Bakar Inuwa 3

 


*_Episode 3_*



..........Shigarsu secondary school ya ɗan fara canja wasu da ga halayen Raudha, taɗan fara rage kwaikwayon halaye irin na mahaifiyarsu. Bata da yawan magana, bakuma tason taga iyayen nata na faɗa tamkar karnuka a tsakar anguwa kowa na kallonsu yana ALLAH wadai. Hakan kuma ya farune sakamakon ƙulluwar soyayya

tsakaninta da malamin islamiyyarsu sayyadi Abubakar.  Tun tana zama taita kuka idan suna raba hali harta koma tana nuna musu fushinta. A lokacin da suke ss1 farkon shigarsu wani faɗa da iyayen nata suka tafka har takaisu ga police station sakamakon yanzu Abbansu talauci ya masa katutu, takai ma nauyin gidan iyayen nasu mata ne ke ɗauka. Dan tunda kamfani ya kamashi akan satar kayan da yake jigila suka kafa masa kahon zuƙa, da yaga asirinsa zai tonu asabe ta zugeshi ya kwance tayoyin motar ya saida, motar takai shekara a ajiye, sai da komai ya lafa ya saidama ƴan gwangwan ita ya kawo kuɗin gida suka hau kai shi da Asabe da ƴaƴanta suka dinga cin daɗi sai ɗan abinda ake samma su baba nafi wataran. Acan kamfani kuma akace ya mutu. Ko shekara kuɗin basu ƙullaba komai ya ƙare, dan kuwa dai a ashararancin ɗan-azumi babu abinda ya canja na neman mata da busa sigari da caca. Tunda kuɗi suka ƙare zaman lafiya tsakanin Asabe da Dauda ya ƙaura. Kullum sune faɗa kamar kaji, taje ta nafko masa bashi dolensa ya biya ko bai ƙaunar ALLAH, idan yaƙi biya su tumu sama dan bala'i su dire bisa ƙasa. Dan kullum zancenta shine ya saketa bata halaka rayuwarta da ƙuruciyarta a ƙarƙashin runfar talauci. Shiko yace bata isaba tunda ta shigo ta shigo kenan. A randa taje ta cicciɓo masa wani bahagon bashi da har akazo aka saka wani filinsa kasuwa da yake ta burin gina mata aljannar duniya ta koma tun tana amarya ALLAH baiyiba ya sakasu yin faɗa na tashin hankali harda jima juna ciwo, shine aka kwashesu zuwa ofishin ƴan sanda daya saka Raudha tsananin baƙin ciki. musamman akan habaici da zagin da akema iyayen nasu akan sunyi dai-dai da juna kowa ɗan barikine ai, tunda dama a zauren dandi suka haɗu, wama ya sani koba zaman auren suke ba.

     Wannan ƙananun magana sun matuƙar ƙona ran Raudha harta kaita da kasa kuka saboda bushewar zuciya. Kowa baije yay beilingn su ba, sai ita taje duk da ƙarancin shekarunta. Ƙyawunta da ganin ƙarancin shekarunta yasa d.p.o ɗin sonyin amfani da mutuncinta sannan ya sakar mata iyayenta. Da farko taso tai masa zagin ƙare dangi, sai kuma ta fasa saboda wani abu daya zo mata rai. A take ta amince masa akan ya sakar mata iyayen bayan kwanaki biyu zata kawo masa kanta. A tunaninsa bata da wayo, musamman da yay dubi da halin iyayenta na ƴan bariki. Kai tsaye ya sake su, tana ganin an fiddosu tai wucewarta gida ta barsu duk da magana da suka dinga mata. Ta rigasu zuwa gidan, dan haka kowa bai san itane taje ta fiddosu ba. Dama kuma tun a hanya suka taho suna hirarsu ta arziƙi tamkar basune aka amso hanun hukuma ba saboda tazubar ɗinsu.

       Koda suka dawo gidanma sun kaɗa sun raya Raudha taƙi tanka musu, taƙi cin abinci ta kuma daina shiga harkar kowa a gidan. Tun suna ɗaukar al'amarin nata wasa harya fara cin ƙarfinsu, da ga ƙarshe dai suka haɗa baki da wani malamin islamiyyar su Raudha ɗin da suke yawan jin sunansa a bakinta da ganin tana tsananin girmamashi dan yana ɗaya daga cikin wanda suka gyara tarbiyyarta dake a bauɗe tunda farko sannan Raudha ta sakko harta nema gafarar iyayen nata (Sayyadi Abubakar). Dan Ya sayyadi Abubakar ya sanar mata su iyaye ba'a fushi dasu, ko wanne irin hali garesu lallaɓasu ake da ƙyaƙyƙyawan kalami. koda anji ciwo akan kuskurensu shanyewa akeyi ayi haƙuri. Saɓawa ALLAH ne kawai ba'a yarda kamusu biyayya akansa ba wannan haramunne. 

      Raudha taji wannan nasiha hartazo ta bama iyayenta haƙuri. Daga lokacin kuma ta dinga taka tsantsan da harshenta a kansu da fushinta. Idan ma taga abu zai basu saɓani ta gwammace ta amshi laifin ita koda zasu mata hukunci ne. Idan batasan tushen rikicin nasu ba kuma zatabi duk hanyar data dace ta sasantasu cikin hikima. Sai dai kuma kuka ya zame mata tamkar abokin rayuwa, dan sam bata ƙaunar halin mahaifan nata guda biyu ko kaɗan.

       A yanzu haka Raudha da sauran ƴan uwanta na sauran ƴaƴan ɗakunan biyu sa'anninta suna akan zana jarabawar gama secondary school ne. A ƙalla shekarunsu Fatisa goma sha takwas, Raudha kuwa sha bakwai ita da Iklima da Binta. Kasancewar babu wani batun Noziri a karatun nasu yasa suka kammala da ƙarancin shekaru, musamman ma ita dasu Binta duk sun girme mata.

          Halin talauci da fataran da suke ciki ga shegen son kuɗi na Asabe ya saka ƴaƴanta su Fatisa fara kaucewa hanya wajen biyema samari. Duk da kuɗin da yaran ke shigowa dasu na ban mamaki da kayan kwalliya basu sana'ar ko asi bai taɓa saka Asabe nuna damuwa ba balle tuhumarsu. Sai dai ma ta baje suci su sha mai daɗi tana kiransu masu farin jini. Tabbas *ZINA* tamkar sharri take, dan ƴar aikece komin daren daɗewa saita dawo cikin zuri'arka. Hakanne ya faru akan su Fatisa dama wasu a ƴaƴan mal ɗan azumi na sauran ɗakunan, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rayuwarsu ta ɗakko hanyar lalacewa Dauda naji na gani babu halin magana, duk da abun na ƙona masa rai da soya zuciyarsa. Dan ko yayi magana Asabe ta taresa da masifar cewar yanama ƴaƴanta sheri saboda shima aikinsane zina. Maƙiya masu baƙin ciki da hassada wa farin jinin ƴaƴanta na ɓoyewa bayan ƙofa suna musu dariya. Sai dai abinda Asabe bata sani ba na ƴaƴan ɗakintane ya fito, amma itama Larai nada Kangararru irin su Fatisa har su uku. Wani lokacin duk da gogewar ɗan-azumi a bariki, Asabe ta fisa bala'i, shiyyasa idan taja yaja sai ya sakar mata dan zuwa yanzu girma yaɗan fara kamashi, ga ciwo dake cinsa a tsaye na hawan jini wanda ko ba'a faɗaba asabe ce silarsa, gefe ɗaya taba ta gama cinye masa naman jiki sai ƙashi da jijiya da fata.

     Halayyar su Fatisa na matuƙar ƙona ran Raudha, sai dai babu yanda zatayi dan ko tayi nasihar basaji. Ita kanta samarin na yawan kawoma rayuwarta hari, musamman daya kasance ta fisu ƙyau nesa ba kusa ba. Hankalinta yakan tashi matuƙa, shiyyasa akoda yaushe cikin suturta jikinta take da kayan mutunci harma da niƙab wani lokacin. Takan yawaita neman tsarin ALLAH daga ƙaddarar zina a gareta.

         Rashin samo kuɗi da batayi yasa Asabe tsangwamarta a ɗakin fiye da kowa. Dan hatta Yasmin ta fita daraja duk da kuwa Asaben tafi son Raudha fiye da kowa acikin ƴaƴan nata. Sai dai lallaɓa da lallashin da take mata akan ta dinga kula samarin sai tafi su Fatisa samo kuɗi, amma Raudhan na bijirewa yasa ta ɗauka karan tsana ta ɗaura mata ita da su Fatiman. Kullum cikin caccakarta suke da magana mara daɗi. Da yake miskilace kuma bauɗaɗɗiya ko kulasu batayi ma balle ta nuna ta damu, fatanta kawai tai aurenta tana gama secondary school da ya-sayyadinta Abubakar da kowa yasan suna soyayya zuwa yanzun.

         

         A ɓangaren sayyadi Abubakar shima babban burinsa mallakar Raudha matsayin mata. Dan haka suna fara exam ya sanarma iyayensa akai kuɗi. Sunyi farin ciki da farko dan basusan ƴar waye ba a Hutawa. Dan haka suka tambayesa acewar mahaifinsa sai sun fara bincike tukunna. Abubakar ya shiga fargaba, amma sanin Raudha yarinyar ƙwaraice mai kamun kai, kuma da ita zai zauna yasashi jin ƙwarin gwiwa.

       Bayan kwana biyu mahaifinsa ya kirasa shida ƙanensa sukai masa wankin babban bargo, tare da gargaɗinsa ya fita sabgar Raudha bata fito cikin gidan arziƙi da mutunci ba, su bazasu haɗa zuri'a da ɗan-azumi ba. Idan ma ƙyawun yarinyar ke ɗiɓarsa yaje akwai ƙyawawa da suka fita ya nemo. Idan kuma ya sake koda yima Raudha magana ne ALLAH ya isa basu yafe ba. Itama sunje har gida sun gargaɗi ubanta akan ta fita hanyarsa. Daga karshe suka hanashi cigaba da koyarwa a islamiyyar su Raudha ɗin baki ɗaya. Sukama maida rayuwarsa can cikin birinin Ɗillo wajen wani ƙanin baban nasa dake can da iyalansa.

     Wannan shine sanadin raba Raudha da Sayyadi Abubakar. Tayi kuka kamar yanda shima yayi nasa. Kusan dukansu sai da suka kwanta a asibiti dan ba karamar shakuwace a tsakaninsu ba. Halin data shiga yasa ɗan-azumi da Asabe zuwa har gida sukaima iyayen sayyadi Abubakar tas. Wannan ya ƙara harzukasu suka kara jin tsanar tushen Raudha da ƙyamar haɗa zuri'a da su.

     Sosai wannan lalacewar aure taima Larai daɗi, dan kuwa tana ɗaya daga mutanen da suka sake lalata zancen auren, mahaifin Sayyadi Abubakar nada ɗan hali, shiyyasa tun yana zuwa wajen Raudha takeji baƙin ciki da hassadar hakan. Sai dai tabi duk wata hanyar rabasu hakan bai samu ba, sai gashi cikin sauƙi komai ya lalace. Da wannan damar tai amfani wajen zuwa har gida ta sakema Asabe da ɗan-azumi batanci fiye da wanda iyayen Sayyadi Abubakar suka jiyo ga wasu mutanen. Sai ka rantse ɗan-azumin ba mijinta bane.

     Raudha ta ɗanɗana azabar rashin Ya sayyadi Abubakar har batasan mi take rubutawa a jarabawa ba har suka kammala. Bayan kammalawar tasu ta sake dawowa gida zaman sabuwar jiyya, a dalilin hakan ciwon Asthma ɗinta da bai cika karfi ba ya sake ƙarfi har takai yana yawaita tashi yanzu. Gefe kuma ga azababben ciwon mara idan zatai period har suma take wani lokacin. Dama dalilin ciwon marar natane sayyadi Abubakar ya yanke shawarar data kammala secondary school suyi aure kawai, sai ta cigaba da karatunta a gidansa. Sanda suna tare saboda tsabar kiyaye yanayin nata da wata ya kama zai kawo mata magunguna da allura ta ajiye, da abin ya fara mata za'a nemo wani yaron makwafcinsu dake da kyamis yay mata allurar. Ta hakane take samun sassauci sai abun yazo da sauƙi..


_Wannan kenan😚👌🏼._

No comments

Powered by Blogger.