Bamagujiya Complete Hausa Novel
*PAGE 1
★★★~~~★★★~~~★★★
“Bibo! Bibo!! Jummala wai ina Bibo ne nifa gsky na fara kosawa da abinda takeyi Mana Kullum zamuje gurin bauta saita makarar damu karshe ma tace bazata ba Jummah
idan bazata rinka zuwa ba ta fadamin na daina wahalar da kaina"Fitowa tayi daga dakin kasar da take ciki tace “Kincika korafi lantai Nifa bawai gurin bauta ne banson zuwa ba samarin garin nan ne suke takurani amma yau naji inason zuwa da alamun addu'a ta zata karbu gurin uwa me tsarki"
Jerawa sukayi kowacce dauke da yar salkarta ta ruwa suna tafe suna taɗinsu suna dariya, Lantai da Ladiyo da Innu sune suke ta shewarsu itakam Bibo hankalinta yabar garesu kamar yanda ta saba ji idan sun tunkaro wajen bautar yauma hakan ta rinƙa ji gabanta na faduwa zuciyarta na harbawa da ƙarfin da takasa sanin dalilinsa.
Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka dubi juna Lantai tace “Bibo yau ranar zagayowar haihuwar ki saboda haka ranar ta zama takice me daraja saboda haka kece zaki jibanci lamuranmu zuwa ga mika bukatunmu ga uwa me tsarki"
Lumshe dara²n idanunta tayi ta buɗesu tare da karyar dakai suka fara hawa saman Tsaunin gawo wanda wannan Tsaunin shine ya samar da asalin sunan wannan ɗan karamin kauye me dauke da albarkatu birjir a cikinsa kama daga ma'adanan ƙarƙashin ƙasa dake da jiɓi da manyan duwatsun da sukayiwa ƙauyen ƙawanya da kuma albarkar noma data samu tushe da tushiya tun kaka da kakanni da kuma albarkar ruwa wanda yake kewaye da manyan duwatsun da suka zagaye garin,
Wannan tasa al'ummar wannan ƙauye suke rayuwa cikin wadatar buwayi gagara misali. Al'ummar Kauyen Tsaunin gawo sun kasance Asalin Hausawa na fil azal marasa sallah wato waɗanda ake kira maguzawa, asalin kakanninsu suna rayuwa a saman wannan tsauni da ake kira Tsaunin gawo wanda ya kasance shine tushensu.
Mazansu da matansu yaransu da manyansu sun kasance suna bautawa wani dutse ne a saman wannan tsauni da suke kira Uwa me tsarki.
Shi wannan abin bauta tasu ya kasance wani mulmulallen dutsene da yake tsaye cikin hukuncin Ubangiji saman wani babban dutse kamar dai ka ajiye kwai kwaya ɗaya saman faifai.
Asali ba wannan ne yaja ra'ayinsu wa bautawa wannan dutse ba face ya kasance wannan dutse Ubangiji ya gina shi kamar ganga in ka sanya hannunka ka daki dutsen zakajishi da tauri ko kara bayayi amma idan kasami itaciya ko dutse ka buge shi dashi sai kaji yana baka wani sauti me zaƙi da daukar hankali kamar dai kana kada ganga haka zakaji sautin na tashi ya cika dukkannin dajin da wannan tsauni yake.
Ba iyanan bane abin ya tsaya a gefe da gefen wannan dutsen bauta akwai wasu dogayen massu guda biyu da suka kangeshi daga gangagewa idan iska ta busa, kuma su wadannan massu duk wata canza kala suke yi batare da kowa yasan lkc da sa'o'in da yake canzawa ba sannan ta saman su tsinin mashin kenan yana fesar da ruwa a kowanne lkc yana gangarawa kasa yana haɗewa da wani babban kogi da suke kira kogin wankin zunubi, shi wannan kogi aikinsa na zuwa ne a duk lokacin da wani ko wata ya aikata wani aiki da wannan al'umma take dauka na tur ne da Allah wadarai.
To a wannan lokacin ne za'a kama mutum a daure shi da sarkoki ajashi a ƙasa a kaishi a jefashi wannan kogi a tafi a barsa idan yayi kwanaki uku za'a dawo a dauki gawarsa to wannan shine yake nuna ya mutu salihin bawa domin sunada tabbacin uwa me tsarki ta yafe masa shiyasa ta karɓi rayuwarsa, idan kuma ba'a ga gawar mutum ba to wannan yake tabbatar da cewa wannan bai samu yafiya daga uwa me tsarki ba.
*****
Isa sukayi gaban abin bautar suka dunkule hannayensu tare da lumshe idanunsu suna karanto wasu addu'o'i da su kadai suka san meye suke cewa,
Tsayin lkc a haka sannan suka buɗe idanunsu Wacce suka kira da Bibo ta durƙushe saman gwiwowinta ta kika hannunta tafin yana kallon sama ta ɗora kanta samansa dogon gashinta ya bazo ya rufe mata fuskarta gabadaya bata damu da gyarawa ba domin tayi imanin a gaban majiɓinciyar lamuranta take,
Cikin siririyar muryarta me kama da busar sarewa tace “Mun kasance masu biyayya a gareki da gujewa saɓa Miki ya abar bauta meye yasa kullum nake kawo kukana gurinki baki sharemin hawayena Jimo Ciwake ya kasance me yawan ziyartarki da hidimtawa gareki, yau gashi can cikin halin jinya baya iya gane kowa da komi saidai ayi masa komai.
Yake wannan Uwa me tsarki idan har kin tabbata abar nufi da bukata to a matsayina na wacce bantaɓa aikata zunubi ba ina nemawa mahaifina lfy da amincewark....."
Da sauri dukkansu suka dago lkcn da ƙarar faduwar wani abu me karamin sauti ta ziyarci dodon kunnensu suka zubawa sashin da sukaji motsin idanu tare da miƙewa a tare saboda ganin baƙin halittun da suke takowa daga nesa dasu.
Turawa ne su uku sai wasu baƙin fata biyu samari, Ja suka fara yi da baya suma wadannan baki suka tsaya suna kallon kallo can Lantai tace “la ashe idan mutum yana mafarki gani shikayi uwa me tsarki jiya nayi mafarki naga fararen kwaɗi ashe turawa zan gani" yanda tayi mgnr ya Bama daya cikin bakaken fatar nishaɗi har Saida ya dara inda shi kuma dayan hankalinsa ke kan Bibo da ta sunkuyar da kanta ko dagowa batayi yana mata wani kallo na sama da ƙasa zuciyarsa na bugawa da ƙarfi hakanan yaji ruhinsa ya kwaɗaitu da son ganin fuskarta.
Ɗaya cikin turawan ne ya dubi abokan tafiyarsa yace “ ma iya tafiya ko?" Cikin harshen nasara yayi mgnr, inda wanda aka kalla ɗin yayi firgigit ya dawo hayyacinsa yayi gaba, suka rufa masa baya har zuwa lkcn idanun Bibo na ƙasa Saida ta fahimci sunyi nisa sannan ta dago idanunta tabi inda suka bi da kallo karaf idanunta ya faɗa cikin na dayan cikin bakaken hakan ya haddasa masa tsayawar da bai shirya ba zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yace “Hasbinallahu wa ni'imal wakil........"
Tashin hankali wanda baasa masa rana jin kalamin wannan mutumin yasa Bibo saurin watsa sumarta baya ta zari kallabinta ta zuwa takalmanta ta nemi hanyar tsira da mugun gudu hakanan suma su Lantai suka rufa mata baya.
Sunaji wadannan baƙi na kiransu amma tsoro da tashin hankali ya hanasu juyowa saima ƙarawa gudun su ƙaimi da suke yi.
Baƙuwar kalmar tayi mugun firgita su karma Bibo Sarkin tsoro taji lbr musamman data tuna sanadin haɗa idanunsu ne yasa shi yin wannan furuci, to me yake nufi? Kodai tsorata yayi da ganin fuskarta kamar yanda da yawan mazan ƙauyensu suke faɗa? Ko kuma dai wannan kalmar ɗin waƙe ne a gareshi?
Batada amsa har suka isa cikin garin basu dakata da gudun ceton ran da suke yi ba inda suka bar waɗannan baƙi da mamaki gami da dariyar yanda suka razana da ganinsu amma banda wannan matashin mai furuci shi a bangarensa zuciyarsa ce tayi masa nauyi tsoro ya mamaye ruhinsa tunani barkatai suka cika masa kansa kardai ya tabbata duk abinda ya gani cikin mafarkinsa saiya zama gaske yayi mafarki zaije wani ƙauye na marasa addini kuma abubuwa da yawa sun faru ciki harda wannan fuskar daya gani yau a saman Tsaunin gawo wadda a lissafin falsafar mafarkinsa itace ƙaddararsa ta zuwa wannan ƙauye.......
“Meye ma'anar hakan?" Ya furta lkcn da suke isa ga dutsen da suka zo bincike akansa.... Duba na tsanaki Najeeb abokin tafiyarsa yayi masa “sauyin yanayi cikin ƙanƙanin lkc Abokina meye ne yake faruwa na lura daga kallon fuskar wannan ƴar maguzawan komanka ya canza anya ba gamo mukayi garin kurɗe kurɗenmu na masifa ba?"
Haɗiye wani ɗaci yayi a maƙwallatonsa ya furzar da iska ta bakinsa ya saita injin narkakakun idanunsa masu zubawa abin kallo kasala kan Najeeb yaja numfashi yace.
“Ba gamo mukayi ba Sarkin Gida ita ce ƙaddarata......" Da sauri ya kalleshi yace “Bamagujiyar Prince Habeeb meye haɗinka da BAMAGUJIYA da har zata zama ƙaddara?" Yarfa hannu yayi cikin halinsa na ko in kula yace “shine nima bansani ba Sarkin Gida gabana yana faduwa zan bar dajin nan na koma cikin gari kuyi duk abinda ya dace"
[3/27, 10:12 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
Leave a Comment