Abokin Aikina Book 1 Page 29
ASHIRIN DA TARA.*
"Ba za ki mutu ba!"
Zancen da na faɗa mata kenan cike da karsashin da ke cikin raina. Wani kallo take yi mini ko ƙyaftawa babu, kafin ta muskuta kaɗan tare da sauke ajiyar zuciya ta ce,
"Ni kaɗai na san yadda nake jin zafin abin a cikin raina. Yanzu haka ke za a yi wa kishiyar nan, amma wallahi har zuciyata nake jin ƙunar kishin a haɗa ki da wata, a matsayin abokiyar zama a cikin gidan nan."
"To ki ma daina, don ni babu wani abu da zan gani yanzu a gidan nan, wanda zai ɗaga ni sama balle ya buga ni a ƙasa na ji zafinsa. Ke ma da za ki sauke tulin nauyin da kike ƙoƙarin lodawa, da kin taimaki kanki kin huta da tashin hankalin da zai iya bijiro miki a gaba."
Na faɗa mata maganar ne daga zuciyata, don na fara ƙosawa da ɗora ta a kan hanya tana zamewa. Shiru ya ratsa tsakani ba tare da mun sake cewa komai ba.
Girgizar ƙafar da take yi, tare da haɗe fuska da cizon leɓe; ya tabbatar mini da ba ta ji daɗin maganar da na yi ba. Hakan ya sa na yi hanzarin faɗin,
"Ki yi haƙuri da ni Maman Taufiƙ! Amma Allah ya gani ba na son wannan zaƙewar da kike yi wa kishi, maimakon ki yi masa rigakafi tun kafin ya riske ki; amma ke kullum sai ƙara taryar gabansa kike yi domin ku yi arangama."
Na tsahirta da maganar ina karantar yanayinta, sannan na ɗora da cewa,
"Ina faɗa miki wannan maganar ne a matsayinki na wadda na yarda da ita, kuma nake yi mata kallon ƙawa, aminiya, kuma abokiyar shawara. Don haka ki yi haƙuri da gaskiyar da nake faɗa miki tsakani da Allah babu rufa-rufa."
"Na san gaskiya kike faɗa mini, amma zancenki na ƙarshe ya yi matuƙar taɓa mini zuciya. Domin ina ji a raina tamkar kina mini bushara da zuwan tawa kishiya bayan taki."
"Maganar da na faɗa ko kaɗan ba ta danganci hakan ba, don ba na fatar a yi miki kishiya ko don wannan zazzafan kishin naki. Amma ina miki hannuka mai sanda ne saboda ki karɓi abin da ya shiga gabanki; ko don kare kanki daga matsalar da ke biye da ke, ba tare da kin shirya wa zuwan ta ba."
Miƙewa ta yi tana dakan ƙasa da ƙafafuwanta tamkar wata yarinya, fuskar tausayi ta yi tare da langaɓe kai ta ce,
"Oh my God! Kin sake kwatawa Maman Haidar. Ni wallahi shi ya sa ban cika son muna zancen kishiya da ke ba. Saboda kina bar mini zantukanki koyaushe suna mini zillo a zuciya."
"To na daina mu zubar da zancen duka! Gobe idan Allah ya kai mu za a yi wa amarya jere. Me kike ganin ya dace a yi musu a matsayin abincin da za su ci idan sun zo."
Zama ta yi tana haɗe rai tare da aiko mini harara ta ce,
"Wannan nauyin ai ba naki ba ne Hajiya! Ki jira idan angon ya zo ku yi shawarar abin da za a yi musu. Don haƙƙinsa ne, kuma shi zai bayar da duk abin da za a dafa daidai ƙarfinsa."
Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Yo to ni ina na san yadda abin yake? Na ɗauka kamar yadda muke dafa abincin gida haka za a ba su su kora da ruwa. Ashe abin babba ne ba yadda na zata ba?"
"Idan ya zo kuka gama shawara, sai ki kira ni a waya ki sanar da ni. Saboda goben a yi komai da wuri ba sai sun zauna jira ba."
Natsuwata na shiga sosai ina ɗaga mata kai tamkar wata doluwa, saboda tunanin da zuciyata ta faɗa. A kan yadda za mu kwashe da shi hanyar 'yan barkono idan na yi masa zancen. Na so ko bai sani ba na yi musu girkin na fita kunyar idonsu, saboda ba za su yi zaton shi ne da laifin ba idan an hana su abincin. A kaina komai zai juye su je su yi ta zagi na a banza ban ji ban gani ba.
Daga haka muka kitse zancen na rako ta har bakin ƙofar gidan, muna ci gaba da tattaunawa su Ummu Salma suka dawo makaranta.
Cikin sa'a shi ma mai mashin ya dire shi a ƙofar gidan yana shan ƙamshi, Maman Taufiƙ ta yi hanzarin shigewa gidanta ni ma na koma cikin gida. Tsakar gidan na ja na tsaya bayan yaran sun shige ciki.
Ya shigo gidan ko sallama bai yi ba zai wuce buguzum! Na yi hanzarin bin sa a baya ina faɗin,
"Magana za mu yi ranka ya daɗe!"
Ya tsaya ba tare da ya waigo ba, na je ta gabansa kamar ban taɓa jin haushin sa duniya ba.
"Gobe za a yi wa amarya jere. Me za a tanadar musu a matsayin abincin da za su ci, da wanda za su riƙa idan sun je gida su raba?."
Kallon mamaki ya fara bin fuskata da shi kafin ya ce, "Me ya haɗa ki da tambayar abin da ya shafi aure na?"
"Saboda ina cikin gidanka ina amsa sunan matarka a zahiri."
Na ba shi amsa cikin gadara don na fahimci take-takensa ba zai bari mu ƙare maganar cikin daɗin rai ba.
"To wannan ba abin da ya shafe ki ba ne! Ki fitar da kanki cikin abin da babu ruwanki."
Yana ƙare maganar ya wuce fuu zai shige falo, na bi shi ina faɗin, "Da ruwana fa! Don ba na so a ce ban tarbe su da komai ba, a matsayina na uwargidan amarya mai ƙashin arziƙi."
Ƙanzil bai ce da ni ba ya shige ɗakinsa, dariyata na ƙumshe ina faɗin,
"Ka kira mana Barirar mu ji su nawa za su zo? Domin a yi musu komai a wadace babu harkar ƙaranta."
Bai kula ni ba har ya gama abin da yake yi a ɗakinsa ya fito ya nufi hanyar fita yana haɗe rai,
"Na ce ka kira mana Barirar mu..."
"Yanzu don biyar diddigi har da sunanta sai da kika binciko? Ai da kin yi haƙuri idan ta zo komai za ki gani da idonki."
"Yo ita Barirar da ta gama gantalin talllar awara zan bi diddigi don na binciko wace ce ita?"
Dariya na tuntsure da ita ina riƙe ciki saboda ganin yadda ya yi shock tare da ƙura mini ido baki a sake. Hakan ya ƙara mini kuzarin faɗin,
"Kai ma dai da neman zance kake wallahi. Allah dai ya ƙara danƙon ƙauna mijin Barira mai awara."
"Ko kashi take kasawa a kasuwa ai sana'a ce balle awara. Don haka ni ita na hango ba awarar da take sayarwa ba, ki je ki ci gaba da tsegumin ki tun da ba sata take yi ba Alhmdulillah!"
Na bar wurin ina ta dariyar ƙeta, saboda safci faɗi ne kawai ya sa na laƙaba mata tallar awarar. Ashe da gaske na yi sara a kana gaɓa, tun da ya kasa shanye damuwar ya tona wa kansu asiri a ƙoƙarinsa na wanke ta.
Har ga Allah na ji na ƙara raina auren a raina, na ji haushin kashe kuɗina domin na yi musu barazana. Ashe ma a hakan da nake na fi ta kyaun gani ko da ban yi wanka ba, saboda duk macen da ta san kanta ba za ta iya talla ba.
***
Tun da safe wayar Maman Taufiƙ ce ta katse mini baccin da na koma bayan sallar asuba. Tambayar da ta yi mini a kan girkin ya sa na wartsake daga baccin ina faɗin,
"Ki bar shi kawai, ashe ma ya ba da komai a gidansu za a dafa a kawo musu."
Daga haka muka gama wayar na sauko daga kan gadon, saboda ganin su Ummu Salma har sun gyara katifar da suka kwana an ɗauke ta Haidar.
Ƙamshin wainar ƙwan da na ji yana tashi ya tabbatar mini da Ummu Salma tana kitchen. Faɗawa na yi idona a kan plate ɗin da nake da tabbacin kalacina ne ta zuba.
Gaishe ni ta fara yi sannan ta ce, "Yanzu nake zancen na tayar da ke kada Indomien ta yi sanyi."
Ƙwan da take soyawa na karɓa ina faɗin, "Je ku shirya kada ku yi latti lokaci ya tafi."
Na gama soya wainar ƙwan da ta rage na saka wa kaina, sannan na buɗe kulolin su Haidar na jefa musu tasu wainar. Ita ma na saka mata a wani plate ɗin silbar da take cin abinci da shi idan ta yi ra'ayi.
Sanin ba ta son zuwa da abinci Makaranta, ya sa na ɗauki plate ɗina da nata na fito ina ƙwala wa su Iman kira su zo su ɗauki kulolinsu.
Na taras ta saka unuiform na ajiye mata plate ɗin a kan mirror ina faɗin,
"Ki yi sauri fa! Don yau kun makara."
Tura Indomien take yi cikin sauri sai ga su Haidar da gudu suna faɗin ta fito Najib ya zo. A gurguje ta lamushe ta fice da plate ɗin tana faɗin,
"Mun tafi Mama!"
A dawo lafiya na yi musu har sun fice na ji dawowar Haidar da gudu yana faɗin,
"Ba a ba mu kuɗin tara ba!"
Jakata na janyo na zazzage kayan cikinta, na lalubo nera ɗari na miƙa masa ya fice da gudu. Addu'o'ar tsari na dinga yi musu ina jefawa a bakin ƙofar kamar suna wurin, sannan na je na yi brush na fito na karya.
Ina gamawa na share gidan fes sannan na wanke kayan da aka ɓata, na ɓoye wasu kayana. Wanka na faɗa na shirya cikin shigar da ni kaina na san na yi kyau. Sallamar su Sajida da na jiyo na fito daga ɗakin ina zuba ƙamshi da murmushi a kan fuskata. Sajida da Mamarta na hango, sai wasu yayun Mukhtar na 'yan'uwa tare da yaransu.
Gaisawa muka fara yi da su babu yabo babu fallasa sannan na zauna. Sajida ta fara koɗa ni bakinta a sake take ta yabon kwalliyata, ina hankalce da Mamarta tana aika mata harara ta gefen ido.
Ganin ba za ta daina rawar ƙafar da take yi da ni ba ta miƙe tana faɗin,
"Abincin masu jere za mu dafa. A fito mana da tukanen girkin mu je mu yi abin da ya kawo mu."
Na miƙe tare da kiran Sajida da wasu yaran da suka zo da su muka nufi kitchen. A nan muka fito da manyan tukanena da murhu biyu, tare da wasu kayan da za a buƙata duka muka fitar da su a tsakar gidan.
Ina ƙoƙarin shige falo na ji ihun yara suna faɗin ga motar kayan amarya nan ta iso. Dam-dam! Na ji dakan lugude a tsakiyar zuciyata, da murmushin yaƙe na zauna falo ina kiran lambar Firdausi.
Bayan ta ɗauka nake sanar da ita Mukhtar zai yi aure yau ake gyaran ɗaki,
"Ai na ɗauka ba za ki faɗa mini ba har sai an kawo amaryar mu zo ganin ta."
"Kwantas Hajiya! Ni ma daga sama na tsinci zancen auren. Don haka gobe ki fito ku danne mini ƙirjina."
Na ƙare maganar a daidai lokacin da ake shigo da kayan gadon amarya ana shigar da su ɗakinta. Miƙewa na yi na koma ɗakina, mayafi na ɗauko mahaɗin kayan na saka, sannan na rufe ɗakin da key na yi wa matan da ke shigowa sannu da zuwa.
Na fice tsakar gidan bayan jikina ya ba ni shaidar kallon da dangin amaryar suke yi mini. Maman Taufiƙ na kira a waya na ce ta fito ga aikin an kawo mana har gida.
Hannu na saka ina taya su aikin ba tare da na damu da kallon mamakin da Yayunsa suke yi mini ba. Na dinga jan Sajida da hira muna dariyar da iyakacinta kan fuskata, saboda ina so na nuna wa kowa ba na baƙinciki da auren a zahiri.
Ko da Maman Taufiƙ ta shigo har mun fara cin ƙarfin aikin, tare da ita aka dafa jallop ɗin shinkafa. Sannan aka yi musu tuwon da za su je da shi gida bayan jinjer drink.
Najib mai adaidatana na kira a waya ya siyo mana ƙanƙara da nufin idan ya zo na ba shi kuɗin. Babu ɓata lokaci ya siyo mini ya kawo na biya shi, aka baza ta cikin jinjar da aka shaƙe kula biyu da ƙullinta.
Muna tsaka da haɗa kayan Mukhtar ya shigo gidan ya kira Mamar Sajida, wasu manyan ledodi biyu ya miƙa mata yana faɗin,
"Don Allah a saka musu yadda na bayar kada a bari a taɓa musu komai."
Ban bari na sake kallon inda yake ba ma balle abin da yake faɗin kada a taɓa. Sajida kawai ta kira tana faɗin ta samo wata kula a kitchen a saka musu naman kajin a ciki.
Shock na yi da jin maganar kajin, nan take raina ya ɓaci ta yadda har na kasa ɓoye damuwa a kan fuskata. Miƙewa na yi ina faɗin,
"Bari na kawo miki don kulolin suna ɗakina kuma na rufe."
Ba ƙaramar jarumta na yi wurin haɗa kalmomin ba, saboda muryar kuka da ke ƙoƙarin tona asirin zuciyata. Toilet na shige na yi kukan rabin lokaci, sannan na wanke fuskata na fito na ƙara goga mai na bi da 'yar hoda sama.
Kulolin na ɗauko a cikin durowar Kitchen ɗina da na kulle da makulli. Sannan na rufe ina ƙoƙarin ɗagowa na ga Sajida a saman kaina, murmushi ta yi mini tana ƙoƙarin goge hawayen fuskarta ta ce,
"Ki yi haƙuri Aunty! Duk da na san ba a kyauta miki. Amma kuma hakan ba zai hana na ba ki haƙurin ba, don na fahimci ba ki ji daɗin abin da Baba Mukhtar ya ce ba."
"Kada ki damu! Na saba da halinsa ko kaɗan ban ji komai a kan zancensa ba. Kuma ai yana da gaskiya, idan ba mu ƙara ba ba zai yiyu mu rage musu ba."
Ina ƙare faɗar hakan muka fito kitchen ɗin muka koma tsakar gidan. A nan na ji Mamar Sajidar sun haɗa kai da wata 'yar'uwarsu, suna ta gulmar kayan ɗakin amarya.
"Ni fa ina ganin kamar ba sababbi ba ne fenti ne."
"Da gaskiyarki Maimuna! Don ko kujerun gyaransu aka yi ba sabon katako ba ne."
Murmushi na yi mai sauti sannan na matso kusa da su na ce,
"Kaya ba su ne aure ba Yaya Maimuna, ku yi musu fatan zaman lafiya sai ya fi yi da sun da kuke yi."
Kallon juna suka fara yi a muzance, kafin Yaya Maimunar ta ja kular da Sajida ta ajiye gefenta tana faɗin,
"Iyayi ne fa saka suruka makarantar boko. Tun da ya samu mai son sa tsakani da Allah ko yau ya mutu ya bar tarihi. Don ya ƙwaci wuyan hannunsa daga muguwar damƙar da aka yi masa."
Murmushi kawai na yi mata na bar wurin, saboda idon Sajida da ke kanmu. Kuma na tabbatar da duk abin da zan faɗa a wannan lokacin ba mai daɗi ba ne, kuma dole sai ta ji zafi domin ba zan yi ƙasa a gwiwa wurin rama daidai abin da ta faɗa mini ba, wataƙila ma na zarce awa wurin ƙoƙarin mayar da raddin na ci zarafinta a banza wofi."
Hmmmmm! Shiru ma ai magana ce Zaituna.😢
Leave a Comment