Bakar Inuwa 8

 


*_Episode 8_*

............“Nikam dai nake ga kamar anzo gaɓar daya kamata ace nasan minene damuwarka?”.

     Dattijuwar tsohuwa fara ƙal ta faɗa tana duban dattijon dake kishingiɗe a gefenta

yana buɗe kwanikan data ajiye masa masu ɗauke da tuƙaƙƙen tuwo dawa daketa tashin ƙamshin kanwa. Duk da jin daɗi dake tattare da yanayinsu hakan bai hana bayyanar tsufanta ba ƙarara, sai dai jikinta nada ƙwarinsa musamman daya haɗa da cikar kamala da nutsuwar dake tattare da ita. A fuska kawai zaka fahimci ita ɗin bamai yawan wasa bace sam. Sai dai hakan bai hana kwarjininta bayyana akan fuskar ba.

      Yanda ta tsatstsare sa da idanunta masu girma da haske duk da tsufan dake tattare da zagayen fatarsune ya saka Alhaji Hameed sakin murmushi yana tashi zaune sosai.

      “Nifa kibar hukuntani da idanun nan naki Jannatu, tunda ko kwanikan nan da kika ajiye shaidane banyi wani laifi ba”.

     Murmushi ta saki a karon farko tana girgiza kanta mai cike da furfurar gashi dake shan gyara. Ta gyara zamanta tana gyara kwanikan tuwon data zuba masa a gabansa. “Nima ba hukuntaka nakeba Dattijo. Kawai dai idaniyatace ta gaji matuƙa da ganin yanda kullum tunaninka keyin nisa da ni. Tun randa kukai zama da shugaban ƙasa na fahimci ka kasa sukuni. Daka zauna ko wani ya gusa a jikinka zakai nisa da duniyar mutane zuwa wata daban. Idan har ban shiga hurumin daba nawaba mizai hana na sani ko inada abin cewa dazai kawo mafita dattijo”.

        Komai baiceba. Sai dai yayi murmushi mai sanyi da cigaba da cin abincinsa da yakeji a duk duniya babu abinda ya kaisa daɗi da nutsuwa a garesa. Itama ɗin bata sake cewa koman ba, dan ta fahimci ma'ana da dalilin shirun nasa. Sai ma ta maida hankalinta ga television ɗin dake manne a ƙayataccen bangon falon nasu kawai.

     

        “Babu wanda ya shigo cikin yaran nan?”.

        Alhaji Hameed ya faɗa dai-dai yana ture kwanikan abincin nasa alamar ya kammala. Hakan kuma yayi dai-dai da juyowar matar tasa garesa tana gyaɗa masa kanta. “Babu wanda ya shigo, kasan yau jajibirin salla, mafi yawansu suna can wajen gyaran jikin kwalliyar salla. Garama ja'irarnan Bilkisa data shigo ɗazun da hantsi tacemin can zataje sallar juma'a wajen uwarta Asma'u”.

       Kansa kawai ya jinjina mata tare da ɗaukar ruwa yasha. Sai da ya ajiye kofin dayin hamdala ga UBANGIJI kafin ya gyara zamansa sosai da sake nutsuwa fiye da farko.

      “Jannatu tabbas akwai abinda ke damuna, sai dai na barsane a iya ni da tunanin zan samo mafita mai ɓullewa kafin ki sani k da Basheer. Kamar yanda kikayi tunani damuwata nada alaƙa da zuwa ofishin shugaban ƙasa.” yaja numfashi, batare da ya bata damar cewa wani abuba ya cigaba da faɗin, “Ya buƙaci na fito takarar shugabancin ƙasar NAYA saboda rikicin da aketa tafkawa akan wanda zasubama takarar a wannan jam'iyyar. Dan kusan mutane biyar ne suka nuna sha'awar hakan, sannan dukansu sun cancanta a fuskar gudunmawar da suka bama jam'iyya da shi Excellency ɗin. Kai kawon daketa wanzuwa ya sakashi ganin duk su huta shi ya ɗora wanda yaga ya cancanci ɗorawa daga ayyukansa. Shine bai tunkari kowaba sai ni”.

       (Murmushi) ta saki murmushi mai faɗi tana sake fuskantarsa. “UHMM!! That's a salient point Dattijo. Sai dai kai wace amsa ka bashi?”.

       “Ban san dalilinki na jingina tatsuniyar tasa da muhimmiya ba. Sai dai na yarda dake wajen warware matsaloli cikin sauƙi. Amsar dana basa ɗayace wadda nasan kema zakiyi tunanin hakan, shine ba zanyiba, banga dalilin dazai sakani yin mulki a wannan shekarun nawa ba na tsufa. Kai ni bamma taɓa sha'awar hakanba shima ya sani. Siyasar kanta ma sai da kukayi yaƙi sosai kafin na shiga domin bada shawarwari badan tana cikin tsarina ba. Sai dai bijirewata baisa ya ƙyaleniba. Ya kawo dalilai masu yawa da yake ganin Basheer ya cancanta....”

        “Shima bai cancanta ba”.

Ta katsesa tana kallonsa da murmushi yanzu ma.

    “Miyasa kikace haka Jannatu?”. Ya tambaya cikin mamaki da taraddadi.           “Dalilai masu yawa dattijo. Sai dai ba kowa zai iya kallonsu a dalilan ba, amma nasan kaima zaka fahimci wasu a hakan”.

     “A dalilin fahimtar wasunne ma yasa kai tsaye nace shima ɗin bazaiyiba Jannatu. Tayaya ma excellency ke tunanin zanbarma duniya Basheer alhalin shine kawai inuwar hutuna a yanzun. Shine kaɗai ɗan da muka haifa, a kuma wannan gaɓar dukkan wani kaiwa da komowa na abinda ALLAH ya azurtamu da shi a hannunsa yake, hasalima bana tunanin yanada interest akan mulki shima”.

        “Wannan gaskiyane dattijo. Naji daɗi da tunaninmu yazo iri ɗaya. Duk da dai ni da kai akwai banbancin hange a tafiyar. Rashin cancantar Babangida ko kai a siyasa bashike nufin zamuƙi amsar wannan damar ba da ALLAH ya matso da ita a tafin hannunmu, domin taimakon talakawa da ƙasarmu ta NAYA.”

       “Ban gane mikike nufi ba? Mizai amfanar damu a cikin amsa bayan munsan babu mai riƙewa to?”.

      “Akwai!”.

“Akwai?! To wa kenan?”.

       *_RAMADHAN!”_*

A take dukkan Murmushin da ke shimfiɗe a saman fuskarsa ya ɓace ɓat. Wani abu mai kama da fushi da ɗaci ya bayyana. Kansa ya kauda gefe tamkar bazaice komai ba, dan ita kanta ma harta fidda rai da ga jin wani abun a bakinsa.



★★★__________★★★

         A lissafi yau kwankinsu biyar kenan cif da shigowa cikin birnin na Bingo, inda a cikin kwanaki biyar ɗin nan Asabe tasha matuƙar fama wajen neman yafiyar mahaifiyarta data turje cewar bazata riƙe su Raudha ɗin ba. A cewarta ita kaɗai ta haifa, ita kaɗaice dolenta da idan Dauda ya koro zata amsa. Amma ƴaƴansa su shirya ta basu kuɗin mota su koma gidan ubansu suma.

     Hankalin Asabe yayi matuƙar tashi harma dasu Fatisa, dan haka suka dage wajen roƙo da taya Mommynsu magiyar ganin an barsu sun rayu a kusa da ita. Sai dai ga Raudha sam abin ba haka yakeba. Dan gaba ɗaya zubin kakar tasu da ɗabi'unta basu mataba, domin tun ba'ai nisa ba ta auna ta ɗora abubuwa da yawa na kakar tasu a mizani da ya cire mata sha'awar rayuwa anan ɗin. Duk lalacewa gara gidan mahaifinta, tunda dai acan babu mai takura maka akan tilas sai kabi wata hanya mara tushe.    

          Abinda ya ƙara tada hankalin Raudha da zama cikin ƴan uwan mahaifiyar tata shine.... *Halayensu*, dan a kallo ɗaya idan kai musu da wahala ka ɗorasu a mizanin mutanen kirki kai tsaye. Kamar yanda kukaji tun a farkon labarin su Asabe su huɗu ne a wajen hajiyar birni, Asabe kuma itace auta, sannan itace ta fara bijirewa wajen ganin tayi aure. Sai dai bayan auren nata yayarta da suke uba ɗaya wadda itace ta uku a gidan itama ta sake ɓallewa tai aurenta a birnin Bina. Yayinda hajiyar birni ta cigaba da zama da sauran ƴaƴan nata biyu suna neman arziƙi ta kowacce irin hanya.

     Sai dai kuma bayan shuɗawar wasu shekaru da adadinsu bai wuce uku zuwa huɗu ba itama babbar yayarsu tai aure anan cikin Loss ɗin.  Amma kuma sai aka samu matsala auren bai wani yi ƙarko ba ya mutu sakamakon mijin data aura baisan haihuwa. Ta fito da ciki inda ta haifi ƴan biyu, suka kuma cigaba da zama anan wajenta, dan duk bushewar zuciya irin na hajiyar birni bata amince ƴaƴanta suyi nesa da itaba. Duk inda zaka kaje da rana ka dawo ka kwana a gida. Koda babbar yayar su Asabe ta yaye yaran nata sai ta sake wani auren duk da hajiyar birni bata so. A wannan karon tayi auren ne a jihar Dokato, inda shima auren bai kai ko'ina ba ya ƙare sakamakon jarababbiyar kishiya data samu. Nan ma ta fito da yaro, duk da shi sai da akai kicimilli kafin ubansa yabar mata akan tilas. Bayan fitowar tata kuma ƙanwarta mai bi mata itama ta auri wani ɗan siyasa mai faɗa aji anan Loss (Aunty Hannah), sai dai a nan Bingo suka zauna.

     Itakam ta zauna harda yarinyarta guda data haifa da shi, sai dai sheka guda kenan auren ya mutu ta dawo gida da zama itama, ta kuma faɗa harkar siyasa dalilin sanin manyan mutane da tayi tun tana gidan tsohon mijinta ya taimakama nasarorinta ƙwarai da gaske. Dan a yanzu haka tana kusa sosai da matar shugaban kasa harma da shi shugaban kasa ɗin kansa, duk da dai bata fito da hakan a fili ga mutane saboda tsohon mijinta. A taƙaice dai a yanzu haka hajiyar birni duk tana tare ne da yaran nata da jikoki huɗu a wannan gida. Sai kuma ƴarta ta uku dake aure a Bina itama da yaranta uku. Sai Asabe mai yara huɗu, kuma sune za'a kira kamar manya a jikokin na hajiyar birni duk da uwarsuce ƙarama.

     Bayan magiya da roƙo da aka dinga mata tare da yayun Asabe biyu da suka kasa zaman aure suma sai ta amince. Sai dai ta amince ne da sharaɗin zasu tashi su nema na kansu dan bazata iya ciyar dasu har su huɗu ba. Kai tsaye Asabe ta amince bisa shawarar yayun nata da suka kwaɗaita mata wani abu daban ba wanda zuciyarta take ƙyamata ba a yanzun. 

      To ayanzu dai haka gasu a zaune bisa sharaɗin neman nakan nasu, wanda a dalilinsa hajiyar birni tace su Raudha su shirya bayan salla zasu fara mata aiki a restaurant ɗinta. Dan zasu iya samun wasu ayyukan a dalilin zamansu wajen, tunda masu hannu da shuni ne ke dabdala akoda yaushe. 

       

         Kamar koda yaushe tunda suka zo garin yau ma ta buga uban tagumi bayan kammala aikin gidan da a yanzu ya zame musu tamkar wajibi ita da sauran ƴan uwanta. Sai dai halinsu na rashin son moriya kesa duka aikin ya dawo kanta sai abinda Yasmin taɗan iya tsakura a ciki ta rage mata. Duk da azumi ne haka take dagewa ta gyara komai tsaf, hakan ya saka gidan canjawa cikin ƙanƙanin lokaci, da'alama dama rashin zama a gyarashine ya sashi canja kamanni......

      “Raudha!”.

   Asabe ta kirayi sunanta da ɗan ƙarfi a karo na biyu. Firgigit ta juyo ta kalleta dan sam bataji na farko ba.

      Hannu Asabe ta shiga tafawa na taraddadi tana salati. “Oh ni Asabe Raudha wai mi kike son maida kanki ne? Duka shekarunki nawa da zaki jefa kanki cikin masifar tunane-tunane mike damunki?”.

      “Mommy babu komai fa, kawai na zaunane naɗan huta Yasmin ta fito wanka nima na shiga”.

      “Ƙarya kike Raudha, ki faɗamin gaskiyar abinda ke damunki tun kafin mu saɓa.”

      Ajiyar zuciya Raudha taja da ɗan ƙarfi tana haɗiye ƙwallar data cika mata ido. Cikin yunƙurowar dukan damuwar dake akan ƙirjinta ta fara magana. “Mommy so nake na koma islamiyya, kinga dai rayuwa bazata tafi da ƙyau ba babu neman ilimi, tunda babu tabbacin samun cikar burin yin makarantar gaba da sakandire (secondary) inaga ya dace ace mun maida hankali akan na addinin matuƙa, a ƙalla dai mun mori wani yanki na arziƙin duniya dazai amfanar damu har a lahira. Amma idan na ɓata miki rai a zancena kiyi haƙuri”.

         Sosai zuciyar Asabe ta karye da tausayin ɗiyar tata. Ta sani duk cikin ƴaƴanta babu mai nutsuwar Raudha. Yarinyace mai hankali da sanin yakamata. Ya rinyace abar alfaharin kowaɗanne irin iyaye. Sai dai yarinyace mai murɗaɗɗen hali da wuyar sha'ani. Ba komai take kallo dai-dai da ra'ayin mutane ba, ta rasa inda ta kwaso wannan bauɗaɗɗen halin nata da taurin zuciya. A ido zakai mata kallon mai sauƙin kai, amma sam ba haka baneba, wanda ya nutsu ga fahimtar halin Raudha ɗinne kawai zai gane ra'ayinta yasha banban dana mutane.......

      “Mommy kiyi haƙuri..”

Sassanyar muryarta ta katse tunanin Asabe. Guntun murmushi ta saki tana kaiwa zaune kusa da ita, tare da kai hannu ta kamo nata. “Karki damu indai islamiyya ce zan sakaku Raudha, sai dai ki sani bazai zama dai-dai da yanda kike zuwa ta gida ba har sau sama da uku. Saboda kinga nan zaku ringa zuwa wajen aiki, kinga dai yanda sauran ƴan uwana ke tsaye bisa ƙafafunsu, babu wanda ke zaune yana dogaro da Gwaggo. Kowa neman na kansa yake yi ta yanda nima bazai yuwu na zauna na zuba ido Gwaggo ta cigaba da ɗawainiya damu ba”.

           “Hakane Mommy, sai dai ina roƙon dan ALLAH komi zamuyi ya kasance bisa ƙyaƙyƙyawar hanyar da bazamuyi dana sani ba watarana mu da ke. Bazan ɓoye mikiba Mommy wlhy sam rayuwar gidan nan batamin daɗi, nafison hutawa....”

        Harara Asabe ta dalla mata da ture hannayenta a cikin nata, rai ɓace tace, “Uban hutawa kikafi so mara mutunci, Raudha bar ganin ina lallashinki wlhy zan ɓata miki rai. Duk da buhun wulaƙanci da tozarci da ubanku yay min har kike iya kallon cikin idona kina faɗamin baƙya son nan kin fison Hutawa. To dan ALLAH ga hanya nan koma Hutawar mtsoww mara mutunci kawai”.

      Hayaniyar Asabe ce ta fito da Hajiya Mama babbar yayar su Asaben da yau bata fita ko'ina ba tana gidan tana barci. 

     “Asabe lafiya? Wa kikema ihu haka?”.

     “Wannan mara mutuncin yarinyar Raudha mana.”

    Ta faɗa a hasale tana harar Raudhan datai ƙasa da kanta hawaye na gangaro mata bisa kumatu. Cikin ɓacin rai Asabe taima yayar tata bayani kamar ta rufe Raudha da duka dan taji zafin maganar datai sosai a ranta. Itama Hajiya Maman faɗa tahau Raudhan da shi sosai har tana mata gorin ubansu bai iya komaiba sai bin mata kamar tsohon bunsuru da busa sigari. Ba Raudha kaɗai ba, hatta su Fatisa wannan furuci na Hajiya Mama ya zafesu a rai matuƙa. Ana tsaka da wannan kicimilli ɗayar yayar Asaben da suke kira Aunty Hannah ta shigo gidan. Da alama fita tayi, dan sanye take da kaya na alfarma sai bula ƙamshi take. Babu yanda za'ai mai kallo yace daga wannan gidan ta fito duk da shima gidan nada ƙyau gwargwadon iko. Sai dai shigar tata tafi kama data hamshaƙan mata da duniya ke kan ganiyar ƙaunarsu da rungumarsu a jikinta. Ta ajiye key ɗin motar ta bisa centre table ɗin falon tana kaiwa zaune.

        “Nikam lafiya kuka rufe yarinya ƙarama da ihu tamkar wasu kishiyoyinta?”.

       Sanin halinta na rashin son ganin ana takurama yara Hajiya mama tai saurin faɗin, “Hannah bar wannan ba abar goyon baya baceba....” nan itama ta shiga zayyana mata abinda ya faru da Raudha ta faɗa harya fusatasu.

       Saɓanin su ita murmushi tayi tana gyara zama saboda wani abu daya cuɗanya tunaninta da zancen Raudha ɗin cikin ƙanƙanin lokaci, har takai ƙwaƙwalwarta ta haska mata wani nasara a ƙananun daƙiƙu, dan yanzu haka daga government house take.

       “Raudha badai islamiyya kike so ba? To zakije islamiyya”.

Ta faɗa murmushinta na sake faɗaɗa tare da shafa kan Raudha a hankali. Su Asabe na buɗe baki da nufin yin magana ta girgiza musu kanta tana miƙewa. Dukansu binta sukai da kallon mamaki harta shige cikin ɗakin barcinta. Bawai amsa buƙatar Raudha ɗin bane abin mamaki a wajensu, dan sun san itaɗin mace ce mai son yara sosai, sannan ma tun zuwan su Asabe gidan kowa ya fahimci irin son da take nunama Raudha, dan ko abu zata saka ai mata kafin ta saka su Fatisa ta saka Raudha, sannan har zama take suyi hira da Raudha ɗin. Abinda ya basu mamaki ta shigo a yanayin damuwa sosai, amma dagajin abinda suke ɗauka laifi ga Raudhan sai saɓanin hakan ya bayyana a fuskarta, dan a zahiri tamkar abinda Raudhan tayi ne ya warware dukan damuwar data shigo da shi cikin gidan.........✍




_Tofa minene a ran aunty Hannah da har yay dai-dai da burin Raudha kuma?🤔_


No comments

Powered by Blogger.