Bakar Inuwa 72


_Episode 72_*



.........Rayuwa ta cigaba da shuɗawa gwamnatin Ramadhan nata sakin manya-manyan projects naban mamaki. Ko'ina ka

zaga a cikin ƙasa sai sambarka akeyi. Domin ƴan matsalolin dake shigowa tarin ƙoƙarin ayyukan da ake shimfiɗawa suna dannesu ƙwarai da gaske. Hatta da ƴan bani na iya abokan hammaya bakunansu sun mutu dan babu abin faɗa kuma, sai dai duk da haka sukan ɗanyi takale-takalensu a gidajen redio dana talabijin. 

     Suna dire zance masoyan Ramadhan ke basu amsa dai-dai da su, amsar da su kansu basu da bakin sake maida murtani, dan kuwa dai kowa shaidane ga Ramadhan tun bai cika shekara akan gadon mulki ba manya-manyan ayyukansa sun fito fili ma duniya. Ga tausayin talaka. Ayyukan yi ga matasa da matan aure harma da ƴan mata. Ɓangaren lafiya da wutar lantarki da ruwa duk Alhmdllhi. Duk da ba komai ne ya wadaci kowaba hundred percent anci kaso mafi yawa na gyara. Makarantu tsaye ake akan albashin ma'aikata da cire kowane irin bara gurbi da zai iya dakusar da ilimin ta hanyar alfarma ko cin hanci da rashawa. Babban abin birgewa a matsayinka na ma'aikaci idan an cireka a gurbin da baka cancantaba za'a kaika wani gurbinne daya dace dakai bawai korarka za'ai ba a aiki balle kaje ka kama wata sabgar mara ƙyau kuma. 

         A koda yaushe idan tunanin abu yazo masa yakan tunkari Raudha da shawara kafin ya fitar da shi ga abokan mulkinsa. Kasancewarta ta tashi ƴar talakawa, cikin takalawa da talauci yana taka rawar gani matuƙa wajen zaƙulo masa abubuwa masu muhimmanci na halin ƙunci da talakawa ke ciki a ƙasar. Idan kuma har yay bincike hakan yake samu. Wannan abu na ƙara saka masa ƙaunar matarsa mai yawa a zuciya, ko saɓani suka samu ta ɓata masa rai yakan rangwanta mata idan ya kalli hidimarta garesa....


        Duk fa wannan ƙoƙari na Ramadhan yana a idanun su forma president da god fathers nasu. Sai dai sunyi likimo ne na nuna goyon bayansu gareshi ɗari bisa ɗari har ya cika shekara biyun da suka ɗiba masa tun farkon fari. A cewarsu daga nanne wasan zai fara kuma. Tunaninsu ya ƙara tsaiwa ne akan abinda ya faru game da zubama Raudha maganin zubar da ciki da sanadinsa har yanzu kuku ke a hanun security na gidan gwamnati. Sunbi duk wata hanya daya kamata susan wani abu game da case ɗin amma an rufesa ruf sun gagara jin komai. Hakan yasa zukatansu ke basu akwai wani abu aƙasa da umarnin Ramadhan kuma aka cigaba da ɓoye kuku tabbas. Domin a bincike ɗaya da suka samu kansa suka tabbatar da hakan. Akwai yaransu cikin masu kula da cctv room na gidan, kuma sune suka sakasu lalata camara ta cikin kitchen da koda aka bibiya ba'a samu komai ba, sannan falon sama da bedrooms na shugaban ƙasa da first lady ke ciki babu cctv saboda sirrinsu ne, a ganinsu tunda har babu waɗannan hujjojin bai kamata ace ancigaba da riƙe kuku ba amma sai gashi har yanzu babu labarinsa.

     Waɗan nan dalilan suka sakasu tattara komai suka ajiye gefe acewarsu ya cika 2years ɗin da suka ɗiba masa tunda idan yasan wata ai baisan wata ba. Yana shaƙar poison a ac, yana sha a drinks wannan kaɗai ya ishesu. Kashe Bappi kuwa sun gama shirinsu tsaf akan hakan rana kawai suke jira.

         Itama Aunty Hannah wannan shine dalilinta na rage zuwa wajen Raudha ɗin, sai dai tana nan tana shimfiɗa mulkin da ko first lady ɗin batayinsa, wandama bai sani ba ya ga yanda ake bata tsaro idan zata fita saika ɗauka first lady ce, ga matan ƴan siyasa da masu mukaman gwamnati tun ta tattare ta saka a aljihu tanayin yanda taso dasu.

     Duk abinda take Hajiya Fanta naji kuma tana gani, sai dai ta bata lokacine acewarta ta gama nata kafin itama ta kammala nata shirin. Rashin sanin alwashin na hajiya Fanta kesa forma First lady Hajiya Bushira hamada da Aunty Hannah kejin duniyar da damar duka tasu ce a yanzu. Shiyyasa suke sake baje kolinsu yanda suke so.


To bara mu cigaba da binsu muga yaya wasan zai kaya🚶🏻😮😖.


*_TAURA HOUSE_*


            “Nifa nata ƙoƙarin naga na danne amma yaƙi dannuwa, hakan ya tabbatarmin zuciyata akan gaskiyarta take ba wasa baneba”.

       Pa dake kallon abokin nasa Alhaji Sageer Dogarai mai maganar yay ƴar dariya. 

      “Alhaji Sageer yau kuma labaran almara ka koma kokuwa zaka fara tsara littatafai ne na marubuta, danni dai banko fahimci inda zancen naka ya kama hanyar zuwa ba balle dosa”.

     Dariya Alhaji Sageer yayi, tare da ƙurbar ruwan dake gabansu yana gyara zama. “Ko ɗaya Taura. Yanzu zan fiddo maka ainahin zancen dan na fahimci kai hausarma neman ƙwace maka take a harshe saboda yawon bin kasashe kamar ɗan sama jannati”.

    Dariya sosai sukayi a tare. Kafin su tsagaita Alhaji Sageer ya cigaba da faɗin.

      “Idan baka mantaba, a ranar ɗaurin auren yaran nan sanda muke shirin fita da kai bayan nazo na gaida Bappi, mun gamu da tawagar matar vice president”.

    “Ƙwarai anyi haka”.

“Yauwa Alhmdllh, matar da muka ɗan bigi juna har wayata ta faɗi itace tushen zancena. Sai dai zuciyata na cike da ruɗanin matar aure ce kokuwa?”.

       Ɗan shiru Pa yayi na nazari, sai kuma yaja numfashi da tunano ko wacece hakan ta faru. “Dogarai tabbas ban sanka da neman mata ba ko wani abu makamancin hakan tun bayan rasuwar matarka kuma komai bai sauya ba, to amma bazance zuciyata bazatai hasashen wani abu game da hakan ba. Dan a yanda na sanka bazakaima matar nan irin son da nake tunain zai dace da ita ba”.

        “Taura har yanzu ban canja ba, ina a yanda ka sanni wlhy. Ka ture batun yanda ka sanni akan son auren wayayyar mace mai zurfin ilimin boko, idan rawa ta canja dolene kiɗa ya canja shima a wasu lokutan. Ba wayewarta ko ilimnta na kallaba. Yanda naga kuna nuna jin kunyar juna kamar wasu surukai ne yaja hankalina sosai gareta, gata cikin shigar mutunci da kamala saɓanin sauran wanda ke tare da matar vice president. Wlhy har cikin raina sonta ya shigeni lokaci guda batare dana shirya hakan ba.”

        A karan farko Pa yay murmushi, dan yasan wanene Alhaji Sageer Dogarai. Abokinsa ne tunna kuruciya koma muce amini. Shekarar matarsa huɗu kenan da rasuwa yaransu biyu. Tunda ta rasu kuma bai sake aure ba duk da matan nakai masa tallar kansu tare da cece kucen jama'a da dangi akan ƙin sake auren nasa tunda bawai ya wuce hakan bane. Pa ya ɗan ɗage kafaɗa. “Bazance ban yarda da kai ba. Sai dai zance inhar kasan ba hakan bane a ranka dan ALLAH karka aikata abinda zai zubar da kimarmu. Domin kuwa ita wannan mata da kake magana surukatace. Mahaifiyace ga matar Ramadhan kuma a yanzu haka bata da aure dan sun rabu da mahaifin matar Ramadhan ɗin tuni. Yaranta huɗu, ta aurar da ɗaya akwai uku gabanta, sai dai tana shirin aurar da biyu yanzu haka ma”.

       “Alhmdllhi. Alhmdllhi”. Alhaji Sageer Dogarai ya faɗa yana kai goshinsa ƙasa domin yin sujudar shukur. Wannan ya sake tabbatar ma da Pa da gaske ne fa.


        ★Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai babu ɓata lokaci Pa ya tunkari Anne da Bappi da maganar. Sunji daɗi sun kumayi farin ciki, dan haka Bappi yace yabar komai a hanunsa. 

     A ɓangaren Bappi ma bai tsaya jan al'amarin ba ya tunkari su Hajiyar Birni da shi, sai dai kamar yanda yay hasashe Asabe ta nuna bijirewa su Hajiyar Birni sukai mata can. Murmushi kawai Bappi yayi, tare da basu shawarar su barta tayi tunani, amma ta bama Alhaji Sageer Dogarai ɗin damar zuwa gareta tukunna sai ta yanke hukunci. Ta aminta da hakan, babu kuma ɓata lokaci Alhaji Sageer yazo gareta washe gari.

        Mutum ne kamilalle kuma mai tarin nutsuwa. Ba wani tsufa yayba dan shekarun nasa bazasu gaza dai-dai da Pa ba, ga iya magana dan a ƙankanin lokaci ya siye zuciyar Asabe har taji ta gamsu da shi. Sai dai bata amsa masa ba sai da ta garashi sosai. Shiko bai gajiya da binta ba har sai da ya samu amincewarta. Hajiyar birni kam ai likafa taci gaba burikanta nata tabbata bayan wahalar da taci a rayuwa da garari akansu. Wani lokacin bawa nayin gaggawa ne akan abinda baida masinaiyar UBANGIJI ya tanadesa cikin ƙaddararsa. Sai son zuciya ta sakashi tsayawa wajen nemansa koda ta hanyar data saɓama shari'a ne. Sai kaga yazo ya samu abin kuma daga baya.

      Alhaji Sageer ya matsa shifa ayi aurenau kafin nasu Fatisa. Itako ta dage akan a'a sai anyi nasu Fatisa. Bai haƙura ba ya cigaba da jajircewa har hajiyar birni ta tabbatar masa yanda yakeso haka za'ai. Sam Asabe bataso hakanba. Sai dai bata ƙaunar yima mahaifiyarta jayya ko kaɗan, sannan Aunty Halima na ɗorata akan shawarar ƙwarai na gara tai auren ko bikin ƴaƴan nata ya ƙara mutunci a idon mazajensu da al'ummar da zasu halarci bikin. Tasan gaskiya Aunty Halima ta faɗa mata, dan haka ta tara yaranta ta sanar musu Raudha kuma aka faɗa mata ta waya. Kamar yanda su Fatisa suka nuna kishin Abbansu a fili haka ma Raudha. Dan kuka ta dinga rusawa akan ita bata yarda Mummyn nasu ta sake aure ba.

       Shi dai Ramadhan ma da yaji tushen kuka. tagumi ma kawai yay yana kallonta. Sai da tayi mai isarta sannan yay magana.

       “Oh ni Ramadhana naga takaina. Ni karma a haifamin yara masu kukannan fa? Yanzu ke Partner dan ALLAH ba abin farin ciki bane Mummy tai aure? Kinada ilimin addini fa, kin kuma san babu sauran aure tsakaninta da Abba taya zata cigaba da zama kuma a haka bayan har yanzu shekarunta basuyi nisan da hakan zai kasance ba”.

      Baki ta tura gaba da juya masa baya zata kwanta ribda ciki ya riƙota. “K rufamin asiri, da wannan cikin zakiyi wannan kwanciyar?, ga Abba ya samu mai tayasa kishi ni ki halakamin nawa.”

     Dama ba kwanciyar zatai ba. Dan yay magana tai hakan, ta sake tura baki da buge hanunsa dake riƙe da cikinta daya sake fitowa sosai yanzu kowama zai iya shaida akwaishi. 

        “Ni dai yi haƙuri karki cinyeni da baki, yarana suzo suga an gama gwaguyeni”.

      Filo ta ɗauka ta shiga kai masa duka yana karewa da dariya, sai kuma ta mike daga gadon ta sauka tana daddaga kafa. Saurin riƙota yay ya zaunar a cinyarsa. Zata ɓare masa da kuka ya ɗaura lips nashi kan nata daga haka labarin ya canja.

      Bai bartaba sai da ya tabbatar dukkan damuwarta ta gudu sannan suka shiga toilet suka tsarkake kansu tare. Bayan sun fitoma nasiha ya dunga mata har sai da ta fahimcesa ta sakama auren albarka. Suka kuma kira Asabe tare suka gaisheta da nuna mata goyen bayansu dan yanzu dama Ramadhan kanyi waya da Asabe da M. Dauda lokaci-lokaci. Hakanne ya ɗan ƙara sakama Asaben nutsuwar zaman Raudhan tare da shi.............✍ 


No comments

Powered by Blogger.