Bakar Inuwa 59
*_Episode 59_*
.........Bayan kwanaki biyar da wannan magana Bappi ya shirya da kansa yaje har masarautar Bina sukai magana da mai-martaba, sai dai bai sanar da shi ainahin dalilinsu game da sihiri dake tare da
Ramadhan ba. Ya nuna masa suyi hakanne kodan gudun abinda zaije ya dawo ga mutanen ƙasa akan kallo da fasararar da zasuma al'amarin. Da yake mutum ne mai fahimta kuma yayi matukar yarda da Bappi a take ya amince ya kuma gamsu. Sai dai ya tsuke bakinsa ko fulani bai tunkara da zancen ba.Haka shirye-shirye ya cigaba da gudana har biki ya rage baifi saura kwanaki takwas ba. Su gimbiya Su'adah nata shirye-shiryen fara sanarwa a gidajen redio da television Pa ya dakatar. Cikin ɓacin rai ta nema dalili yace idan lokaci yayi zata sani ai. Acan bangaren mai-martaba ma ya dakatar da Fulani da Adda Asmah, dan koda mijinta ya tsawatar shi da yake ya zama mijin tace batajiba, saima tujara data zuba masa gwargwadon iyawa shiko ya sanarma mai-martaba da dama shine ya bashi umarnin shima.
Wannan abu ya cuɗa musu zuciya. Babu kunya Gimbiya Su'adah harda kai karar Pa gaban su Bappi. Anne zatai magana Bappi ya girgiza mata kai, yace Gimbiya Su'adah taje zaiyo magana da Pa. Sai dai har yau da ya rage saura kwanaki biyar basuji komai daga bakin Bappin da suka san zai iya yiwa har mai-martaba magana ya janye sharaɗin daya sharɗanta akan duk wanda yay wani abu babu umarninsu a bakin auren Fulani ne. Tashin hankali kennan da ba'a saka masa rana. Domin kuwa wannan furuci na mai-martaba ya matuƙar birkita kowa a cikinsu har Ramadhan ɗin kansa da Gimbiya Su'adah ta kira a waya ta sanarma komai lokacin yana office. Da wannan ɓacin ran ya tabbatar mata zai shigo gidan da dare dama Bappi nata damunsa da son ganinsa ya sharesa.
*_GOVERNMENT HOUSE_*..
Yau kam da wuri ya shigo gida saboda son zuwa Taura house da anyi magrib. Raudha najin shigowar motocinsa kuwa ta mike daga falo inda suke zaune suna tattauna tsare-tsaren bikin Bilkisu da ayanzu ta zame mata ƙawa dan dama bata da su sai school mate kuma ita iyakarta a gaisa babu aminiya. Saurin riƙota Bilkiau tai ta zaunar. “Ni banga amfanin wannan wasan ɓuyan da kike da shi ba, kiyi zamanki dan ALLAH karma ya samu kafar rainaki dan zai ƙara aure ko ya zata wani kishinsa kike ma”.
Kamar Raudha zatai kuka sai dai komai batace ba ta koma ta zauna ɗin. A haka Ramadhan ya shigo ya samesu.
Akan Raudha ko ya fara sauke idanunsa, itama anyi sa'a kallon nasa take. Lokaci ɗaya zukatansu suka harba cikin bugu mai tsanani. Raudha da taga ya rame mata a ido sosai sai dai ya ƙara haske da ƙyau ta fara janye nata idanun fuskarta na nuna wani yanayi mai wajalar fassara. Shiko ido ya ɗan tsura mata tamkar mai nazari ko kuma yau ya fara ganinta. Sosai ya ga ta ƙara masa girma da cika. Dan duk da ciwo da take fama da shi a watan nan baki ɗaya saita kara buɗewa tai ƙiba da girma. Sannan komai nata ya ƙara girma ga haske tayi sosai mai tafe da wani sirrintaccen ƙyawu da duk hassadar mai hassada bai isa mata kallo guda ya ɗauke ido ba.
Kansa ne yaji ya sara masa. Yay saurin janye idanun a kasalance, sai kuma yay ƙoƙarin barin wajen kamar da ƴar sassarfa dan ko gaisuwar da Bilkisu ke masa bai amsa ba. Ƙofar ya maida ya rufe tare da jingina a jikinta lokcin da ya iso bedroom ɗin nasa. Ya ja ajiyar zuciya da sauke nanauyan numfashi idanunsa har sun kaɗa sunyi jajur. Ya jima a wajen tsaye kafin yaja kafafunsa da ƙyar zuwa toilet, agogon kawai ya cire ya sakarma kansa shower. Sai da yay sharkaf daga shi har kayan dake jikinsa sannan ya ragesu yay wanka....
Raudha da dama a cikin yanayi. dauriya take zaune a wajen ta miƙe da gudu tabar wajen hanunta toshe da bakinta. Da sauri Bilkisu ta bita har cikin toilet data shiga. Amai ta shiga kwarawa tamkar zata amayar da hanjin cikinta. Hankalin Bilkisu ya sake ɗagawa matuƙa ta riƙe Raudha. Sai da komai data ɗanci ya fita tas sannan aka samu lafiya. Bilkisu ta tamaka mata ta gyara jikinta da wajen suka fito tana jera mata sannu.
Cikin sauke numfashi a wahale tana kaiwa kwance ta ce, “Kai aunty B ƙamshin turare nan na Yaya babu daɗi”.
Sosai Bilkisu ta zaro idanu waje, sai kuma tace, “Kutt Aunty Raudha ƙamshin _Boucheron_ ɗinne baida daɗi? Anya kuwa kin shaka dai-dai?”.
“Ni wlhy lafiya lau na shaƙa, kuma dai tun yashe muke zaune a falon na ƙamshin komai bai dameni ba sai daya shigo ne ƙamshin turaren nan mai kama da ka.....”
Da sauri Bilkisu ta ruƙe mata hannu tana dariya, “Uhmm to lallai Taura grandchild bai zo da wasa ba.”
Sam Raudha ba wani fahimtarta tai ba. Bakuma tabuƙaci ba'asin mganar ba tama lumshe ido dan barci ke ɗan figarta ga kanta daya fara ciwo.
*_TAURA HOUSE_*
Cikin matuƙar bayyanar tashin hankali Ramadhan ya ɗago yana duban Bappi da ya gama masa jawabi. A take idonsa ya rufe yama manta da wanda yake tare.
“Gaskiya bazai yuwuba Bappi, duk ma wada yake tunanin sharɗanta hakan ya janye dan ba yarda zanyi ba. Tayama kamar ni za'ace a ɗaura aurena a sirri sai kace wani funafunci? Na muku biyayya na amince da zabinku kukai yanda kuke so nima dole a barni nai yanda nake so akan nawa zaɓin. Sannan maganar events banajin akwai ɗaya da za'a janye a ciki, ba sai kun dinga nuna hassadarku da adawa aka dangin mahaifiyata zan san kun isa da ni b.....”
Ji kake “tauuuu!!” Wani bazafaren mari ya sauka a saman kuncin Ramadhan har sai da ya kifa kamar zai faɗi. Pa da yake a fusace zai ƙara masa Bappi ya dakatar da shi. “No Basheer barsa barsa. Kai Ramadhan mu kake faɗama muna adawa da hassada da dangin uwarka!!”.
Har yanzu hanunsa a saman kuncinsa dan da gaske marin yay matuƙar ratashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake birkicewa gaba ɗaya, idanunsa suka rufe ruf. “Idan ba hassada ba a gayamin mi kuke musu? Kun rabani da su komai sai ku, tun ina 2years a rabani da uwata tayi kawaici ta bar muku amma hakan baisa kunga haƙurinta da kawaicinta ba. To wlhy daga yau ku sani ta ƙare, idan kuma kunce a'a to muzuba mu gani!!”.
Ya ƙare maganar cikin ƙaraji da nufar hanyar fita.
Da sauri Pa ya miƙe cikin wani irin fushi yay kansa shima. Sai da Bappi yay azamar riƙo hanunsa yana girgiza masa kai. Duk yanda Pa yaso yin magana Bappi ya hana shi, ganin yanda jikinsama ke rawa sai kawai ya rungumesa yana shafa bayansa murmushi na subuce masa na tsantsar zafin da yakeji a ransa. Da wahala kaga fushin Bappi. Mutum ne mai yawan fara'a da dattako, akoda yaushe fuskarsa ɗauke take da murmushi. Duk abinda kaga faɗansa akai an ƙuresane.
*_GOVERNMENT HOUSE_*
Baƙaramin faɗuwa gaban Raudha dake zaune a gado tana karatu yayi ba. Babu haske mai yawa a ɗakin. ta zabi tai zaman karatu ne kafin lokacin da zata tashi ganawa da UBANGIJI ne. Ta zaro manyan idanunta akan Ramadhan daya shigo a tsananin fusace. “Innalillahi.....” har ƙarshe take ambata a jajjere harya iso inda take, wata irin muguwar damƙa yayma gashinta dake daure a tsakkiyar kai da hanunsa....
“K!! Har kin isa saboda aurenki a hanani yin yanda nakeso akan auren wadda zanyi? Wacece ke? Mikika taka?!.. Wato kinje kin kai munafunci garesu dansu hanani, to ai in gaya miki babu ubanda ya isa. Yau zan tabbatar miki ke ɗin ƙaramar mara kunyace kuwa wlhy...”
Kuka sosai Raudha keji jikinta na tsananin rawa. Ta shiga yarfa hannayenta duka biyu kuka mai ƙarfi na ƙwace mata ganin yana kunce belt ɗin wandon jeans ɗin jikinsa. Abu biyu ta kawo a ranta. Duka ko abinda yay mata ranar, dan haka tai yun ƙurin ceto rayuwarta sai dai hakan ya gagara. Dan tuni ya damƙota ya jefa saman gadon har sai da bayanta ya amsa dan azaba.......
★★★
Ihun Raudha ya matukar tada hankalin Bilkisu da ke ɗaki har barci ya fara daukarta. Ta fito a waje zuwa ɗakin sai dai ta samesa a kulle. Bugawa ta shigayi tana kiran sunan Raudha. Sai dai wata shegiyan ashariya da batasan Yayan nasu ya iyaba sai yau ya mulmulo mata daga ciki. Ai babu shiri tabar wajen a guje. Sai dai koda ta koma ɗaki wayar Anne ta kira. Tana dagawa ta fashe mata da kuka da fara zayyana mata abinda ta sani.
Sosai hankalin Anne da Bappi ya tashi, dan sun san ba kamar yanda Bilkisun ke tunanin Ramadhan dukan Raudha yake ba. Su sun san illolin daya dingama Amnah idan irin wannan ɓacin ran mai tsanani ya riskesa. sai dai suna ƙoƙarin rufe hakan ga kanensa idan ka cire Mardiyya da Safina dakan san wasu a wani lokutan.
Hankali a tashe tsoffi nan suka baro gida a daren nan tare da Dr Hauwa da suka taso itama ta waya suka nufo government house. Dan Dr Hauwa ce ma da kanta taja motar.
Lokacin da suka iso Ramadhan ya riga ya gama illata Raudha har jini ya ɓalle mata. Tunda ya fito a hargitse Bilkisu na son shiga tanajin tsoro. A durkushe suka sameta bakin ƙofar tana kuka. Tana ganinsu ta faɗa jikin Anne ta rungumeta.
“Anne ya kasheta, wlhy ya kasheta Anne!!”.
A tsawace Bappi yace, “Yana ina!?”.
Cikin kuka Bilkisu ta sanar masa ya koma dakinsa. Hakan ya bama Anne da Dr Hauwa damar shiga. Bappi kuma ya tisa keyar Bilkisu ta nuna masa bedroom ɗin Ramadhan.
Hankalin Dr Hauwa da Anne ya tashi a yanayin da suka sami Raudha, dan haka babu wani kace nace Dr Hauwa ta fara ƙoƙarin ganin ta tsaida jinin. Tsahon lokaci ta ɗauka da taimakon Anne dake fama da tsufanta suka samu nasarar hakan.
“Anne bazai yuwu mu barta anan ba. Inaga muje da ita can wajenki dan tana buƙatar kulawa mai tsanani yarinyar nan a wannan gaɓar tunda Alhmdllhi cikin dake jikin nata mun samu ya tsaya. Da dai anyi dilay kam da labarin da ake ba wannan bane”.
Wasu hawayene masu sanyi suka sakko akan fuskar Anne. Farin ciki da cikin Raudha, da damuwar halin da jikanta yake sakamakon son zuciyar mahaifiyarsa.
A can kuwa ɗakin Ramadhan shigar Bappi tayi dai-dai da fitowarsa wanka, ya sauke towel ɗin da yake goge fusakarsa zuwa suma kawai yaji saukar mari haggu da dama. Gaba ɗaya wutar kansa ta ɗauke ganin wanda ya maresan. Bappi, abinda bai taɓa faruwa ba ko a tarihin ƙuruciya. Dan ko laifi yayi yana yaro sai dai Anne ko Pa su dakesa amma ba Bappi ba. A karshe ma Bappin ke komawa lallashinsa da masa nasiha. Amma sai gashi yau da girmansa. Shekara dai-ɗai har 36 a duniya kakan nasa ya rufe ido ya yarfata masa maruka har biyu bayan wanda Pa ya masa ɗazun....
“Ramadhan ka kiyayi haduwata da kai wlhy!!”. Bappi ya faɗa cikin gargaɗi da ke nuna tabbatarwa. Kafin yay wani yunkuri kuma ya juya yay ficewarsa.........✍
Leave a Comment