Bakar Inuwa 65-66
*_Episode 65-66_*
...........Fitowarta dai-dai da ƙoƙarinsa na kammala busar da sumarsa. Ya kalleta kawai ya ɗauke kansa baice komaiba. Dan rigartace dai a jikinta data shiga da ita ala dole babu
abinda tayo. Sai da ya shimfiɗa abin salla ya miƙa mata wandonsa mai taushi na adidas da farar t-shirt. “Saka muyi salla lokaci na shigewa”.Kanta a kasa batare data kallesa ba tace, “Bafa abinda ya sameta”.
“Humm Ameenatu kenan, karki manta na rigaki zuwa duniya. Bayan rigaki shekaru kusan goma sha takwas na baki, kinga a lissafi kuwa lokacin da nake a mizanin shiga shekarun girma na ɗa namiji aka haifeki”.
Kunya kamar ta nutse. Dan sam batai tunanin ya ganeba. Dama sotai ta masa dabara sai sun tada sallar ta gudu ɗakin Anne ta canja kayan tai salla.
“Hallo! Ko sai na nuna miki shaida ne dan rigar kanta ta tona miki asiri tare da wannan”. Ya tura hanunsa cikin hular kanta ya jawo silin jiƙaƙƙen gashinta a ciki. Da sauri ta kwashi kayan zata koma toilet”.
“Hii aini ba surukinki bane canjasu anan konazo na canja miki kina ƙara makarar damu”.
Babu yanda ta iya dole tabi umarninsa, bayan ta saka kayan suka gabatar da sallar. Suna idarwa wayarsa ta hau ruri, yasan Anne ce dan haka ya miƙe zuwa bedside drawer ya zauna a bakin gadon yana daukar wayar....
“Kai ka fita idona kawomin yarinya taci abinci tana fama da kanta”.
(Mutum da matarsa ƙarfin hali kenan) ya faɗa a zuciya yana sakin murmushi. A fili kam yace, “Okay Gimbiyar Bappi yanzu kuwa maida wukar”.
★Gaba ɗaya Raudha jitake kamar ta nutse dan kunya. Kanta a kasa ta risina ta gaida Anne da Bappi. Zata zauna kusa da Bilkisu dake tare da su yaja mata kujerar kusa da shi tare da kamo hanunta yanda su Bappi bazasu gani ba. Sai dai ya makaro sun gani ɗin. A kuma kallo ɗaya Anne ta fahimci wayo yaje yayma Raudha, sai dai addu'arta ALLAH yasa bai aikata abinda zai cutar da itaba tunda ɗinkin jikinta bai gama warkewaba. Tunda tazo ɗaki taga babu su tai niyyar kiransa a waya Bappi ya hanata. Acewarsa yasan Ramadhan na cikin hankalinsa bazai sake yarda ya aikata abinda zai cutar da Raudha ba. Gara su barsu su sasanta kansu da wuri kodan su Gimbiya Su'adah ma.
Bilkisu ce ta zuba musu abincin, dan Raudha dai ta kasa motsin kirki. Gani take kamar su Anne sun fahimci abinda duk ya faru tunda har abu yakai ga canja kaya. Kowa nacin abincinsa hankali kwance amma banda ita. Tsakura kawai take kaɗan-kaɗan.
“ALLAH in bakici abincin nan ba zan tonaki yanzu su Anne susan mikika aikato a ciki da hujja”.
Wani irin ƙululu cikinta ya bada. Harta kasa daurewa saida ta ɗan dubesa. Gira ɗaya ya ɗage mata da sakin wani munafukin murmushi daya tilastata maida kanta ƙasa da hanzari. Duk abinda suke su Anne na lure da su, sai dai kowa ya ɗauke kansa kamar bai san anaiba.
Farfesun kan rago Ramadhan yace Bilkisu ta zuba masa. Kamar jira tana buɗe bowl ɗin Raudha tai saurin toshe hanci da rike numfashinta. Babu wanda ya lura da hakan Bilkisu ta fara zubawa, kasancewar kusa da shi take tuni ƙamshin ya ƙara karfi a kusa da ita. Har takai amai na yunƙuro mata. Ta mike zaram zata bar wajen ya rikota.
“Lafiya kuwa?”.
Kanta ta shiga girgiza masa da nuna masa ya saketa amma yaƙi. Anne ce ta fahimci abinda ya ɗaga hankalin Raudhan da sauri tace, “Ramadhan saketa”. Tai maganar tana mikewa.
Sam ya kasa fahimta, a zatonsa wani abune daban, ina kafin ya samu damar cewa wani abu ta kasa daurewa ta fisgi hanunta da ƙarfi. Sai dai kafin takai toilet na bayin ta saki aman a waje. Gaba ɗayansu sukayi kanta har Bappi, dama Ramadhan tunda ta fisge ya bita. Amai sosai takeyi a wahale. Shiko gaba ɗaya ya cimimiyota jikinsa duk a ruɗe. Sai tambayarta yake mike damunta?.
“Ramadhan ka barta taji da abinda ya dameta mana Please”.
Anne ta faɗa cike da tausayin Raudha. Sai da ya tabbatar ta gama ya ɗagata cak ya nufi sashensa da ita. Anne zata bisu Bappi ya riƙo hanunta yana girgiza mata kai da murmushi a fuskarsa. “Barshi shi daya jawo yay aikin”.
Murmushi kawai tai da girgiza kai tana mintsininsa da nuna masa Bilkiau da ido. Yay karamar dariya da ita kawai tajisa. Mai aikin Anne ce tazo ta gyara wajen. Su kuma suka koma kan table suna karasa cin abincinsu kowa da tausayin Raudha a ransa
Bayan kamar mintuna goma sha biyar Ramadhan ya fito, a lokacin sun bar dining sun koma falo.
“Yaya jikin nata?”.
Bappi ya tambaya cike da kulawa. Cikin damuwa Ramadhan daya koma duk wani kalar tausayi yace, “Bappi na barota kwance zan sama mata wani abincin a kuma kira Momyn Jabeer”.
“No kiran Mommyn Jabeer ba shine mafitaba ai. Da alama kamshin naman kan canne bataso. Taci abinci saita kwanta ta huta ALLAH ya raba lafiya”.
Wani irin yarrr yaji har saman kansa. Cikin rawar harshe yace, “Anne ban gane ba?”.
Hannu Bappi ya mika masa da faɗin, “Ajiye goro na ganar da kai”.
Ganin Bappi a serious sosai Ramadhan yay ƴar dariya yana shafa aljihu. Sai dai babu komai a ciki, hatta wayoyinsa na ɗaki. “Bappi na maka alƙawarin baka koma mi kakeso faɗi dan ALLAH”.
“Tabb ai an daina aikin banza a NAYA kai dai ajiye kasha labaru”.
Rasa mima zaiyi yay, sai kawai ya kwanto agogon hanunsa ya ɗora a hanun Bappin. Bappi ya ɗan juya agogon, sai kuma ya taɓe baki. “Ba laifi mai nauyine ai. Bilkisu bashi yasha”.
Bilkisu dake dariya cike da ɗoki ta nufi Yayan nata tayi ɗan hugging nashi, sai kuma ta sakeshi. “Yaya na kusa zama Mummyne fa, Aunty nada cikin wata biyu da kwanaki....”
“What?!!!”.
Ai kafinma ta ƙarasa bayani ya juya da sauri ya bar wajen zuwa sashensa. “Na yafe miki sauran labarin”. Ya faɗa yana ɗago hannu sanda yake gab da shiga.
Mi su Anne zasuyi inba dariya ba. Pa dake tsaye tun ɗazu batare da sun sani ba yay murmushi kawai yana girgiza kansa. Ɗansa kenan abin alfaharinsa. Murɗaɗɗen mai wahalar fahimta ga wanda ke nesa da shi. Da yawan mutane akace musu Ramadhan mai sauƙin kaine a cikin gida zasu karyata. Domin shi mutumne mai yanyin mutanen da ake kira da girman kai kai tsaye. Dan kuwa tabbas magana ma sai yaso da wanda yay niyya yakeyinta. Dariya ko mutane da yawa kance basu taɓa gani daga garesa ba. Dan akan jima baiyi hakan ba sai a inda yaso. Sai dai ga wanda yaso kuma ya aminta shi mai sauƙin kaine da iya mu'amula matuƙa.
Cikin ɗan barcin daya fara figarta kawai taji an rungumeta. Tare da fara bata zafafan kiss's tako ina da ina a jikinta.
“Ya Ramadhan lafiya?”.
Raudha ta faɗa a kasalance dan da gaske barci ya fara ɗaukarta. Bai bata amsa ba. Sai rungumeta da yay tsam a jikinsa yana jero addu'ar nan ga wanda abin farin ciki ya sama.
*الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .*
*_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._*
_Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._
*اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.*
*_Alhamdulillahi ala kulli halin_*
_Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._
Rigar dake jikinta ya ɗaga nanma yana sumbatar cikinta. Kafin ya kwantar da kansa akai wasu hawaye na tuna Haseenah na sakko masa. Ashe bayan Haseenah yana da rabon sake haihuwar ƙanen a duniya. Ɗagowa yay ya sake sumbatar cikin, sai kuma ya fara karanto addu'ar nemawa ƴaƴa tsari (iyaye dan ALLAH a dingayi, kai ko yaron cikine dake karanta ki shafe cikinki kafin ya fito ki ɗora dayi masa a zahiri😘😢. Domin kuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar: ).
*أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.*
*_O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah._*
_Ina neman muku tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa_.
Raudha dake murmushi takai hannu ta shafa kansa. “Irin wannan security ba ɗaga ƙafa haka?”.
Tasowa yay gareta shima fuskar tasa da murmushi, ya kwanta kusa da ita tare da tokare kansa da hanunsa ya lakace mata hanci. “Uhmm barni gara na tofe abina tun yanzu kodan masu ƙarancin tsoron ALLAH. Yanzu nan Baby Luv kinsan da wannan abin farin cikin tun ɗazu kikaƙi sanarmin? Anya kuwa kina sona?”.
Dariya tayi tana mai saka tafukan hanunta ta rufe fuska. “Kai Ya Ramadhan kawai kuma saina kama faɗama inada cikin ɗan fari dan banda kunya”.
“Lallaima yarinyar nan”.
Ya faɗa shima yana dariya da son zame hanunta. Ƙin yarda tayi, sai ma juyowa datai da sauri ta sinne kanta a ƙirjinsa. Idanu ya lumshe a hankali tare da rungumota ya kanƙame ta shima. ji yake kamar ya haɗiyeta kawai ya huta. “I love you sweetheart”.
“I love you too Noorullah”.
“Nice name dear I love more. Na huta an daina kaƙabamin Yaya babu dangin gabas babu na yamma. Dolene yau nayi celebrations biyu kenan”.
Siririyar dariya ta saki tana mai ɗagowa ta sumbaci lips nasa ta sake maida kanta ta kudindine a jikinsa.
“Hummm wlhy yarinya ki bani kwana uku kacal saina maidaki mara kunya ta bugawa a jaridar duniya”. Yay maganar yana mai rungumeta sosai a jikinsa murmushi yaki barin fuskarsa.
Babu wanda ya karajin ɗuriyar Ramadhan da Raudha a gidan, kuma babu wanda ya nemesu. Garama ya kira Bilkisu daga baya ta kawoma Raudha sabon abinci taci ya busar mata da gashinta daga nan sukai kwanciyarsu............✍
Leave a Comment