Bakon Lamari 11


 *BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *11*


Ya ɗaura faffaɗan tawul a ƙugunsa Ya shiga Bathroom.

Ya Jima aciki yana wanka kafin ya fito Ya shirya Cikin wata Black jallabiya mai gajeran Hannu wadda aka mata aiki da Golden Ɗin zare mai layi layi Daga gaban ta Kuma a buɗe yake wanda ya bawa Gashin dake saman  ƙirjinsa wanda ya tawo har ta wajan wuyan shi damar bayyana a sarari.


Turare mai daɗin ƙamshi ya fesa sannan ya ɗauki wayar shi daya aje a saman gado ya fita daga Ɗakin Gaba ɗaya ji yake ya gaji,Jin ana kiran sallar magariba yasa ya Ɗaura alwala a famfon dake Bakin Ɗakin nashi ya fice masallaci Zaman jiran Jam'i yayi har aka taru a masallacin suka yi sallar magariba sannan ya fito ya Nufi cikin Gida.


Babban falon Mama ya shiga Bakin sa ɗauke da Sallama.

Jin Shuru a falon ya tabbatar masa da duka Ƴan gidan sallah suke Domin hatta Tv an kashe ta.

A hankali yake taka ƙafarshi A saman Shinfiɗaɗɗan Carpet Ɗin daya malale Falon Har ya sami damar ƙarasawa Bakin Ƙofar Bedroom Ɗin Mama sai da ya buga ƙofar sau Uku sannan tai masa gyaran Murya.

Murɗa Handle ɗin Ƙofar yayi ya shiga Cikin Bedroom Ɗin Bakin sa ɗauke da sallama yana mai Lumshe idanunshi wani irin haɗaɗɗan Ƙamshin Turaren wuta wanda ya haɗe da Iskar Fanka na ratsa masa dukkan sassan Jikinsa.


Gyaran Murya ta kuma yi masa sabida haka sai ya nemi Gefenta ya zauna wadda take zaune a saman darduma tana lazimi da ƙaton Carbi mai Dubu a gabanta.

Zaman kusan Minti Talatin Yayi kafin ta shafa addu'ar ta Ɗago da kanta Cikin murmushi tace masa.

"Barka da dawowa Ina maka fatan nasara a cikin rayuwarka"

Ta furta hakan cike da so da ƙaunar ɗan nata cike da Ranta da zuciyarta.


Wani irin ƙayataccen Murmushi Ahmad ya saki yana shafa saman kanshi da Hannun shi cikin nagartacciyar Muryarsa mai cike da Haiba da nagarta yace.

"Mun same ku lafiya Mama? Yaya gida da yara Ina Alhaji tun da nazo ban gan shiba ko a masallaci?"


Cikin Murmushin daya ƙi gushewa a saman Fuskarta tace masa.

"Alhaji ya fita Cikin gari Gaisuwar abokin sa, Gida kuma Alhamdulillahi da kowa da Kowa muna cikin Godiyar Allah"

Daga haka taja Bakinta tayi shuru.


Shima Sunkuyar da kanshi yayi a ƙasa bai Kuma cewa komai ba sabida Rashin sabon doguwar Maganar da bata fiye shiga tsakaninsu ba sakamakon Alkunya da Mama take masa ta ɗan fari.


Ɗakin yayi tsit kamar Babu mutum aciki.

"Kaje falo akwai abincin ka"

Daga haka ta kuma shuru.


"Mama Muje tare dan Allah yaushe rabona dake ai mayi Hirar yaushe gamo"

Ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

Ɗago kanta tayi ta zabga masa harara tana mai kawar da kanta Gefe ɗaya Sanin ba zata tanka masa ba yasa ya miƙe Yana cigaba da dariyar daya keyi wadda In ba a gaban maman ba babu mai samun arziƙin Ganin dariyar tashi.


Dining area ya Nufa wanda aka jere shi da manyan Food Flask ɗin abinci kamar wanda za'ai ƴar ƙaramar walima ya Kuma shafa kanshi yana Cigaba da Murmushi yasan aikin Mama ne wannan wadda take Masa Hidimar Cikinsa duk sanda yake Gida ba dare babu rana dan baya yarda da girkin kowa sai nata.


Yayi Bisimillah ya zauna a saman Kujerar Dining Ɗin ya soma Buɗe food flask ɗin waɗan da akai girki kusan kala Uku aciki, kuma kowanne kalar Girkin daze gani daban waɗanda Duka abinci ne Irin namu na gargajiya.


Ya Ɗauki plate da Spoon ya aje a gaban shi sannan ya ɗauki Sarving Spoon ya Buɗe Flask ɗin  Dambun shinkafar daya ji gyaɗa da Zogale da Albasa da wadataccen Man gyaɗa da ƙananun Hantar da aka yanka aciki ya matsar da Plate ɗin gaban flask ɗin  ya saka sarving spoon yana ɗiba wani haɗaɗɗan ƙamshin Dambun na dukan Hancin sa.


Ɗan kaɗan ya zuba sabida bai da yawan cin abinci sannan ya rufe flask ɗin, ya janyo na farfesun Ƙoda da hanta da Tumbin da akai wanda Aka yanka manyan albasa acikin sa shima sai ƙamshi yake ya zuba wadatacce a saman Dambun sabida Yana da son Naman kayan ciki A rayuwar sa.

 Bisimillah yayi ya ɗauki spoon ya soma Juyawa yana ɗiba Haɗe da farfesun yana kaiwa Cikin Bakin sa Daɗi Mai ma'ana yana kaiwa ƙwaƙwalwar sa Ziyara A ranshi yana addu'ar Allah yasa Zainab Ta iya Girki Domin mace wadda tasan kan ludayi itace Mace Duk macen da bata iya Girki ba sunanta Sorry Bini Bini daya ci loma ɗaya zai ɗauki Cup ya tsiyayi ruwa a Roba ya kai bakin sa har ya kammala Cin Abincin yayi Hamdala Ga Allah tare da Ɗaukar tissue ya goge bakin sa Lokacin daya tashi daga saman dinnig Ɗin wayar zainab kusan ta Biyar na shigowa bai ɗauka bane sabida ƙa'idarshi idan yana cin Abinci Baya magana har sai ya gama Kuma Bashi kaɗai ba wannan tarbiyar Duk wani Ɗan gidan Mama ne.


Bin kiran nata yayi Lokacin daya ƙarasa Saman one seater dake Falon Mama ya zauna ya ɗaura Ƙafa ɗaya kan ɗaya yana girgizawa.

"Baby ina ta kiran ka baka ɗauka ba wai baka tawo bane ba?"

Ya shafo gemun shi tare da cewa.

"Zainab sau nawa ina gaya Miki Ni musulmi ne ki soma yi min sallama kafin ki fara Min magana"

Ya faɗa Muryar shi a dake.


"Kai haƙuri Ina ɗaukin Ganin kane Tun ɗazu nasa masu aiki suka maka girki Ni kuma naje Gidan Kwalliya yanzu Haka kai nake Jira kai Min waya nazo airport Ɗin"


Tausayin tane ya tsirga masa har Ranshi Zainab na son shi Haka Shima yana son mace mai Son shi wadda zata Nuna masa tattali da kulawa.

"Ina gida yan zu haka nagama cin Girkin Mama na"

Ya faɗa a dake.

"What!! Girkin wa? banji me kace ba haba Ahmad kana Nufin duk wahalar dana sha Na kwalliya da sakawa ai maka Girki ya tashi a banza kenan?"

Ta ƙarasa maganar tana Kuka!

"To ya za'ai kinsan Ni ba korarre Bane Ina da gidan mahaifa Kano ai gida ce Ki min uziri yau na gaji Amman Gobe zan Zo"

Ya faɗa Cikin kwantar da Murya.

Kuka kawai zainab take masa na takaici da Baƙin cikin abin da yayi mata.

Gajiya yayi da Jin kukan nata dan shi bai iya rarrashin mace ba sabida haka sai ya kashe wayar tashi Baki ɗaya.

Ya kwantar da kanshi Jikin seater  Yana mai rufe Idanunshi.


"Har ka gama cin abincin?"

Yaji Muryar mama wadda take zama a kujerar dake kallon shi.

Da sauri ya zame daga saman Kujerar ya zauna a ƙasa.

"Na gama mama Amman ina son Baƙin shayi asa Kamal ya miƙa Min ɗaki"

Ta Jinjina kai tana cewa.

"Daman na dafa maka mai kayan ƙamshi sai ya miƙa maka idan ya shigo"

"Nagode Mama"


Ta kuma fuskantar sa taga  yadda ya nutsu a gabanta yay ƙasa da kanshi sosai.

"Amatu tana gida fa Auren ta ya Mutu, wannan abu da shi na kwana na tashi dashi da Alhaji ya gayan Jiya duka yaushe akai auren nata amman yaron nan ya sake ta ga jaririya ina ga basu yi arba'in ba! sannan Ina son kaje kaga Jikin Babanka sha'aibu yakamata ai wani abu akan wannan Jiki nasa sannan Kuma ka ƙaro Kayan abinci Wa matan kawun ka da sauran matan gidan sai Kuma Kuɗin makarantar Yaran kawunka suma naji ance an koro su Jiya"

Dama a ƙa'ida idan sukai waya da mama tana gaya masa dukkan buƙatun Gidan da kuma abin da ya faru sabida shine Babba a kaf ƴaƴan gidan, Gudun kada a ce bata gaya masa Komai. To yau kuma ganin Allah ya kawo shi yasa take gaya masa waɗancan maganganu waɗan da dama tace zata bari In yazo ta gaya masa tun sanda yace mata zaizo.


"Sannan ina son Hafsa ta dawo gida ta haihu kaga haihuwar fari ce"

Ta kuma faɗin hakan duk da yayi shuru ya ƙi cewa komai.

"A,a mama ki barta a gidan ta kawai In yaso a ɗauki mai aiki ta kula da ita"

Ya faɗa batare daya  ɗago ya kalleta ba.

"To shike nan hakan za'ayi"


"Mama dama Amatu ta haihu aini ba wanda ya gaya Min, Shi Mijin nata ɗan ina ne?"

Ya jefo mata tambayar.

"Kasan yadda auren yazo ai koshi Alhaji faɗan daya gama yi Jiya kenan ai Hadiza ta cuci Yarinyar nan Wallahi sam batawa haihuwa adalci ba"

Mama ta faɗa daga gani abun yay mata ciwo a matsayin ta na uwa.

Bai ce komai ba yaja Bakin sa yay shuru yana mamakin yau wace rana mama ta zage tana magana  a gabansa  wadda ko a waya bata jan doguwar magana dashi koda magana ce mai mahimmanci data gaya masa take kashe wayar.

Cikin haka Alhaji ya shigo wanda suka gaisa da Ahmad sosai kuma Suka tattauna akan aikin daya kawo shi wanda yace Nan da ranar Litinin Zai tafi can barrack Ɗin da aka Tura su wanda zasu haɗa team ɗinsu su shiga ƙauyukan sai dai zai na zuwa gida week end addu'a Alhaji yayi masa sannan ya Miƙe yana Musu sallama dan ya gaji bacci ne a idanun shi sallar isha'i kawai zai yi wadda tuni akayi babu shi sai ya kwanta...........*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*




*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.