Bakar Inuwa 2
*_Episode 2_*
*_ƘASAR NAYA_
.........*_(DALLO STATE): HUTAWA L.G.A._* Da gudu budurwar ta miƙe ta shige ɗaki tana cigaba da kuka, ganin a yanda ta shigo ta wuce tana kuka, ƴammata biyu da za'a iya kira tagwaye kuma yayunta suka kwashe da dariya suna faman taɓe baki da ɗaga kwalbar lemonsu suna ɗaɗɗaka hankali kwance.
Sai kuma suka maida dubansu akan Asabe data shigo tana cigaba da zazzaga ruwan tujara.
“Kina wuta momyn mu!!👍🏼”.
Ƴammatan suka faɗa suna mata jinjina da kwashewa da dariya a karo na biyu. Zama tai kusa da su taja kwalbar lemo guda tasa haƙori ta ɓalle murfin tana huci. Batare data cema ƴammatan komaiba ta ɗaga tasa a baki, kamar ƙiftawar ido sai gashi ta zuƙi kusan rabi sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya.
Wadda tafi hasken sosai dake kallon kwalbar lemon ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Mommy sunan wannan shan lemon naki shan huce takaici”.
Tsaki tayi tana gyara zama da ɗaukar tsokar nama dake gabansu ta danna a bakinta. “Yo wannan uban naku inba shan huce takaicin kakema ni'imar da ALLAH yay maka ba ai tuni yake tsotse maka ruwan jiki, ga waccan mara mutuncin dake abu uwa ba jinina ba.”
“Yo Mommy bayan kamanin da take dake ai sai muce muma ko'an canja miki ita ne a asibiti? Muda yakamata muyo kamanin naki hegiyar mai taurin kan tsiya da kicifi duk an haɗa ita an bata.”
Duk abinda suke budurwar nan na jiyosu daga uwar ɗaka. Dan haka ta sake fashewa da kuka zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗin halin iyayen nata da ƴan uwanta. Tun tana ƴar ƙaramarta takejin ana zagi da la'antar halin mahaifanta a cikin layinsu, har gashi yau tsahon shekara goma sha bakwai bataji komai ya canjaba sai ma abinda ya ƙaru a dalilin ƴan uwanta guda biyu da kullum cikin janyo masu wata sabuwar maganar suke. Duk da dai itama ta fara rashin ji mai kama da nasu ALLAH ya tarota ta nutsu sanadin malamin islamiyarsu sayyadi Abubakar.
Hannu tasa ta share hawayenta da gyara kwanciyarta zuwa rufda ciki, duk da yunwa dake cinta saboda azumin data kai hakan bai dameta ba, ta lumshe ƙyawawan idanunta data gada wajen mahaifiyarsu Asabe a hankali Murmushi na suɓuce mata mai haɗe da hawayen tausayin kanta na rasa Abubakar. Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta rasashi, ya tafi har abada bazai sake dawowa gareta ba kamar yanda iyayensa suka faɗa. Wannan ciwone a rayuwarta mafi muni da har abada bata tunanin warkewarsa, dan ya zama gyambo a ƙirjinta. A tsaye take da sunanta, amma a zuciya ta jima da mutuwa tun sanda iyayen abubakar suka saka ya fita a rayuwata.
“Ya ALLAH ka ɗauka raina inhar zaifi zama alkairi a gareni”.
Ta faɗa cikin kuka mai ban tausayi da tsum rai.
Sunanta shine *_AMINATU_* sai dai ana kirana da *_RAUDHA_* sakamakon sunan kakarta da taci wadda ta haifi mahaifinta. Kamar yanda kukaji a bakin mahaifiyarta sunan mahaifinsu DAUDA, sai dai ana kiransa ɗan-azumi. Tun a ƙuruciyar mahaifinsu mutum ne marajin magana. Al'amarin nasa ya sake turewa a lokacin daya fara bin wani ɗan anguwarsu driver matsayin karen mota. Kamar yanda kakarsu ta taɓa basu labari tarbiyyar Abbansu da rayuwarsa ta sake gurɓacewa a dalin wannan bin mota, dan bai rufa shekara ba a hanun uban gidansa sai shima ga tashi motar. Tun yana jan ƙaramar mota harya koma babba irin ta company ɗin nan da ake ɗaukar kaya trailer. Fara jan motar trailer yasa albarka a hanunsa, dan babu wani tazara da hakan kuɗi suka fara zauna masa. Da ƙyar ya yarda ya auri matarsa ta farko Nafisa, wadda ɗiyar ƴar uwace ga kakarsu. Nafisa tanada matuƙar haƙuri, hakan yasa bata taɓa kai karan ɗan-azumi ba a duk gallazawa rayuwarta da yakeyi. Basu rufa shekara da aure ba ya auro sabuwar amarya mai suna Larai. Larai fitinanniyar mace ce mai kauɗi da rashin barin kota kwana. Yanda ta hana Nafi zaman lafiya haka ta hana Mal. Ɗan-azumi. Mahaifiyarsa tayi-tayi ya saketa yaƙi. Babu jimawa da auren Larai Nafi ta haihu, itama Laran bata cika shekara ba a gidan ta haihu. Zamansu ya cigaba da kasancewa babu wani daɗi, yayinda Mla. Ɗan-azumi ya cigaba da sake kutsa kai a yawon tazubar. Dan kuwa a kaso biyu bisa ukun kuɗin da yake samu suna tafiyane ga neman mata da ashararancinsa. Sune manyan ƴan duniyar duk wani gari na baɗala da ire-iren gurare na ashararanci da akasan direbobi na kakkaɓe dukiyarsu a wancan zamanin.
Nafi ce kawai ke damuwa da halin banza na maigidan nasu, Larai ko ko'a kwalar rigarta tunda akwai kuɗi, dan ita kam dama sune matsalar rayuwarta tunda itama acan ya kwasota a tashar ƴan tazubar ɗin. Suna da haihuwa hurhuɗu Nafi da cikin na biyar Ɗan-azumi ya sake sabon aure daga birinin Loss. Ba kowa ya auroba kuwa sai Asabe ɗiyar *Ɗahare (Hajiyar birni)* mai tuwo-tuwo a ƙarƙashin gada.
Ɗahare mace ce mara mutunci da duk wani shege daka sani ɗan yankin nan dake zaman tazubar a Loss ya san da zamanta. Asalinta a ƙasar saudia take tana TIKARI tsahon shekaru, a wani yaya da akayo alƙawarin ALLAH ya cika aka yayota zuwa ƙasar Ghana. Kasancewarta shaharriya acan ɗin ma yasata ko NAYA bata dawo ba ta sake komawa. Dan kuwa yaranta nacan su huɗu wanda ta haifa da wasu larabawa biyu, sai dai dukansu aure tai da su. Na farko rasuwa yay ya barta da yara biyu mata *Samiha da Hannah*, na biyu kuwa rabuwa sukai saboda Ɗahare ta wuce dukan tunanin mai tunani. Kwasotan ma da akai shine yay shunenta dan yana so ya sace yaransa dake hanunta su biyu. Sai dai kuma ta koma domin tanada hanya sosai. Komawar Ɗahare da biyu ne. Na farko da ƙudirin ɗaiɗaita rayuwar balaraben nan ne uban ƴaƴanta guda biyu, *Halima da Nasiba (Asabe)*. Na biyu ƙudirin rabo ƴaƴanta biyu daga hanunsa ne, dan labari yazo mata tana barin ƙasar yana zuwa ya kwashesu yabar wanda ta haifa da mijinta na farko. Kamar yanda ta tsara kuwa hakance ta kasance, dan kuwa dai duk da balaraben nan bawani mai shaharren arziƙi bane, dan kuwa baƙauyene ma. Sai dai yana da arziƙin dabbobi matuƙa na kiwo dana tatsar madara. Duk irin makircin da Ɗahare ta ƙware sai da tabi wajen ganin ta rabashi da wannan dukiyar, jin ana bincikenta a kama yasata tattaro duka ƴaƴanta huɗu ta baro saudia bisa taimakon wasu mutanenmu dake can masu ɗaure musu ƙugu. Koda ta dawo gida kuma babu inda ta yada zango sai tsakkiyar birnin jihar Loss. Inda ta fara tuwo-tuwo yaranta huɗu ƴammata zagaɗa-zagaɗa na taimaka mata.
Game da ƴaƴan nata tamkar kumbo kamar kafinta ne. Dan kuwa a kaf halayyarta babu wacce suka bari musamman ma Asabe mafi ƙyawun fuska da ƙyan sura a cikinsu. Dan kuwa ƙyaƙyƙyawar balarabiyace da kallo guda bai isar mai dubanta. Dan-danan alhazan birni suka fara wawarsu da sheɗanci, dan kuwa inma kace da aure kazo garesu to tabbas kuwa Ɗahare da sunanta ya koma Hajiyar birni ba daga maka kafa zatai ba. Zatai maka wankin babban bargo tace bata gama more wahalarta ba za'a tura mata ƴa cikin ɗaki, sam bata yarda ba.
Ko'a jikin ƴaƴan, dan suma basu buƙatar auren sai harkar neman kuɗin kawai, sai dai banda Asabe. Dan duk kauɗi da rashin mutuncin Asabe ita dai tafi buƙatar aure sama da rayuwar barikin. Bawai batayi bane, a'a bata cika sakin jiki tayi ɗin bane tamkar wata karya. A wannan halin ALLAH ya haɗata da Mal. Dauda ɗan-azumi, wanda yake tsaka da tashen kuɗi. Gashi shima masha ALLAH ƙyaƙyƙyawan bakatsine bafulatani. Dandanan ya fara sakar mata kuɗi na hauka, tare da zazzafar soyayya dan kwashi dai tunda ya ɗana sau ɗaya yaji bazai iya haƙuri yabarta ba sai ya aureta. Duk wani shigi da fici irin na ƴan bariki kwararru ɗan-azumi yayi ga malamsa na masa aiki, cikin ƙanƙanin lokaci ya rikita zuciyar Asabe tace inba shiba sai rijiya mai gaba dubu. Hankalin uwarta ya matuƙar tashi dan tafi kallon sa'arta jikin Asabe fiye da sausan ƴaƴanta saboda ƙyawu da ALLAH ya bata na larabawan asali da ko'a cikin ƙasar saudiyar abin kallo ce. Ganin Hajiyar birni zata bashi matsala itama ya rufe mata baki ruf. Babu ɓata lokaci aka shiga hidimar bikin daya bama kowa mamaki.
An ɗaura auren Asabe da Dauda, aka ɗakko amarya zuwa garin hutawa dake a jihar Ɗillo inda Dauda ke zaune da iyalansa. Ƙyawun Asabe yasa ake layin zuwa ganinta har wasu na faɗin ɗan-azumi ya auro aljana wadda zatai maganin sheɗancinsa. A zahiri ba aljanar bace, amma bakin mutane kam ya bisa dan Asabe ta zame masa *BAƘAR INUWAR..* daya gwammaci aljanar ya aura. Asabe ta take Larai rashin mutunci ta shanye. Dan ita ko kusa ko alama bata shakka ko kunyar tsige Dauda tas a bainar nasi ko gaban ƴaƴansa balle uwarsa. Inhar zai faɗa mata cuta saita mayar masa da mutuwa koda zata kaisu da dambe a tsakar anguwane. A haka ta samu ciki, inda ALLAH ya azurtata da haihuwar ƴaƴanta mata ƴan biyu masu tsananin kamanni da DAUDA. dan ko kaɗan basu biyo Asabe ba sai dai ace ko na jini dole ka gani a fisge. Ko kaɗan bata damuba, dan kuwa ƴaƴan soyayya ma take kiran ƴan biyun nata mata da sukaci sunan Faɗima da Fatisa. Bayan haihuwar su Fatisa ko wata uku bataiba ALLAH ya sake bata wani cikin, wanda shima ta sulluɓo ƴarta mace mai tsananin kamanni da ita a wannan karon. Dan kuwa ƴar nan duk da jinjirace duk wanda ya kalleta sai ya sake duba. Dan ta wani fannin za'ace ta hado ƙyawune na uwa da uba. Saboda ta ɗakko ɗan duhun fatar Dauda da hasken mahaifiyarta. Idan ka kalleta kai tsaye zaka kirata half cast kawai. Itako taci suna *Aminatu* asalin sunan inna kenan mahaifiyar dan-azumi. Sai dai kuma Asabe tace ana ce mata *Raudah* dan duk kishiyar data faɗar mata sunan uwar miji a gidan ranar za'aga ƙarshen bala'i da jidali. Bayan haihuwar Rauda Asabe ta sake haihuwar mace itama mai suna Yasmin. Itama dai kamanni biyu ta ɗakko na Asabe da Dauda. Sai dai itama baƙace sosai ba kamar Rauda ba.
Basai an faɗa makaba, dan kuwa batun tarbiyyar babu ita ga ƴaƴan Asabe a gidan, tasu ta fita daban data saura. (Ƴaƴanmu kan fara koyon ilimine daga ɗabi'unmu iyaye, dan haka sai mu kula dan ALLAH kodan gaba da zasu kai girma su gallabemu). Sam ƴaƴan Asabe ƴaƴane na rashin ƙwaɓo a gidan, duk taɓararsu babu ubanda ya isa nuna musu yatsa har a wajen Dauda. Dan har gori yakema sauran matansa akan basu taɓa haifa masa ƙyawawan yara ba balle mai kama da shi, dan su kam ƴaƴansu tamkar haɗin baki duk kamanninsu suka kwaso. Ko aike babu wanda ya isa aiken ƴaƴan Asabe sai ita, ita ɗin ma sai sun gadama suke zuwa. Hakan kuma bazaisa ta nuna ta damu ba. Hatta da Raudha ma haka ta taso a cikin nasu sai a hankali, dan itamadai halin ƴan uwan natane tsaf sai dai ma ace ta ɗarasu da shegen miskilanci da baƙar zuciyar tsiya da jan magana, dan kullum cikin faɗa take da yara harma da manyan. Sai dai kuma tanada ɗan sauƙin kai ta wani fannin kaɗan idan taso, ba komai ya jawo rashin jin Raudha fin na sauran ƴaƴan Asabe ba sai gatan da Mal ɗan-azumi ke mata a gidan fiye da kowa dan tana da sunan mahaifiyarsa.........✍️
Leave a Comment