Bakar Inuwa 27


..........*_GOVERNMENT HOUSE_*


      Barci sosai tayi har taji babu daɗi. A kowanne motainta Tambaya kan leƙa ta tabbatar tana lafiya. Bata farkaba sai bayan la'asar. Taji daɗin jikinta sosai dan magunguna masu kyau Dr Farhat ta bata. Wanka ta farayi mama tambaya ta gyara mata ɗakin tunda dama aikinta ne. Bata

tambayeta wacece ita ba tunda tasan a irin wannan gidan dama dole a samu ma'aikata. Bayan ta gasa jikinta da ƙyau ya sake warwarewa tayo alwala ta fito. Ɗakin ya sake komawa tsaf sai ƙamshi yake. Batabi takan komai ba ta gabatar da sallolin dake a kanta sannan ta miƙe ta buɗe akwatinan da aka zube matan. Cikin sa'a ta samu ɗinkakkun kaya kala kusan biyar da sai daga baya aka amso a wajen tela dan bai kammala mata na fitar biki ba da a aka kai wancan ranar. Riga ne da skirt na atanfa less Onion color. Sai ratsin milk kaɗan a jiki da stones da aka kawata ɗinkin da shi. Kayan sun mata ƙyau da fiddo kalar fatarta musamman data ɗan rame kwana biyun nan.

       Duk wanda ya ganta yaga amarya kodan gyaran jikin da tasha na nagartattun kayan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* da duk amaryar da akaima gyara da su dole tazama abar kallo. (Amare dama mata ƴan ƙwalisa dake buƙatar kayan gyaran jiki na musamman, tun daga kan ƙamshi na turarurrukan gida dana jiki, har zuwa gyaran fata da kayan mata ingantattu ku garzayo ga *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* domin samun naku kuma. Masu iya magana kance siyen nagari maida kuɗi gida😘😋🤗), ga lallin ƙafarta da hanunta raɗam tamkar bazai fita ba. Mama tambaya ce tazo ta sanar mata an shirya mata sabon abinci tunda breakfast ya huce, anma fiddashi tuni. Ta amsa cikin mutuntawa ga mama Tambaya dan koba komai zata iyama jika da ita.

     Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma tanajin yunwa. Dan haka tai dauriyar fitowa falon saman inda mama tambaya ta saka kuku ya shirya abincin. Sosai mamaki ya cikata ganin table ɗin a cike, dan babu wani zancen ƙauyencin gidan ko tsarin abubuwansu tattare da ita kasancewar an mata lectures na koma kafin ta shigo. hasalima ta shigo ɗin tun kafin a kawota matsayin matar gidan. “Mama wannan abinci duk suwaye zasu cisa haka?”.

      Kan mama Tambaya dake tsaye a ƙasa tai murmushi. “Ranki ya daɗe ke da shugaban ƙasa ne kawai, duk da bamu da tabbacin shigiwarsa gida a yanzun”. 

     Mamaki da takaici ya kume Raudha a rai. dan kai tsaye ta danganta hakan da almazarancine kawai. Talakawa nawane suke wahala babu ko ruwan kunu da zasu sha a yau, amma an shirya abinci fin kala huɗu a dining ɗin gidan shugaban ƙasa wai dan shi kawai da matarsa. Tabbas ta sake yarda mulki BAƘAR INUWA ne kawai. Dan hakkin mutane kawai aka barka da shi ka shiga uku. Ta rumtse idanu da haɗiye ɓacin ranta, cikin saisaita murya tace, “Mama yayi yawa ai, ya kamata a dinga dafa iya wanda za'a iya ci kawai ya wadatar. Dan ALLAH daga yanzu a dingayin dai-dai misali. Idan kuma ansan ma shugaban ƙasa bazai dawo yaci ba adaina girkawa da shi har sai idan shine ya bukaci hakan”.

       “Amma ranki ya daɗe haka tsarin yake tun a wancan shugaban kasar mai sauka dana sani nidai.”

       “To mama inaso a canja yanzu danni dai bana buƙata sam”.

      “Insha ALLAHU za'a gyara ranki ya daɗe, dan dama dai tun ɗazun duk ma'aikatan gidan nan suka gama taruwa domin gabatar da kansu gareki”.

      Duk da gaban Raudha sai da ya tsinke ya faɗi dan fargaba tausayin kanta sai ta dake tace, “Ba damuwa sai a sanar musu na tashi to”.

     “An gama ranki ya daɗe. A fito lafiya”.

            Kai kawai Raudha ta iya ɗaga mata, dan babu abinda ƙirjinta keyi sai luguden daka. Ita Raudha, ɗiyar Mal. Ɗan-azumi da Asabe na Hutawa ce a wannan ajin na ƙaddara. Itace akema wannan girmamawar duk da ƙarancin shekarunta. Itace matar shugaban ƙasa wadda kowa zai iya kira da first lady a ƙasar NAYA da ƙetare a yanzun. Itace matar shugaban ƙasa *_Ramadhan B. Hameed Taura_*. Ɗan ƙwalisar gayen nan maiji da giyar kuɗi da lokaci, ƙyaƙyƙyawa mai girman kai da jan aji wa manyan mata. Wannan wace irin ƙaddara ce haka mai kama da almara ko hikayoyin marubuta. Badan tayi imani babu mai iya ja da ikon ALLAH ba da tace kodai ta mutune ko barci take har yanzu komai nazo mata a mafarkine ba gaske ba. Wannan ƙaddara ta mata nauyi da yawa a zahirin rayuwa da baɗini. Gaskiya mahaifiyar Ramadhan ɗin ta faɗa ita ba kowan kowa bace, sannan Ramadhan yafi ƙarfin yafi ƙarfin kowa nata. Sayyadi Abubakar ma da bai kama ko ƙafarsa ba iyayensa suka tabbatar da ya fita balle shugaban ƙasa.

     Waɗan nan tunane-tunanen suka hanata sakin jiki taci abincin kirki har mama Tambaya ta sake dawowa ta isar mata da saƙon taruwar kowa. Tambayar mizai hana su shigo nan tayi. Cikin girmamawa mama Tambaya tace, “Ranki ya daɗe basu da wannan hurumin sai mu huɗu kawai. Ni da Chief kuku da mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa sai mai gyaran falon nan kuma.”

      Ɗan jimm Raudha tayi tana dubanta, sai dai komai bataceba ta miƙe da ɗaukar milk gyalenta data fito dashi ta yafa har saman kanta sannan suka fito. Tana gaba mama Tambaya na take mata baya


       ★Falo ne babba da za'a iya kiransa mafi girma a duk falukan gidan. Komai na cikinsa kalar tutar ƙasar NAYA ne. Ya ƙawatu matuƙa da kayan more rayuwa. Ma'aikatan da adadinsu zai kai kusan hamsin suka rissinar da kai domin girmamawa. Gareta suna miƙa gaisuwa. Duk da ba kabilarta bane su duka haka ta amsa musu cikin mituntawa dan babu wanda bai kere shekarunta ba a cikinsu.

     Shugaban ma'aikata na sashen nata ne ya fara gabatar da kansa, sai shugan kuku's da sauran kukus ɗin, sai Mama Tambaya da mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa. Kafin sauran su cigaba ɗaya bayan ɗaya. Tun ma Raudha na fahimtarsu har da daina tunaninta ya tafi wani wajen da ban. Cikin nutsuwa ta ɗaga musu kai da fara faɗin,

       “Masha ALLAH naji daɗi, ina kuma fatan zaku riƙe amana dan nasan babu wani addini dake goyon bayan cin amana ko zalunci. Bazance karku cutar damu ba ko a haɗa baki daku wajen cutar damu. Sai dai zance kuji tsoron ALLAH karku zaluncemu da son zukatanku ko biyewa ruɗin kuɗi. Idan kun kiyaye kuma ALLAH zai kiyayeku ya ɗaga darajarku zuwa wani matsayi da baku taɓa zato ba. A duk lokacin da bawa ke tsoron rasa wani abu wani nacan ya samu yayi shi. Idan murna da farin cikin samu kake wani nacan shi kukan rasawa yayi. Sai musa a ranmu duk zamu iya zama ɗaya daga cikin wannan matsayin. Dan a duniya babu mai wahala sama da _mai buƙatar abu a lokacin da abun baizo ba. Da kuma mai ƙin abu bayan ana tsaka da samuwar abun_. ALLAH yasa mu dace, ya bamu ikon sauke nuyin juna bisa bigiren tsoron ALLAH da cire son zukatanmu ko yanke hukunci akan umarnin zuciya”.

      Sosai sunji daɗin kalamnta, wasunsu da zamansu nada alaƙa da kalamnta na son cutar dasu sai jikinsu ya fara sanyi. Gata dai ƙaramar yarinya amma tanada cikar kamala da kwarjinin manya. Uwa uba iya sarrafa harshe cikin taka tsantsan da mutunta kowa. Wasu kuwa da yake zuciyar ta bushe ko'a jikinsu, a ganinsu ma ta cika iyayine da son nuna ita mai addini ce.

     Sun shiga mata godiya bayan ta sallamesu. Daga haka ta koma ciki abinta. Zaman ɗaki ta cigaba dayi har ƙarashen wannan yini babu shugaban ƙasa babu alamarsa. Maganinta da tasha ya sata barci da wuri ma batare da ta damu da yanda wanda ya aurota ya banzatar da ita ba. 


*_BAYAN KWANKI BIYU_*


         Yau kwankin shugaban ƙasa da amaryarsa biyu kenan a gidan gwamnati, sai dai tunda suka shigo gidan babu wanda yaga ɗan uwansa. Dama Raudha bata saka a ka ba, sai dai duk sanda za'a nunasa a television takanji wani iri a ranta tamkar mai ganin laifinsa. A gefe kuma tana yaba iya tsara adonsa da kyawun haiba da ALLAH ya bashi. Shi mutum ne da ko yaya yasa sutura ko badan kwalliya ba saita nuna kanta a jikinsa, koda bamai muhimmanci bace da rashin tsada. Abu mafi ɗaukar hankalinta shine ƴar tsagar kan girarsa dake nuna tamkar irin ta gayun zamani, tunaninta ya tsayane kawai akan ya bada wanzami yay masa hakane saboda gayu. Bama ita ba, mafi yawan mutane haka suke fassara tsagar dake kwance da wani salon style tamkar an tsara bisa girarsa ta dama. Da ace tanada dama da saita masa tambaya akan tsagar.

     Ba komai yake mata daɗi ba a gidan, musamman abinci da kaɗaici suna sukar ranta. Sam girkin su kuku baya mata ɗan ɗanɗano a baki, ga kewar momynsu da ƴan uwanta musamman Yasmin da suka shaƙu matuƙa. Kai har ƴan hutawa kewarsu takeyi sosai. Sai kwaɗayin karatunta na islamiyya.

      A tarewar tasu sau uku tai baƙi manyan mata masu ji da kansu da zasu iya haifarta har jika da ita ma, wai matan gwamnoni ne sunzo gaisheta. Sai wasu kuma matan manyan ƙasar ne ƴan siyasa. Ita dai nata gaisuwane a garesu da godiya. Dan duk da ƙarancin shekarun Raudha nasihar sayyadi Abubakar ta jima da maidata mai halin manya. Tanada nutsuwa da zuciya, ga miskilancin tsiya. shiyyasa takeda takatsantsan akan abubuwa masu muhimmanci. Ba komai takema garaje da rawar kai ba har saita nutsu ta fahimcesa. Hirarsu Aunty Hannah na taka rawar gani wajen bude mata ido da sanya ido ga duk wanda zai raɓeta a yanzun. Dan zuciyarta ta kasa yarda da kowa da komai na gidan. Kullum kuma cikin yin nazarin ta yaya zata kuɓutar da shugaban ƙasa take.


     A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yayi matukar zama busy ne. Sam baya samun kansa yanda ya kamata a kwana biyun nan da fara shigarsa office. Wani abu daya faru randa ya fara zuwa office ya sakashi fara binciken wani abu akan jerin sunayen cabinet ɗinsa da suka tattauna akan zai naɗa. Sai dai kuma yana gabatar da su ga mashawartan nasa  wasu a cikin manyan jam'iyyasa sukayo masa ca akan akwai tsarin da sukebi wajen naɗa cabinet na shugaban ƙasa. Shi kuma a take zuciyar maza ta motsa yace bai yarda ya hau kujerar dan ya zama a ƙarƙashin mulkin mallakar wasu ba, dolene a barsa da zaɓinsa ya samu abokan aikin da zai sauke nauyin talakawan ƙasa. Ja'inja ta ɓarke sosai a tsakaninsa da su wannan shine ya ƙara ɗauke hankalinsa ga Raudha har ma da su Gimbiya Su'adah data cika tai fam da tunanin ɗan nata na can na rugurguzar amarci da holewa a gidan gwamnti ya manta da su.

     Tayi kiransa har sau uku amma bai daga ba. Daga karshe kuma tama bar samunsa kuma bai biyota ba. Abun nan ya sake harzuƙa mata zuciya dajin tsanar Raudha. Sai dai UBANGIJI shine kawai masanin gaibu akan abinda zuciya ke hasashe babu tabbaci. Abinda gimbiya Su'adah bata sani ba shine shugaban ƙasa baima da lokacin kansa. Dan cikin kwana biyu kawai su Alhaji Yaro glass sun gama hargitsa shi, harya fara hange da saka inuwar mulki a jerin BAƘAR INUWA ce kawai ga wanda ya tsinci kansa a cikinta. Wayar da duk family contacts nasa ke ciki a gida yake barinta, hakan yasa taketa kira ba'a ɗaga ba bakuma a bita ba. Daga karshe ta mutu saboda karancin caji. Shugaban ƙasa bai luraba kuma sai yau da kewar su Anne ta ishesa yaga ya dace ya kira. A gefe kuma yana buƙatar yin magana da kakansa akan wannan rikicin nasu na fidda sunayen cabinet ɗin dake faruwa tsakaninsa da ƴan jam'iyya. Dan bai tunkaresa da zancen bane a tunanin zai iya shi kaɗai, yanzu ko yana buƙatar shawarar sa.

       Sai da yay ma wayar caji kafin ya kunnata, da saƙon gimbiya Su'adah ya fara cin karo. Yay ɗan tsamm kafin ya buɗe ya duba. Tun a layuka ukun farko na saƙon zuciyarsa ta tsarga da abinda ya ta rubuto, ya ɗan dafe kai yana rumtse idanunsa da cije baki, sai kuma ya buɗe idanun ya ƙarasa karantawa. Missed calls ɗin nata ya duba, kafin ya ajiye wayar yana jan numfashi da ƙyar. Yasan Maihaifiyarsu mutum ce mai saurin fushi, sannan tanada yanke hukunci akan abu batare data bincika ba. To amma a wannan gaɓar maganarta ta tabbatar masa da cewar tana da hujja, dan kuwa ko Anne idan bai manta ba a ranar ta turo masa wani guntun saƙo itama mai nuni da faɗa akan abinda yay ma yarinyar da shi tunma da aka kawota gidan bai ko ganta ba. Leɓensa na ƙasa ya tura cikin baki yana ɗan taunarsa kaɗan-kaɗan. Tuni idanunsa da gaba ɗaya sun koɗe saboda rashin isashen barci da samun hutu suka sake rinewa da takaici. Mi yarinyarnan ke nufi da abinda tayi? Itace ta faɗa musu ya aikata wani abu da ita kenan? Maganar mahaifiyarsa ta wancan daren ta shiga dawo masa a cikin kai, sai dai kafin tunanin nasa yakai ko ina kira ya shigo a wayar. Tun kan ya ɗaga yasan Anne ce, dan ita da Pa da Bappi da Maa duk ya banbanta musu ringtone. Cikin furzar da fushinsa ya ɗaga yana kaiwa kunne.

        Daga can Anne ta ɗan sauke ajiyar zuciya, cikin damuwa tace, “A tunaninmu dawowa ka mulki ƙasar NAYA zai kusantamu da kai ne? Sai gashi yana sake nisantamu Ramadhan ”.

     Murmushi ya ɗanyi mai sauti, cikin tsokana yace, “Ba kune kuka jawo hakan ba Anne.”

      “Uhm hakama zakace dan gidanku”.

Murmushi ya sakeyi mai faɗi, ransa fal ƙaunar tsohuwar. “Am so sorry sweet Anne na, wasa nake miki”.

         Itama murmushin tayi da ga can, har yana iya jiyo sautinsa. Ta cigaba da faɗin, “Shike nan ko waya ma ta gagara muyi da shugaban ƙasar NAYA, sai dai mu gansa a television”.

     “Kuyi haƙuri Anne, ni kaina tausayin kaina nakeyi, babu komai a mulkin nan sai baƙar izaya. Wanda ke nesa damu ne suke hangenmu cikin wata ni'imtacciyar inuwa, amma wlhy Anne mulki BAƘAR INUWA ce kawai...”

      “Asha Ramadhan! Asha. Karna sakejin hakan kaji, komai na rayuwa jarabawace kawai da rubutacciyar ƙaddara. Ka zama jarumi mai magana ɗaya kawai, sannan jajirtacce wajen tunawa da ɗunbin talakawan da suka dage rana da dare wajen ganin ka zama shugabansu. Ka kuma zama mai haƙuri da juriya kamar yanda na sanka kaji”.

     Numfashi ya sauke mai nauyi, cikin ƴar nutsuwar da kalamanta suka bashi yace, “Inaha ALLAHU Anne nagode sosai ”.

       “Babu damuwa. Ina Aminatu? Yanda kai wahalar ji itama tayi, har yanzu ban samu damar jin yaya jikinta ba haɗani da ita”.

     Ɗan jimm yayi na alamar ɗaukewar numfashi, sai kuma ya shiga lalubo abinda zaice domin kare kansa. Sai dai ƙarya ba halinsa bace, dan haka harshemsa ya suɓuce wajen faɗin, “Tana ɗakinta”.

       Kamar Anne zatace wani abu sai kuma ta share, sai kawai tace, “Daure ka haɗani da ita naji yaya take?”.

     Baida wani zaɓin daya wuce bin umarninta. Dan haka ya amsa mata da cewar, “To Anne zan kira”.

      Komai bata sake cewa ba ta katse kiran. Miƙewa yay cike da nutsuwarsa, ya ɗauka t-shirt mara nauyi baƙa ya sanya, tare da baƙin 3quarter na wando. Ya shigo gidane da wuri saboda burin yin barci, dan ko sallar magrib da isha'i ma a massalacin gidan yayi su. Slippers masu taushi baƙaƙe ya saka a ƙafarsa ya nufi ƙofa, sai kuma ya tsaya cak riƙe da handle ɗin ƙofar, dan haka kawai ya samu kansa da buƙatar sanya turaren da bai sakama jikin nasa ba, sai dai duk da haka yana ƙamshin sabulan wankansa, suma kayan suna nasu ƙamshin na kaya da yakan ajiye a Wadrobe, tun yana ƙaraminsa Anne ke masa haka, koda ya girma abin ya zame masa jiki koda yaushe zaka samu turaren kaya a Wadrobe ɗinsa.

     Komawa yay da baya-baya yana ɓata fuska tamkar wanda akaima dole, ya sako turare kala biyu masu sanyin ƙamshi sannan ya fice. Duk wanda ya kallesa ya kalli yanayinsa dolene ya dangantashi da mutum mai girman kai, dan ko a tafiya abinda ke gabansa kawai yake kallo, sannan ba kowa bane yake ganin ya isa ya saka a sabgar rayuwarsa koda ta magana ce. Ko abokai sai ya gadama yake kula wasu. Ba kuma wai dan baya magana bane ko dariya, dan ko kusa baya kama da miskili. Mutum ne shi mai surutu a inda yaso ga kuma wanda yaso..........✍


No comments

Powered by Blogger.