Bakar Inuwa 11


 *_Episode 11_*



............*_SALLA BIKI ƊAYA RANA_*


         A duk wanda ka duba yau inhar musulmi ne na ƙwarai zaka fuskanci farin cikin zagayowar wannan rana ta salla bisa fuskarsa. Rana ce da mafi yawan al'umma suka ganta suka kuma sake ganinta. Sai dai hakan baisa ta gunduresuba. A kowace

shekara murnar zagayowarta ake yara da manya tamkar lokacin suka fara riskarta.

    Ƙarfe goma na safe tawagar ɗunbin al'ummar musulmi dake a sassa da dama na babban birnin ƙasar Bingo da ke a NAYA suka kammala sallar Edi. Bakin kowa a washe yana gaida ɗan uwansa ko aboki. Yayinda irin su Raudha baƙi a garin keta ƙoƙarin ganin sun fito da ga harabar babban masallaci idin domin samun abun hawansu. Dan kuwa dai aunty Hannah ce da kanta ta kwaso ƙwai da kwarkwatar yaran gidan ta taho dasu filin na idi.

    Duk da a ƙurarren lokaci su Raudha sukazo Bingo tsaf Aunty Hannah ta haɗama kowansu kayan salla na gani na faɗa. Wanda a zahirin gaskiya first lady ce ta bada maƙudan kuɗaɗe domin yin hakan. Su dukansu matan sanye suke cikin baƙaƙen abayoyi ƙirar Egypt, sai dai ta kowa ta banbanta da kalar adon da yafi buƙata. Kasancewarsu ƙyawawa jinin ƴaƴan larabawa duk da ba kowanne a cikinsu ya biyo iyayen nasu ba sai gasu ɗas tamkar wasu ƴaƴan manyan mutane.  

     Tafe suke Yasmin da twins na surutu da bada labarin yaran da suka zauna kusa da su basu iya salla ba su Fatisa na dariya. Sai Raudha da kusan ke ƙarshe a bayansu tana tafiya a nutse dan sam bata iya sauri ko garaje ba. Kanta a ƙasa yake tana ɗan kallon yara daketa kaikawo cikin shigar malam bahaushe abin sha'awa. Kamar ance ta dubi gefenta idanunta karaf akan wani matashin saurayi da kallonsa kawai baida daɗin yi. Duk da ranar salla ce kuma shigar farar jallabiya yayi fara ƙal a jikinsa saita banbanta da jikin nasa. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci baiyi kama da mutanen kirki ba. 

       Gabanta ya faɗi ganin yana gyara wata ƴar wuƙa dake a hannunsa sai ƙyalli takeyi. Abinda ke manne a kunnensa ya kai hannu ya gyarama zama alamar magana yakeyi da wani, dan bakinsa sai motsi yake yayinda idanunsa ke kallon saitin inda yake tunkara. Juyawa tai da ƙyau itama tana duban wajen. Zuciyarta ta ɗan harba sabida yin tozali da wani kamilallen dattijon tsoho ƙyaƙyƙyawa. Duk da shekaru sunja garesa hakan bai hana bayyanar cikar kamalarsa da jin daɗi ba. Tsaye yake akan ƙafafunsa cikin ɗanyar shadda fara ƙal da ko ba'a faɗaba kasan an narka kuɗi wajen ɗinkata. 

     Ya sake damƙe hannun mutumin da suke tare fuskarsa na sake ƙawatuwa da murmushi alamar gaisuwa sukeyi irin wadda take nuna an daɗe ba'a haɗu da mutum ba. Sake maido kallonta tai ga saurayin nan daketa sake tunkararsu. A take jikinta ya fara rawa, tanaji a ranta akwai abinda saurayin ke ƙullawa mara ƙyau a zuciyarsa game da kamilallen tsohon da takejin nutsuwa a zuciyarta game da shi. Badan ta sansa kota taɓa ganinsaba sai ɗazun da suke shigowa massallacin idin da wani tsoho daya fisa tsufa sosai ya kusa faɗuwa. Dakaga tsohon na ɗazun kasan talakane, amma sai ga wannan dattijo ya zaburo har shima yana shirin faɗuwa ya tare tsohon a jikinsa yana masa sannu, kasa ɗauke ido tai a kansu a ɗazun har suka shige cikin massallaci yana riƙe da shi. Kwarjininsa da cikar kamalarsa da shekarunsa na girmane kawai sukaja hankalinta da zuciyarta nason taimakonsa, (sai dai ta yaya?). Ta ambata a zuciyarta batare da tasan amsa ba. Farga da saurayin na gab da kaiwa garesa ga shi zai juya baya ya sakata zabura ta nufesa. Kusan a tare suka ƙarasa ga dattijon ita da saurayin.

      Cikin ƙwarewar aiki na iya kisa saurayin ya kaima Alhaji Hameed Harith Taura yanka da kakkaifar wuƙar hannunsa gayama jini na wuce yanka ta gefen ciki. Inda ya tabbatar idan ya yanka sai ya mutu kuma. Sai dai kash, wuƙar na gab da kaiwa kansa batare daya fargaba dan yayi kamar zai wucene Raudha tazo ta tare yankan ya sameta a cinyarta sakamakon ɗan tsallen da tayi nason cimmasa.

        Wata irin ƙara ta saki da damƙe cinyarta da hannu guda ɗayan kuma ta damƙo rigar jazuga dake son sake kaima Alhaji Hameed Taura wani yankan ganin wannan Raudha ta tare. Kusan duk wanda ke a kusa da su a wajen sai da ya juyo, a take kuma duk akayo kanta. Inda Alhaji Sammani yay azamar janye Alhaji Hameed Taura dan bashi kariya daga yunƙurin saurayin a karo na biyu. Hakanne yasa saurayin fincike rigarsa daga hannun Raudha datai ƙasa zata faɗi ya arta cikin na kare (gudu). 

       Da sauri Alhaji Hameed ya kai hannu ya riƙo Raudha jikinsa na rawa. Dan duk mai hankali ko ba'a masa bayanin komaiba zai fahimci abinda yay shirin faruwar. Sai dai kafin ma kowa ya nema ba'asi wani yaro da bazai gaza shekaru goma sha uku ba yake faɗin duk abinda ya gani. Dan kuwa akan idonsa Raudha taima Alhaji Hameed Taura garkuwa daga suƙar wuƙar saurayin.

     Cikin ƙanƙanin lokaci ahalin Alhaji Hameed Taura suka zagaye wajen, ga securitys da ƴan agaji suma duk sun iso. Duk mai tausayi sai ya zubarma Raudha hawaye ganin irin mugun yankan da saurayin yay mata a cinya, dan ma ansa abu an yane ƙafar dan har rigar ya tsarge. A sume take jikin Alhaji Hameed Taura dake cikin matsanancin tashin hankali. Musamman yanda Yasmin tazo ta faɗa jikin Raudha tana kuka da girgizata. 

      Isowar Ambulance ɗin da ake jirace tasa mutane darewa ma'aikatan asibitin suka iso wajen da keken ɗaukar mara lafiya. Da taimakon Alhaji Basheer Hameed Taura da shima jikinsa ke rawar tashin hankalin abinda yaso samun mahaifin nasa aka ɗora Raudha bisa keken har cikin Ambulance ɗin.


      Daga ahalin gidan Taura har su aunty Hannah kaiwa da komowa kawai suke na tashin hankali a ƙofar ƙayataccen asibin na musamman da aka kawota. Wanda tabbas badan dalili ba ko katangarsa bai zama lallai Raudha ta taɓa taɓawa ba harta ƙare rayuwarta. Da farko ƴaran gidan Taura hankalinsu yafi tashine akan jin kakansu aka kawoma harin ALLAH ya tsaresa. Sai da sukaga hankalin Pa ɗinsu da kakan nasu su kuma akan Raudhan yake sannan suka ɗan koma jimantawa. Koda za'a kawo Raudha asibitin badan securitys da ke biye dasu har nan ba da gida zasuyi wucewar su. Har mamakin yanda Bappi da Pa suke a ruɗe sukeyi, sun san yarinyar tayi ƙoƙarin kodan jarumtar da tayi na tarar wannan azaba. Sai dai mafi yawansu sunaji a ransu tayine dan neman suna ko kuɗi ko wani abu daban koma tare take da saurayin. Dan sun san haka kawai dai mutum bazai tarema wani mutuwa ba babu dalili, ballema ƙaramar yarinya irinta. Wasu ko a cikinsu gani suke koma bakin saurayin da Raudha ɗaya ne, maybe akasi aka samu kawai, ko kuma ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya.

     To koma dai miye Alhaji Hameed Taura da ɗansa Alhaji Basheer Hameed Taura su ba haka bane a nasu zuciyar. Ɗunbin tausayine na Raudha da jinjinama ƙundunbalarta a ransu, sai fatan ALLAH ya bata lafiya da taraddadin wanene ya aiko saurayin ga wannan aikin? Dan kuwa dai cikin hayaniyar mutane ya ɓace ɓat, har suka baro wajen securitys na nemansa ne amma babu alamar zasu gansa.


       Aunty Hannah da su Fatisa na rakuɓe a gefe suma rayukansu fal mamakin abinda ya faru. Dan sam babu wanda ya kula da sanda Raudha ta tafi bama Taura kariya sai ƙararta sukaji, sai ko sauran bayani a bakin mutane da suka tsinta. Yasmin dake kuka Alhaji Hameed Taura yazo ya durƙusa gabanta, duk da tsufansa da matsayinsa bai dubaba. Yasa hannayensa biyu yana share mata hawayenta. Cikin lallashi yace, “Minene sunanki?”.

       “Yasmin!”.

Ta bashi amsa cikin shashshekar kuka. 

      “Oh mai sunan larabawa to kukan ya isa haka ok? Kima aunty addu'a zata tashi lafiya kinji!”.

     Kanta ta jinjina masa tana jan tagwayen ajiyar zuciya. Tausayinta ya kamashi matuƙa. Ɗunbin kamannin daya gani tsakaninta da mara lafiyar ya sashi hasashen ƴar uwartace. Hannunta yaja ya zaunar a kusa da shi yana kai kallonsa ga Muneera data koma can gefe tana waya kamar bataso a jita, da alama dai wani take sanarma abinda ya faru. Ya san kuma bazai wuce mamansu Gimbiya Su'adah ba. Dan tun ɗazun yakejin kira na shigo masa waya ya tabbatar Anne ce amma bai ɗauka ba. Yasan dai zuwa yanzu labarin abinda ya faru ya karaɗe kowacce kafar yaɗa labarai abinka da babban mutum.

       Ko wane gidan tv ka kalla daga nuna sallar idi sai zancen an kaima Alhaji Hameed Harith Taura hari a filin idi. Yayinda hoton Raudha na kwance cikin jini a hannunsa shima keta kai kawo.

      Babu yanda Alhaji Basheer baiyi Bappi ya koma gida ba amma yaƙi, ya tabbatar masa bazai iya barin wadda ta fansar da lafiyarta a gareshi cikin wannan halin ba ya iya komawa gida ya samu nutsuwa. Dole ya ƙyalesa har lokacin da doctors ɗin dake tare da Raudha suka fito suna sanar musu Alhmdllh ta farfaɗo. an kuma mata ɗinki a wajen tare da alluran kariya daga gujewa wasu cututtukan. Domin a bincikensu sun gano jikin wuƙar akwai dafin maciji.

      Wannan abu ya sake tayarma da Alhaji Hameed da zuri'arsa hankali. Dan tabbas da an samesa babu makawa zai iya rasa ransa kodan yanayin jikin tsufa dake tare dashi..


*__________________________*


            “Sai da nace maka yaron nan bazai iyaba Mr JK amma ka dage akan ƙwararrene ta hanyar wannan aikin”.

    Ɗan takarar shugaban ƙasar NAYA a jam'iyyar adawa ya faɗa cikin ɗunbin tashin hankali da ruɗani yana nuna mutumin dake daura dashi a ƙayataccen falon na alfarma. A tsakkiyar falon kwanikane barbaje na abincin salla, sai sauran mutane uku dake ta gefen hannun haggunsa suma bisa kujerun rayukansu duk a ɓace.

     Wanda aka kira Mr JK ya girgiza kansa cikin takaici shima yana faɗin, “Karkaga laifina Engineer. Ku kanku kunsan badan yarinyar can data bashi kariyaba babu shakka sai aikin yaron ya tafi dai-dai, sai yanzu na sake tabbatar da Alhaji Hameed Taura ya wuce ifiritu sai dai hatsabibi. Duk yanda muke tunanin cimmasa cikin sauƙi abune mai wahala”.

       Cikin sauran mutane ukun ɗaya ya amshe da faɗin, “Tabbas abune mai wahala, sai dai ya kamata musan yarinyar nan ƴar uban wacece ne? Sannan minene dalilinta na bashi kariya?.”

        “Wannan yanada muhimmanci Alhaji Sale Sukini, sai dai babban mai muhimmancin shine Alhaji Hameed. Domin wannan abun daya faru babu abinda zai ƙara masa sai farin jini ga jama'a. Ka duba kaga cikin ƙanƙanin lokaci kowacce kafar watsa labarai data yanar gizo ta ɗauka. yaya kuke tunani idan rana tsaka ya fito da manufarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar NAYA kuma?”.         

         “Kuma gaskiya fa maganarka nakan hanya Alhaji Badamasi. Domin barin Alhaji Hameed Taura a raye tamkar hana yuwuwar nasararmuce. Babu yanda zamu haɗa takara da shi a dubemu a ƙasarnan, su kansu abinda suka fahimta kenan shiyyasa suka jawoshi ya hau kujerar dan sauran da suka nuna sha'awa a jam'iyyar tasu duk ruɓaɓɓune, babu wanda zai iya kawo kujerar. Shiko duk da bawai siyasar ya bama ƙarfi ba suna cewa gashi jama'a zasu amsa”.

       Duk da ac dake aiki a falon hakan bai hana Engineer zame hularsa ya hau fifita ba, dan wata irin zufa ce ta ruɗani ke karyoma duka sassan jikinsa. Ya tabbatar duk abinda abokan nasa suka faɗa shine gaskiya. Shiko a yanzu babu abinda yake buri da fata sama da shugabancin ƙasar NAYA. yayi shekaru goma cif yana mulkin bisa muƙamin gwamna. Yaji daɗi sosai ya koma a kujerar majalissa itama shekaru biyar kenan, yanzu kuma burinsa yakai ga kujerar daga ke babu wata. A da hankalinsu kwance yake da hangen nasara saboda waɗanda suke hasashen jam'iyyar mai mulki zata bama takara duk bazasuyi armashi ba. Sai dai labarin daya zo musu sati kusan guda kenan akan zaman shugaban ƙasa da Alhaji Hameed Taura da kowa ke tunanin takara sukeson bashi ya ɗaga musu hankali. Domin kuwa a majiya mai ƙarfi sukaji hakan daga bakin wani munafikinsu dake cikin mulkin na shugaban ƙasa a yanzun. Sun yarda da shine bisa dalilin ba yaune karo na farko daya kawo musu labariba kuma ta tabbata daga fadar shugaban ƙasar na NAYA.

     Zaman sake sabon ƙulli sukai akan Alhaji Hameed Taura da baisan sunayi ba ma....



*_Tofa maƙiya ta ko ina🤔_*




*_GOVERNMENT HOUSE_*


           Kamar yanda abokan adawa kecan suna tattaunawa anan fadar ta shugaban ƙasar NAYA ma hakanne. Dan kowannensu na kallon abinda ya farunne ta fuskar siyasa. Alhaji Hameed Taura mutumin kirkine da kowa ke yabon halayensa tun ƙuruciya. Dan ko lokacin daya ɗan fara bayyana kansa a siyasa mutane ƙalilanne suka soki hakan.

     Su kansu rayuwar Alhaji Hameed Taura bawai damuwarsu bace. Sai dai basa buƙatar rasata a yanzu har sai sun cimma nasu burin sannan. Dan haka zasu sake tsayawa tsayin daka wajen ganin sun bashi kariya har su tsallake.

          *_(ya ALLAH. Siyasa batai ba??🚶🏻)._*


         Duk da tare shugaban ƙasa yay salla da Alhaji Hameed Taura a babban masallaci kuma har abin ya faru bai koma gidaba hakan bai hanashi sake sabon shiru shi da tawagarsa suka nufi asibitin da aka kai Raudha ba. Dan labari ya samesu cewar Alhaji Hameed Taura na asibitin. Dolene suma suje su nuna jimaminsu da bama al'amarin muhimmanci tunda shima ya ɗaukesa da girma. 


*_TK SPECIAL HOSPITAL_*


        Cikin ƙanƙanin lokaci asibitin ya ƙara samu tsatstsauran tsaro a dalilin isowar shugaban ƙasa da tawagarsa. Hakan bai bama kowa mamaki ba saboda sanin amintakar dake tare da shugaban ƙasar da Alhaji Hameed Taura. Dole aunty Hannah ta ɓuya dan bata buƙatar shugaban kasa yasan tanada alaƙa da Raudha a yanzun.

    Bayan sun duba Raudha dake cikin ƙyaƙyƙyawar kulawa shugaban ƙasa ya tilasta Alhaji Hameed fitowa suka ɗunguma zuwa Taura house tunda jikin nata Alhmdllh. Da wannan damar suma sauran yaran duk suka gudu gida tunda daman zaman kakansu sukeyi anan ɗin. Sai dai anbar Raudha cikin tsananin tsaro da kulawa ta kowanne fanni. Ga ƙyaututtukan maƙudan kuɗaɗe da waɗanda suka rako shugaban ƙasa duk sukai mata. Sai a lokacin su Aunty Hannah suka sami damar shiga suka dubata da ƙyau suma. Dan ɗazun Alhaji Hameed ne kawai ya shiga da Pa.

     Sun tausaya mata ƙwarai da gaske, dan ƙafar tata ta matuƙar kumbura sai ma ratayeta akai jikin wani ƙarfe. Barci takeyi ga jinin data zubar ana ƙara mata. Kusan mintuna sha biyar akace su fito dan ba'a buƙatar kowa ya zauna da ita saboda gudun abinda zaije ya dawo. Hakan yasa dole Aunty Hannah ta kwashi su Fatima suka koma gida suma. Dan tun ɗazun dama Asabe ke kira da wayar hajiyar birni tana kuka akan su sanar mata idan Raudha ta rasu ta haƙura kawai. Dan duk wanda yaga Raudha a hoton dake yawo babu tantama zai ce ta mutu ne, musamman yanda jini yay faca-faca a jikinta cikin ƙanƙanin lokaci. Danma baƙar rigace a jikin, sai dai adon farin zare da akai mata yasaka jinin bayyana ga idanun mutane..........✍



*_Tofa wannan fa shine ake kira ƙaddara ta riga fata. Su aunty Hannah na neman ƙulla hanyar dalili, ga dalilin wanda ya fisu sanin gaibu shi ya ƙulla ta hanyar da basuyi zato ko tsammani ba. Masu karatu yaya za'a kwashe kenan to?🤔_*


No comments

Powered by Blogger.