓen ƙasa a lokacin da na gama shafa hoda sama-sama. Wata doguwar rigar atamfata na saka fited gawn, kuma mai fitting ɗina sosai a duk lokacin da na saka. Turaruka nake fesawa ina jiyo sautin muryoyinsu suna yaba tsarin falon.
A daidai lokacin da suka shiga kitchen na fito na kunna tv sannan na zauna kan kujera ina kallo. Duk da ba na gane komai amma ban ɗauke idona daga kan tv'n ba jefi-jefi na latsa wayata.
Sun ɗauki minti sha biyar a kitchen ɗin, suna ta maganganun da ba na tantance abin da suke faɗa. Sannan suka fito daga Kitchen ɗin suna faɗin,
"Ma sha Allah wuri ya yi kyau! Sai fatan Allah ya ba da zaman lafiya da ƙazantar ɗaki."
Kaina na ɗago daga latsar wayar da nake yi na ce da su, "Amin, har kun gama?"
Wasu biyu suka wuce suna faɗin
"E, mu za mu tafi."
Yayin da wasu masu hankalin cikinsu uku suka ce, "Mun kammala, gobe idan Allah ya kai mu za mu zo a yi jere. Allah ya ba ku zaman lafiya da haƙuri da juna."
Da murmushi a kan fuskata na ce da su, "Amin-amin." Suka nufi hanyar fita na rako su ina yi musu godiya da Allah ya tsare.
Sai da suka fice gidan sannan na rufo ƙofar na juyo zuciyata a cunkushe da takaicin Mukhtar. Don da ya faɗa mini za su zo, dole ne a tanadar musu wani abu, saboda babu daɗi su tafi hannu rabbana ba a ba su komai ba.
Ko zama ban yi ba Maman Taufiƙ ta shigo na tarbe ta da fara'a muka zauna. Kallon tsarin falon ta shiga yi da kujeruna da muke kai, fuskarta a sake ta ce da ni,
"Kujerun nan sun yi mini kyau Maman Haidar!"
"Na gode" Na faɗa cike da murmushin da ya kasa barin fuskata. Zamanta ta gyara tana faɗin,
"Wasu mata na gani sun fito daga gidan nan suna ta yabonki. Kuma jikina ya ba ni kamar dangin amaryarsu ne?"
"E, su ne. Sun zo duba ɗakin amarya da tsarin gidan."
"Cabɗijam! Lalle kin fara aika musu makaman nuclear. Domin kuwa da kunnena na ji wata yarinya daga cikinsu tana faɗin"
'Ni fa haushi ya hana ni tsayawa na fito gidan. Don wannan haɗaɗɗiyar mata ko ni aka haɗa kishi da ita an cuce ni balle Barira. Cabɗi! Na tausaya wa mata gaskiya, don ta kawo kanta inda za a ga kasawarta'
'Idan ban da ma hali irin na maza da ba a iya musu; mai irin wannan zankaɗeɗiyar macen ne zai auri Barira?'
'Shi aure ai nufi ne na Allah! Ita ce matarsa shi ya sa ya nemo ta. Don haka ku zo mu je mu bi su da addu'ar zaman lafiya, saboda alamu ya nuna a fili ta yi sa'ar kishiyar da babu ruwanta'
Sanyin daɗi na ji ya tsirga mini, domin labarin da Maman Taufiƙ ta faɗa mini ba ƙaramin faranta zuciyata ya yi ba. Shiru kawai na yi ina ta murmushi, sai da ta yi 'yar kuwwar jin daɗi sannan ta sake cewa,
"A gaskiya Maman Haidar ke ƙwaro ce! A tashi guda kin hargitsa musu lissafi sun fita da ke a bakinsu."
Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Ai shi yaƙi ɗan zamba ne, idan ba ka iya shi ba za ka sha wahalar kashe abokan gaba, kuma za a yi saurin gano maɓoyarka domin a kawo maka farmaki. Don haka ta wannan hanyar kaɗai zan iya rama abin da ake ƙoƙarin yi mini a fakaice. Saboda faɗa da tashin hankali ba zai kawo gyara ba, kuma ba zai sa a fasa abin da aka yi niyya ba. A ƙarshe ma biyu babu ake yi a rasa mutunci kuma a ɓarar da ƙima."
"Kai jama'a! Maman Haidar ke ta daban ce a cikin dubban mutane. Ban taɓa cin karo da macen da za a yi wa kishiya ta yi juriya irin taki ba. Wai don Allah da gaske ba kya jin komai a cikin ranki? Ni fa na kasa gasgata wannan lamari naki mai kama da almara."
Tambayar da ta yi mini ba ƙaramar dariya ta saka ni ba, saboda yanayin da ta yi maganar tamkar wata zautacciya. Sai da na gama dariyar sannan na ce da ita,
"Kowace mace tana da kalar nata kishin Maman Taufiƙ! Amma da a ce za a yi koyi da kalar kishin da magabata suka yi; Da mata da yawa ba su ɓarar da damar da Allah ya mallaka musu ba. Don sau da yawa namiji ba don ba ya son matarsa yake ƙara aure ba, ke wani lokaci ma ba ya ƙara ƙaunarki; har sai ya jera ki da wata ya gano akwai tazara a tsakaninki da sauran mata. Saboda haka da a ce za mu gane mu daina zafafa kishin maza idan za su ƙaro aure, da mun taimaki kanmu mun rage nauyin wahalar da muke ɗaukar wa kanmu a kan ɗa namiji. Ni kin ga ma a ranar da ya zo mini da zancen auren..."
Na kwashe duk yadda muka yi da Mukhtar na faɗa mata, dariya ta shiga sheƙawa har da riƙe ciki. Sai da ta gaji don kanta tana goge ƙwallar dariyar ta ce da ni,
"Wallahi ba ki da kirki Maman Haidar! Wannan tura haushin har ina saboda Allah?"
"Da a ce ban yi masa hakan ba, hauka zai siyo kasuwa ya manna mini ban ji ban gani ba. Saboda duk wani tashin hankalin da zan yi a lokacin; kai-tsaye zai ɗora shi a mizanin taɓin hankali. A ƙarshen ma zagina mutane za su dinga yi ba tare da sun yi duba da ƙunar da zuciyata ke yi, su tausaya mini ba."
"Wallahi zancenki gaskiya ne Maman Haidar! Amma kin san me? Ni ba zan iya wannan dauriyar ba. Allah kada ka jarrabe ni da irin wannan musibar mai wuyar shanyewa, don na san duk ranar da Amini ya sanar da ni zai yi aure; ba zan ɗaga daga inda nake ba zan mutu."
Leave a Comment