Bakon Lamari 4

 


*BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *004*


A hankali sautin ƙarar shigowar Motar shi cikin gidan ke kaɗa mata hanjin Cikinta, Daga cikin Ƙirjinta Kuwa dokawa yake da ƙarfi wanda In mutum yana kusa da ita tsaf zai ji sautin dokawar da Ƙirjin nata yake.


Tun Bayan fitar Ameerah daga gidan take zaune a falo ita ɗaya gaba ɗaya tsoron dawowar Imran gidan take wanda hakan ya zame mata al'adar Rayuwarta Koda yaushe In ya fita Tana cikin Raha da Nishaɗi amman da zarar Ya dawo to duk wani Ɓurɓushin Farin cikinta Gushe wa yake yi.


Tsayin watanni tara kenan da auran su da Imran amman har zuwa wannan lokaci ta Kasa samun farin ciki kamar ko wace mace acikin gidan Mijinta.


Curewa take a waje ɗaya tana haɗe jikinta tamkar mai jin sanyi, A hankali Taji sautin shigowar sa cikin Falon bada ban tayi da gaske bama da bazata ji sallamar tashi ba.


"Sannu da dawowa"


Ta faɗa masa kanta yana ƙasa.


Yayi mata banza kamar bada shi take magana ba.


"Amatullah"!

Ya kira sunanta a dake.


Ta ɗago tare da zuba masa Manyan Idanunta tana kallon shi kafin daga bisani tace masa.


"Na'am Yallaɓai"


Ya ɗan gyara tsaiwar shi yana soke Hannun shi a cikin aljihun wandon shi.


"Taso Muje gidan ku anwa baba aikin Idanu daga nan muje shoping"


Ya faɗi hakan yana wucewa ɗaki Minti biyar ya fito sanye da wasu kayan na daban.


Ta miƙe tana Ƙoƙarin gyara Hijabin Jikinta.


"A,a Je maza ki shafa Powder sannan ki ɗan saka wannan maiƙon naku na leɓe"


Sosai Abin ya bata mamaki amman sai ta wuce taje tayi yadda yace Ɗin daga bisani ta dawo Har ya wuce waje abin mamaki ba wannan Motar daya Shigar da ita gida ya Shiga ba ashe akwai wata a waje mai kyau sabuwa ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ta zauna Yaja suka hau Titin Rijiyar Zaki inda anan layin Rumfar shehu gidan su yake.


Sai da ya tsaya a wani Store yasai kayan abinci aka shigar dasu Motar sannan ya shigo suka ja Suna tafiya ita bata ce mai ba shi bai ce mata ba har suka ƙarasa layin.


A bakin Ƙofar Gida Yay parking bata jira shiba ta ɓalle murfin ta fita wajan ƙatuwar tabarmar Su Alhaji Babba ta ƙarasa wanda Suke zaune suna shan Iska sallama tayi agaban su ta tsugunna tana gaishe dasu.


Kafin Imran ya ƙaraso shima ya tsugunna yana gaishe dasu.


Cikin Jin daɗi Alhaji Babba yace.


"Ma sha Allah! Amatullah kece da wannan Lokaci barka barka da zuwa naji daɗin Ganin ki Allah ya ƙara zaunar mana dake lafiya, Koke fa da kika kwantar da hankalin ki"


Aranta tace Alhaji ba zaku gane yaran ba, Nidai zan cigaba da haƙuri.


Amman a fili sai tace.


"Nagode Alhaji"


Nasiha sauran ƴan uwan mahaifin nata sukai mata kafin ta miƙe tabar wajan ta nufi Cikin gida.


Babban Gida mai sassa da dama acikin sa wanda ya haɗe ƴaƴa da jikoki sashin su ta shiga da sallama a bakin ta.


Umma tana zaune tana bawa Baba ayaba a bakin shi ta ɗago cikin sakin fuska take amsa wa Amatullah Sallama.


"Kece da wannan daran dafatan dai lafiya?"


Amatullah ta dubi Ummah da mamaki sannan tace.

"Tare dashi muke yace ne nazo na duba Jikin Baba"


Bata kai ma da rufe bakinta ba Umma ta miƙe tsaye tare da Nufar Ƙofar Gida da sauri Amatullah ta riƙe Hannun Ummah tana gyaɗa mata kanta.


"Ummah yanzu fa zai shigo Gidan Dan Allah ki Koma ki zauna"

Ta Doke hannun Amatullah tana cewa.


"Cikani Dan ubanki so kike Su hure masa kunne a waje ko? Su roƙe mashi Kuɗi a banza"


Amatullahi ta sunkuyar da kanta cikin takaicin Halin Ummanta batace Mata komai ba Umman na ƙoƙarin Fita Imran ɗin ya shigo.


Sosa kai Umma tayi tare da cewa.


"Lale maraba da zuwan ka Imirana daman yanzu take cewa tare kuke"


Ya zauna a saman dardumar daya gani a shinfiɗe cikin jin kunya yake cewa.


"Eh Muna tare dasu Alhaji ne muna gaisawa"

A take ilahirin annurin fuskar Umma ya ɗauke dan bata ƙaunar wani ya raɓi surukin nata bare yaci arziƙin sa.


Tana ƙoƙarin yin magana ƙannen Amatullahi Hassan da Hussaini suka soma shigo da kayan abincin daya siya a hanya Bakin Ummah kamar Gonar auduga.


Sai albarka take shiwa Imran wanda yake ta sakin murmushi mai tarin ma'anoni da yawa.


Sam Ummah bata tambayi Amatullahi yaya zaman su da Mijinta ba bare ta jata ajiki ta shigar da ita ɗaki su ɗan zanta irin na ɗa da mahaifi sai ma mayar da hankalinta kan Imran datai suna ta hira.


Ganin Haka yasa Amatullahi taja Jikinta zuwa wajan Babanta wanda yake kwance.


Ta ƙarasa wajansa ta zauna tana kallon shi shekara Kusan Biyar yana kwance ga matsalar ƙafafu da basa takawa ga matsalar Idanu damma yau an masa aikin Idon wanda aka sanya masa glass a idanun nashi ba wani tsufa yayi ba, Amman lalura ta saka girma ya hau masa da wuri.


"Sannu baba Allah ya baka lafiya"


Jin Muryar ƴar tasa, a kusa dashi yasa ya kama hannunta yana cewa.


"Amatuna kece a gidan?"


Ta ƙaƙalo murmushin dole kana tace masa.

"Baba tun Ummah na baka ayaba nai sallama baka ji bane?"

Yayi murmushi yana cewa.

"Banji ba Amatuna, Kinga mijin ki ɗan albarka ya biya min kuɗin aikin idanu yanzu Ganin ba kamar da ba"


Tayi murmushi tana cewa.


"Damma yau akai amman nan da kwana biyu ma zaka fi haka gani, Nina ɗauka ma kana asibiti Allah dai ya sawaƙe"


Baba yace.


"Ai Amatuna baki ga  asibitin ba, na masu hannu da shuni ne, Daga an maka aikin kai ƴan awanni zasu sallame ka"

Amatullah tace.


"Baba Allah yasa an yi a sa'a Amin"


Baba ya kuma karkatowa ya dube ta.


"Amatuna mijin ki yaron kirki ne, Ki haƙuri ki zaman ki agidan ki, Allah ya ƙara muku zaman lafiya"

Gabanta ya faɗi Imran ya siye baba kenan da idan tazo gida da maganar zaman auren ta baba yana ƙoƙarin fahimtarta to shima yau Ga shi nan yana yabon Imran fiye da zaton ta.


Hawaye masu zafi suka Zubo mata a saman Kuncin ta bata bar kowa ya gani ba ta share su, Ta sunkuyar da kanta Baba ya cigaba da yi mata Nasiha mai ratsa Jiki.


Har wajan taran dare suna Gidan Kafin ta miƙe tace wa Ummah zata Leƙa sashin Matan Kawun nan ta su gaisa.


Ta Dubi Nana ƙanwarta wadda Daman su biyu ne mata ita da Nana sai Ƴan Biyu maza dake binta, Nana take bi musu, Tace mata tazo ta rakata Ɓarin su Ameerah su gaisa da sauran sashin Nana ta Tura baki tana cewa.


"Ni bana shiga sai kin dawo"


Ga Mamakin Amatullah Ummah batai wa Nana magana ba, Sai ma kuma jan hirar da tayi da Imran kamar ba surukinta ba.


Amatullah ta yi waje tana Jinjina halin ummanta na son abin duniya wanda shine jagora ga halin Ummah na farko.


Sashin Su Ameerah ta soma zuwa sukai gaisa da Anty babar su Ameerah sama sama.


Ta fito Ameerah ce ta rakata Sauran sassan ƙannan mahaifinta Guda Huɗu, Sannan suka Nufi sashin Su Yaya Ahmad wanda shine na farko ma daga ka shiga Gidan.


Mamaki sosai Amatullahi tayi yadda taga an ƙere sashin kamar ba'a cikin Gidanba ga hasken ƙwan sola kota Ina bata sha mamaki ba sai da ta shiga falon Mama wanda yaci uban saitin Kujeru masu kyau ga ƙatuwar Tv sai faman aiki take Iskar fanka kota ina.


Sallama sukai Ƙannen shi ƴammata Su Biyu Waɗanda basuyi aure ba  suka amsa musu cikin sakin fuska Zama sukai a ɗaya daga cikin kujerun Sannan Surayyah autar su ta nufi Bedroom ta gayawa Mama.


Minti kaɗan Mama ta fito Cikin wata dakakkiyar shadda tana tafe tana taƙama.

A ran Amatullah tace ashe har yau Izzar tana nan.


Ba yabo babu fallasa suka gaisa sannan suka baro sashin wanda Naja'atu ƙanwar shi wadda suke sa'anni ta rakosu hanya.


Anan suka haɗu da Ƙanin Ahmad Kamal suka gaisa yana ƙoƙarin Shiga ɗakin shi.


Sai da su Ameerah da Naja suka rakata har bakin sashin su, sannan suka koma Ɓangarorin su.


Koda ta koma ma Imran har ya miƙe suna sallama da Ummah wanda ya ɗauko damin Kuɗi ya bata ta saka hannu ta amsa Jikinta har yana Ɓari Takaici Baƙin ciki sune suka wa Amatullah ca a zuciyarta.


Haka suka Nufi Mota yaja suka tafi ya biya Ta wani super market yayi mata uwar siyayyah.


Sannan suka wuce Gida.


Wanka tayi bayan ta shigar da siyayyar tata.


Kana ta koma Ɗakinta ta saka kayan bacci ta kwanta bayan ta kashe ƙwai.


A hankali Imran ya shigo ɗakin Jikinsa sanye da Guntun wando da singlet ya raɓa Jikinta ya kwanta aran shi yana ayyana tabbas Yau Burin sa zai cika Tabbas sai ya fitar da maitar shi ta san Neman ta tabayan ta.


A hankali ya haɗe jikinsa da nata yana shafo mazaunanta ta baya yana fitar da wani Irin nishi.


Cikin Baccin daya kwasheta taji yana shafa mata jikinta.


Tsoro fargaba tashin hankali sune suka dirar mata a zuciyarta mai Imran yake Nufi tsayin wata tara tana rayuwar gidan shi bai taɓa kusantarta ba sai sau ɗaya Tun daran farkon su, Kullum burin shi ya nemeta ta bayanta Allah bai bashi Iko ba shine yau ya ritsa ta a wannan daran zai ƙara far mata Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un rana zafi Inuwa Ƙuna ta faɗa a ranta kafin da sauri kuma ta Miƙe zaune........

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*








*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.