Bakon Lamari 19
*BƘNLMR019*
Bata Juyo ba kuma ba ta daina Ƙoƙarin Buɗe Ƙofar ba, haka kawai taji Gabanta yana faɗuwa sannan Kuma tana jin tsananin Zafin shi.
"Amatuhh!"
Yaja Sunan da wani Irin salo, Mai kashe Jiki A hankali ta saki Murfin Motar ta Koma da baya ta Jingina da Seater ta takure Jikinta kamar Mai Jin sanyi.
Idanunta Lumshe wani Irin sanyi na ratsa mata Jikinta.
Ya matsota sosai Har tana shaƙar Ƙamshin mayen turaren sa wanda ya cika Motar.
"Yau rana ce mai daraja a wajena ranar da zan kasance da masoyiyata Duba Jikina kayan ɗaurin aure ne amman haka na tsallake na Bar komai akanki Why Amatu ki dawo Kina ƙunci mai nai miki duk irin Hidimar Da nake Miki kamar bakki gani"
Gabanta ne ya kuma faɗuwa Eh yau kam ranar auren shice base ya gaya mata ba, Jitai kamar da gayya ya gaya mata hakan ta rasa mai yake damunta taji ta damu akan wannan aure nashi.
"Base ka gayan kana son matarka ba Nima na shaida soyayyar da kake mata Tunda Har ka iya auren ta Nima yau zan Koma gidan Mijina"
Tana faɗin haka ta fincike Iman daga hannunshi ta Buɗe Motar ta Fice.
Abin mamaki duk inda ta wuce Binta ake da kallo harta tsargu da kallon da ƴan bikin keyi mata.
Haka ta ƙarasa sashin mama ta tarar dasu Cirko cirko.
Mama ta zabga tagumi Wasu mata zaune masu kama da mama daga gani ƴan uwanta ne sai maganganu suke cikin faɗa har ɗayar na cewa Mai yasa basu zane ƴar banza ba.
"Lahh Mama ga Amatullah Ɗinnan"
Cewar Surayyah ƙanwar shi Gaban Amatu ya faɗi ta tsaya cak a tsakiyar falon ta kama Iman ta ƙamƙame Mama wadda ta faɗa duniyar Tunani tun bayan Fitar Umman Amatullah wadda ta gama ciwa mama Mutunci tsaf har tana tutiyar In bata jama ɗanta Kunne ya rabu da ƴarta ba wallahi sai ta makashi a kotu da ƙyar aka fitar da Umma dan sai da ƙannen mama sukai ma Umma caaa suka ce zasu zane ta sannan ta fita
Tun bayan Fitar Umma wadda bata jima da fitar ba mama ta zabga tagumi Ina Ahmad yakai Amatu itafa bata son tashin hankali dan jaraba yau ana ɗaurin auren shima bai tsaya ba ya fitar da ita.
"Dama wannan ce ƴar tata ashe ma bazzawara ce Ah ba mamaki dan ta ɗauki Baba yawo ai daman Ƙananun yaran nan idanun su a wanke yake danna san Baba baze ɗauketa su Fita ba sai dai ita tai masa wayo"
( da yake baba ƙannen mama da ƴan uwanta ke cewa Ahmad sabida sunan mahaifin su gare shi )
Cewar Wata daga cikin Ƴan falon.
Dariya suka kwashe da ita ɗaya daga cikin ƙannen mama tana nuna Amatu tana cewa.
"Ke ƴar marar tarbiya yanzunan dabbar uwarki tazo ta ciwa ƴar uwarmu Mutunci akan Kin ɗauki Baba Kun fita Ina mai baki shawara akan Ki fita daga sabgar Baba, ba sa'anki bane Ki lallaɓa Ki Koma gidan Mijin ki nan ne aka san darajarki munan ko kinzo baki da Fus matar Baba gaban ki take akomai shegiya ƴar matsiyata wuce ki bani waje na ƙara ganin ki a sashin nan sai na ɓalla ƙafarki Munafuka"
Da sauri mama ta ɗago tana makewa ƙanwar tata baki tana Ƙoƙarin yin magana Ahmad Ya shigo falon tsabar kwarjinin sa da Tsare Gidansa yasa Falon yayi Tsitt babu komai sai tashin Kukan Amatullah wadda ta Tsaya kamar An dasa ta tana zabgar Kuka.
Jikin Ahmad Har rawa yake wajan ƙarasawa wajan ta bai Tsaya kula da na cikin falon ba baki ɗaya hankalin shi na kanta.
"Amatuh waya taɓa ki Me akai Miki Kuma?"
Duka ya jera mata tambayoyin.
Bata Kula shiba taja ƴarta ta fice daga falon da sauri.
Da wani Irin zafin nama ya take mata baya yana kiranta daga Falo kowa ya cika da mamaki musamman Mama data zabga tagumi tana kallon Ikon Allah.
Da ƙyar ya cimmata a bakin sashin su zata shiga ya kama Hijabinta gam! ta saka hannu ta doke mai Hannunshi Ya girgiza kai yana Binta da kallo Hankalinshi a tashe.
"Mai akai miki a part Ɗin mama?"
Ta Murguɗa mai baki taƙi cewa komai sai ma Ƙoƙarin tuɓe Hijabin jikinta take dan ta bar masa ta Shige Ciki haka.
Ganin hakan yasa ya ɗaure Fuska yana mai daka mata tsawa.
"Nace mai akai Miki?"
Ya faɗi a hargitse.
Tai alƙwarin ba zata bashi amsa ba dan haka tai mai banza ta Tuɓe Hijabin ta bar mai a hannun shi ta wuce Ciki da sauri.
Ya girgiza kai ranshi a ɓace ya Koma ɗakinshi batare daya koma part Ɗin Mama ba.
A hargitse ta shiga sashin su Tana shiga taci karo da Umma na kai komo a Tsakar Gida.
"Dama jiranki nake dan Ubanki yau Koki Koma gidanki kona Tsine Miki ke wallahi sai ma kin Koma Ko zaki Mutu zan kai gawarki Gidan Imran"
Babu tsoro Ko fargaba ta ɗago tana kallon Ummah zuciyarta ta Bushe Komai ya fitar mata akan ta tace mata.
"Umma Kiyi haƙuri wallahi bazan Koma gidan Imran ba nagaji ba mai karɓar min Ƴan cina toni zan tsaya ma kaina da ƙarfin Ikon Allah"
Umma ta wanke ta da mari ta kuma ƙara mata wani nan da nan ta rufe ta da Duka Har tana samun Iman.
"Ni zaki gayawa maganar banza Ban haifi ɗan daze gayan magana ba Wallahi sai dai Ki bar min Gidana amman ba zaki zauna min babu aure ba mai Imran yay Miki mai yake Miki da har kikai masa wannan tsana ɗa ɗan mafita ɗan Kirki mai tausayi da sanin darajar mahaifan ki"
Cikin Kuka Amatullah ta ɗago tana cewa.
"Haƙiƙa Umma Kin jefa zuciyata Cikin shakku Ina tunanin anya kece kika haife ni Umma zan gaya Miki wata magana akan Imran Umma makirine Imran Macuci ɗan iska ba irin azaba da masifar da bai gana mini ba Ummah idan Kika cire Ameerah babu wani mahalukin dana taɓa gayawa cewa Imran nema na yake Ƙoƙarin Yi ta bayana duk wannan bala'i akan naƙi aminta dashi ne "
Amai makon Ummah ta ruɗe sai ta rangaɗa Buɗa ta cokalo ɗauri gaba.
"Allahu akbar lauya! nace lauya! haka Ahmad Ɗin ya kinsa Miki masharran ciya to ko duk Jikina Kunne ne bazan yarda Imran bawan Allah na Ƙoƙarin Neman ki ta baya ba Munafuka maza Ki ɗauki ƴan kayanki Muje na rakaki ɗakin Ki sam bazan amshi wannan magana marar makama bare Tushe ba"
A Razane Amatullah take Kallon Umma wadda bata kama maganarta ba Burinta kawai ta Koma gidan Imran.
"Ummah bazan Koma Gidan Imran ba Inna koma umma Komai yana iya faruwa zuciya bata da ƙashi"
Wani wawan Bugu takai mata Amatullah ta Fice daga Gidan agigice tana Ihu hanyar waje tai tana Kuka Tana ma Gidan kallon ƙarshe dan bata zaton zata kuma dawowa Cikinsa wannan bala'i har Inah.
Ƙamshin turaren shine ya sanar mata da wanda taci karo ya sanya tattausan hannunshi ya riƙota sabida Ƙoƙarin Faɗuwa take.
A hankali ya saki hannun nata Kuma yana zuba mata ido.
Tana Ƙoƙarin raɓe shi ta fice ya kuma tare mata hanya.
"Kaban waje yaya wallahi umma ba zata sake ganina ba na gaji duniya zan shiga komai ta fanjama fanjam.......saukar tagwayen maruka saman Fuskarta shine yasa ta dabur ce ta ɗimauce tana ƙoƙarin rasa Nutsuwarta.
"Ni ka mara akan Me? mai nayi maka Okey bakwa sona Ko to wallahi kashe kaina zanyi kowa ya Huta Tunda na zama Marar galihu"
Ya zaro mata jajayen Idanunshi.
"Idan kika sake faɗin zaki shiga Duniya ɓallaki zan na watsar ƙarewar Mari banza marar Tunani ke Kinsan meye shiga Duniyar? okey ga Duniyar Shiga da kanki zaki Kuka"
Ya faɗi yana zabga mata harara.
Durƙushewa tai a ƙasa tana cigaba da Kuka.
Allah yasa magariba tayi babu Kowa a gidan shima daga sallah ya dawo yaci karo da ita.
"Ki wuce Mu koma gida malama"
Ta ɗago.
"Tace sai dai na bar mata Gidanta in bazan Koma gidan Imran ba Kai ma inka takura Min akan na koma wallahi zaku rasani na kuma faɗi"
Ya zuba mata ido Duk ta ƙare ta rame sabida masifa ya fahimci akwai wata a ƙasa ba akan abin da ta gaya masa ɗazu taƙi Komawa amman baze takura mata akan sai ta gaya masa ba.
Umma wace Irin uwace wadda bata san darajar haihuwa ba ya faɗa a zuci yana kallon farfajiyar Gidan gabas Da yamma babu kowa .
"Wuce Muje mota"
Ya faɗi batare daya bata ƙofar Tambayarshi ba Haka ta Rungume Iman suka wuce motar shi daya barta a waje tun ɗazu.
Ta shiga Ciki ta zauna shima ya zauna a mazaunin Driver ya kunna motar ya Ɗauki hanyar barin Unguwar Titin janguza ya ɗauka direct Bokabo barrack ya Nufa gwara ya nesanta ta da Gidan Allah bashi ko iyayenta zasu san darajarta zai Musu wasa da hankali ze Ɓoyeta a inda aka sauke shi har sai zuwa lokacin da Umma zata gane Kurenta yafi son yaga Ummah tai nadama akan dukkan abin da tai ma ƴar tata. tazo tana nemanta idanu Rufe...........
Bari mu waiwaya baya domin Jin yaya tarihin waɗannan bayin Allah yake. Yana da kyau duk makarancin wannan littafi daya Nutsu ya duba wannan waiwaye don anan zai gane Kan labarin Nawa.
*WAIWAYE ADON TAFIYA*
Garin kano unguwar galadanchi.
Gidan Malam Abdallah makama mahaifi ga Ali makama ( Alhaji Baban su Ahmad ) Shu'aibu makama, ( Baba Babansu Amatullah ) Yusuf Makama ( Baffa Babansu Ameerah ) Bello makama ( kawu ) Muhammad Makama ( kawu ƙarami )
Waɗannan zaratan Ƴaƴa maza Su biyar cif sune ƴaƴa ga Malam Abdullahi Makama da Matarsa Hafsatu Ƴan asalin Jihar kano anan cikin Unguwar galadanci, wanda anan Gidan shi yake kuma anan gidan Iyayen shi yake da sauran ƴan uwan shi harma dana matar shi wadda take kusan ƴar uwace gare shi, Malam Makama ɗan kasuwane anan kasuwar Rimi yake saida kayan Koli Allah yasa ka mai albarka a kasuwancin Nashi wanda Har yakai da yana iya ɗaukar nauyin matarsa da ƴaƴansa Biyar waɗanda suka taso Cikin Nutsuwa da tarbiya ya sanya su a makarantar Boko data islamiyya wadda anan suka sami damar sauke alkur'ani mai girma Gaba ɗaya yaran nashi sun taso kusan kai ɗaya sabida haihuwar kwanika da Hafsatu keyi wadda tsiran kowanne da ɗan uwan shi shekara ɗaya ne daga ta yaye take samun Ciki wannan tasa yaran nata suka taso Kusan kansu ɗaya Ali shine ya soma gama karatun secondry wanda yana gamawa Mahaifin su Malam makama yaja shi kasuwa Allah ya sanyawa Ali nasibi a harkar kasuwancin Ƴar Rumfa Malam makama ya bashi ya zuba masa jari ya mallaka masa dan ya gane harkar ya tsaya da ƙafafun shi sai dai kafin shekara Ali ya dangana da siyan babban shago wanda anan yake saida Kowani irin nau'i na kayan kwalliyar mata Daɗin kasuwa ya hana shi Cigaba da karatu Sai Shu'aibu da su Yusufa ne suke karatun Bokon sosai Domin shu'aibu ma a lokacin har ya kammala secondry ya faɗa Buk yana karatun shi babu sanya.
Yusufa shine yake matakin ƙarshe a secondry.
Ganin yadda Allah ya buɗa ma Ali yasa Malam Makama ya Nema masa auren Ƴar abokin shi Malam Ahmad Modibo Bafulatanin jihar adamawa wanda zama ya kawo shi kano yana nan A galadanci yana sana'ar kayan Koli shima irinta Malam makama wannan tasa suka shaƙu suka zama aminan Juna Shi Malam Ahmad Modibo ƴaƴa mata gare shi har Guda Shidda bai da namiji Ko ɗaya Fatimah Bintu ita ce babba wadda ta kammala karatun ta na secondry tai saukar alkur'ani mai Girma sai sauran Ƙannen ta, Binta nada nutsuwa da haƙuri da kawaici bata da yawan magana sosai Gashi a lokacin ma hausa bata gama isarta ba Sabida agidansu basa hausa sai Fulatanci ita da Innarta da sauran ƙannenta da Baffanta Binta fara ce tas mai Kyawun gaske, Magana akai ta Gemu da Gemu wadda sai da suka tsaida Maganar aure sannan Malam makama ya cewa Ali yaje gidan abokinsa Malam Modibo ya amso saƙo, Koda yaje ashe Dubara yay masa irin ta manya anan suka gaisa da Malam Modibo kana ya turo masa Binta Kallo ɗaya Ali yayi mata yaji ta shiga ranshi Nan suka zanta a kunyace ya dawo Gida Da mahaifin shi ya tambaye shi kota yi masa a kunyace yace masa Eh.
An saka ranar aure shekara Guda wanda Hakan yasa Ali ya mayar da Himma wajan son ganin ya mallaki Muhallin kanshi da zasu zauna aciki hakan tasa yaje Unguwar Rijiyar Zaki Lokacin Duniya na kwance Komai na sauƙi cikin Kuɗi ƙalilan ya mallaki Filotai Biyar dan Burin shi ya zauna tare da ƴan uwanshi dan da harda su Malam makama ma zai saya Malam Ɗin yace Shi babu mai rabashi da galadanci Da murna Ali ya dawo Gida ya sami Su Shu'aibu ranar suna gida yake shaida Musu cewar yasai Musu Filoti zai ja babbar katanga Wadda zata zagayesu sai dai kowa ya Gina nashi da kanshi ranar Su shu'aibu sunyi Murna sosai haka Ali ya mayar da hankalin shi akan nashi Ginin wanda yake so kafin auren su da Binta ya tabbatar ya kammala Ginin nashi........
*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko uwargida ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*
BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
Leave a Comment