Bakar Inuwa 30

 


*_Episode 30_*



.........Cikin sauri-sauri Raudha ta sake packaging ɗin komai yanda ya dace. Sannan ta ƙarasa shirinta tare da saka hijjab ɗinta mai hannu daya je har gwiwa, yasha karin guga sai ɗaukar ido yakeyi. Duk wanda ya kalleta yasan tayi ƙyau kodan shigar mutunci da tayi, duk da tasan da ga mota sai gida.

Ɗauke da manyan souvenirs bags guda uku ta fito a hannu, sai ƴar side bag ɗinta dake rataye a gefen kafadarta. Bata saka turare mai karfi ba, dan sai kazo gab da ita zakaji sanyin ƙamshin khumrah ɗinta da na turaren da tasa.

        Kusan a tare suka fito daga corridors ɗin bedrooms ɗin nasu, shugaban ƙasa Ramadhan dake sanye cikin shadda blue ɗinkin half jamfa yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Har cikin rai yaji daɗin ganinta da Hijjab, duk da gashinta da batasaka ɗan kwali ba ya fito ta gaba kaɗan saboda zamawa da hijjab ɗin yay baya. Baiyi magana ba, duk da yana da bukatar ta ɗaura ɗan kwalin, sai dai girman kan nasa da ganin idan yay mata magana kamar zubar da kai ne ya sashi zaɓar yin shiru, cigaba yay da takowa cikin falon cike da mazantaka da salon tafiyarsa da mutane da yawa suke fassarashi da mai girman kai. Hular kansa ya ɗan sake gyarawa dai-dai yana gittawa ta gabanta. A tare ƙamshin junansu ya dinga rige-rigen shiga hancinansu.


     Maimakon Raudha taga sun fita ta ainahin downstairs ɗin da zai kaisu ƙofa sai gani tai yabi ta hanyar da yake shigowa gidan, nanma kuma dai benan ne yay ƙasa zai kaika ƙaton faluka har biyu kafin ka fita baki ɗaya, sai dai a gefe akwai wani ƙarami na hutawa shima. Bayansa tabi, koda ta fito sai taci karo da falukan da sukafi waɗan can da take gani kullum haɗuwa. Wajen ya matuƙar kayatar da ita, hakama harabar wajen dan tana ganinsa ta windown ɗakinta. Sai dai bata taɓa gigin ko tunanin zuwa ba, tunda batasan ta ina zatabi ba. Da alama fitar tasu ta sirri ce, dan mota biyu kawai ta samu a tsaye alamar suna jiransu. Kuma driver ne kawai sai securitys biyu. Cikin matuƙar girmamawa suke gaishesu ana buɗe musu ƙofofin bayan security ɗaya ya amsa kayan hanunta ya nufi booth. Shi ya fara shiga sannan itama ta shiga cike da fargabar ganin duk a baya zasu zauna kenan. 

      Fitar ma ta karamin gate dake wajen sukabi, kanta dake ƙasa yasa batasan taya suka ɓullo kan titi ba. Tafiyar mintuna ƙalilan ta kawosu katafaran gidan na Taura house. Kai tsaye motocin a ƙofar sashen su Anne suka tsaya, kasancewar ana kiraye-kirayen sallar magrib ita kaɗai ta shiga ciki, shi kuma suka fita massallacin ƙofar gidan.


         Sosai Anne dake ƙoƙarin fita da ga kitchen zataje ɗakin don gabatar da salla tai mamakin ganin Raudha, dan yanzu babu jimawa ta gama waya da Ramadhan. Sai dai sanin halinsa na zurfin ciki ya sata ture mamakin ta maye gurbinsa da farin ciki. Dan sosai taji daɗin ganin Raudha ɗin har fuskart ta kasa ɓoyewa. 

       A tare suka gabatar da sallar magrib a bedroom ɗin Anne. Bayan sun idar suka sake gaisawa. Sosai Raudha kejin daɗin zama da tsohuwar. Mutum ce ita mai cikakkiyar kamala da dattako, ga tsafta da mutunci. Ko kaɗan rashin sakin fukar Anne bai damun Raudha, dan ta fahimci anan Ramadhan ya ɗakko rashin walwala da sake fuska, da kuma wajen mahaifiyarsa, dan itama ta lura gwanar ɗaurewace.

       Fitowarsu falo tayi dai-dai da shigowar Bappi riƙe da hanun Ramadhan. A kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin shaƙuwa da ƙaunar dake tsakanin jikan da kakan. Shima Raudha ta gaisheshi cike da girmamawa. Amsa mata yake da fara'a da ƙauna. Sai sanya musu albarka yake tare da addu'oin zama lafiya da zuri'a ɗayyiba. Daga haka suka ɗan cigaba da taɓa hira har aka kira sallar isha'i.

         Bayan sun dawo daga masallaci mai aikin Anne ta shirya musu abinci a dining. Tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya da man shanu. Sai gasashiyar hanta da taji kayan lambu. Anne dake duban Shugaban ƙasa Ramadhan daya ɓata fuska tai murmushi. Tasan hakan nada nasaba da ganin miyar ƙubewa dan bayaso.

        “Anneee!”.

  Ya faɗa a tunzure.

Sai da taɗan gintse fuska tace, “Lafiya!”.

      “Ki bani fura”.

“Saboda anyi maƙiyarka kuɓewa”.

Sake cuɗe fuskar yayi fiye da farko. Bappi ya kauda kai gefe yana murmushi.

       Kujera yaja baya zai miƙe Anne tace, “Malam koma ka zauna”.

     Yanzun kam tamkar zai fasa kuka, ba Bappi ba hatta Raudha dariya ya bata, to ashe ba ita kaɗaice ta tsani miyar kuɓewa ba tanada ɗan uwa. Sai dai ta kula nashi har yafi nata. Salamar mai aikin Anne da sauke tiren da take ɗauke da shi ya saka Ramadhan dakatawa da ga maganar da yay niyya. Tana barin gurin Anne ta tura trayn gabansa. “Kure uban ƴancin nama sai kaita kaya gashi nan”.

           Kamar bazai kula ba sai kuma yakai hannu a nutse ya buɗe kwanikan guda biyu. Ɗaya gasashen kaza ne a ciki, ɗayan kuwa farfesun naman kai. Zaman Raudha a wajen ne ya hana bakinsa buɗewa. Amma duk da haka sai da yay ɗan ƙunƙunin da Anne tasan mi zai iya faɗa. sai dai bata kulashi ba ta maida hankalinta ga Raudha.

          “Aminatu zuba abinci mana”.

   Cikin jin kunya Raudha tace, “Anne na ƙoshi ALLAH”.

      “Tab anan gidan? Aiko bazai yuwu ba. Inma tuwonne bakiso ai ga nama nan. Ko kuma ki faɗi abinda kike so a girka miki”.

       Da sauri Raudha tace, “A'a Anne wannan ma yayi”.

        “To Alhmdllhi, kinga juya kuci naman gashi nan wajen mijinki, dan nasan kema dai kwanan nan zai koya miki kurancinsa.”

        Ƴar dariya Bappi yayi yana kallon Ramadhan ɗin da tuni ya fara kai laumar naman duk da akwai zafi. Ita dai Raudha batai gigin saka hannu ba. Sai dai ta zuba tuwon leda ɗaya. Maimakon miyan ƙubewan saita ɗan saka gasashen hantan a gefe ta dingaci da shi a haka. Ko tari shugaban ƙasa Ramadhan bai sakeyi ba, sai da yaji yayi nak da naman kazar nan sannan ya turama Raudha ƙasusuwa da fiffike sai wuya. Duk yanda taso daurewa kasawa tai, ta ɗago tana masa kallon mamaki, a bazata ya wani kashe mata ido ɗaya ya ɗauke kansa. 

     Wani irin muguwar ƙwarewa Raudha tayi, dan harga ALLAH salon nasa yazo mata a bazata da sakata a wani yanayin ruɗani. Anne ce ta bata ruwa, shiko sai ya ɗauke kai ma. Ko sannu da suke jera mata shi baiyi ko guda ba. Anne na niyar masa magana Bilkisu ta shigo falon. Haka take kullum tana nane da tsoffin, shiyyasa bayan Ramadhan itace ta biyu da suke matuƙar so da ƙauna a jikokin nasu.

        Da sauri tazo ta rungume Raudha tana farin cikin ganinta. Sai kuma ta koma shagwaɓan miyasa Anne bata kirata ta sanar mata Yayan nasu yazo da Raudha ba tun ɗazun.

      Anne tai mata daƙuwa da faɗin, “Kinci gidanku, tunda nice bbc uwar magana ko? Yanzu da kikazo bagasu kin gansu ba. Kimaje da ita ta shishshiga ta gaida iyayen naku”.

        Bilkisu ta amsa mata da “to”. Bayan Raudha taba Anne da Bappi tsabansu ta ɗauka sauran ita da bilkisu suka fita. Sashen su Yafendo suka fara zuwa. Inda tsoffin sukai mata tarba ta mutuntawa. Basu wani jimaba sosai ta basu tsarabansu suka fito.

         Sun shiga sashen Gimbiya Su'adah suka tarar tana salla. ƴammatanta kuma duk suna ɗakunansu. Dan haka Bilkisu ta bata shawaran su je su gaida su Ammy to. Bata musaba suka fito zuwa sashen Hajija Mufida. Itama dai ta tarbesu kadaran kadahan. Raudha bata damu ba suka ajiye mata tata tsaraban suka fito. sashen hajiya Shuwa suka shiga, sai dai sun iske tana wajen Pa dan itace da girki. Can ɗin suka nufa suma. Pa ya tarbi surukar tasa da kulawa. Yayinda itama takai duƙe gabansa tana gaisheshi da girmamawa shi da Hajiua Shuwa dake gefensa.

     Shima dai addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba yay musu, yayinda Hajiya Shuwa ke tayasa da Amin da murmushi yaƙe. Dan harga ALLAH matan na Pa na matuƙar jin kishin duk abinda ya shafi Ramadhan a gidan bisa dalilai masu yawa. Sun kusa mintuna goma sha biyar kafin su fito domin komawa sashen Maa.


        Da sauri Lubnah dake dakon fitowar tasu ta koma ciki tana sanarma gimbiya Su'adah. “Maa gasu nan yi maza ki zuba tsakin kukar a burner, shegiya mayya zamuyi maganinta yau ai. Idan ma shi Yayan ta lashe masa kurwa mu tamu bazata lasu ba”.

          Dai-dai gimbiya Su'adah na rufe murfin burner ɗin Raudha da Bilkisu sukai sallama. Gimbiya Su'adah bata amsa ba, sai Lubnah ce ta amsa cike da isa tana wani yamutse fuska kamar maijin warin kashi.

      Raudha takai tsugunne tana gaida surukar tata, yayinda hayaƙi mai haɗe da yaji-yaji ke sake tasowa cikin hancinta. Cikin ƙarfin hali da dauriya ta juya tana gaida Lubnah duk da a yanda gimbiya Su'adah ta amsa mata. Tsaki Lubnah taja mata. Bilkisu tace, “Kai Aunty Lubnah gaishekifa tayi”.

       “To dan uwarki bazan amsaba ko dole ne? Shegiya uwar shishshigi, ki cigaba da nane mata ta lasheki”.

         Raudha da tuni numfashinta ya fara fisga saboda hayaƙin tsakin kukar tai ƙoƙarin jan bakin hijjabinta zata toshe hannci amma ta kasa. A take jikinta ya fara rawa. Maimakon ganin yanayin nata yasa gimbiya Su'adah fahimtar akwai matsala sai zuciyarta ta raya mata yanayin Raudha na tabbatar da itaɗin mayyace kamar yanda lubnah ta faɗa. Murfin burner ɗin ta buɗe ta sake matso dashi gaban Raudha.

         Raudha ta miƙe tsaye da sauri tana ƙoƙarin buɗe baki tayi magana sai ta kasa, da sauri-sauri numfashinta ke ja, laluben bag ɗinta data manta ma tana sashen Anne ta shigayi a ƙoƙarin ta na ɗaukar inhaler ɗinta, amma ya gagara. Sai ma baya datai luuu. Tabbas taji ta faɗa jikin mutum, da ga haka bata sake sanin mike faruwa ba.... 


       Shigowarsa ɗakin yayi dai-dai dayo baya da Raudha tayi zata zube ƙasa saboda numfashinta daya dunƙule a ƙirji ya kasa isa huhunta balle yazo maƙoshinta ta fitar kota shaƙa. Mamaki ne ya kamashi, amma sai yay dauriyar tallafota da ƙyau jikin nasa saboda jin yanda take ɗin tamkar kokawa da numfashinta. 

        Kafin yayi wani yunƙuri Bilkisu da tayo wani uban tsalle ta dire a gabansu cikin rawar jiki take faɗin, “Ya ALLAHU. Aunty Raudha lafiya?!”. Kakarin azabar jan numfashi da Raudha keyi cikin ficewar hayyaci ya saka Bilkisu saurin faɗin, “Yaya kodai tanda Asthma? Tabbas Asthma ne, kuma ina ƙyautata zaton wannan abunne ta faɗa tana nuna burner ɗin itama tana kare hanci” shi kansa daba Asthmatic ɗin ba yana shigowa abun ya fara hawa masa kai. Dan haka bai jira wani ƙarin bayani ba ya ɗauka Raudha dake gab da rasa numfashinta ya fice da ita a ɗaki.

        A rikice Anne da Pa da Bappi dake falo suna hira da cin kilishin da Raudha ta kawo musu suka miƙe suna tambayar lafiya!. Bai samu damar amsa musu ba, ya shimfiɗe Raudha bisa doguwar kujera. Bag ɗinta dake ajiya ya fusga ya fara zazzagewa. dan yasan inhar asthmatic ce ita baza'a rabata da yawo da inhaler ba. Ilai kuwa sai gata ta faɗo. dan itace kawai a ciki ma sai turare da sweets. 

      Girgizawa yay sannan ya tallafo kanta ya matsa mata a baki. Da ƙyar ta iya zuƙa kaɗan, sake matsa mata yayi, ta shiga da ƙarfi kasancewar numfashinta da ya fara fisgowar dawowa. Matsowa Anne tai ta zame mata hijjab ɗin gaba ɗaya, sai Raudha ta samu damar sauke numfashi da ƙarfi.

         A hankali Shugaban ƙasa Ramadhan ya kai zaune a kujerar kusa da ita yana dafe kansa da rumtse idanu, ya huro iskar bakinsa. Shi kansa sai yanzune ya samu damar sauke kakkauran numfashi.

     “Garin yaya haka ta faru? Dama tanada Asthma?”.

        Maimakon Ramadhan ɗin ya bama Anne datai tambayar amsa sai Bilkisu ce ta ɓige da bada amsar. “Wlhy Anne Accident ɗin ya faru a sashen Maa ne. Saboda wani turaren wuta da suka saka. Yanayinsa zaisa dole mai Asthma ya samu attack gaskiya.”

       Babu wanda ya sake cewa komai, sai sannu da suka shiga jerama Raudha ɗin. Shiru babu wanda ya biyo bayansu daga sashen gimbiya Su'adah har kusan mintuna arba'in. Hakan ya bama su Anne mamaki, sai dai basuyi magana ba. Pa da yasan ƙiyayyar da matar tasa kema surukar tasu ransane ya ɓaci. sai dai komai baiceba. Ganin Raudha ta dawo normal harta tashi zaune sai ya sake miƙewa ya nufi sashen mahaifiyar tasa somin gaisheta.

        Yanayin sallama a falon sukai shiru daga taruwar zaman zagin Raudha da sukai, Lubnah na sake tabbatar musu mayyace ai. Tunda gashi ansa tsakin kuka a wuta ta kasa zama. Basma ce kawai babu dan tana ɗaki tamayi barci batasan bidirin da akeyi ba.

      Komai baice musu ba, duk da baiji akanmi suke ƙus-ƙus ɗin ba ya wuce bedroom ɗin mahaifiyar tasu. Itama acan tararwa yay tana waya da Adda Asmah tana sanar mata sun tabbatar Raudha mayyace yau. Sallamar tasa baisa ta dakata da wayarta ba sai da ta kammala. Sama-sama ta amsa masa gaisuwarsa kafin ta rufesa da masifa, tare da jadada masa su Lubnah zasu dawo zama tare da su domin su saka mata ido akan Raudha karta lashe mata shi dan yau ta sake tabbatar da Raudha ɗin mayya ce. Tunda gashi nan ta saka tsakin kuka a wuta Raudha ta kasa zama a sashenta. Komai baice da itaba har tayi ta gama. Ya bata haƙuri sannan yay mata sallama ya fito.


    Koda ya dawo sashen su Anne bai zauna ba yace Raudha ta tashi su wuce. Sabuwar gasassun kajin da Anne tasa aka gasa aka kawo musu tare da fura da farfesun naman kai da shugaban ƙasa Ramadhan yace a saka masa a cooler zaije da shi.

      Har bakin mota Bilkisu da Anne sukai mata rakiya, itako tanata musu godiya. Shiru motar babu wanda yake ko ƙwaƙwaran motsi har sukai ƴar tafiya. Shugaban ƙasa Ramadhan dake lafe jikin kujera idanunsa a lumshe yace, “Dakata anan”. 

      Gangarawa drivern yay gefen titi kaɗan, yayinda Raudha ta ɗan dubesa a sace dan catake barcima yakeyi. “Malama bada kuɗin nawa kilishin”.

     Sam Raudha batai tunanin da ita yake ba, amma sai ta ɗan juyo ta dubesa. Dai-dai ya buɗe nasa idanun shima da ɗan karkato kansa gefenta suka haɗa ido. 

          “Kina zaton zaki sayama kowa ne ni na haƙura”.

      Ƙasa tai da kanta mamakinsa na neman hakalata. sai kuma tai saurin cewa, “To ai ban fito da kuɗi ba ALLAH”.

     Kamar bazai tanka ba, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ya kwantar yana lumshe ido kamar yanda yake da. “Ba damuwa zan ara miki, idan munje kiban abina”. 

     Yanzun ma dai sai da ta sake kallonsa saboda al'ajab. Bata ida narkewa da al'amrin nasa ba sai da taga ya miƙama driver atm ɗinsa batare da ya buɗe idon nasa ba.

          “Na nawa zaki siyamin?”.

   (Ya ALLAHU, mutumin nan so yake ya kasheni). Raudha ta faɗa a cikin zuciya. Kafin a fili cikin fisgar numfashi tace na “10k”.

     Yasan driver yaji kuɗin, dan haka ya faɗa masa pin ɗin atm ɗin har yanzu yana a yanda yake. Shiru motar ta sake ɗauka Raudha nata juya al'amarin a ranta har driver ya dawo da kilishin. 


      Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan, kamar yanda suka fita ta barauniyar hanya tanan suka dawo. Raudha ce ta amshi ledar kilishin, shi kuma ya ɗauki saƙon Anne, duk da driver yaso dauka amma ya hanashi. Suma securitys ɗin sun gwada amsa ya hana nan ma. Suna shigowa ya miƙa mata hannu alamar ta bashi. Babu musu ta miƙa masa. Ya ajiye mata na Annen. Ciki-ciki yace, “Raba ki ɗau naki, ki kuma kawomin kuɗina”.

        “Na bar maka”.

   Ta faɗa kanta a ƙasa ganin zai wuce riƙe da kilishin da aka sakata saya dole. 

        “Oh nice”.

Ya faɗa a daƙile yana dawowa baya ya ɗauka kulolin biyu. Sai da yaje gab da corridor ɗin ɗakinsa ya sake faɗin, “Wannan ƙyautar bashike nufin zan yafe kuɗi na ba fa”.

         Karon farko da lamrin nasa ya sakata sakin murmushi, ta ɗan girgiza kai tana nufar nata hanyar ɗakin itama. Tana shiga batai ƙasa a gwiwa ba ta ɗakko sauran kuɗin da suka rage mata. 10k ta irga ta fito. Karo na farko a zamanta gidan ta nufi corridor ɗin da bedrooms nasa suke. Rasa gane wanda yake a ciki tayi, taita canki canka. Daga ƙarshe dai ta yanke shawarar yin knocking ɗin na ƙarshen. Tayi knocking kusan sau uku babu alamar akwai mutum, har zata juya na kusa da shi sai kuma aka buɗe ƙofar.  

           Saurin yin ƙasa tai da kanta gabanta na faɗuwa ganin da gashi sai guntun towel. Jikinta naɗan karkarwa da tsuma ta miƙa masa kuɗin. Komai baice mata ba ya amshe abinsa ya maida ƙofar ya rufe. Da sassarfa tabaro corridor ɗin zuwa nata bedroom ɗin, tana shigowa ta zube a gado dan jitake kamar numfashinta na sizing..........✍


No comments

Powered by Blogger.