Bakon Lamari 8
*BAƘON LAMARI...!*🌹
{ Eternal love }
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*008*
A razane Amatullahi Ta ɗago tana kallon Imran wanda ya tsaya akanta yana Huci tamkar kumurcin maciji Ƙamƙame Iman tayi ajikinta wanda nan da nan jikin nata ya ɗauki Ɓari tana mai bin Imran da kallo Ruwan hawaye yana Ta wanke mata fuskarta.
Ya dube ta a wulaƙance tare da ƙara taku Biyu a gabanta sannan yaja ya tsaya.
"Kije gidan iyayen ki, Ni bazan sake kiba Kuma bazan dawo dake gidana ba haka zan jinginar dake da aure na akanki har ki koma ga Allah! ta yadda wani baze taɓa Neman auren ki ba, Nayi alƙwari kamar yadda kika ƙi aminta da buƙata ta Nima haka bazan taɓa bada takardar sakin ki ba Kije kita zama a kusa da wannan shegiyar kwaɗayayyar uwar taki mai kama da Mayu"
Kuka! ne mai ƙarfi ya ƙwace mata yi take ta ƙi dai na shi bakinta yayi nauyi bata da wata kalma da zata iya furtawa.
"Kuka yanzu kika soma so nake na bar Muku darasi a rayuwarku, dake da mahaifiyar ki da mahaifinki ina son Ku ɗanɗana baƙin ciki da Ƙuncin rayuwa na har abada bana muku fatan samun sassauci"
Ta ɗago da sauri Muryarta duk ta dashe tace masa.
"Imran tsakanina dakai sai sakayyar Allah tunda nake auren ka ban taɓa samun farin ciki ba kai Min ciki na haihu batare daka Nunan wani daga cikin dangin kaba, Rabon dana san wani naka tun a neman aure na, sannan kazo kace naje gida ba tare da shaidar saki ba Nan gaba idan ƴata ta tashi wa zan nuna mata a matsayin mahaifinta Ni kenan a haka zan cigaba da rayuwa ta cikin Ƙunci? dan kawai na bijirewa saɓon Allah In sha Allah Imran ƙarshen ka baze yi kyau ba"
Ta ƙarasa maganar cikin Kuka!
Dariya mai ƙarfi ya saki wadda ta sanya Iman farkawa da wani gigitaccen Kuka wanda ta ke yin sa da iya kacin ƙarfin ta Amatullah bata da zaɓin daya wuce itama fashewa da kukan.
Wannan wace irin rayuwa ce wannan wace irin ƙaddara ce ke bibiyar rayuwarta tabbas idan Haƙƙin wanda ka zalunta haka yake saurin Bibiyar bawa da anrage Cin Amana a duniya.
"Na baki mintuna Goma idan har na dawo na tarar dake a gidana tabbas zan sauya Miki kalar halittarki da yadda idan kinje gida mahaifan ki ba Zasu gane kiba"
Ya faɗa a gadarance yana mai Juyawa yabar ɗakin da mugun sauri.
A garin saurin miƙewa daga wajan yasa Ta yarda Iman a ƙasa wadda ta kuma canyarewa da kuka kamar wadda ake Mintsini Abu goma da ashirin ya haɗar mata Nan da nan jikinta yahau rawa kaya kala Huɗu ta ɗauka Sai ƴan kayan Iman haka ta fita daga ɗakin tana share hawayenta a garin Ta goya Iman ma ta kuma Faɗuwa yarinyar sabida rashin sabon goyon da bata saba ba
A daren ta fita daga Unguwar ga hannunta babu ko sisi tafiya kawai take a ƙafa ga Uban Hadarin daya haɗo sai faman iska ake Titi duka sahu ya ɗauke Tana zuwa daidai Rijiyar zaki layin Muhalli aka tsuge da ruwa wanda kafin ta ƙarasa Gida Ruwan yayi musu duka ita da Iman Lokacin da taje layin su kuwa dare yayi sosai dan an rufe Ƙofa haka ta saka Dutse tahau dukan Ƙofar wanda ta jima tana Duka kafin taji Muryar Alhaji babba yana cewa.
"Wanene ke Bugu haka lafiya?"
Cikin rawar ɗari tace.
"Nice Amatullahi Alhaji"
Da sauri Alhaji ya zare sakatar Ƙofar yana haskata da Tourch light.
"Subuhanallahi Amatullah da wannan dare kusan ƙarfe ɗaya lafiya dai?"
Fashe masa da kuka tayi tana cewa.
"Alhaji Imran ne yace na tawo gida"
Alhaji yayi jim kafin yace.
"To gashi kuma Babarki bata Nuna mana dangin sa ba bare Gobe koni naje wajan iyayen nashi, ai daman shashanci ne Da nuna mu bamu isaba da Hadiza tayi taje danginta suka ɗaura Miki aure sama taka sabida taga kuɗi to gashinan tun yanzu an haifi ɗan da babu idanu"
Kuka! ne ya kuma ƙwace mata duk da Ummah mahaifiyarta ce amman ta cuceta cuta mafi Muni arayuwa yau ga ranar nadama tazo mata.
Maganar Alhaji ce ta kuma katse mata kukan.
"Saboda taga ɗan uwanmu bashi da lafiya alokacin yana kwance tagama ɗibar mana albarka tai gaban kanta kamar ke ɗin ƴar mace ce sannan Kuma tazo ta Bimu da zage zage da Cin zarafi duka to yanzu gashi nan wa gari ya waya?"
Amatullah tace.
"Ni Alhaji sabida Ummah har tafi son Imran akaina nima alokacin duk yadda naso na fahimtar da ita illar Hakan taƙi daga ƙarshe tace zata tsinen In ban bi umarnin taba to Alhaji yaya zanyi? ƴan uwanta suna jin tsoron gaya mata gaskiya kaikuma da kake babba acikin mahaifan mu bata ga girman kaba, Alhaji dukkan abubuwan danai a wancan Lokacin wallahi ba laifi na bane ummah ce ta mini barazanar tsinuwa"
Tsananin tausayin yarinyar ya kama Alhaji babba lallai dace da iyaye nagari sune tushen samuwar al'ummah ta gari Yarinya ƙarama Hadiza nason jefa rayuwarta Cikin garari yanzu meye amfanin auren? ko shekara ba'aiba ta haihu gashi kuma Miji ya korota batare da ansan taka maiman Iyayen shiba bare aje a neme su.
"Wuce gida Allah ya kawo mana mafita"
Ya faɗa mata hakan da tausayawa.
A raɓe ta shiga sashin su ta tura ƙofa tai sallama da yake lokacin ruwa ya ɗan tsagaita yasa Ummah dake zaune tana wa Baba firfita tace.
"Waye ne?"
Amatullah ta bankaɗa labule ta shiga cikin ɗakin tana mai cewa.
"Ummah nice"
A zabure ta ɗago tana cewa.
"Daga ina? a wannan dare kar dai kice Kin kaso auren ki munafuka? daman Imran ya gayan duk irin baƙin halin da kike masa har kina hana shi halal ɗinsa to wallahi inma auren ki kika kaso ba'a.........
Da sauri baba yace.
"Hadiza kada ki rantse dan ba gidan ki bane gidana ne kada kika ina kwance kice zaki ciwa ƴata Mutunci inke bakya son ta ni ina son kayata"
Kuka Ummah tasaka tana cewa.
"Sha'aibu ni zaka gayawa haka akan Amatullah? shekara nawa kana naɗe ina hidimar ka kai kashi na kwashe kai fitsari na kwashe sannan kazo kana mani wasu maganganu Wanda ƴaƴan naka kawai haihuwar su kai mai ka sani nasu? shine dan ta kaso aurenta a inda nake dandalar arziƙi zaka Min maganar banza"
Da sauri Amatullah ta zaro ido tana kallon Umma wace irin mace ce Ummah ta manta sanda Baba keda Kuɗi yake musu Komai dan Allah ya jarabce shi shine har zata na waɗannan maganganu lallai rayuwa babu tabbas.
Shima baba a fusace yace mata.
"Daga yau ki daina dukkan abin da kike min Kiga idan Allah baze Mini ba, Kinga yarinya cikin dare babu ba'asin komai Kinzo kina mata faɗa akan wasu maganganu can na son zuciya daya gaya Miki Hadiza kada ki fusatani fa ko waccen Lokacin da kikai gaban kanki dan bani da lafiya ne ban san inda kaina yake ba"
Baba ya faɗa a matiƙar fusata.
Ummah tace.
"Oho dai kaima ai kaci arziƙin auren nata bada ban Mijin nata ba da tuni kana kwance kai ba gawa ba kai ba mai rai ba kuma ke buɗe kunnen ki kijini da kyau"
Ta faɗa da ƙarfi tana kallon Amatullah..........
*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko uwargida ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*
BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
Leave a Comment