Bakar Inuwa 37
*_Episode 37_*
..........“Vary interesting”. ya faɗa a hankali, batare da ya basu damar maganaba ya cigaba da faɗin, “Inaga zamubi exactly idea ɗin nata, sai ka shirya muku zama a tura musu invitation ok”.
“Yes ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara lafiya da shekaru masu albarka.”
Raudha ce kawai ta amsa da amin tana sauke ajiyar zuciya kusan sau uku a jere. Harga ALLAH tayi matuƙar yin ƙarfin hali ne kawai wajen faɗa. Ba komai ya sata kawo hakan ba sai tunawa da su tsohon shugaban ƙasa. Dan tabbas zasu iya bin kowacce hanya domin ganin anƙi hukunta su waɗan nan ƴan kwangilar, sannan yanda suke ɗane da shi a tarko fara fiddo manufarsa kai tsaye ga duniya cutarwa ce garesa. Dan ta tabbatar bazasu ƙyalesa ba yay aikin shekara biyun da suka ƙudiri aniyar bashi damar yi ɗin. (Duk da tasan su basu isa hana zartar da ƙaddarar da babu wani hannu daya ƙirƙiri rubutata a doron duniya).....
Hotunan dake saman cinyarta da ya ɗauka ya sata dawowa a hayyacinta. Bayan ya duba waɗanda ta zaɓa batare da yace mata komai ba ya mikama cos.
“Okay sir an gama insha ALLAH. Za'a kaima Chairman ɗin zuwa safiya zasu fara aikinsu.”.
Kai kawai shugaban ƙasa ya jinjina masa tare da tura masa sausan files ɗin dake ajiye saman centre table ɗin. “Babu yuwuwar zan duba waɗan nan ɗin a yanzun. Inaga ma ƙarasa a office idan ALLAH ya kaimu, idan na fito ina buƙar fara ganawa da vice president”.
“Okay ranka ya daɗe, ALLAH ya huta gajiya ya ƙara lafiya. A huta lafiya ranki ya daɗe”.
Cos ya faɗa cikin rissinar da kai alamar respect sannan ya mike da takardun daya tattare ɗin ya tura a bag ɗin da ya shigo da su. Raudha na ganin ya fice itama ta yunƙura da nufin miƙewa dan mararta ta takura mata dauriyarta neman fara ƙarewa takeyi. Jitai an cafko mata hannu.
Da ƙarfi ta rumtse idanu dan harga ALLAH wannan sabon salon nashi na harmutsata. Abune da shi kaɗai ya fara mata su a rayuwa....
“Nace na gama da ke ne?”.
A hankali ta girgiza kanta tana faɗin, “Kayi haƙuri” ta koma ta zauna tana ƙoƙarin cire yatsun hanunta a nashi. Gaba ɗaya yanda yake murzasu ɗin harmutsa mata jinin jiki yake yi. Sakinta yay shima, ya koma jikin kujerar ya lafe yana ɗan furzar da iskar bakinsa. Sai dai yanda maƙogwaronsa ke kai kawo zai baka tabbacin magana yake da zuciyarsa. Dan harda ɗan matse idanu yayi lokacin da yake tura lip nashi a baki yana ɗan ciza. Sai kuma ya buɗe idanun a kanta da alamun kore tu anin dake bijiro masa ya ɗan tsuke fuska
Takardun da ke gefensa ya ɗauka ya miƙa mata, “Komai ya kammala akan school naki. Akwai sabon driver da zai dinga kaiki yana maido ki.”
Hannu biyu tasa ta amsa tanajin kamar ta tashi taita tsallen daɗi. Amma sai ta daure ta shiga masa godiya da addu'a cikin dauriyar danne ciwon da ke taso mata.
Gyaran murya ya ɗanyi cikin kausasa harshe ya cigaba da faɗin, “Barinki kije makaranta bashike nufin zaki iya duk abinda ranki ya so ba. Ki kama kanki dan a yanzu kinada banbanci da baya. Akwai aure a kanki banason shigar banza. Sannan ki sani ke matar shugaban ƙasa ce, komai naki a yanzu abin tallatawa ne ga mutane koda bai kai ya kawo ba. Ya rage naki ki riƙe wannan darajan ko kiyi sakaci da shi komai zai iya faruwa. A waɗan nan takardun akwai na bank a ciki, ki cika komai kiyi musu singing za'a maidasu can. Karatu nada muhimmanci a gareki matuƙa a wannan gaɓar, saboda ƙarancin shekarunki da matsayin da kike kai a yanzu, ya rage naki ki maida hankali kiyi abinda ya kaiki kokiyi wasa da damarki.”
Ganin yanda yake magana serious ya sata sake nutsuwa itama. “Insha ALLAH zaka sameni mai kiyayewa. Bazan gaji da maka godiya ba da fatan alkairi a rayuwarka. ALLAH ya baka ikon sauke nauyin al'umma ka gamawa lafiya cikin farin ciki tamkar yanda aka zaɓeka cikin farin ciki. ALLAH ya saka maka da alkairi kai da zuri'arka baki ɗaya”.
“Amin, thanks”.
Ya faɗa yana miƙa mata leda mai tambarin apple ƴar madaidaiciya. Sai kuma ya marairaice fuska cike da salon tsokana ya fara faɗin,
“A duk lokacin da zaki fita a gidan nan ina son na dinga sani Ustazah. Dan bana bukatar matata na rayuwa tamkar akuyar sake da ko'ina zata iya jefa ƙafa a lokacin da take so. Kinada damar canja driver ko securitys ɗin da za'a kawo miki idan halayensu basu miki ba. Karkiyi tunanin yin amfani da matsayin da ALLAH ya bamu wajen taka wani, idan haka ta kasance hukunci zai iya bi ta kanki kamar kowa. Idan kinada buƙatar wani abu zaki iya faɗa”.
Murmushi mai faɗi Raudha ta saki har haƙwaranta na bayyana a waje. Ramadhan dake kallonta yay azamar lumshe idanunsa da jan numfashi a fisge. Raudha da batasan murmushi nata ya zama wani abu daban ba ta ɗago idanunta taɗan kallesa tana jera masa addu'ar fatan alkairi a rayuwa.
Kansa kawai ya jinjina mata batare da ya buɗe idanun ba. Wani irin murɗa mata maranta yayi, tai saurin kife kanta a hanun kujerar jikinta na rawa. Sunan ALLAH take ambata a zuciyarta da damƙe hanun kukerar da iyakar ƙarfinta.
Shurun da Ramadhan yaji ne ya sashi buɗe ido da nufin sallamarta dan yana son zuwa shima ya hutama ransa. A gajiye yake matuƙa sakamakon motsa jiki da yayi yau sosai da yammar nan. Dan ya fita a keke, sai dai securitys na biye da shi a mashina da mota ɗaya badan yaso haka ba.
“Zanje ciki, kije abinki kema”.
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa. Sai dai ganin taƙi ta ko motsa ya sashi sake dubanta dai-dai yana tsayawa kan ƙafafunsa. “What happend?”.
Ya faɗa yanabin hanunta data matse hanun kujera da kallo, ga kuma kamar jikinta ma na rawa. Duk yanda taso ɗagowa ta amsa masa kasawa tai, sai ma ƙoƙarin zamowa da take akan kukerar alamar abin ya fara tsauri. Shi tsoro ma abin yaso ɗan bashi, amma sai yay dauriyar matsowa ya tareta ganin zata kai ƙasa. Birkitota yay a jikin nasa, amma sai yaci karo da uban zufan data haɗa cikin ƙanƙanin lokaci. Ta ƙanƙamesa da iya ƙarfinta cikin azaba.....
“Ya ALLAH. K! What's wrong with you?”.
Ina batama san yanai ba, dan hankalinta ya fara nisa da duniyarta. Ganin yanda ta matse cikinta da hannu guda ya sashi kai hannu wajen ta saman hijjab ɗin. Sai kuma ya furzar da iskar bakinsa yana miƙewa ɗauke da ita gaba ɗaya. Dan ya fahimci yana buƙatar zuwa ɗaki da ita ya bincika da ƙyau.
Hawowarsa cikin falon yayi dai-dai da fitowar su Aynah da ga ɗakinsu zasuje ƙasa cin abinci. Turus sukai cikin al'ajab. Sai dai tun kallo guda da sukai musu kowanne yay ƙasa da kai dan sun san halinsa. Shiko baima ko kalli inda suke ba ya nufi bedroom ɗinsa ɗauke da Raudha da zuwa yanzu ma numfashinta ya fara nisa da ƙirjinta.
“What!”.
Munirah ta faɗa lokacin da ya ɓacema ganinsu.
“What! Ko what sisto. Amma dai wannan tsinanniyar yarinya anyi makira dai. Ɗauka fa? Lallai an gama shanye kurwar Yah Ramadhan a wajen nan”.
Cikin takaici Lubnah ta juya bedroom ɗin nasu batare data tanka musu ba tana ƙoƙarin kiran Gimbiya Su'adah.
A can ɗakin Ramadhan kam lokacin da yake shinfiɗe Raudha a gado sai ya fahimci ma ta suma ai. Mamaki abun ya bashi tamkar almara ko wani shirin film. Suma fa. Duk da abun ya bashi tsoro sai baiyi wani irin nuna rikicewa da ruɗani a zahiri ba dan mutum ne shi da bai iya gaggawa ba akan komai. A nutse ya zare mata dogon hijjab ɗin jikinta. Sai ga kayan barcinta wando iya gwiwa da mitsilar rigar best sun bayyana. Ruwan dake ajiye a side drawer nashi ya ɗauka ya shafa mata a fuska. Na farko ko motsi batai ba, sai da ya zuba mata da yawa ta kawo nannauyan numfashi. Sai kuma ta fashe da sabon kuka tana kiran sunan ALLAH da kira Mummy.
Hanunsa ya ɗan kai a goshi ya murza hanunsa ɗaya riƙe da ƙugunsa yana kallonta, sai kuma ya kai zaune kafarsa ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe ɗayar a saman gadon ya ɗan tallafo fuskarta.
“Please relax mike damunki ne Ameenatu?”.
Duk da ta jisa bata iya bashi amsa ba, saima damƙo hanunsa da ke ƙoƙarin riƙo nata tayi cikin rashin fahimtar manta dawa take tare ta ɗora saman mararta tana jan wahalallen numfashi.
Duk da akan rigane sai da tsigar jikinsa ta tashi. Ya ɗan lumshe idanu sa sakamakon jin wani irin ɗumi da marar ta ɗauka. “Oh my GOD ”. Ya ambata akan laɓɓansa. Da ƙyar ya samu ta barshi ya janye hanunsa a wajen, ɗaya a cikin wayoyinsa ya ɗauka ya fara neman layin Anne. Dan shi dai baisan wata doctor mace ba bayan kanwarsa Safina da zai nema tazo ta dubata a yanzun. Bugu ɗaya kuwa Anne ta ɗauka saboda wayar na hanunta ne tana duba abu.
“Kai lafiya kira a daren nan Ramadhan?”.
Hannu ya kai saman goshinsa ya murza da tura lip ɗinsa a baki ya ɗan ciza kafin cikin damuwa yace, “Anne akwai damuwa ne. Bata da lafiya ko zamu samu doctor ne?.”
“Ya ALLAHU, waye baida lafiya? Aminatu?”.
Yanda tai tambayar ta kuma bama kanta amsa ya sashi sakin ɗan murmushi duk da damuwar da fuskarsa ta nuna.....
“Kaga ina zuwa bara na nemo Doctor Shamsu......”
“A'a Anne i no need him. Mace nake bukata”.
“Naji uban ƴan kishi”.
Anne ta faɗa tana yanke kiran.
“Kishi!!?”.
Ya maimaita kalmar yana janye wayar a kunensa cike da mamaki. Dan kalmar tazo masa a bazata. Baki ya ɗan taɓe da ɗage kafaɗa irin (I don't care) Ɗin nan. Sai ma ya dire wayar a gefe kawai ya kamo Raudha dake cigaba da murƙususun ya ɗaura kanta bisa cinyarsa. Ai kamar jira take ta kife kanta a cikinsa ta zagayesa da hannayenta biyu ta ƙanƙame dan azaba.
Harga ALLAH kaɗan ya rage ya saki ƙaramin ihu, amma sai ya dake ta hanyar rumtse idanunsa gam da tura lip ɗinsa cikin baki ya taune da ƙarfi kamar zai hudashi ko shi yay laifin.
Cikin abinda bai wuce mintuna 30 ba doctor Hauwa ta iso tare da Bilkisu datai mata rakkiya. Sai dai basu samu damar shigowa ba sai da mama ladi taje tai magana kai tsaye. Yanda suka samu Raudha a jikinsa tanata murƙususu ya saka Bilkisu jin nauyi ta juya ta fita bayan ta gaida shi. Kai kawai ya iya ɗaga mata, kafin ya dakatar da ita daga ƙoƙarin fitar.
Dole ta dawo kanta a ƙasa ta taimakama Dr Hauwa'u ta dubata kamar yanda ya buƙata. Dan shi ya samu ya zame Raudhan a jikinsa da ƙyar ya tashi ya basu waje saboda Dr Hauwa'u maƙwafciyarsu ce. Hasalima babbar mace ce sa'ar su Maah. Yana mata kallon uwa ne kodan dalilin ɗanta da suke tare tun ƙuruciya. Sai dai koda ya koma gefe ya zauna cikin sofa ransa fal wasiwasin mike damunta haka?.
Dr Hauwa'u data ɗan duba Raudha da a yanzu take a jikin Bilkisu ta juyo ta kalli Ramadhan da idonsa ke kansu shima. “My son gaskiya tana tare da babbar matsala na ciwon mara yarinyar nan. Da ace ma a asibiti muke ina buƙatar mata gwaje-gwaje kafin nasan miya kamata na mata...”
Cikin girmamawa yace, “Mom to yanzu yaya za'ayi kenan?”.
“Eh to ba damuwa, zan mata wata allura insha ALLAH zata samu sauƙi, sai dai bayan ta samu lafiya ina buƙatar ganinta a hospital kar kuyi wasa”.
“Insha ALLAHU Mom”. Ya faɗa nan ma da girmamawa a gareta.
Raudha ba wani tsoron allura take ba, dan haka cikin sauƙi Dr Hauwa tai mata allurar, mintuna goma ba'a cikaba ta fara yunƙurin amai. Cikin sauri Bilkisu ta taimaka mata zuwa bayi
★★★
A can ko ɓangaren su Munirah tuni ta dannama Gimbiya Su'adah kira. Cikin sa'a kuwa ta ɗaga a bugun farko dan tana bedroom ɗinta tana shirin wucewa turaka. Cikin tashin hankalin bayanin da Munirah tai mata a kausashe tace, “K ban san shashanci wace irin magana ce wannan?”.
“Wlhy da gaske nake Maah! Yanzu haka ma ga Aunty Bily tare da Momyn Ya Suraj nan sunzo gidan da alama zata dubata ne. Kinga ko inba ciki ba taya za'a taso Momyn Ya Suraj a yanzu duk da bawani dare ne yayi ba. Dama tun ɗazun nake lura da ita tanata wani yamutse-yamutse, da kuku ya shirya lunch ma bataci ba catai ya samo mata farfesu mai yaji”.
“What! Impossible hakan ta kasance ina raye. Ramadhan!! Ashe zan tabbatar maka da ni wacece idan ka manta”.
Gimbiya Su'adah ta faɗa a matukar tsawacen da har ta firgita Munirah mai kai gulmar. Cikin daka tsawa ta ce, “Maza jeki haɗani da shi!!”.
Idanu sosai Munirah ta zaro kamar tana gabanta. Hankali tashe ta ce, “Abeg Maah. Taya zan kai masa waya ki masa wannan maganar bai ɓallani ya zubar da banza ba. Dan ALLAH ki rufamin asiri, zamowar Yaya shugaban ƙasa bawai yana nufin yayi laushin da zan iya kai masa wargi bane Maah. Please na roƙeki ki kirashi a layinshi”.
Tsaki gimbiya Su'adah tai tare da ɗaga wayar tata ta dasa da ƙasa. ALLAH ya taimaka akan gado ta faɗa da lallai saita tashi aiki a yau. Ita Su'adah har tana raye ɗanta yayma yarinyar data fi tsana fiye da komai a duniya ciki batare data farga ba, ita yaron nan zai cima amana ya haɗa shimfiɗa da jinin karuwai bayan ta masa gargaɗi. Wlhy bazai yuwuba, bazata taɓa haɗa zuri'a da yarinyarnan ba. sai dai komi zai faru ya faru. Kuma lallai sai taci mutuncin Ramadhan fiye da yanda yake zato ko tsammani).
Ita kaɗai taketa surutanta a zuciya tana kaiwa da komowa a tsakiyar katafaren ɗakinta tamkar mai dawafi.
★★★
Ramadhan da bai san anai ba tuni Dr Hauwa ta bama Raudha duk wani taimako da ya dace, ta kuma tabbatar masa da Raudha zata samu barci mai ƙarfi da zai taimaka mata wajen samun nutsuwa. Amma kar suyi wasa bayan ta samu lafiya ta sameta a asibiti. Da ga haka sukai masa sallama zasu wuce bayan Bilkisu taje ɗakin Raudha ɗin ta ɗakko mata part da pant data fahimci tana bukata. Sai dai a ranta tana jin daɗi da mamakin yaushe Raudha suka ɗinke da Yayan nasu haka har da kwana a ɗakinsa. Koma dai miye tayi farin ciki ita kam dan tana ƙaunar wannan haɗin har cikin ranta.
Sosai Raudha da barci ke ɗibar idonta taji daɗin abinda Bilkisu ta ɗakko mata. Tana son tace zata koma ɗakinta ta kasa ɗaga baki saboda barci. Dole ta haƙura ta lumshe idanun bayan ta sake cusa pant da part ɗin cikin hijjab ɗin jikinta wai kar Ramadhan ya gani.
Ya jima zaune bai motsa ba a inda suka barshi har Raudha tai nisa a barci. Abubuwane birjik a cikin kansa da UBANGIJI kaɗai yake fatan yay masa tallafi a kansu. A hankali ya miƙe ya nufi gadon saitin inda Raudha ke kwance a baki-baki, dan a nufinta ta ɗan kwanta ne idan su Bilkisu sun tafi itama ta koma ɗakinta.
Tsaye yay a kanta ya zuba mata idanu kawai tamkar mai son gano matsalar tata a kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. A hankali ya turo iskar ƙirjinsa zuwa baki ya fesar dai-dai lokacin da yake kai hannu ya ɗage hijjab ɗin jikinta da nufin cire mata gudun karya cutar da ita.........✍
Leave a Comment