Bakar Inuwa 14

 


*_Episode 14_*



...........Sai da motar ta tsaya a harabar asibitin sannan Alhaji Hameed Taura ya dubi Ramadhan da ke kwance jikin sit ido a rufe. Sai faman jan numfashi yake a gwame alamar ransa har yanzu a ɓace yake. Sumar kansa yayma kallon second goma ya sake

ɗauke kansa, batare da yace komai ba ya miƙa hannu a booth ya ɗakko ledar dake ajiye da huluna a ciki ya duba wadda yake zaton zata dace da shigar Ramadhan ɗin ya ɗakko. Dama shekaran jiya ya sayesu domin Ramadhan ɗin, sai dai ya mantasu ne a motar bai kuma sake shigartaba sai yanzun.

     Kari yay mata sannan ya ɗaura masa akan hannu, hakanne yasa Ramadhan buɗe idanunsa da suka ƙanƙance da canja launinsu.

    “Saka hular nan muje”.

Komai baice ba ya ɗauka hular ya ɗora saman kansa kawai batare da duba tayi ko bataiba. Kai Bappi ya ɗan girgiza da riƙo hannunsa ganin zai fita. Batare da shima yace masa komai ba ya gyara masa ita ta zauna ɗas tamkar dan shi akayita. Sosai ya fito asalinsa na bahaushe cikakke. Wanka na ɗaukar jikin Ramadhan ko wanne irine. Sai dai a duk lokacin da ya saka manyan kaya yakan zama babban mutum da cikar kamalarsa ke daɗa fitowa a zahiri ga masu kallonsa. Sai kaga yayi maka wani irin kwarjini dake saka mutane jin shakkarsa da bashi girma koda basuyi niyya ba.

     Duk da ya fahimci asibiti sukazo bai tanka ba har suka shigo ɗakin da Raudha ke jinya, police ɗin da president ya bamma Alhaji Hameed Taura biye dasu tamkar jela. Ko'a dacan da ƙuruciya Alhaji Hameed baya son bodyguard tare da shi balle yanzu da tsufa yay masa kamun kazar kuku, yake ganin rayuwar ƙiris ta rage masa ma.

        Bappi ne kawai yay sallama a zahiri duk da yasan babu kowa a cikin. Ramadhan kuwa a saman laɓɓansa yayi yana biye da Bappin tamkar dole. Ɗaki ne babba dake ɗauke da komai na buƙatar mara lafiya ɗan gata. Sai Nurse ɗaya dake tare da Raudha data farka tun asubahin yau. Tun ɗazun doctor ya shigo yay mata dukan abunda ya dace tare da dubata. Aka kuma bata abinci taci tare da magunguna. Yanzu haka idanunta biyu tana kallon television ɗin ɗakin da ake nuna wani wasan salla na yara daya ɗauke hankalinta, yayinda Nurse ɗin ke zaune tana faman latsa wayarta.

      “Barkanku da zuwa ranka ya daɗe”.

Nurse ɗin ta faɗa cikin ɗan rawar jiki tana miƙewa zaune. Ranta fes kamar an bata ƙyautar kujerar makka yau gata ga babban ɗan kasuwar nan daya gawurta a ƙasar NAYA da ƙetare a gabanta. Tare da young millioner grandson ɗin sa a gefensa. Dan fuskar Ramadhan sananniyace ga mutane sakamakon rawar da yake takawa shima akan dukiyar tasu wajen juyata da kuma nuna bajintar taimakon talaka akan aikinsa na lauyanci. Babban abinda ya sake bayyanama duniya fuskar tasa lokacin daya rasa matarsa sakamakon shan guba da sukai, dan labarin babu gidan jarida da redio da yanar gizo da bai zagaya ba. Hatta da Raudha taga labarin duk da a lokacin tana jss 2 ne a secondary.

    Dan in bata manta ba alokacin har gulmar tsarin halitta da iya ɗaukar wankan Ramadhan ɗin tayi a ranta, duk da kuwa a jikin jarida ta gani ita a wajen wata ƙawarta Rahma Salisu.....

      “Masha ALLAH, Alhmdllhi ya rabbi”.

Bappi ya faɗa yana duban Raudha murmushi na sake faɗaɗa akan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa.

    Murmushin ƙarfin hali itama tai masa, dan haka kawai ita dai dattijon ya shiga mata rai. “Abba ina kwana”.

    Ta faɗa da dasashshiyar muryarta tana satar kallon Ramadhan da ko kallon ɗaya a cikinsu baiyi ba balle ɗakin. Tunda suka shigo ya jingina da bangon farkon shigowa ya tura hannunsa a aljihu ya fiddo wayarsa dake tsuwwa yana dubawa. Hakan yasa Raudha bata ganin fuskar tasa da ƙyau yanda ya kamata. Sai dai ƙamshin turarensa da yanda kayan suka zauna ɗas a halittarsa yay mugun fisgar idanunta daga kasa barin kallonsa da son tuno a inda ta taɓa ganinsa......

       “Lafiya lau ƴar albarka, yaya jikin naki?!”.

Bappi ya sake katse mata tunani a karo na biyu yana kallon ƙafarta da akai hanging jikin wani ƙarfe, har yanzu a kumbure take sosai abin tausayi. 

     “Alhamdulillahi naji sauƙi Abba”.

“Zadai kiji soon insha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Ya cigaba da baki kariya a duk inda kika shiga a faɗin duniya. ALLAH ya share hawayenki ya azurtaki da zuri'a ta gari da zata zama lulluɓin nagartacciyar inuwa ga ƙaddarorinki”.

      Hannu Raudha ta kai ta share hawayen da suka silalo mata tana amsama bappi. Zuciyarta sai sake faɗaɗa take da ƙaunar tsohon.


      Magana da Bappi yayma Ramadhan ne ya sakashi ɗan matsowa gaban gadon, a karon farko yayma Raudha kallo guda yana tura wayarsa a aljihu, tare da ɗauke idon nasa da ya saka tsigar jikin Raudha tashi. Ƙafar yaɗan kalla, sai kuma ya watsa mata harara. Tun a jiya daya karanta abinda ya faru kafin ya iso ƙasar, da kuma bayanin da Bappin yay masa akan yanda abin ya faru sai zuciyarsa ke raya masa akan wani dalili Raudha ta aikata hakan. Dan in babu dalili babu yanda za'ai ta bada jikinta a raunata saboda kakansa. Na farko kodai akwai shiri a lamarin, ma'ana tanada alaƙa da makashin. Na biyu ko tayi hakanne domin kuɗinsu ko wani abu makamancin hakan. Na uku tanada alaƙa da waɗanda suka halaka masa mata da ƴars......

      “Ramadhan!”.

Bappi ya ambaci sunansa a nutse ganin kallon banzar da yake yima Raudha a kaikaice. Fuska ya sake ɓatawa da jan ƙaramin tsaki a ransa. Harya buɗe baki zaiyi magana ya maida abunsa ya tsuke ganin Bappi ya ɗan ja baya yana kai wayarsa da aka kira cikin kunne alamar amsawa.

         Tuni Raudha ta ɗauke idanunta daga kallonsa. Saboda kallon banzar da taga yana binta da shi ya saka zuciyarta yin ɗaci. Tanada haƙuri, amma tana da zuciya. Sannan ta tsani wulaƙanci koda ga wanda ya girmeta ne......

      A hankali cike da ƙasaitarsa da jin eh ya isa ya taka gaban gadon sosai fiye da farko, ƙamshin turarensa ck one ya sake sirɗaɗawa cikin hancin Raudha yana keta cikin jininta zuwa ɓargo, saboda ƙarfinsa da tasirinsa ga ma'abocin shaƙansa. Ƙarfen gadon ya dafa saitin kanta tare da ranƙwafowa har tana iya jin fitar sautin numfashinsa. Ya saki wani sihirtaccen murmushi mai ɗauke da ma'anoni da yawa dai-dai gaɓar da yake cafke ƙwayoyin idanun Raudha da mamakinsa ya sata ɗagowa ta kallesa cikin nasa. 

      “Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke *_BAƘAR INUWA ce_*. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki *_BAƘAR INUWAr_* da sai kin gwammaci *_GARA RANA DA NI!_*.   

          A kausashe furucin ya fita daga harshen Ramadhan, cikin ƙasaitacciyar muryarsa mai faɗi da kauri ya shiga dodon kunnen Raudha. Da ace ba kusa gab yake da kunnuwanta ba, ita da kantace zata ƙaryata cewar shine ya faɗa ɗin, dan duk wanda yaga yanayin nasu zai ɗauka wata maganace mai daɗi a sanadin tausayawa. 

      Kafin ta iya ce masa wani abu ya fincike idanunsa a cikin nata cike da tabbatar da gargaɗinsa. Ya ɗan dubi Bappi dai-dai yana ɗagowa ya miƙe akan ƙafafunsa da ƙyau. Ganin Bappin su yake kallo sai ya sakar masa murmushi yana ɗan kai hannu ya shafo ƙeyarsa...

       Tabbas wani abu da Ramadhan bai kawo a ransaba a wannan gaɓar ya shiga ran Bappi a bazata. Tun a daren jiya yake cuɗawa da kwancewa wajen laluben nemo hanyar da zai kwatantama Raudha da iyayenta alkairinta, amma sai ya gagara samowa. Dan gani yake kuɗi, gida, ko makamantansu dan ya bama Raudha bai biyata ba. Saboda ita ransa ta fansa. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ALLAH ya haska masa wata hanya da yake ganin ko bai saka mata ba, zai kwatanta kusantata gareshi harya samu alkairi daga alkairinta a cikin zuri'arsa..... Ya saki wani ƙasaitaccen murmushi yana kai hannu bisa kafaɗar Ramadhan ya ɗan bubbuga cike da salon manya idan abu yay musu daɗi.

        (Lallai sun dace) ya ayyana a ransa yana duban Raudha data kauda kanta gefe zuciyarta na luguden daka daga kausasan kalaman Ramadhan da zuciyarta ta kasama fashin baƙi. Sai kawai nan ma Bappi ya fassara kauda kan nata da tunanin jin kunya duk da baisan wane furuci jikan nasa ya furta a gareta ba.

        Ramadhan da shi sam baima kawo abinda Bappin ke ayyanawa ba a tunaninsa sai kawai ya nufi hanyar fita dan gaba ɗaya ya gundura da zaman asibitin. So yake yabar ƙasar nan a daren yau dan tuni ya kammala booking flight. Sai dai zai tashi ne ta jihar Loss shiyyasa yake son barin Bingo da wuri yaje can ya ɗan huta kafin daren.

       Nanma da kallo Bappi ya bisa yana murmushi, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Raudha da har zuwa yanzu ruɗani bai bar tunaninta ba...


*_TAURA HOUSE_*


      Tun fitarsa take ƙame a tsaye, sai da ta fahimci jinin jikinta sulalewa yake zuwa ƙasa sannan tai jarumtar jawo numfashin dake neman barin ƙirjinta yana bin jininta dake sauka a ƙafafunta. A ƙa'idar kowanne ranakun bikin salla na babba da ƙarama washe gari a masarautarsu take yinta ita da dukan iyalanta dama ahalin masarautar garin ta Bina. Shiyyasa a yanzu haka jirgin da zasu bi a shirye yake tsaf zuwa jihar BINA fitarsu kawai ake saurare.

      Waya ta jawo da sauri dan bazata iya jira har sai ta isa garin Bina ba zuciyarta zata iya fashewa. A yanda take ƙoƙarin dialing numbern na ƴar uwarta Asma zai baka tabbacin a ruɗe take. Ta saka wayar a hansfree dai-dai shigarta. Bugun shigar kiran na bugawane dai-dai da bugun zuciyarta. Sai dai abin takaici harta tsinke ba ɗagaba. Sake kira tai nan ma babu amsa. Sai da ta jera kusan kira biyar amma ba'a ɗaga ba. Lallai babu lafiya, dan a ƙa'idar gimbiya Su'adah daga kira ɗaya bata sake yima mutum ko yaya suke, mai-martaba ne kawai keda wannan alfarmar da arziƙin a gareta. Amma a yau sai gata da jera har biyar batare da taji ta gundira ba.

     Da sauri ta maida akalar kiran nata ga mai-martaba saboda zuciyarta ta ayyana mata shine kawai maganin kukanta a yanzu bama Asma ba. Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa a ka ɗaga, domin kuwa abune a bayyane kowa yasan gimbiya Su'adah ƴar gaban goshin mai-martaba ce saboda sunan wadda ta riƙesa da yakema kallon uwa aka saka mata.

    Cikin girmamawa tamkar tana a gabansa ta rissina tana gaishesa. Daga can ya amsa da sakewa cike kuma da ƙasaita irin ta masu mulki. 

      “Mamana kun iso ne?”.

  Cikin girgiza kai da sake raunan murya ta ce, “A'a Abi bama mu taho ba. Dama Ramadhan ne yazo NAYA jiya, bamma san da zuwan nasa ba sai a safiyar yau. Koda ya shigo gaisheni yayiminne tamkar maƙiyarsa ba mahaifiyarsa ba. Daga ƙarshe yake sanarmin a yau zai koma America. Nama tabbatar yanzu yana gab da barin ƙasar..” ta ƙarasa faɗa tana sakin wani kuka mai ban tausayi gamai saurarenta.

     Mai-martaba ya saki ƙasaitaccen murmushi yana gyara kishingiɗarsa. “Ni ban san randa Mamana zata girmaba har yanzu. Yanzu dai akan   Ramadhan kike ɓatamin hawayenki? To sharesu ki kwantarmin da ranki. Yanzu babu jimawa mukai waya da Alhaji Hameed akan zasu ƙaraso nan tare da shi, suna airport ma a yanzu haka”.

     Wani irin wawuyar ajiyar zuciya ta saki da murmushi lokaci guda. Sai hawayenta data kai hannu ta share da faɗin, “Nagode Abbi”.

      “Godema ALLAH”.

Ya bata amsa yana yanke wayar.

Tuni ta manta da hawayen fuskarta ta hau sakin murmushi. Koda Addah Asma ta kirata batabi takan kiran ba dan tasan yanzu zasuje su haɗu ai....


*_TK SPECIAL HOSPITAL_*


          Ita ɗin yarinyace mai kaifin basira da hangen nesa. Hakan yasa tun bayan barin su Ramadhan ɗakin ta shiga cikin zurfin tunani da fassarar kalamansa. Sai dai kafin ta samu damar samo amsar sallamar ƴan uwanta da su Asabe harma da kakarsu Hajiyar birni ya katseta. Taji daɗin ganinsu dan dama tunda ta farka take tambayar likita ina suke. Dan da farko ta tsorata da tsadajjen asibitin da taga kanta a ciki.

      Rungumeta Asabe tai tana kuka, dama shi ta kwanayi a daren jiya. Dan gani take Raudha ta rasu ne su aunty Hannah na ɓoye mata. Hakama Yasmin tana kallon ƙafar Raudha ɗin ta fashe da kuka, kukanta kuma yaja hankalin su Samha suma dake ƙananan yara suka fara.

       Sai da hajiya mama ta ɗan musu tsawa ne ganin aunty Hannah na lallashinsu sunƙi su nutsu. Yanzu kam tsit sukayi sai Asabe ce ke nata tana jerama Raudha addu'oin samun lafiya....


   ★


    Kasancewar Alhaji Hameed Taura ba ƙaramin mutum bane cikin ƙanƙanin lokaci zancen sake ziyararsa asibiti tare da jikansa ta baje kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo. Harma abin ya bama Bappin mamakin tunda yasan baici karo da ɗan jarida ko gudaba. Sai dai tunawa da cewar yanzu waya ta maida kowa ɗan jaridar kansa ya sashi watsar da kokwanton.

      Yabo dai kam yana samu akan ƙoƙarin tsayawa tsayin daka ga Raudha. Dan yanda kowa yasan wanene shi ba'ai tunanin zai bada lokacinsa gareta ba. 


*_JIHAR BINO PLACE_*


          Duk da Ramadhan nata ɓata fuska a cikin jirgi hakan bai hanashi jin daɗiba a ransa sanda suka iso cikin masarauta. Dan suna sauka a airport ƙayatattun motoci na alfarma guda huɗu wanda uku ke tare da hadimai, ɗaya ta ɗaukarsu suka iso filin jirgin.

        Alhaji Hameed Harith Taura kowa yasan abokine ga Sarki Abdul-wahab tun da ƙananun shekaru. Dan kuwa tarihi ya tabbatar da sunyi karatun degree na farko tare a jami'ar Bino. Sannan harkokin kasuwanci sun sake haɗasu a wasu fannoni kafin mai-martaba ya haye karagar milkin jihar ta Bino. Sai kuma gashi sun zama surukai a dalilin auren ƴaƴansu.

       Yau ranace da masarauta ke cike da baƙi tako ina. Amma hakan bai hana a samarma da su Ramadhan tarba ta musamman ba. Ramadhan na gama gaisawa da mai-martaba daketa tsokanarsa akan ya'akai kuma ya baro masu jajayen kunuwan?. Ko sun gaji sun koroshine da kansu. Shi dai murmushi kawai ya dingayi dan ba kasafai irin wannan wasar ke shiga tsakaninsa da kakannin nasa ba. Daga su Bappi har su mai-martaban sunyi trianing nashi ne like iyayensa ba kakanni ba. Garama Fulani takan ɗan tsokanesa. Sai dai kuma shi ɗin bawai ya iya wasan baneba iyakarsa murmushi ko ada can ma balle yanzun.

     Fahimtar magana su mai-martaba kesonyi ya sashi zame jikinsa zuwa cikin gida domin ya gaisa da kakar tasa da iyaye da ƴan uwa. Yako karancesu da ƙyau, dan yana fitar suka hau tattauna dalilin zuwan Alhaji Hameed ɗin dan awa ɗaya kacal suke da ita saboda mai-martaba na amsar baƙuncin manyan mutane masu barka da shan ruwa da barka da salla.

     Abubuwa masu muhimmanci guda biyu suka tattauna. Wanda ya shafi auren Ramadhan da Bappi atake ya sanar ma mai-martaba har yayi masa mata. Da kuma batun fitowa takara da zata bayyana nan da ƙanƙanin lokaci. 

   Duk gaba ɗaya mai-martaba yayi farin ciki ya kuma sanya albarka da fatan alkairi a cikin lamarin, tare da bada goyon baya dan a ganinsa ai babban cigabane jikan nasu ya samu. Daga haka ya ƙara da nasa shawarwarin shima...........✍



*_Barkanmu da dawowa._*😘😘👌🏼


No comments

Powered by Blogger.