Bakar Inuwa 15
*_Episode 15_*
..........Su Bappi basufi mintuna talatin da isowaba Gimbiya Su'adah da tawagar ƴaƴanta mata suka iso suma. Anan ne ta samu damar haɗa hannu da fulani (mahaifiyarsu Uwargidan sarki) da Adda Asmah suka rufe Ramadhan da faɗa sosai akan abubuwa da dama, ciki harda batun zamansa babu aure, duk da dai basu fiddo maganar zaɓa masa mata ba.
Shiko dai ya cinkushe fuska yana saurarensu kawai. Sai da sukayi mai isarsu ya basu haƙuri kawai yay fitowarsa. Dan Bappi ya kirasa akan ya fito su wuce. Idan kuma ya barsa anan to?. Da sauri yacema Bappi a'a zai bisa, dan so yake yaje ya wuce loss, sai dai bai faɗama bappi ƙudirin nashiba kai tsaye.
Yanzu kam ya iske mai-martaba tare da Bappi da Pa da suka iso da Gimbiya Su'adah. baiyi mamakin ganin Pa ɗin ba, tunda tun yana ƙarami yasan a irin wannan ranar ta washe garin salla suke zuwa gaishe da mai-martaba ɗin daman. Zama yay gefen mai-martaba daya nuna masa yana satar kallon Pa da fuskarsa ke a haɗe alamar har yanzu yana kan fushinsa na jiya. Koda yake har suka baro Bingo dama baiko kallesa ba duk da har falonsa yaje ya gaishesa.
Sai da suka tabbatar da nutsuwarsa sannan Bappi ya fara magana cikin nuna alamar babu wasa tattare da shi.
Ramadhan ya ɗago a firgice yana duban mai-martaba. Kafin ya maida dubansa ga Pa da baice uffan ba.
“Bappi!”.
Ramadhan ɗin ya faɗa cikin rawar harshe.
Bappi dake kallonsa cike da tausayawa a can ƙasan ransa. A fili kam ya dake ya jinjina masa kai. “Umarnine wannan ba shawara ba Ramadhan. Domin nasan zaka iya insha ALLAH. Zaka kuma kawo cigaban da muke fata wa ƙasar nan ta hanyar basira da ƙuruciyar da ALLAH yabaka. Domin NAYA irinka take buƙata, tabbas irinka take buƙata.”
Miƙewa Ramadhan yayi yana girgizama su Bappi kansa. Ya kai hannu ya tura hular kansa baya saboda zufa dake ɓillowa a kowacce ƙofa ta gashinsa. Babu abinda zuciyarsa ke ambata sai sunayen ALLAH. Ya sake buɗe baki zaiyi magana Pa ya dakatar da shi....
“Biyayya ga iyayena dole ne a gareka, domin bazasu taɓa jefaka a hanyar halaka ba. Tunda har su Bappi suka amshi tayinsu, dolene kaima ka amsa da ga garesu kayi biyayya. Idan ba hakaba babu ni babu kai da ga yau da ga wannan likaci....”
“Pa Please yayi girma da yawa....”
“Baiyi ba Ramadhan. Domin kaima kayi abinda kakeso a shekaru biyar muka kuma ƙyaleka, duk badan kafi ƙarfinmu ba. Dolene yanzu kaima kabi abinda mukeso dan lokacinmu ne.”
“Ya ALLAH”.
Ya faɗa cikin sake shiga tashin hankali yana komawa baya ya sake zubewa a cikin kujerar da ya tashi. Gaba ɗaya ƙwayoyin idanunsa sun sake canja kala a lokaci ƙanƙanin. Ɗan sassaucin daya samu na damuwar jiya wadda ta fita ta sake maye gurbinta. Gaba ɗaya gashin jikinsa ya mimmiƙe sai faman tura yatsun hannunsa yake cikin sumarsa dan son control ɗin abinda ke taso masa...
Duk da Bappi ya san Ramadhan ɗin yakai maƙura gab yake da birkice musu bai sassauta masa ba. Dan a ganinsa gara ayita baki ɗaya ta ƙare kawai. Hakan yasa kai tsaye ya ɗora da faɗin, “Sai kuma batun aure, shima mun riga mun maka mata dan ko munce ka nemo ba kawowa zakai ba. Bakuma zai yuwu ka hau mulki babu mace ba, idan har ALLAH ya ƙaddara zaka hau ɗin. Dan haka mun gama yanke hukunci mu zamu nema maka aur.....”
Kafin ma Bappi ya ƙarasa numfashin Ramadhan ya fara fisga. Ya shiga laluben hanun bappin dake kusa da shi, da ƙyar ya samu ya riƙosa ya damke. Cikin sauri Bappi ya miƙe ya ya rungumesa a jikinsa da kiran sunansa yana girgizashi.
Su dukansu ɗunbin tausayinsa ne a cikin ransu. Wannan yanayi da yake shiga idan ransa ya ɓaci yana tada musu hankali, babu irin likitan da basu gani ba, amma iya bincike akan sanar musu lafiyar ƙwaƙwalwarsa kalau. Sai dai maimakon su maida hankali gana musulinci sai suke sakaci, dan tabbas al'amarin nasa yana kamanceceniya da nai mai iska ko sihiri, ga diabetis kuma da shima ya zame musu na gado. Dan shi kuma Bappin ne ke dashi, shima Alhaji Basheer ɗin nada, hakama Ramadhan ɗin da wasu a cikin yaran gidan ƴammata.
“Ramadhan relax, calm down Please”.
Bappi ya faɗa yana shafa kafaɗarsa da ɗora masa kofin ruwa a baki. Babu musu ya sha kusan rabi, sai kuma ya miƙe ya sake rungume Bappin. Murmushi Bappi yayi da sake rungumesa da ƙyau shima yana shafa bayansa.
“Please Bappi a sassauta mini koda maganar auren a janye”. Ya faɗa lokacin da Bappi ke ɗagosa da ga jikin nashi.
Murmushi Bappi yayi mai ƙayatarwa da shafa sumar Ramadhan ɗin yana girgiza masa kansa. “Babban sassauci kawai bin umarninmu Ramadhan. Idan kayi hakan sai ALLAH ya albarkaceka da nasarori a rayuwarka ok?”.
Maimakon amsa sai ya sake faɗawa jikin Bappin ya ƙanƙamesa har takai mai-martaba da baice komaiba har yanzu sakin murmushi. Shi kansa Pa gefe ya maida kansa yana nasa murmushin dan yasan mai shiga tsakanin Bappi da Ramadhan sai ALLAH. Shi kansa ya buɗe masa wutane dan yasan sa sarai akan kafiya da dagiya kan abinda bayaso. Shiko bazai taɓa yarda mahaifinsa yaji kunya ba tunda har ya riga ya amshi tayin su president ɗin....
*_GOVERNMENT HOUSE_*
Tarba ta musamman Alhaji Hameed Harith Taura ya samu shi da Ramadhan a fadar ta shugaban ƙasa, kasancewar tun a daren jiya Bappi ya sanarma mai-girma shugaban ƙasa zuwan Ramadhan ɗin NAYA ta hanyar text Message.
Duk da tarin liyafar da aka shirya domin Ramadhan hakan bai wani birgesaba, dan tunda suka baro masarautar Bina zuciyarsa bata tare da gangar jikinsa duk da nasiha mai ratsa jiki da mai-martaba da Pa da Bappi sukai masa.
Sai kuma Raudha dakan faɗo masa a rai. Sai yanzu yake ƙara yarda da hasashensa kan dalilin Raudha na bama Bappi kariya. Dan haka kawai bazata bada ranta akan wanda bata saniba ko rashin dalilin, zuciyarsa na sake tabbatar masa a yanzu abinda tayi nada alaƙa da wannan batun na fitowarsa takara, lallai akwai wani shiri a ƙasa da su Bappi basu fahimtaba. Sai dai wanene ke shiryawa? Akan mi? Akan wane dalili? Duk bai saniba shima.
A zuciyarsa yake ayyana. (Inko hakane dolene nabi dukkan hanyar daya dace dan na sani koda kuwa hakan na nufin zai iya rasa raina).
Taro ne daya tara manyan jiga-jigan jam'iyyar tasu, sai dai gaba ɗayansu sunada masaniya akan son tsayar da Ramadhan takarar. Amma kowa yanada manufarsata ta amincewar kuma. Wani yanki a cikinsu kamar su Alhaji Yaro glass sune suka san ainahin manufar. Sauran kuma suke kallon hakan bisa ƙyaƙyƙyawar niyyar manyan jam'iyyar na kawo dai-daito akan rabuwar kawuna dake neman shiga tsakaninsu a dalilin yawan ƴan takara. Sai dai kuma duk da haka wasun su zukatansu a ƙuntace suke da rashin son Ramadhan ɗin musamman da suka gansa yaro ƙarami saboda mafi yawansu sun haura sittin su, kawai dai basu da ƙarfin faɗa ajine sai ya zam dole suka zuba ido wajen bin gangar yarima asha kiɗa.
Bayan anci an sha da ga abinda aka tara wanda Ramadhan ko ruwa bai sha ba a wajen suka fara gudanar da abinda ya tarasun. Shugaban jam'iyya da sauran jiga-jigai sukayi bayanai da welcoming ɗin Ramadhan cikin su, tare da fatan zai basu haɗin kai wajen yin aiki tuƙuru da ƙara ɗaga darajar jam'iyya.
Ba wani fahimtarsu yake ba, dan sam hankalinsa baya a tare da su. Amma magana da ido da Bappi yay masa ta tilasta masa miƙewa yay bayani shima. Bayan godiya da jinjina a garesu ya tabbatar musu zasu sameshi fiyema da yanda suke buƙata.
Jin kalmar (fiye da yanda suke buƙata) a bakinsa ya sasu ji a ransu zasu iya juya Ramadhan duk yanda sukeso domin biyan buƙatunsu.....
*_JIHAR ƊILLO. HUTAWA_*
Tunda Asabe tabar gidan gaba ɗaya sai ya koma tamkar wani zararre. Duk masifarta da gantalin faɗansu da baya ƙarewa itaɗin ta daban ce a gareshi. Dan a gidan Asaben ce kawai zata samu abunta ta bashi batare da baƙin ciki ba. Amma ko baba Nafi duk haƙurinta akwaita da halin banza a wani fannin itama. Sai dai nata da sauƙi akan na Larai.
Da farko Larai tata ƙoƙarin ganin neman auren da Alhaji Maude Dallatu Kema Raudha ya dawo kan ɗiyarta ne Zabba'u. Dan tata lallaɓa M. Dauda akan hakan tare da banka masa rubutu da magungunan malam. Ance tsafi gaskiyar mai shi, dan ta ɗan fara samun kansa harma da manta Asabe da ƴaƴanta da taso yayi, sai dai kuma ba'aje ko inaba aikin ya watse.
Dan a ranar salla tunda labarin abinda ya faru da Raudha yazo kunnensa sai ya rikice harda kukansa. Ya dinga tsinema Alhaji Hameed Taura akan yaja an kashe masa ɗiyarsa saliha mai addini. Dan kuka rurus ya zauna yanayi a bakin masallaci. Mutane suka taru a kansa anata bashi haƙuri da lallashi amma M. Dauda sai sake ɓare baki yake yana fyatar majina.
Daga ƙarshe yace inhar anaso yay shiru sai a haɗa masa kuɗin motar zuwa Bingo inba hakaba yata kuka kenan har sai Alhaji Hameed Taura yazo Hutawa. Mutane sun san halin M. Dauda ƙwallon ɗan is.... Ne shiyyasa basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara haɗa masa wasu ƴan kuɗaɗe. Yai kwanaki biyu kenan kuwa ana haɗa kuɗin a masallaci. Ba wani kuɗin kirki bane suke badawa. Mai hamsin mai ɗari ne kawai, shiyyasa haɗa kuɗin yaɗan ja lokaci duk da sun san zuwa yanzu ya samu fiyema dana motar.
Ilai kuwa a daren jiya aka tattare kuɗin naira dubu bakwai aka bashi harda canji a sama. Daɗi ya sakashi fara godiya yana kuka, harda cewa baisan ana ƙaunarsa a anguwar tasu ba har irin haka. Sudai mutane dariya suka dinga gumtsewa kawai. Shi ko ko'a jikinsa, ana idar da sallar asuba ma ko wanka baiyiba yaje gida ya canja babbar riga kawai, rigar duk ta fita hayyacinta da tsufa da dauɗa amma bai damuba. Dan itace kawai rigarsa ta arziƙi ta ganin shugaban ƙasa. Ya dakwarra wata shegiyar hula da ko wanki babu tare da ita balle sitatin kirki.
Duk jarabar da Larai taita masa da ƙirƙirar suyi rigima ta lalube kuɗin bai kulata ba, sai ma ɗakko bakko ɗin kayansa data gama shiga uku dan tsufa yay yayi fitowarsa. A ƙofar gida yaci karo da malam Gambo abokinsa. Yay wani gaba kamar zai kifa sai kuma ya dawo baya ya dafe bango yana hangame baki da haɗe fuska.
“Kai kuma lafiya na ganka anan harda malum-malum?”.
Baki M. Gambo ya washe yana miƙewa tsaye da leda viva ɗinsa a hannu, shi kansa ba ƙaramin a harmutse yake ba, dan har gwarama m. Dauda ɗin ta wani fannin. “Kai abokina ya kake magana haka kamar ka manta ni abokinka ne na amana. Ai bai kamata na barka kaje kai kaɗai ba babu kara. Dole ne na bika muga halin da yarinyarmu ke ciki tare. Mu kuma san matakin da zamu ɗauka akan tsohon nan Taura”.
Da farko ƙanƙance idanu M. Dauda yayi yana harar M. Gambo Ƙasa-ƙasa. Sai kuma tunawa da yay M. Gambo ya fisa tujara ƙila idan sun sami ganin Taura zaifi ƙwato musu ƴanci. Dan yayi alƙawarin idan Taura bai sauraresu ba gidan redio zai dawo ya masa terere duk da a yau yaji a labarai an sake cewa Taura da jikansa sunje sun sake duba Raudha a asabitin da aka ɓoyeta ana bata tsaro na musamman. Ciwon Raudha ya damesa, amma a ƙasan ransa gani yake silar arziƙinsa ce a wajen. Dan yasan dai baza'a nakasta masa ɗiya a dalilin Taura ba Taura yaƙi jiƙashi da kuɗaɗe. Wannan yanada ɗaya daga son zuwan nasa Bingo...
“Abokina daina tunanin nan muje da-ALLAH kar rana tayi”.
“A'a ai ba tafiyar bace matsalata M. Gambo, ka sani duk fa abinda muka samo sammaka zanyi ba raba dai-dai zamuyiba. Dan nasan badan ALLAH kake son mini binbinin nan ba.”
Kamar m. Gambo zaiyi magana sai kuma ya fasa, dan yasan halin buyagin M. Dauda. Lallamashi kawai ya shigayi harya haƙura suka tafi tasha neman motar Bingo.....
*_BINGO CITY (TAURA HOUSE)_*
Komai ya ƙwace masa, babbar damuwarsa hanashi komawa da Pa da Anne sukayi America. Dan Bappi dai yaƙi yace masa komai tunda suka baro gidan gwamnati. Shima ɗin bai yarda ya zauna da kowa ba ya shige ɗakinsa dake a sashen na su Anne. Koda yake bazamuce ɗaki kawai ba. Dan shima tamkar wani part ne na musamman a wajen. Falone har guda biyu ƙarami da babba, ƙaramin an shiryasane kawai dan hutawa, inda glass ne kawai ya rabasa da babban sai labulaye. Sai bedrooms biyu, kitchen, store, dining, da ƙofar da zata sadaka da backyard inda akai wani haɗaɗɗen ƙaramin garden da yasha tsirrai masu ni'ima, ga madaidaicin swimming pool a gefe da akai masa wani style da ruwa ke fitowa ta wani dutsuna tamkar ƙorama. Daga can gefe keɓantaccen wajene da akayi da glass an cikashi da kayan motsa jiki ().
Duk gidan bamai shigowa wajen sai idan aikosa akai, dan ko baya nan mai kula da shine kawai ke shigowa saiko Bappi idan yanason kaɗaice kansa. Idan kana hango wajen daga cikin falonsa saboda glass ne a bangon saika ɗauka bama cikin NAYA kake ba, dan daga falon kana jiyo ƙamshin furanni dana saukar ruwan dake fita a dutsen nan, ga grass carpet ta ko'ina lamarin ba'a cewa komai.
A yanzu hakan ma dai a cikin garden ɗin yake kwance bisa kujera irin wadda akan ajiye gaban ruwan nan domin hutawa kawai, ƙafarsa ɗaya a ƙasa ɗaya tana kan kujerar, yayi kwanciyar rigingine ne fuskarsa na kallon sama, yay filo da hannunsa ɗaya yayinda ɗayan ke riƙe da gorar ruwa, ya ƙurama sama ido tamkar yana irgen gajimaren dake yawo ne a cikinta.
Abu biyune sukafi komai masa kaikawo a yanzun. Maganar siyasa da su Bappi keson tsundumasa batare da shi ya taɓa ra'ayin hakan ba. Sai ɗunbin zargin Raudha da yake ganin tayi komai ne da wani dalilinta kona sakawar waninta. Na ƙarshe ma tana ɗan sukarsa sai dai ba sosai ba, wato maganar aure, babu zancen ƙara aure a budget ɗinsa, dan haka koma ƴar wacece ake son aura masan shi zai gargaɗeta ta bijire ma su Bappi. Dan haka baya ɗaukar wannan babbar matsala........✍
To Ramadhan B. Taura bara mugani koba babbar matsala bace kamar yanda ka ɗauka😜🏃🏃.
Leave a Comment