Bakar Inuwa 23
*_Episode 23_*
............A ɓangaren Ramadhan kam yama manta da wani batun aurensa balle Raudha. Harkokin gabansa kawai yakeyi na shirye-shiryen rantsarwa da zaman meeting-meeting da suke yawanyi da ƴan jam'iyya a gidan gwamnati. Shi kansa ma haushi meeting ɗin ke basa a mafi yawan lokaci, dan wasu yakan rasa gane kansu balle inda suka dosa. Sai dai yana nutsuwa dai wajen maida kansa yaron da suke kallonsa yana karantar komai da nanufofinsu.
Sai dai abinda Ramadhan bai sani ba a garesa ne kawai ya manta da abatun aure, ga jama'ar gidansu da masu so da masu ƙi duk abin na ransu. Domin shiri su Anne keyi na musamman akan auren, lefe ya kammala haɗuwa tsaf, hakama abubuwan da duk za'a buƙata ga taron biki.
A ɓangaren su gimbiya Su'adah ma dai suna nan akan bakansu na hana tabbatar wannan aure, sai dai kuma tun randa Pa ya ritsata tana waya da Asma yaji kuma mi suke faɗa yaja mata dogon gargaɗi, tare da alwashin inhar wata matsala ta shigo a auren nan ta shirya amsar matsala a nata auren itama. Wannan ne ya tada mata hankali ya kuma ja mata birki, sai ta koma zungurin Ramadhan akan auren. Sai dai kuma rashin zamansa a gidan ya taimakesa da masifarta.
A yanzun kullum cikin ƙulla yanda zasuci uban Raudha suke inhar ya tabbata sai anyi auren. Tare da ɗaukar alwashin aurama Ramadhan Aina'u koda daga baya ne.
A hutawa ma dai Mal. Dauda ya shirya tsaf, dan gyara na haƙiƙa yayma gidansa tamkar bashi ba. Ya baza ɗinkuna yayma kuma kowa na gidan. A yanzu haka Innarsa da ƙaninsa da iyalinsa suma sun dawo nan gidan da zama. Hakan yasa Larai ta rasa kataɓus dan Inna cin uban surukai take babu ɗaga ƙafa. Balle ma yanzun da take ganin ɗanta yay arziƙi, ai koda wasa babu wanda ya isa zagin Asabe a gabanta duk da bata nan. Takance Asabe ai farar uwa ce tunda gashi sanadin ta haifi Raudha suna hutawa. Takanji takaicin saki ukun da ta saka Mal. Dauda yay ma Asabe a yanzun. Inama ɗaya ne ko biyu da yanzu sai ta dawo abinta.
To anan ma dai shirinsu suke tsaf duk da babu amarya har anko an fitar ma.
*_SATIN BIKI_*
Shiga satin biki ya saka ango da amarya dawowa cikin hankalinsu. Dan kuwa sun tabbatar yanzu kam da gaske ake ƙwarai. Ta ko ina sanar da wannan ɗaurin aure ake a kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo, yayinda wasu baƙi dake ƙasashen ƙetare suka fara sauka ciki harda su Sultana daba taron bikinne ya kawotaba kai tsaye. Dan tunda akace Ramadhan ya fito takarar shugabancin ƙasar NAYA take son zuwa, sai kuma ga batun aurensa da yay matuƙar tada hankalinta har takaita da kwanciya asibiti. Halin data shiga yasa Babanta yarda su Mufeed suzo da ita taga Ramadhan ɗin.
Sai dai kuma tun jiya suka iso amma ganin Ramadhan yay musu wahala
saboda yana can suna shirye-shiryen zancen rantsarwa. Za'a ɗaura auren ne juma'a, asabar ayi rantsuwa, lahadi su tare gidan gwamnati tilitin shugaban ƙasa ya fara shiga office.
______
Ga amarya kam itama ta yarda dai auren nan babu fashi, tunda aka shiga satin bikin aka sake ninka yanayin gyaran jikinta da akeyi, tayi ƙoƙarin toshe duk wata hanya bata sake haɗuwa da Alhaji yaro glass ba duk da yana yawan zuwa gidan yanzun. Ana saura kwanaki biyu ɗaurin aure daren da washe gari za'a maidata Hutawa kusan sha biyu yunwa ta addabeta, dan duk yinin yau bataci wani abincin kirki ba saboda damuwa. Bata son auren nan ko ɗigo a ranta, gefe ga tsoro da fargabar tsantsar ƙiyayyarta data hanga a cikin idon Gimbiya Su'adah da wasu a ƙannen mijin nata. Jin har kamar zuciyarta na tashi dan yunwa ya sata fito da nufin zuwa kitchen ko tea ta haɗa.
Da sauri taja birki jin kamar ana magana ƙasa-ƙasa dai-dai tana ƙoƙarin sanyo ƙafarta a falon, ta ɗan laɓe tana leƙe daga corridor ɗin ɗakunan barcinsu ita da su Yasmin. Aunty Hannah ta hango da wasu mutane uku, babu wanda ta gane a cikinau sai Alhaji Yaro glass kawai. shima dan rabin jikin aunty Hannah nakan nasane. Dan tana zaune kusan a jikinsa ne ko kunyar sauran mutanen bataji. amma sauran ukun babu wanda ta sani.
Jin an ambaci sunanta yasa gabanta faɗuwa. taɗan sake matsowa daf da hanyar fita corridor ɗin ta kasa kunne taji da ƙyau.
Wanda yake a kujerar ƙarshe mai sanye da jallabiya baƙa ya ƙara fuskantar aunty Hannah yana faɗin, “Hannah kinga dai mun matuƙar yarda da ke, dukkan wani shirinmu a yanzu tamkar ya rataya a wuyanki ne. Bama son kuskure ga yarinyar nan, dan idan aka samu kai tsaye ke zamu ɗaurama alhakin hakan”.
Kanta ta jinjina masa tana tashi zaune sosai. “Alhaji Wada karkaji komai, na riga na ɗaura Raudha bisa kowacce irin hanya da bazata iya bijire mana ba. Ku ɗauka tamkar yaron nan ya mutu ya gama a shekara biyun da kuka ɗeba masa. Adai ɗaura auren jibi, da zarar sun tare za'a fara bata maganin tana saka masa a abinci, ko abin sha kamar yanda first lady ta sanar min..”
“Hakan shine dai-dai, dan munaso ya fara masa aiki a hankali yanda ko bayan mutuwarsa za'a ɗauka diabetis ɗinsa ce ba wani ba, tunda dama maganin zai ƙara ƙarfin diabetis ɗinne ya kuma haifar da hawan jini mai ƙarfi. Sannan a yau da safe duk wani poison an sakashi a cikin ac ɗin falonsa da bedroom dan a hankali mukeso ya fara ratsa jininsa shima ta yanda zai zama bashi da wani kuzarin nutsuwa yay aikin ma, dan cikin idon yaron nan ka kalla kasan bazaiyi mutunci ba. Yana gama gane kan mulkin nan mukanmu ba ɗaga mana ƙafa zaiyiba wlhy.”
Alhaji Yaro glass ya karɓe da faɗin, “Ai dama shegene yaron nan, yanda kaga kakansa da taurin kai haka shima yake. Ni gani nakema mizai hana ita Raudha mu fito mata ƙuru-ƙuru akan aikin da muke son tai mana kawai dan yarinyace sai yanda mukai da ita.”
“A'a wannan ganganci ne, idan kuma aka samu akasi ya faɗa sonta fa? Ko kuma itama tana sonsa yanzu haka? Dan yaron nada qualitys ɗin da mata zasu so sa a ƙanƙanin lokaci. Giyar soyayya kuwa zata iya janta ta sanar masa. Kawai muyi yanda muka tsara ayi amfani da ita”.
Cikin zafin rai Mr MM yace, “Idan ma mun sanar matan tace zata tona mana asiri halakata zamuyi itama a banza....”
“Ai ko yanzu ɗin ba tsira zatai ba. Kana tunanin zata dinga shaƙar gubar nan ta cikin ac ta tsallake itama. Yanda zata dinga masa illa a hankali itama hakanne zata kasance. Sai dai akwai wata allura da za'ai mata wadda gubar bazata yi tasiri a jikinta da wuri ba kamar shi”.
A tare duk suka kalli Aunty Hannah bayan sun ɗauke idonsu ga Dr Bonba daya gama bayanin.
Kanta ta kaɗa musu tana watsa hannaye baya. “Miye na kallon nawa?, kun san dai Raudha ɗiyar ƙanwata ce. Duk da kuwa ina son zama first lady bashike nuna bana son abata ba. Nasan bai wuce kuce ya shawarar ta canja ba game da allurar riga kafin guba. Ku zauna kuyi tunani da hankalinku, babu ta yadda za'ai mu bari gubar tai tasiri a jikinsu lokaci guda, dan komai zai fito ne. Amma idan bayan ya shi ya mutu ne itama ta mutu za'a iya cewa zuciyartace ta buga saboda rashinsa itama tabisa”.
“Woow!”.
Suka faɗa a tare suna tafawa. Shugaban ƙasa mai sauka yace, “Hannah kinada basira, anya kuwa idan mutumina ya zama shugaban ƙasa bake bazaki koma juya ƙasar ba kuwa?”.
Wata shegiyar dariya tayi tana juya idanu, Alhaji Yaro glass ya sake rungumota jikinsa da manna mata kiss a kumatu. “Inaga shugaban ƙasa biyu kam zakuyi”. Ya faɗa cikin raha. A can ƙasan ransa kuwa yana ayyana ashe kuwa itama zata mutu nan kusa, dan Hannah bata isa shiga masa hanci bai fyatota ba duk da take matarsa.........
Zuwa yanzu sosai hajijiya ke neman yadda Raudha a ƙasa. Tai azamar dafe bango jin zata zube a ƙasa. Laɓɓanta sai faman rawa sukeyi amma sun gagara furta komai, dan ko tace zata furta ɗin batasan mi zata furta ba. Da ƙyar ta cigaba da laluben bango ta koma ɗakinta, batasan a yaya ta zube saman gadon ba harda jan bargo ta lulluɓe, jikinta ya shiga wani irin karkarwa na rawar sanyi
Yanzu ta fahimci ba ahalin Ramadhan bane zasu zama BAƘAR INUWAR ta ba, ba Ramadhan bane BAƘAR INUWAR ta ba, aunty Hannah itace BAƘAR INUWAR ta. Shi kansa Ramadhan sun tittiɗashi ya hau kujerar mulki ne badan ya ni'imtu ba, badan ta zame masa INUWA da irinsu talakawa suke hangen masu mulki na ciki ba. bai san sun kaisa BAƘAR INUWA bane, gara ace a rana yake da shiga cikinta. ta sake fashewa da kuka.
ALLAH sarki talaka. A kullum gani yakeyi shi a RANA YAKE, mai mulki shike cikin Ni'imtacciyar inuwa, ashe baisan da wata BAƘAR INUWAR MUKIN gara ranar da shi yake a ciki ba. Yau gashi saboda mulki yayar mahaifiyarta ta ɗauketa da hannunta ta kaita BAƘAR INUWA. Shiyyasa suka dage ashe, shiyyasa suka hana mahaifiyarta nuna ƙin auren, shiyyasa suka babbake ko ina da ina. Miye mafita? Zata bijirema auren ne ta hanyar guduwa ko zata haƙura ta zauna ta ceci rayuwar wanda a yanzu take kallo da fatan ya zama adalin shugaba madubin al'umma kamar yanda talakawa suka ɗora yaƙininsu a kansa da ƙwarin gwiwarsu?.
A take kanta ya fara sarawa, dan tama rasa kalar tunanin da zatayi saboda ƙarancin shekarunta. Ga wani irin tausayin Ramadhan ɗin da ahalinsa na dirar mata a zuciyarta, dan ta taɓajin cewar kakansa Baba alhaji aka bama takarar shi kuma ya bashi saboda yace bai ra'ayin mulki a shekarunsa. Ashe baisan ya kai jikansa BAƘAR INUWA bane. Tabbas bazata iya fahimtar komaiba a yanzu dole saita san komai, sanin komai kuma bazai yuwu a gareta ba sai ta yarda da auren Ramadhan. Sai dai kuma tana buƙatar shawara wajen na sama da ita, wazata tunkara? Hajiyar birini! (Kai a'a gwaggo sai a hankali ce) Hajiya mama (kai itama a'a duk tafiyar ɗaya ce) Mommynsu! (Ina bazai yuwu ba zata sake tada mata hankali) Su Fatisa! (Ina basu da hankalin da zasu iya fahimtarta ta wani fanin ma gara ita). Take wani irin zazzaɓi mai zafi ya rufeta, sarawar da kanta keyi ya ƙara ƙarfi..
Koda suka wayi gari da safe Raudha babu lafiya aunty Hannah bata kawo komai a ranta ba sai tunanin fargabar aure da akasan kowacce amarya da shi. Tunda sassafe suka nufi can gidan dan yau zasu wuce Hutawa su duka har Hajiyar birni. Su Fatisa kam tun jiya suka wuce harda su Yasmin.
Asabe ce kawai ta damu da ganin halin da ɗiyar tata take ciki. Suko hankalinau nakan kuɗaɗen da aka aiko daga gidan su Ramadhan injisa aba amarya na hidimar biki, sai tarin kayan rabo. Ko irin ɗan faɗa da nasihar da akema amarya babu wanda yay mata a dangin mahaifiyar tata. Sai ita Asaben ce ta jata gefe taita lallashinta da mata nasiha. Tare da ƙarfafa mata gwiwar ta ɗauka Ramadhan shine zaɓin ALLAH a gareta. Maybe shine kuma mafi alkairi. Dan ita kanta tayi addu'a tayi sadaka akan rushewar wannan aure amma babu alamar zai rushe ɗin.
Raudha ta yarda da maganar Mommy takuma ɗauki aniyar haƙuri, dan ita kanta tayi addu'ar sosai akan zaɓin ALLAH game da auren komai kuma bai canja ba, tunda gashi har gobe idan ALLAH ya kaimu ɗaurin aure.
Ƙarfe kusan sha biyu suka bar Bingo zuwa jihar Dillo a ƙaramar jukumar hutawa. Kasancewar lafiyayyar motace kuma drivern yasan aikinsa zuwa huɗu na yamma sun iso. Asabe tayi mamakin yanda aka tarbesu, ga gidan nasu data sani duk ya cinye a baya ya zama wani haɗaɗɗe yanzun. Dan harda su gate aka saka.
Kowa burinsa yaga Raudha matar shugaban ƙasa. Dan haka maƙwafta da ƴan anguwa sukaita tururuwar shigowa ganin amarya. Sai dai kuma ita amarya Raudha ta ɓoyewa ganinsu saboda zazzaɓi dake damunta har yanzu. Abu biyu ke tayar mata hankali. Zancen su Aunty Hannah da tsarin auren nasu daya sha banban dana saura. Babu wani jituwa tsakaninka da ango balle wani maganar biki ma ya shiga. To gaba daya ma sau biyu ta taɓa ganinsa a zahiri, babu kuma wanda wata maganar kirki ta shiga tsakaninsu a ciki.
Duk yanda taso cigaba da zurfafa tunanin nata dole ta haƙura saboda hayaniya da gidan ya ɗauka. Kai kace yau ne ɗaurin aure. Ga dj ya warware kiɗa tun da safe dan su Fatisa suka ɗakkosa tun daga Bingo. Tun kuma a daren jiya aka fara raƙwashewa duk da amarya bata iso ba. Shiko Mal. Dauda dama babu ruwansa, dan shi kansa yana gefe da abokansa yana ɗan rausaya ƙafa saboda yanda kiɗan ke shigarsa tsumin baya na neman motsawa.
Kowa ka gani a cikin farin ciki yake a gidan, ƴan uwa da wandama kalan dangine duk bakuna a washe. Musamman Inna dake nuna cewar yanzu tafi son su Raudha fiye da kowa a duniya. Larai ce kawai take cikin tashin hankali, dan ta koma gidan malaminta yafi sau shurun masaƙi yana cemata ta dai jira ai ba'a ɗaura auren ba ko. Kowace daƙiƙa ta agogo dake matso da lokcin ɗaurin auren na bugawane da bugun zuciyar larai. Duk ta fita hayyacinta tsabar rashin nutsuwar zuciya. A daren jiya har faɗa sukai da Mal. Dauda ya shashaheƙa mata mari da tabbatar mata idan ta ɓata masa farin ciki a taron bikin nan zai yanka mata jan ticket ɗin komawa gidansu dan bazai zauna da mai masa baƙin ciki ba.
Wannan shine dalilin daya sakata kama kanta sai idan ta shiga ɗaki taita haɗiyar zuciya. Baba nafi kam babu ruwanta. ta shige cikin dangin Asabe dana mijinta anata harkokin arziƙi da ita. Hakama ƴaƴanta na ma'auri da wanda basuyi auren ba. Yanda take ɗin yasa Mal. Dauda mata ƙyautar kuɗi masu tsoka wai itama ta tarbi baƙinta.
A daren ranar duk yanda Raudha taso maƙalewa taƙi fita ƙofar gidan inda su Fatisa suka tara ƙawayensu dama wanda ba'a gayyataba hakan bai yuwu ba. Acewarsu yaune sukai taronsu na ƙawaye. Dole aunty Hannah ta matsa mata shiryawa cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar Material a cikin akwati guda da aka kawo mata na kayan fitar biki. dan ba'a kawo lefe ba Ramadhan ya hana. Yace idan an ɗaura zai bata da hanunsa. Su Bappi sun goya masa baya dan auren Amnah ma haka yayi. Shiyyasa aka kawo mata kayan fitar biki kawai da aka ɗinka akwati guda da duk abinda zata buƙata na ado.
Light makeup Feena da suka taho tare saboda kwalliyar amarya tai mata, aka gyara mata dogon gashinta data gada wajen Asabe tare da naɗa mata ɗauri mai ƙyau. Kanta ke matuƙar ciwo ga zafin zazzaɓi amma haka ta daure ta fitan. Nanfa ƙawaye suka shiga mata hotuna duk da dare ne harma da jama'ar gari. Burin kowa ace ga hoton matar shugaban ƙasa a wayarsa ya samu na fafar faɗama wasu yanada alaƙa da ita koda anan gaba idan ganinta ya musu wahala. Wasu ko a take suka shiga watsashi a media dan hannayensu na ƙaiƙayi.
Wajen ya sake ƙawatuwane lokacin da Hajiyar birni tazo ta farke ƴan ɗari biyar-biyar ta hau yima Raudha liƙi. Sai itama aunty Hannah ta farke ƴan dubu-dubu. Sai ga Mal. Dauda ma da kansa ya farke nasa dubu-dubun. Nanfa yaran dj da mutane suka shiga wawaso. Abu kamar wasa sai ya zama gasa akaita shigowa anama Raudha liƙi. Wasu ma ƴar dubu ɗaya ce suke canzowa goma-goma ko biyar-biyar suyi dan dai ace suma sunyi.
Alhmdllhi dai sai ga taron ya zama wani ƴar ƙwarya-ƙwaryar wasa. Amarya ce kawai zuciyarta ke a ƙuntace da damuwar data dameta. Suna mata kallon wadda zata shiga Ni'imtacciyar INUWA basu san BAƘAR INUWA bace, gara ranar da suke ciki ta fita kwanciyar hankali.
Jirin da tace tanaji yasa Hajiya mama maidata cikin gida, aka bata tea da magani tasha ta kwanta. Kasancewar maganin naɗan saka barci aka dace barcin yay awon gaba da ita dan dama akwai bashinsa a kanta.
*_WASHE GARI_*
Tunda farar safiya motocin jami'an tsaro kala-kala suka fara shigowa garin Hutawa suna masa zobe. Al'amarin tuni ya fara tsorata masu tsoro suka nutsu a gidajensu. Zuwa ƙarfe sha biyu garin ya fara ɗaukar haramar baƙi. Babu abinda ke danno kai cikin garin sai jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi. Kai harda su helicopters. Tuni gidan hakimi daya amshi ɗaurin auren ya cika ya tun batsa da manyan ƙasa dana baƙin ƙetare. Dan babu kalar fatar da bazaka samu ba. Tunkan shugabanci gidansu Ramadhan babban gidane sannne, sai ya zam samun mulkin ya sake haskesu.
Ƙarfe sha biyu da rabi dai-dai tawagar shugabn ƙasa kuma ango *_Ramadhan B. Hameed Taura_* ta dira cikin garin hutawa. Dan tun a daren jiya nasa baƙin ta kowanne ɓangare ke danna kai birnin Bingo, yau kuma suka ɗungumo a motoci zuwa Hutawa, duk da kuwa su Alhaji yaro glass sun so hanashi ya tabbatar musu bazaibi jirgi ba zaizo a mota saboda wani dalilinsa.
Ta ko'ina garin ya sake harmutsewa. yayinda wasu a abokan nasa ke matuƙar mamakin inda Ramadhan ɗin ya ƙwaƙulo matar aure a wannan garin da idan ka ɗauke ɗai-ɗaikun manyan gidaje da lafiyayyen titi babu komai a cikinsa sai hayaniya da tarkacen talakawa (🙄🤗ALLAH mun gode maka daka yimu a talakawa).........✍
*_Sai ku shirya. Dan bai kamata ayi bikin nan babu mu a wajen ba gskiya. Zafafa biyarma duk zasuje. Dan suna nan suna sallar dare shugaban ƙasa Ramadhan ya haɗasu da muƙaman ministoci😹😹👩🏼🦯_*
Leave a Comment