Daudar Gora Book 1 page 21
*_21_*
...........“Ina kan ƙoƙarin yin hakan yawaitar kiranyanki ya katse ni, amma tabbas wanda ya aikata yana a cikin wannan daula ne, yana kuma da babban shirin daya kamata mu sani tun a yanzu. Ina kuma ji a jikina babban yaƙine da kema ya shafeki, kuma za'a cigaba da amfani da yarinyar ne wajen tabbatar da shi in har tana cikin masarautar nan”.
“Shiyyasa tun farko nace a kawar da ita Uwa, dan babu wani amfani da wannan yarinyar zatamin face cigaba da ɗagamin hankali, gashi kuma har tana neman zama tafinta a al'amurana dake gab da kammala bayan gumurzun yaƙin da naci na tsahon shekaru a baya kafin zuwa lokacin tattara ganima”.
“Abinda kike ƙoƙarin yi shine mafi girman kuskure da zai rusa dukkan nasarorinki Ta-kurya. Domin yunƙurin kashe wannan ƴar shilar da kike tamkar kashe rayuwarki ne baki ɗaya. Tun farko na faɗa miki kasheta kai tsaye bashine mafitar ba, ba kuma shine ƙarshen daƙile yunƙurinta ba ita a karan kanta. Hasalima a yanzu rayuwarta mukafi buƙata, zamu jefata ne matsayin dutse ɗaya dazai wargaza tsuntsaye biyu. An wargaza mana shirin mu na farko a kanta, dan haka zamu tafi na biyu. Yaƙinki a yanzu shine kiyi duk yanda zaki ta baro wancan sashen daga nan zuwa cikar kwanaki bakwai. Zakiyi yanka na baƙar babbar dabba a daren goma sha uku, zakuma ki dawo da rigar data sanya. Kiyi duk wani ƙoƙarin da zai hana kusancinta da Ajlaan a turaka. Dan maganar kaita turakarsa ta rushe kuma zamu sake sabon salo ne domin kama tsuntsu mai wayo.......”
“An gama Uwa mai share kukan masu kuka. Sai dai dawo da rigar nan zai zama abu mai wahala kasancewar tana a hanun Mamma (Malikat Haseena) ne a yanzu haka”.
“Wannan umarni ne Ta-ƙurya”.
“Zanyi iya ƙoƙarina Uwa. Sai kuma maganar mutuwar Hadiman can, Shahanshan da kansa ya saka kwamitin bincike masu tsauri da basu taɓa ƙetare nasarar cika umarnin da'aka basu ba. Kinga akwai matsala kenan tunda waɗan can sun laɓe ne a jikin aikinmu suka zartar da nasu, sannan suka kashe hadiman tamkar yanda muka shirya kafin mu mu aiwatar da hakan”.
Wata irin mahaukaciyar dariya mai amsa kuwwa Uwa ta shiga ƙyalkyalawa, sai da ta ɗauka tsahon lokaci tanayi kafin ta tsagaita ta tsuke fuska tamkar ba itace tayin ba. Har ta ƙurya ta fidda ran samun amsa sai kuma Uwa ta sake ƙyalkyalewa da dariya tana ambaton “Ajlan! Ajlan!! Ajlan!!!” ta ƙara kwashewa da dariya tana mai disashewa a idanun Ta-kurya da zuciyarta ta kasa fassara ma'ana ko dalilin dariyar ta uwa...
🤔Ko miye naku tunanin a wannan gaɓar kuma masu karatu???.
★... ★.★.★ ★...
*_GIDAN BABIY_*
Sun dawo har yanzu da ɗan sauran mutane maƙwafta da aketa ɗan ƙus-ƙus akan lamarin. Cikin ƙanƙanin lokaci aka baibaye motar, waɗanda suka shige gidaje suka fara fitowa. A yanayin da aka fidda Ummu mafi yawansu sunma ɗauka dai bata da rai, dan kuwa da gaske babu alamar rai tare da itan. Kuka da salatin da mafi yawan mutane suka ɗauka na tunanin ta mutun ne yasa Abu Zainab saurin dakatar da su.
“Dan ALLAH kowa ya kwantar da hankalinsa. Umm-Arfa ba mutuwa tai ba”.
Badan hankalin su ya kwantaba sukai shiru, sai dai dama kukan na wasu na munafurci ne dai. Matane suka kamata aka shiga da ita, a tabarmar da suka samu tsakar gida suka shimfiɗeta. Cikin sa'a Abu Zainab yaci karo da wayar Babiy dake yashe a ƙasa. Da alama sanda jami'an nan zasu fita da shine ta faɗi. Jikinsa har tsuma yake a duba contact ɗin wayar, cikin sa'a ya samo number da akai saving da Baba. Baya raba ɗayan biyu mai sunan nada babban matsayin baban a wajen Babiy ɗin, dan haka ya danna masa kira kai tsaye, sai dai harta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kiran yay yana addu'ar dacewa sai ko gashi an ɗaga...
★A lokacin da kiran Abu Zainab ya riski su kaka ta hanyar wayar Babiy ba'a ƙaramin tashin hankali suka tsinci kansu ba shi da Iyyani. Duk da kasancewar yamma tayi kuma yasan a yau dole ne sai ya dangana da daular ruman dole ya bazama neman wani yaro mai mota a ƙauyen nasu dake jigila a ko yaushe, cikin sa'a ya samesa ya dawo kenan ma ko gida bai shiga ba. Amma saboda mutuncinsa da ake gani yana masa bayani babu musu ya amsa masa suka ɗauka hanya harda Iyyani daketa faman sharar hawayen da suka kasa tsaya mata. Ana sallar isha'i suka iso cikin daular ruman. Basu sami mutane ba a gidan kamar ɗazun, sai Umm Yazeed da matar Abu Zainab dake dai tare da ita har yanzun. Zuwa yanzu Ummu ta farfaɗo, sai dai taƙi magana da kowa sai hawaye da taketa faman zirarwa ta gefen ido, ga numfashinta baya fita normal kamar na kowa, tana fitar da shine da fisgosa a wahale sannan a fiffisge. Kuka Iyyani ta sake fashe da shi da rungume Ummu a jikinta tana kiran sunanta. Kaka kam tsaye yay kawai zuciyarsa na harbawa da ƙuna. Suna a haka Abu Zainab ya dawo, dama sallar isha'i yaje. Cikin girmamawa ya gaida kaka, shima ya amsa masa da kulawa da godiya. Ya ɗan murmusa kansa a risine. “Ai ba komai baba yiwa kai ne. Sannan mun zama ɗaya ai mu da Abu Hanash. Ko mu irin haka ta faru da mu zai tsaya tsayin dakane a kan komai. Ruɗanin halin da Umm Arfa ke ciki yasa su bamu bibiyesu musan miya faru ba har yanzu gaskiya. Dan munata yawo a asibitoci amma sunƙi amsarta, ga jikin nata kuma yana buƙatar a duba mata shi, shiyyasa yanzu dana idar da sallar magrib naje na samo ɗan uwana dake aikin asibiti gashi muna tare, sai dai ba wani babban likita bane dai....”
Kai kawai Kaka ya jinjina masa da faɗin, “ALLAH ya saka muku da alkairi, haka ake fatan zaman makwaftaka, domin ita makwaftaka tanada ƙarfin da zata iya fin ƴan uwantaka muhimmanci ma a wani ɓangaren. Yanzu gashi abu ya samesu, kafin mu muzo kun basu ɗauki, da bakwa zaman lafiya kuma hakan bazai yuwuba. Dan haka duk wani mutum na ƙwarai daya san kansa ya dace ya rayu da maƙwafcinsa lafiya da ƙaunar juna”. “Hakane Baba, ALLAH ya saka da alkairi. Bara na shigo da shi”. Murmushi Kaka yayi da jinjina masa kai. Koda suka shigo tare da ɗan uwan nasa shima ya gaida Kaka da girmamawa, hakama Iyyani da har yanzu ke faman sharar hawaye tana tofama Ummu addu'a. Damar duba Ummun Kaka ya bashi dan haka ya shiga aikinsa. Ya tabbatar musu jinin Ummu ya hau matuƙa, amma zai mata allurar barci ta samu nutsuwa dan barinta a ido biyu akwai haɗari komai zai iya faruwa. Sai da suka maida Ummu ɗaki sannan ya saka mata ruwa da allurai aciki, cikin sa'a kuwa babu jimawa barci yay awan gaba da ita. Sosai Kaka yay musu godiya da sanya albarka, dan ko sisi ɗan uwan nasa bai amsaba ma.......
★★.... ★.... ★★.....
An wayi gari da samun canji sosai a yanayin Iffah, dan zuwa yau kam Alhmdllh. Sai dai jikinta dake wani irin saɓa saikace wata macijiya. Sai kuma rauni data tsinci kanta a ciki sakamakon mummunan mafarkin datai akan su Babiy daya haddasa mata matsanancin faɗuwar gaba da akai-akai. Gata dai iya gata tana gani wajen tsohuwa Malikat Haseena duk da bata da lafiyar ƙafa sai a wheelchair take komai. Hakama Daneen Ammarah tsaye take kan Iffah, yanda take kula da ita yasa Iffah jin ƙaunarta batare data san dalili ba, ganinta take tamkar Ummu. Yanda ake tsaye kanta da gata da kulawa yasa ko damar yin ƙwaƙwaran tunani bata da shi, dan da tayi shiru Daneen Ammarah zata nuna damuwa taita jera mata tambayar mike damunta? Ko tamanin wani abu ne a jikinta har yanzu?. Dole take sassauta damuwarta, sai dai tayi matuƙar dagewa wajen ambaton UBANGIJI kamar yanda Babiy da Ummu suka dinga jaddada mata a nasiharsu ta ƙarshe gareta. Labarin mutuwar hadiman da suka kai mata rigar nan ta saka yazo kunenta itama, sai dai jin sanadin mutuwar tasu ya tsaya mata a rai matuƙa, harma ta rasa yaya zata fassara al'amarin...
Bayan idar da sallar isha'i tana zaune tayi tagumi gaba ɗaya hankalinta ya tattara ga tunanin iyayenta da mummunan mafarkin daren jiya a kansu Daneen Ammarah ta shigo hadimai uku biye da ita. A bakin gadon takai zaune tare da kai hannu ta janye tagumin da Iffah tai. Nannauyan nunfashi ta sauke da ɗan ɗagowa ta kalla Daneen Ammarah ɗin, sai kuma ta maida kanta ta risinar da mata sannu da zuwa. Daneen Ammarah dake kallonta cikin damuwa taja numfashi ta fesar batare data amsa ba. Dai-dai nan Hadiman da suke tare suka zube gaban Iffah bayan sun ajiye kayan hanunsu. Gaisheta suke da tsantsar girmamawar da ko iya ɗaga kawunansu basayi su dubi sashen da take. Sam Iffah batajin daɗin yanda suke matan saboda bata sababa, a ranta gani take kamar ƙasƙancine. Hannu Daneen Ammarah ta kaɗa musu alamar suje, zumut suka miƙe tamkar ƙyaftawar ido suka fice. Iffah ta bisu da kallo cike da jin raɗaɗi a zuciyarta.
“Ibnati!”.
“Na'am Mamy!”.
Iffah ta amsa cike da girmamawa ga Daneen Ammarah. Sosai sunan da Iffah ke kiranta da shi ke raunanata da sake jin ƙaunar yarinyar, dan a bakin mutum ɗaya tak take jinsa kafin ita. Taja numfashi da haɗiye hawayen da suka cika mata ido ta maye gurbinsu da murmushi.
“Ibnati bana son cigaba da ganin damuwar nan a fuskarki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai sake samunki. Wanda ma ya sameki ki ɗauka kaddararkice kinji, amma inaji a jikina insha ALLAH kece mabuɗin nasararmu, ke ce hasken da zata haska mana duhun da muke a ciki a Daular nan kinji”.
Kai Iffah ta jinjina a hankali, haka kawai take jin matuƙar nutsuwar kasancewa da wannan baiwar ALLAH, sam batajin irin zafi da tsanar da takema duk wani mai alaƙa da masarauta a kanta. Kallonta take tamkar wata katanga ta wani babban al'amari dake tunkarota. “Mamy bana tare da damuwa in har kina a kusa dani, duk abinda ya sameni kuma dama ALLAH ya ƙaddara sai ya sameni koda banzo nan ba. Ina tunanin su Ummu ne da jin tsananin kewarsu saboda mummunan mafarkin danai akansu jiya, ina tsoron kar wani abu ya samesu ne suma?”.
Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta, “Duk ɗa na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-almilki tana fitane kawai bisa ƙwaƙwaran dalili, zuwa gidansu kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, ɗaya a sirrance, ɗaya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki harda sheɗanu”.
A hankali hawaye suka silalo a kumatun Iffah, bawai lokacin ziyarar bane yay mata nisa, rashin tabbacin kaiwa lokacin ziyararne ya sata zubar hawaye. Ita dake zaman jiran ƙaddarar mutuwarta taya zatai tunanin zuwan waɗan can damarmaki guda biyu na ganin su Babiy, maganar mafarki kam ta san gaskiya Mamyn ta faɗa, itama kuma ba tana dangantashi da zama tabbaci bane, kawai tana matuƙar jin tsoron faruwar wani abu ne a dalilin mafarkanta na baya.... Ganin hawayen Iffah ya matuƙar tada hankalin Daneen Ammarah, a rikice ta shiga tambayarta kamar yanda ta saba in har ta ganta a makamancin damuwar nan. Hannu Iffah tasa ta share hawayen nata da ƙirƙiro murmushi.
“Mamy ki kwantar da hankalinki hawayen sunzo ne kawai da kansu babu dalili”.
“Haba Ibnati, dama ana kuka babu dalili ne? Ko baki faɗaba nasan kinada dalilan yin kuka, amma idan kika zama mai haƙuri da juriya wataran ke zakiyi dariya a gaban waɗanda suka cancanta suyi kuka.” (ALLAH ya tabbatar da wannan ranar) Iffah ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai ta goge hawayen tana murmushi. Hakan yasa Daneen Ammarah yin murmushin itama, kafin kuma ta mike tsaye da kama Iffah suka koma kan dardumar da aka shirya abinci acan gefe na ɗakin, dan ɗakine ƙaton gaske mai dauke da komai na jin daɗin duniya. Tare sukaci abincin, Daneen Ammarah har tana bama Iffah wani lokacin a baki, jitake inama Iffah ɗiyartace, dan da'ace tana gidan aurenta har yanzu ɗiyarta ta fari zata iya kasancewa dai-dai da shekarun Iffah ne. Kulawar Daneen Ammarah ta sake saka sassauci a zuciyar Iffah harta ɗan saki jikinta. Bayan sun kammala ta sakata shiga bayi tai wankan maganin da take amfani da shi, data fitoma da kanta tai mata hayaƙin turare. Iffah ta hau gado ta zauna, Daneen Ammarah a gefenta da littafin tarihin annabawa acewarta zata dinga karantama Iffah har sai taga tayi barci domin ɗebe mata kewa.
“Yauwa Ibnati kin shirya dai ko?”.
Fuskar Iffah da ɗan murmushi tace, “Eh Mamy na”
“Masha ALLAHU ashe dai Habibty na tare dani”.
Hannu Iffah tasa ta rufe fuska tana murmushi, itama dai Daneen Ammarah murmushin take. Ta fara buɗe littafin. Iffah dake kallonta tai dauriyar finciko ɗaya daga ɗunmbin tabayoyin dake cin ranta ganin zata fara karatun...
“Mamy dan ALLAH na tambayeki wani abu?”.
“Oh Ibnati tambayeni mana kanki ma tsaye kuwa.”
Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya..........✍️
Leave a Comment