Bakar Inuwa 13

 *_Episode 13_*




...........A hankali Ramadhan dake a bakin ƙofar ya cigaba da tako tsaftataccen marble's ɗin falon, dan ya cire takalmansa tun a corridor ɗin daya raba falon farko da wannan falon, sai safa baka kawai. idanunsa akan kakannin nasa. Tafiya yake dai-dai da

hurowar iskar hadarin dake kaɗa labulolin falon tare da walƙiya tamkar yana taku a saman kaɗawar tata ne. Harya ƙaraso gaban Baffi basu iya sun motsa ba, ya durƙushe gaban bisa gwuyawunsa tare da sauke jikkar kafaɗarsa. Hannu ya kai bisa kansa a hankali yay baya da hular nutsatstsiyar fuskarsa mai cike da kwarjini da cikar haiba ta bayyana. 

       A hakan ma bai iya dubansu ba, dan har yanzu idanunsa sakaye suke da gilashinsa mai nuna blue. Maimakon ya zaresa sai matsawa yay ya ɗora kansa bisa cinyar Bappin yana sakin wasu tagwayen ajiyar zuciya da lumshe idanunsa masu nauyi da fargaba.


        ★


   A ɓangaren Pa ma yau tare yake da gimbiya Su'adah dan girkintane. Tsananin gajiyar dake tare da shi ta kaiwa da komowar da yayi yau kashi-kashi ya saka shi yin wanka da ruwa mai ɗumi da taimakon gimbiya Su'adah. Fitowarsu kenan a toilet ɗin tana tsane masa jiki da towel ƙarami. Ya kai dubansa ga labulen windows da aka ƙawata adon bedroom ɗin nasa da su. Yanda iska ke kaɗasu abin sha'awa ga mai kallo. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke batare daya ɗauke kansa a jikin labulen ba ya fara magana a hankali.

      “Da ace Bappi zai yadda da ya bar maganar nan ta takara. Saboda na tabbatar abinda yaso faruwa a yau yanada alaƙa da wannan siyasar da bana hango wani amfaninta a garemu ko kaɗan....”

     Wani irin bugawa ƙirjin gimbiya Su'adah yayi. Domin ba ƙaramin ƙwallafa rai da ƙara jin alfahari takeba akan batun fitowa takarar tilon ɗanta namiji da Bappi ya kwaɗaita musu tun daren jiya. Zata iya cewa dukkan farin cikinta na yau da murmushinta yana da alaƙa ne da hakan kai tsaye. Idan ko mijin nata ya cigaba da nuna adawarsa akan hakan ko kokwanto lallai tana cikin ɗunbin rashin nasara kenan. Dan kuwa Bappi zai iya saurarensa akan hujjojinsa inhar ya samesa da batun........

      “Su'adah kinyi shiru”.

Pa ya faɗa cikin katse mata dogon tunanin data faɗa. Numfashi taja mai ƙarfi a ɓoye da ƙaƙaro murmushi tana kaiwa zaune a gefensa. Maɓallan rigar barcinsa dake ajiye gefe take ɓallewa bayan ta ɗakkota a hannunta.

     “Ba shiru naiba Daddyn Ramadhan, nima wani tunani nakeyi game da maganarka. Tabbas zancenka nakan gaskiya, dan ni kaina harna fara jin tsoro. Idan har za'a iya harar mana Bappi irin haka akan wannan batun shi kuma Ramadhan dazai tsaya takarar yaya zata kasance kenan?”.

         “Abinda nake hangowa kenan Su'adah. An illata mana yaro a baya batare da mulki ba, har takai ga ya nisancemu a yanzu saboda tabon da aka bar mana a zukata ya kasa barin ruhinsa. Inaga yanzun da ake son ɗora masa nauyin abinda ya girma shekarunsa. Suma da suke manya masu shekaru basu tsira ba balle shi da dudu shekarunsa talatin da biyar. Ko'a tarihi babu wani shugaban ƙasa a wannan ƙasar ta NAYA da akayi mai ƙarancin shekarunsa fa....”

       “Ƙarancin shekarunsa basu bane damuwar Dadyn Ramadhan. Dan kuwa koba komai anzo da wani sauyine da al'ummar ƙasar NAYA zasuyi farin ciki da shi. Mun cancanci mu damu da gudun abinda zaije ya dawo, sannan kuma ta wani ɓangaren yanada ƙyau muyi dubi da talakawa masu buƙatar irin Ramadhan ɗin a yanzun, domin da gaske ƙasar NAYA irin Ramadhan take buƙata da shekarunsa. Badan shugabannin baya sun gaza ba, a'a suma sun taka irin rawarsu kuma munji daɗin ƙoƙarinsu da yaba musu, dan mulki ba abune na wasa ba. Wanda ke gefe bai isa sanin wahalarsa ba sam. Dan shi daɗin kawai yake hangen maiyinsa na ciki yake, sai dai abunda bamu saniba wahalarsa itace kaso 99. Kaso ɗaya kacal ɗin nan shine kawai jin daɗin ga ma'abota mulki. ALLAH ya sakama shugabanninmu da alkairi, ya yafe musu kurakuransu yay riƙo da hannayensu. ALLAH kuma ya basu ikon sauke nauyin al'umma dake kansu”.

        Numfashi ya sake saukewa da faɗin, “To amin ya rabbi. Amma duk da haka ina jin tsoro Su'adah”.

      “Karkaji tsoro Dadyn Ramadhan. Addu'a kawai zamu duƙufa yi, tare da tunanin ta hanyar da zamu maido Ramadhan gida a yanzu batare da mun sake ɗorama Bappi wani nauyin ba”.

        “Eh kema kinyi batu na hankali. Inko hakane barama na leƙa bappin dan na manta ma ban sanar masa batun kammala fidda komai na zakkar ba yau, duk mun wuni cikin rashin kwanciyar hankali ba'a fitarba kamar yanda aka saba”.

       Miƙewa tai tsaye tana taimaka masa ya saka jallabiya fara bayan ta ajiye rigar barcin gefe, dan tasan bazaije sashen su Anne da kayan barci ba. Hakan al'adarsace da girmamawa ga mahaifan nasa batun yanzu ba. Turare taɗan fesa masa sannan ya fice.

   

         Gimbiya Su'adah ta sauke nannauyan numfashi a ƙasan ranta tana godema ALLAH daya kasance yau girkintane har taji batun nan taima tufƙar hanci da wuri. Taya zata amince maganar nan ta koma ciki bayan ta fito. Da farko bataƙibama ace shi Alhaji Basheer ɗinne zai hau shugaban ƙasar ba. Dan koba komai darajarta zata ƙaru, ta fito daga gidan mulki mafi daraja da kima, gata tana aure a gidan dukiya sahun farko a ƙasar NAYA dama yankin Africa baki ɗaya. A ƙarshe a kirata first lady. Lallai data amsa sunanta *_SARAUNIYA SU'ADAH_* ba gimbiya Su'adah ba. Amma ko'a hakan ma ba komai baneba, dan samuwar mulkin ga gudan jininta wani abune mai girma da za'ayi ƙarnuka da zamanai da bazai mantu ba. Sannan dole ne a kirata uwar shugaban ƙasar NAYA. Dan haka itace da kanta zata zaɓa masa matar aure dai-dai da ra'ayinta. A wannan karon bazata sake sakaci irin na farko ba akan matar da Ramadhan zai aura.


(“Mulki! Mulki!! Mulki!!😣🚶🏻” ).



        Turus Pa yay tare da ƙoƙarin haɗiye sauran sallamarsa a maƙoshi duk da ta kusan gama fita a harshensa. Ba komai ya jawo hakan ba sai tozali da yay da gudan jininsa zaune gaban Bappi da Anne. Gaba ɗaya fuskar tsoffin nasa babu alamun fara'a, yayinda Ramadhan ɗin yay ƙasa da kansa yana magana a kausashe mai cike da ɗaukar alwashi.

       Kai tsaye ya fahimci kausasa harshen nasa nada alaƙa da abinda yaso samun bappin a yau. Sarai ya sani basai an faɗaba, ɗansa Ramadhan mutum ne mai zafin zuciya ainun, abu kaɗan ke fusatashi ya hargitse tamkar baisan wani abuba wai shi sauƙin kai. Amma idan ka kallesa a fuska bazaka taɓa ɗauka ma yana magana mai alaƙa da masifa ba saboda fuskar mutane masu haƙuri da rashin son hayaniya garesa. Sometimes idan yay abu mutanen da basu san ainahinsa ba sukance bashi bane ba, dan a zatonsu ko yatsa ka sakama Ramadhan bazai taunaba saboda haƙurinsa da rashin son magana. Girman kai ne dai kam kowa na masa kallon mai shi kai tsaye, koda sau ɗaya ka fara ganinsa.

      Sai dai su duk sun san ba hakan baneba, Ramadhan bauɗaɗɗen mutum ne mai zafi da tsananin ɗaukar kai (girman kai inji bahaushe😎). Tabbas baida yawan magana badan yana miskiliba, tsabar jin kai ne kawai ke hanashi magana a lokuta da dama koda ace ya dace yayi ɗin. Tabbas anan ɓangaren ya biyo mahaifiyarsa ƙwarai da gaske, dan saima ace ya ɗarata izza dajin mulkin a cikin jininsa fiye da ita da aka haifa a gidan mulkin. Sai dai kuma ta wani ɓangaren yanada wasu halaye kishiyar waɗan can da zama dashi ne kawai zai iya fiddoma wanda ya sanshi da waɗan can ɗin su.....

        “Ramadhan!”.

Pa ya faɗa cikin wata irin murya mai kaushi-kaushi da ɗaci. Dan haka kawai daya tuna yanda suka dinga bin Ramadhan akan yay haƙuri ya manta komai ya dawo ƙasar NAYA amma ya nuna musu bazaibi maganarsuba ya shiga dawo masa a rai.

    Da ga Ramadhan har su Anne juyowa sukai suna kallon Pa ɗin, dan sam basuji shigowarsaba balle sallamarsa saboda tasowar iskar hadari dake ƙaruwa.

     “Pa!”.

Ramadhan ya faɗa da sauri yana miƙewa idonsa akan mahaifin nasa.

       “Miya kawoka gidan nan!!”.

Pa ya faɗa yana ƙoƙarin dakatar da Ramadhan daya miƙe da alamar ɗokin ganin mahaifin nasa da zumuɗin isowa garesa, dan jikinsa har tsuma yake.

      “Pa!......”

Ya sake buɗe baki zaiyi magana Pa ya dakatar da shi. 

      “Karkace komai a gareni!!, zo ka fita a gidan nan yanzun nan!!”.

     Yanda yay maganar babu wasa ya saka Ramadhan duban su bappi, kafin ya sake kallon Alhaji Basheer Taura. 

      “Pa.......!”.

“Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”.

     Alhaji Basheer Taura ya faɗa a tsawace yana nunama Ramadhan hanyar falon.


     Wata irin muguwar hajijiyace ta fara ɗibar Ramadhan. Dan dama can shi bayason ihu, musamman idan yana akan gaɓar bacin rai tuni ake samun matsala kansa ya nema juyewa saboda tsananin yanda ƙwalwar kansa ke kasa ɗaukar tashin hankali mai shallake tunani. Lokacin da yana yaro idan hakan ta faru ansha cemusu yanada aljanu ne masu ƙarfi sosai. Sai dai basu taɓa yarda ba dan su sam basu cika ɗaukar waɗan nan abubuwan da muhimmanci ba (kamar yanda kowa yasan ɗan boko🙏🏻), sai dai hakan baya hana duk lokacin da abu ya faru makamancin matsalar ta biyo baya Anne ta zauna tai masa addu'a a ruwa da saman kansa har sai ya samu nutsuwa sannan. Amma abin mamaki zai iya yini yana ajiyar zuciyar wannan ɓacin ran, ko kuma ya yini a ɗaki yana barci. Sannan sai ya haɗa kwanaki biyu zuwa uku baiyi magana da kowa ba. sai dai ya samu wajen ruwa ya zauna, ba kuma zaici abinci ba duk da kasancewar sa ma'abocin son abinci sai Anne ta takura masa shan abu mara nauyi kamar su fura yogurt, fresh nonon shanu ko na raƙumi da makamantansu. Dan yana tsananin son madara da dukkan nau'ikanta a rayuwarsa. Bayan aurensa da Amnah idan ransa yay irin wannan ɓacin yakan hucene a kanta ta hanyar yin tarayya da ita yanda zata jigata har sai an kwantar da ita a asibiti abinka da sikilla. Dan likitocin kance ko mai lafiya akaima irin wannan kamun babu shakka zataji a jikinta balle Amnah ɗin. A duk lokacin da fushin ya sauka yakan shiga damuwa idan ya kalli yanda ya fiddata hayyacinta. kai wani lokaci ma har saida akai mata ɗinki tsabar lamarin Ramadhan yana bukatar addu'a🤦🏻. Amna kam tana jin jiki da shigar Ramadhan irin wannan yanayin, sau biyu yana sakata ɓarin ciki. da tana raye na tabbatar zatace hakan shine mafi girman tashin hankali a rayuwar aurenta da Ramadhan ɗin, shiyyasa duk wani fushinsa take gujewar wanzuwarsa a karan kanta.

       Yanda ya fara juya kai jijiyoyin na tashi sama da maƙogwaronsa dake kai kawo a wuyansa, gashin kansa na mimmiƙewa yasa Bappi fahimtar mike shirin faruwa. Yasan Ramadhan bazaice komaiba, dan shi mutum ne mai tsananin tsoron saɓama iyaye, shiyyasa daya dage akan bazai dawo NAYA ba a shekaru biyar ɗin nan abun ya basu mamaki matuƙa, dan duk rintsi baya ƙetare maganarsu.

    Da sauri Bappi ya girgizama Alhaji Basheer kai yana miƙewa ya riƙo hannun Ramadhan daya fara ƙoƙarin ɗaga ƙafa yana jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa daya riƙe kan nasa. Tuni idanunsa sun rufe ruf saboda wata baƙar hajijiyar da yake gani falon na juya masa da wani irin shegen gudu.

      Babu abinda ke maimaita kansa a kwakwalwar Ramadhan da zuciyarsa sai *_“Ramadhan!! Nace ka fita a gidan nan yanzun nan!. Bana son sake ganin wannan fuskar taka!!”._* da Pa ya faɗa.

      “Zan tafi Pa, bazan sake nuna maka fuskar nan ba nayi alƙawar.....”

     “Shut up!!”.

Bappi ya faɗa da ƙaraji shima yana katse Ramadhan ɗin bayan ya fisgosa ya zube a saman kujerar kusa da shi. Juyawa Alhaji Basheer Taura yay a fusace yabar falon, shi kansa wani irin jiri-jiri na neman fara ɗibarsa. Sai hakan yasa yakejin yana tafiya tamkar akan iskar dake kaɗawa har zuwa sashen nasa. Bai iske gimbiya Su'adah ba. Da alama taje shirin barci. Dan haka yay kwanciyarsa, koda ta shigo bayan kusan mintuna talatin da kwanciyarsa bai motsaba. Hakan yasa tai tunanin ko yayi barcine. Sai kawai taja bargo ta lulluɓa masa bayan ta rufe wasu a murafan windows ɗin dan iskar ta fara yawa.


*_WASHE GARI_*


         Da mamaki kowa ya tashi yaga Ramadhan a gidan. Sai dai a yanayin da yake na hawa saman dokin zuciya yasaka bakin yaran gidan rufewa ruf. Dan ko kallonsa kayi bakaso sake ganiba fuskar tamkar zatayi aman wuta😜. 

         Gimbiya Su'adah ce kawai ya iya tankama tambayarta itama a taƙaice, dan ita firgitama tayi da ganin nasa. Har zuciyarta na raya mata kodai da gaske Ramadhan ɗin nada aljanune wai?.

     Ko amsa ɗaya bata samu daga tarin tambayoyin da take jera masa ba, sai ma miƙewa yay yana sanar mata cewar zai koma America.

      “America!”.

  Ta maimaita da yanayin ruɗani da tashin hankali. ita dake murna ɗanta ya dawo gareta kuma. Kafin ta sake cewa wani abu yayo waje. Dan dama a bedroom ɗinta ya sameta kasancewar ta duba an kammala shirya abincin breakfast na Pa tazo dan ta shirya, sannan taje ta tadashi a barcin daya ɗan koma na safe bayan dawowarsa masallaci.

     Har ya fice a sashen baki ɗaya bata dawo hayyacinta ba. Dan da alama sumar tsaye tayi kawai.


     ★


“Shiga mota muje”.

      Bappi ya faɗa idonsa akan Ramadhan daya fito daga sashen iyayen nasa a wani irin yanayi. Duk da alamu sun nuna yayi wanka ya canja kaya hakan bai hana fuskarsa bayyana yanayinsa na jiya ba. Sanye yake cikin wani tattausan tissue yadi da basai ance komai game kallo ba wajen hasashen irin kuɗin daya lasa na sayensa dana ɗinkinsa. Duk da simple style ne a jikinsa hakan bai hana bayyanar tsadarsa da fitar ɗinkin ba a bisa ƙyaƙyƙyawar ƙirarsa ta mazantaka da ƙuruciya ba, ga shi baƙi sai farar fatarsa ta sake haskawa. Babu alamar sumar kansa ta samu gyara yau tsabar yanda ta hargitse, sai dai hakan bai hana ƙyawunsa bayyana ba harma ya ɗauka hankalin wasu mutane koda ba kowaba.

       A tunaninsa airport ɗin zasuje, kamar yanda ya sanarma Bappin yau zai koma bayan sun fito da ga sallar asuba. Dan haka babu musu ya shige inda M. Adamu ya buɗe masa kusa da Alhaji Hameed Taura (Bappi). A wata jiƙaƙƙiyar mota data gama haɗuwa. A tsammaninsa ƴan kayan buƙatarsa dake cikin bag an riga an fiddo masa tuni.........✍


No comments

Powered by Blogger.