Bakar Inuwa 41

 


Episode 41_*



...........Yau kwanan shugaban ƙasa Ramadhan da wasu mutanensa uku kenan a ƙasar UK. Zuwa yau kuma Alhmdllhi jikin Raudha yayi sauƙi sosai. Abin ƙarin farin cikin kuma a jiya Asabe da hajiyar birni da Hajiya mama suka zo suka dubata, jitai kamar karsu wuce, dan kuka rurus ta dinga ma Asabe da ta

shagala a kallon fadar Shugaban ƙasa da ALLAH ya jeho ƴarta ciki. Ko'a mafarki, ko'a hasashe bata taɓa kawo kwatankwacin hakan a ranta ba. Wani iko sai ALLAH, shiyyasa masanin gaibu sai shi. Bawa karka takurama ranka da hassada da ƙyashi dan baka isa canja komai daga rayuwar waninka ko taka ba. Duk abinda ALLAH ya ƙaddara masa sai ya cimmawa a duniya ko kana so ko baka so. Sai dai baƙin ciki ya cigaba da zama abokin taka rayuwar. Dan kuwa ita ƙaddara ta riga fata inji bahaushe.

         Gaba ɗaya sai taji ta sake tsanar kanta da abubuwan da suka faru a Hutawa ita da M. Dauda. Tasan ko bajima ko ba daɗe sai an dingama ƴaƴansu har jikoki gori da waɗan nan halayyar, dan ma Raudha bata sanar mata an daɗe da fara mata gori da su ba.

         Zuwan Bilkisu da take kira da Aunty B yay mata daɗi a yau ɗin, dan tazo ne a gabar da take shirin fita wanke kai tunda ya nuna baya ra'ayin kitson duk da ta kasa gano dalilinsa na waɗan nan sharuɗɗan. Tare da Bilkisun suka fita wajen wani haɗaɗɗen gyaran jiki, kai dama dukkan buƙatun tsafta da ƙwalisa na mata. Wajene mai tsaro da sirri, dan mai wajen aminiyar Bilkisu ce. Tunkan su tafi kuma tai kiranta ta sanar mata cewar gasu nan zuwa da first lady tana buƙatar raguwar mutane a wajen.

        Cikin rawar jiki miss xoxo ta sallami kaso biyu da rabi bisa ukun mutanen wajen saloon ɗin nata da kayan ƙamshi. Vip section ma ko empty ya koma dan first lady ba wasa ba. Ta zaɓo ƙwararrun ma'aikatan ta da tasan aikinsu babu wasa a ciki irin su Hafsat Rano, Mamu gee, Huguma, Bilyn Abdull. Ta sakasu shirya komai. 


(To Zafafa's kuma ba'a samu ministers ba an koma aikin saloon a *_YERWA INCENSE AND MORE_* 🚶🚶🏻😜)


      Tarba ta girmamawa first lady Raudha Ramadhan Taura ta samu, duk da zuwane na sirri hakan bai hana wasu farga ba suka fara ɗaukar hoto a sace. Sai dai Alhmdllhi kasancewar shigace ta mutunci a jikinta hijjab har ƙasa da niƙaf ya taimaka ƙwarai da gaske wajen bata nutsuwa. Babu zancen zaman ɓata lokaci bayan gaisuwar girmamawa data dinga samu ga ma'aikatan wajen  da har ƴar ƙwalla tayi aka fara mata gyaran jiki tako ina. Dan kuwa Bilkisu ce ta lissafa duk abinda ya dace a matan.

               Hummm lallai mace ƴar ƙwalisa ce kam. Dan kuwa gyaran da Raudha tasha duk da akwai na amarci a jikinta hakan bai hanata sake fitowa ba fes tamkar wata balarabiya, Bilkisu kanta babu abinda take sai yabawa. Batai ƙasa a gwiwa ba ta shiga ɗaukar Raudha hotuna dan wando da riga ta tilasata mata sakawa da zasu fito. acewarta basai tazo wajen saloon ɗin ana faman sakata rage kaya ba. Badan taso ba ta saka baƙin wandon jeans da top white anyi rubutu da Silver and black ƙyalƙyali a gaban rigar. *_I'm Beauty_*. Sai hijjab data ɗoro kawai a samansu. 

         Yanda hotunan sukai masifar ƙyau yasa Billy turama Yayansu a email ta kuma ɗaura wasu a status ɗinta tare da shafinta na twitter. Duk da babu wanda ya gane Raudha cikin ƙanƙanin lokaci ta fara samun Comments kamar banza da like. Harda masu cewa suna kamu. Dama ga shafin nata na sele... ne cike yake da followers kamar hauka, dan tana harkar business ɗinta da koya girki itama.

     Tana ɗora hoton ta sauka da nufin sai dare zata duba Comments kamar yanda takeyi, suka kuma tattara da ga Saloon ɗin suka fito driver da securitys nata na jiransu. Raudha bata san Bilkisu tayi posting pictures nata ba, kawai dai yanda akai mata gyara na musamman harda jan lallale a yatsu ya sata farin ciki. Sai ɗan baƙi kaɗan da akai mata a bayan hanunta. Ga haɗin turarurruka na *_YERWA INCENSE AND MORE_* miss xoxo ta haɗo mata cikin leda babba.

       Suna dawowa gida suka iske su Lubnah zasu fita gidan su Aynah. Batabi takansu ba dan manna musu hauka take yanzu bata shiga sabgarsu. Dan haka a matuƙar ƙulle suke da ita musamman ma Aina'u da takejin duk duniya a yanzu bata da maƙiyya sama da Raudha.

       Salla suka farayi, barcin da take ɗan jine ya sata kwanciya tabar bilkisu na kallon wani series.


*_ENGLAND (LONDON)_*


          Tashin su kenan a meeting ɗin da shine na uku akan abinda ya kawosu ƙasar a kwanakin nan uku da sukayi. Tafe yake gwamnonin da sukai masa rakkiya su biyar biye da shi sai ministers uku da odilan nashi, babu abinda kake gani sai hasken camaras alamar hotuna yake sha da ga ƴan jarida da dama tun ɗazun suke tattauwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa. Hakama wasu a cikin gwamnonin da ministoci duk an ɗanyi hira da su.

      A gajiye yake, yana shiga masaukinsa abinda ya farayi wanka, ya ɗan sha shayi sannan ya ɗan zauna domin duba abinda ya shafi family nashi da Business da rashin lokaci ya hanashi nutsuwar yi a kwanaki ukun nan. Cak ya tsaya da kofin shayi a baki zafin shayin dana kofin na ƙona masa laɓɓa. Ya dire kofin tare da fitowa a twitter ɗin da ya shiga cikin zafin rai. Haka yakeyi lokaci-lokaci yakan bibiyi shafin kaf ƙanensa na yanar gizo domin tabbatar da abinda kikeyi. Koda bai shigaba ma kika ɗora abu yakan gani. Idan kuma yaci karo da abinda bai masa ba zaka gane kuranka a hannunsa. Babu wani ɓata lokaci yay dialing number Bilkisu da yaga hotunan a shafinta, sai dai iya ƙoƙarin ya kasa samunta. Canja akalar kiran nashi yay zuwa ga number da tunda ya ajiyeta a wayar bai taɓa kira ba. Cikin sa'a kuwa ta shiga........


*_NAYA (BINGO CITY)_*


         Cikin ɗan barcin daya ɗauketa takejin wayarta da ke a bedside drawer na faman vibration data sata. Babu wanda ta kawo a ranta sai Yasmin dan tunda tai wayar nan haka take damunta da flashing da wayar Mummysu ko tasu Fatima. Cikin jan ƙaramin tsaki ta miƙa hanunta ta lalubo wayar batare data tashi ba, da ƙyar ta buɗe ido kaɗan ta ɗaga ta maida kanta a filon da ɗora wayar bisa kunne tace, “Hallo Yasmin!”.

      Wani irin tashi tsigar jikinsa tayi saboda jin yanda sautin muryar tata ke fita a mayen barci-barci. Cikin dakiya ya ture abinda ya tsikari ran nasa. 

          “Dama abinda kikaje yi a Saloon ɗin kenan?....”

    Tuni idanunta suka watsatsake ta tashi zaune dakaka dan bata buƙatar fassara ta gama haddace mai muryar. Batare da ya bata damar yin magana ba ko amsa gaisuwar data fara masa irin na suɓul da baka ɗinnan ga wanda ya shiga ruɗani ya cigaba da magana a zafafe a kuma kausashe. 

       “Tunda ga ɗan iska wanda bai san abinda yake ba ko. Matata ta zama hajar da kowane kare da doki zai iya kalla har a yanar gizo. Tunda tallar jikin kike da sha'awar yi miyyasa baki zauna a gidanku kinyi ba, sai da aurena! Da aurena kike saka wando da riga ana miki hoto a ɗora a shafin yanar gizo! Jikin da ni ban taɓa gani a haka ba wasu dabbobi suke tururuwar gani  I hate you!! Na tsani ballagazar mace da bata iya kame jikinta stupid girl!.....”

        Tuni hawaye sun wanke illahirin fuskar Raudha. Babu abinda jikinta keyi sai tsuma kanta harya fara sarawa saboda yanda yake mata magana a kausashe a kuma tsananin zafafe. Duk yanda take masa kallon mai tsauri ta fahimci ya zarce haka a yau. Dan babu komai a cikin kalamansa sai ɗaci da matuƙar hasala...

        A hankali Bilkisu data shigo ɗakin ɗauke da roba ice-creem da kwalin pizza ta ƙaraso gareta bayan ta ajiye kayan hanunta kan table ɗin gaban sofa. Duk barkwancin data shigo da shi cikin ɗakin tuni ta haɗiye abinta ganin yanda fuskar Raudha ke wanke da ruwan hawaye ga waya a kunnenta. Wayar ta zare a hankali ta kashe batare da ta duba da wa Raudha ke waya ba.  

       Ta kamo hanunta sosai tare da jawota jikinta ta rungume. “Please aunty Raudha relax. Kibar kuka dan ALLAH na roƙeki. Ke da wanene haka da har zai saki kuka ta waya..?”

       Ɗagowa Raudha tayi tana share hawayenta da hannu biyu. “Aunty B dan ALLAH kece kika ɗora hotunan da mukai a yanar gizo?”.

       Cikin ɗan zaro ido Bilkisu tace, “What! Akansu ne kike kukan nan?”.

       “Aunty shine fa ya kira yake faɗa akan ɗaurawan”.

      “Wai kina nufin Yaya!”.

Kai ta jinjina mata wasu hawayen na sake rige-rigen sakkowa. Da sauri Bilkisu ta ɗauka wayar tana ambaton “Ya ALLAH shike nan na mutu, shine na kashe masa kira”. Bata jira amsar Raudha da ba tai dailing number back. Ba'a ɗauka ba, dan yana can ya sake harzuƙa akan kashe masa wayar da akai. Ya riga ya gama fassara ƙarfin rashin kunya da rashin tarbiyyar Raudha. Har shine zata kashema waya? Kalmar mahaifiyarsa na ƴar karuwai danginta karuwai suka shiga masa kai kawo saboda kishi ya hautsinashi. A take kansa ya fara juyawa zuciyar ta sake tunzura da ɓacin rai ya fara huci.......

        Kira ne ya sake shigowa a wayar tasa, tana gab da tsinkewa ya ɗaga da shirin yimata abinda bazata sake gigin kiran layinsa ba ma har abada.

         Bilkisu da ƙirjinta ke luguden daga dan cike da ƙarfin hali ta sake ƙundunbalar kiran ta rumtse ido sakamakon cin karo da kausasan kalaman yayan nasu..... Ta rumtse ido itama da ƙarfi gabanta na faɗuwa dan ta fahimci a birkice yake. cikin rawar murya da ƙarfin hali tace, “Yaya... Am sorry Please nice. Wlhy ba laifinta bane laifina ne batama san na ɗaura pictures ɗin b....”

       “Shut-up stupid!!!”.

Ya faɗa cikin tsananin tsawar da tafi wadda yay ma Raudhan. Dan ya gane bilkisun ce ta amshi wayar. 

      “Na baki mintuna biyu ki saukesu wawuya kawai. Zan sauke miki abinda ke miki yawo a brain tunda media gidan ubanki ne da zaki ɗauketa hoto a haka kikai musu....”

      “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya na tuba na san nayi kuskure”.

      Ƙittt ya yanke kiran batare daya amsa ta ba.....



*_ENGLAND (LONDON)_*  


        A kwanaki biyun da suka rage tawagar shugaban ƙasa Ramadhan sun fahimci bashi da walwala. Kai bama walwala ba gaba ɗaya a cikin yanayin fushi yake. Dan komai yana yinsa ne cikin faɗa-faɗa. Ko a wajen meeting da sukai na ƙarshe kalaman da yay amfani da su da suka nema tada ƙura a ƙasar NAYA ya sake tabbatar da zuciyarsa a wuya take. 

      Dan daga Bappi har Anne da Pa kai tsaye suka fahimci haka lokacin da suke kallon labaran. Sai dai mai magana da yawunsa ya sake faɗaɗa kalaman yanda zasu cire ƙulli a zukatan ƴan ƙasar musamman waɗan da suka ƙullacesa a rai. Wasu sun gamsu wasu ko sun riga sun hau da takaici matuƙa...

    Oho shi baima san sunayi ba. Dan in yana a irin wannan yanayin bawai yana gane yaren kowa bane ba. Shi kansa baya gane kansa ballantana wani. Hatta da su Anne dan karsu kirasa ya kashe wayarsa ne. Sai dai hakan bai hana Bappi bin ta ɗayan layinsa ba shi ya kirashi. kamar bazai ɗaga ba ya dai daure ya ɗaga. Da ƙyar yake magana hakan ya sake tabbatar ma da Bappi akwai matsala...

      Koda ya matsa masa da tabbaya bai ɓoye ba ya sanar masa abinda ya ɓata masa ran. Dan tun yana ƙaraminsa Bappi da Anne sune abokansa, aminansa, iyayensa, kakaninsa. Da wahala yayi wani abu batare da shawararsu ba ko bijirema umarninsu idan sun masa.

     Dariya sosai ta kama Bappi amma sai ya gimtse ta da ƙyar sai murmushi yake. tsaf ya fahimci kishi mai tsanani ke ɗawainiya da Ramadhan. Ya daɗe da sanin jikansa nada kishi mai zafi irin nasa. Dan shima haka yake da tsananin kishi ga matarsa Anne. Kafin suyi aure yasha fasa bakin samari idan ya gansu tare da Anne koda ƴan family nasu ne. Kishinsa na ɗaya da ga cikin abinda yasa iyayensu aurar da su batare da sun jira sun kammala karatunsu ba.

       “To ALLAH ya huci zuciyar maza”.

Bappi ya faɗa murmushi faɗaɗe a saman fuskarsa idonsa akan matarsa data zuba masa ido da son jin mike faruwa da jikan nata.

    Bappi ya cigaba da faɗin, “Bilkisu itace mai laifin bata ƙyauta ba sam. Amma ayi haƙuri a kori gaba. Na tabbata da Aminatu tasan zata ɗaura zata hanata tunda tasan baka so...”

      “Amma Bappi wando da riga fa ta saka itama ta fita waje matsayinta na matar aure. Da bata sa kayanba ita Bilkisun zata ɗauketa hoton ne?...”

         “Uhm itama tayi laifi anan, amma bilkisun ai ta girmeta ya kamata ta fita hankali tunda tare suka fita. Sai dai ina roƙa mata afuwa a tari gaba, idan ta ƙara ni kaina zance a hukuntata kaji babban mutum. Ayi haƙuri zuciyar ta huce haka nan dan ALLAH, dan naga muma ƴan ƙasa fushin ya shafemu har ana mana dogon gargaɗin da gashinan ya tashin hankalinmu baki ɗaya”.

      Murmushi Ramadhan ya saki mai sauti yana kai hannu a goshinsa yana murzawa. “ALLAH Bappi bamma san na faɗa ba yarinyar nan ce duk ta harmutsani.”.

        Dariya sosai Bappi ya ƙyalƙyale da ita da faɗin, “Ja'iri da alama dai kazo hannufa. Ni nasan Aminatu na ba kalar matan da za'a kira na cushe bane ai”.

       Ramadhan ya ƙyalƙyale da dariya harda kwanciya a kujera. “Oh sweet bappi karda ku cika baki, dan nidai cusamin akai”.

        “Nima naga alamar hakan kuwa yau”. Bappi ya faɗa yana dariya shima.



*__________________________*


         Wannan waya itace sanadin hucewar Ramadhan tun a london. Yayinda ita Raudha kenan NAYA cikin damuwa da fargabar karya hanata makarantar daya kwaɗaita mata tunda ya mata gargaɗi tun farko. Gashi gobe idan ALLAH ya kaimu zata fara zuwa monday kenan. Shi kuma yau Lahadi zai dawo kamar yanda ya faɗa kuma aka sanar a labarai. Bilkisu har yanzu tana gidan duk da sanin halinsa ta gwammaci zama harya dawo ta wanke laifin Raudha dan tasan itace da laifi ba Raudha ba. Bata son zama silar haɗa rikicin ma'auratan duk da bata taɓa zama ƙarƙashin inuwar aure ba. Ballema wannan auren nasu na ɗora ɗafini da take ganin matsala kala-kala baibaye da shi, dan duk ƙulle-ƙullen su Maah ta sani bata nunawane kawai tana musu fatan shiriya da ganewa.

      Bilkisun ce ta ƙarfafa mata gwiwa suka shirya masa abinci mai ƙyau, ta kumaje ɗakinsa ta gyaro kamar yanda bily ta nusar da ita karta sake yarda wani yay mata gyaran ɗakin miji da ranta da lafiyarta. Sai kuma tai ƙoƙarin kwashe drinks ɗin da aka zuba masa a fridge duk da bata da tabbacin wannan ɗin akwai guba sakamakon har yanzu wancan kukun bai koma bakin aiki ba ana kan binciken ta yanda aka saka mata ƙwayar zubda ciki tasha kamar yanda taji a bakin Mama Ladi.

       Da taimakon mama Ladi suke wannan ƙoƙarin na canja drinks ɗin a duk sanda aka zuba shi, sai dai ita kanta mama ladi batasan dalilin Raudha nayin hakan ba. Ko data sanarma Anne zancen catai “Bana tunanin yarinyar nan zata cutar da shi Ladi, anya kuwa babu wani abu a ƙasa data sani? Dan akwai wani saƙo da ya zo mana ana gobe ɗaurin aurensu kuma bamu san waye ya aiko ba, da kuma muka bincika mun samo abinda aka nusar damu akansa. Shiyyasa gaba ɗaya gidan gwamnatin nan a tsorace nake zamansu a cikinsa. Amma karki damu, insha ALLAHU munama Ameenatu ƙyaƙyƙyawan zato bazata aikata wani abu na cutar da Ramadhan ba”. A lokacin kai mama ladi ta jinjina tana murmushi kamar tana a gabana, cikin jin sake ƙaunar tsohuwar tace, “Insha ALLAHU Anne”  Daga haka ta yanke wayar, bakuma ta sake maganar driks da Raudha ke ƙoƙarin canjawa ba a duk sanda aka zuba a frighe ɗin sama dana bedroom ɗin Ramadhan.

          Dan haka yanzu ma tare sukayi a sirrance tamkar koyaushe. Daga haka tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa da tai mata ƙyau sosai. Light make up bilkisu ta mata badan taso ba. Sai zuga ƙyawun datai takeyi da ƙarfafa mata gwiwar ya kamata ta koya kwalliya kuma ta dingayi dan tana ƙara mata ƙyau. Ita dai murmushi tayi kawai amma batace komai ba, dan kunyar Bilkisu takeji sosai, bama ita ba ko su Fatisa bilkisu ta girma, amma ita Bilkisun ba ruwanta ta saki jiki da ita sosai tamkar ƙawarta ma. A ranta tana faɗin, (wa zanma kwalliyar? Wannan birkitaccen yayan naku da bai iya komai ba sai jin kai da azabar masifar tsiya yaushe ma na ishesa abin kallo? Yau ka gansa normal gobe bajimin zaki kamar ɗan aljanu).

      Har ɗauri sai da ta mata, ta kuma tilastata suka fito falo suka zauna dan su Lubnah tun randa ya suka fita basu dawo ba wai bikin ƙawar Aynah akeyi suna can gidan Adda Asmah. 


     Ita dai zaune take kawai amma badan tana fahimtar abinda suke kallo a television ɗin ba har aka nuna saukar jirgin tawagar shugaban ƙasa Ramadhan da shi kansa. Shine ya fara fitowa lokacin da aka buɗe jirgin. Kamar yanda ya tafi cikin suit haka ya dawo cikinsu sai dai na yanzu sky blue ne, rigar ciki light yellow. Bai sa necktie ba dan maɓallan rigar cikin ma guda uku a buɗe suke.

          Fuskarsa ɗauke take da ɗan murmushi lokacin da yake gaisawa da masu tarbar tasu sai dai bamai tsawwalawa ba. A hankali Raudha ta sauke numfashi tana lumshe ido ganin fuskarsa da ɗan sakewa saɓanin yanda tai zaton gani, ita kanta ta yarda Shugaban Ramadhan ƙyaƙyƙyawa ne kuma ya iya ado, ba duk mace bace zata kallesa ta iya ɗauke kanta batare da taji wani abuba, ita kanta yana mata kwarjini da cika ido, badan ya ɗara sauran maza ko mutane ba. sai dai ita bata taɓa jin son sa ba. 

      Sake buɗe idanun tai tana kallon television ɗin, sai dai ranta cike yake da fargaba lokacin da ake nuna ya shiga mota ɗan jaridar na sanar da tahowarsa gida kai tsaye domin hutawa..........✍

          


No comments

Powered by Blogger.