Bakon Lamari 5

 


*BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *005*


Gumi duk ya wanke mata jikinta duk da sanyin fankar dake kaɗawa acikin ɗakin.


Muryarta a dashe irin ta mai bacci ta dube shi tana mai zare manyan idanuwanta tace masa.

"Imran meye haka dan Allah ka rabu dani, nace dan Allah ka rabu dani wallahi Allah koda duniya zaka bani bazan taɓa Kaucewa Umarnin Ubangijina akan taka buƙatar ba"


Batai aune ba taji saukar Danshin bakinsa cikin nata wanda shine ya dakatar da ita daga ƙarashe maganar data keyi a haukace yake yamutsa Dukkan sassan Jikinta yana ƙara ribatarta zuwa Cimma muradin Zuciyar sa


Wani tsallan albarka tayi tare da bangaje shi tayi hanyar falo har Rigar Jikinta na zamewa ta faɗi ƙasa.

A haukace ya bita yana cewa


"Dan matsiyatan iyayenki yau babu mai rabani da ke sai Allah, an gaya miki a banza zan ke, kashewa iyayen ki kuɗi to maitar Biyan buƙatar kaina ita ke ingizani zuwa ga aikata koma meye akan mayun iyayen ki, wallahi Tun ranar dana fara ɗora idanuna a bayanki naji ina maitar Jin ɗanɗanon shi"

Ya faɗi a lokacin daya cimmata ya saka ƙafa ya taɗeta ta maku a ƙasan tiles.

Wata ƙara ta saki kafin Numfashinta ya ɗauke tsaf sai kuma Jini ya soma biyowa ta ƙafafunta.


Wanda ganin wannan yawan Jini shiya tsorata Imran yayi saurin ɗauko jallabiyar shi ya sanya ita ma ya zira mata riga da hijabi, ya ɗagata cak sukai mota ya shiga mazaunin driver yaja motar suka Nufi Asibitin kuɗi mafi kusa dasu.


Lokacin da suka ƙarasa ƙarfe Ɗayan dare amman kaman rana sai karɓar marasa lafiya ake, Abin ka da asibitin Kuɗi.

Duk wani cuku cuku yayi nan da nan aka sakata a emergency room wanda Babban likitan asibitin ya duƙufa akanta dan Ceto rayuwarta har asuba Likitan yana tare da Amatullah wadda take a tsakanin Rai kokai Mutu kokai Inji bahaushe.


Likitan ya fita yayi sallah a hanya suka haɗu da Imran wanda har ya Ɗan faɗa sabida fargabar Kada Amatullah ta rasu bai sami cikakkiyar amsa wajan likitan ba.


Sabida haka ya raɓe jikin motar shi, Shikuma likitan ya koma bakin daga.


Wayar shi ya ciro ya kira Umman Amatullah.

Idar da sallar Ummah kenan taji kiran wayarta Nana ta ɗauko mata tana ce mata Yaya Imran ne Mijin Anty.


Jikin Ummah yana rawa ta ɗaga bayan sun gaisa Imran ya sosa kai cike da makirci yace wa Ummah.


"Ummah Muna asibiti fa tun  Jiya Amatullah ta faɗi take zubar Jini"


Salati Ummah ta saki tana cewa wani asibitinne gata nan bara ta gyarawa Baba jikinsa ta fito ta barwa Nana girkin Gidan.


Kwatance yayi mata sannan ya ƙara yin ƙasa da murya sosai yana cewa.


"Ummah ina ganin kamar na haƙura da Auren Amatullahi, Ummah tunda mukai aure sau ɗaya kaɗai ta bani haƙƙina Kullum nazo mata da buƙata sai Munyi dambe ganin bata so nake haƙura dan kawai Jiya nace ta tausayamin ta bani shine ta ɗauki wuƙa tace Koni ko ita to a garin na karɓi wuƙar ne yasa ta faɗi Jini ya ɓalle mata"


Yakai maganar yana dariya ta yadda Ummah ba zata ji ba.


Ummah ta kuma jan salati tana tafa Hannu tana cewa.


"Haka tai maka Imirana To bara nazo dan ubanta Shegiyar yarinya mai ƙashin tsiya tafi son na dauwa ma acikin gadarar faccaloli to wallahi ta kaso auren ta badai wannan gidan ba sai dai ta nemi wani Gidan Uban"


Imran dariya yake har yana ƙwalla Tunda yake bai taɓa ganin mayyar Kuɗi kamar surukar tashi ba haka ya kashe wayar yana ƙarasawa cikin asibitin.


Nurse ce tazo ta kira shi akan Likitan nasan ganin shi bayan ya shiga Office ɗin Likitan suka kuma gaisawa sannan Likitan ya tura masa takarda gaban shi yana mai cewa.


"Muna son ka saka hannu nan da Awa Uku za'a mata C'S don a ceci rayuwarta ita da Bebyn ta don faɗuwar data yi Jiya ya haddasa wa ɗan da ke cikinta juyawa ya koma wani ɓarin Mun samu mun dakatar da zubar Jinin da take yanzu kawai Hannu zaka saka a mata aiki A rabata da Abin da ke cikinta Duk da cikin yana wata takwas ne da kwana bakwai"


Har Likitan ya gama maganar Imran bai iya motsi mai kyau ba Ta yaya tai Ciki har ya isa haihuwa bai sani ba daga kusantarta sau ɗaya shine har zata ɗauki ciki kamar wata akuya.


"Ranka ya daɗe kabar takarda a gabanka kuma kaƙi magana"

Muryar likitan ta katse masa tunanin sa.


"Nifa likita ban gane inda ka dosa ba, wai anyi gabas da kare, yarinyar nan sau ɗaya tak na kusanceta a wata taran data yi agidana sannan kawai a wani zo ace zata haihu ni gaskiya bazan wani saka hannu ba ta Mutu kawai dan ni a yanzu bana buƙatar Wani ɗa a rayuwata"

Likitan ya dubi Imran sanda ya ƙarasa maganar Cikin gadara.


"Amman kai kam musulmi ne?"

Cewar Likitan.


Imran ya juyo a fusace zai magana likitan ya ɗaga masa hannu cikin zafin rai yace.


"To in kai jahili ne kaje kabi malamai akan Halaccin wannan cikin gare ka Yau inda baka taɓa kusantarta bane za'a ce ɗan na waje ne, amman Kai da bakinka ka bada shaidar ka kusanci matarka sau ɗaya, ka sani ko tun a daran Allah ya saka ƙwan haihuwar ka cikin mahaifarta,Wannan ɗa naka ne kuma koda baka saka hannu ba ni da kaina wallahi sai na saka sannan nai mata aikin bayan nan kuma na maka ka a kotun musulunci akan kana barazanar kashe matarka da ɗanka akwai CC camera a office ɗinnan duk maganar da mukai tana naɗe dakai wawa"


Jin Kotu yasa jikin Imran ya hau rawa don a wajan cike file har Hotonsa sai da ya saka yasan babu damar Guduwa sabida akwai cikakken bayanin shi da kwatancen sa a Files ɗin daya buɗe a cikin asibitin.


"Zan saka amman Ciki kamar na aljanu ba laulayi babu girma ni a iya zamana da ita babu ta yadda na gane Tana da ciki"


Likitan yace.

"Allah ne yaso ɗan ko ƴar su taka ƙasa shine yasa ya ɓoye sanin ka da jinka da ganinka akan cikin nata"


Daga haka Imran ya saka hannu ran shi a Matiƙar ɓace ya zama dole ya Ɓoye haihuwar nan sabida kada Uban gidan shi yaji wanda Ya nuna masa harkar da yake a yanzu wanda sai da sukai yarjejeniya akan babu batun kusantar Mace ta gabanta har abada sai ta bayanta............


Yana fita daga Office Ɗin yaci karo da Ummah wadda Ko Kallon arziƙi bata samu wajan Imran ba sai ma wuce tan da yayi ya nufi motar shi ya zauna aciki yana saƙa wasiƙar Jaki na yadda zai salwantar da Amatullah da Ɗan da zata haifa sabida Gudun tonuwar asirinsa a wajan uban ɗakin sa wanda ya mayar dashi kamar matar shi( wa'iyazubillah )


Ummah kuwa Babu abin da take aranta sai zagin amatullah sabida zatonta maganar Ɗazu ce na bijire masan da Amatullah keyi ya saka yaƙi mata magana, Sam Ummah bata ta lafiyar ƴarta sai ta jimamin kada ran Imran ya ɓaci ya sako mata Amatullah suka samu suga rashi.


Cikin Aminci da Yardar Ubangiji akaiwa Amatullah aikin wanda aka samu nasarar Ciro mata Yarinyar ta mai kyau kamar su ɗaya sak da imran sai dai kawai farar fatar uwar ta data ɗauko amman kama kam kamar ka tsaga kara da Imran.


Bayan an gyara yarinyar wadda ko kayan haihuwa babu Sai Likitan ne yacewa Nurse su samo tawul a naɗeta bayan an naɗe ƴar an yanke mata cibi sai akaiwa Amatullah allura aka aje mata yarinyarta a gabanta Likitan yace a barta ta huta har allurar ta saketa.

Koda da nurse ta leƙa waje don sanar da Imran bata ganshi ba kuma bata san Ummah ba sabida haka ta koma ta kuma gyara wa yarinyar kwanciya sannan ta rufo musu ƙofar........

*Wannan salon na da banne kuma ban taɓa zuwa da irin shi a rubutu na ba mai kike jira ki hanzarta biyan naki dan tuni masu biya sun yi nisa labarin ko rabi bamu shiga ba yanzu ma aka fara*

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*








*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.