Daudar Gora Book 1 page 22

 


_22_*



.......Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya, “Immm Mamy dama...” sai kuma tai shiru dalilin gargaɗin da zuciyarta ke mata tunda har yanzu fa Bama wai tasan matsayin Daneen Ammarah ɗin bane a masarautar.

   

  “Dama mi? Kinga karkiji komai kimin duk tambayar da kike buƙata, insha ALLAH zan kasance mai baki amsa, idan kuma bata dace ba zan baki shawara kodan nan gaba”.

      Kai Iffah ta jinjina “Dama dan ALLAH zance ne yanzu mutuwar su hadiman can shikenan ta tafi a banza baza'ai wani bincike a gano ba?”.  

     Kallo na kusan sakan biyar Daneen Ammarah taima Iffah da har tama ɗauka tai laifi, amma sai taji taja numfashi da maida kanta kan littafin hanunta. “Mutuwarsu bazai tafi a banza ba saboda dalili mai ƙarfi Ibnati. Dan duk wanda ya kashesu yana gudun tonuwar asirinsa ne akan cutar da ke da akai yunkurin yi. A yanzu haka Shahanshan ya saka kwamitin bincike, muna fatan kuma ta wannan hanyar za'a gano koma wanene ya saka ki a halin da kika tsinci kanki. Kuma dama kema ana jiran ƙara samun lafiyarki ne aji ko akwai wani abu da kika sani, ko kuma bayan su ukun can da ɗayar da aka samu nasarar ceto ranta ko akwai wasu..”

       Da sauri Iffah ta dubeta. “Mamy akwai wadda bata mutu ba dama?”.  

   “Eh akwai amintacciyar hadimar Umm-Jasrah (haka take kiran Malikat Bushirat) mai suna Diwa. Ita an kaita asibiti kafin gubar da suka sha ta karasa katsa ƴan hanjinta. Alhmdllh kuma an dace dan yanzu haka tana kan shan magani, tana kuma zagaye da tsatstsauran tsaro”   

      “ALLAH ya ƙara bata lafiya, sai dai kuma banajin tanada hannu a cikin al'amarin Mamy, dan da ganinta mutiniyar kirki ce”.   

       “Gane mutanen kirki ba'a ido yake ba Ibnati musamman a wannan masarautar da kowa kansa kawai ya sani, a mafi yawan lokuta ma ba'a gane maƙiyi da halayya. Akwai rikitattun abubuwa dake a matuƙar cuɗe a wannan Daular da gani da ido bazai wadaci mai kallo ba, dan haka nakeso ki nutsu kisa hankalinki waje ɗaya kafin ki koma sashenki ki koyi abubuwa da yawa na salon mulki da tsarin matsayinki na Zawjata-almilki. Saboda kunada matuƙar tasiri da girma a tsarin ƙarfin iko na masarauta da kaikawon talakawan ƙasan ruman. Fatana kuma kece Malikat a cikin Zawjata-almilki insha ALLAHU”.    

      Sam Iffah bata fahimci komai ba ga kalaman Daneen Ammarah, amma sai bata sake cewa komai ba dan a ganinta tana buƙatar samun lokacin yin nazari na musamman a kansu kafin ta fahimcesu dallah-dallah.......  


        ★★...  ★...  ★★....


    Ana idar da sallar asuba drivern daya kawo su Kaka jiya dan hanashi komawa yay saboda dare ya ɗauka Iyyani da Ummu suka wuce. Kaka da Abu Zainab kuma sukai shirin fara neman inda zasu samo Babiy da Hanash. 

     Dai-dai suna shiga mota kaka ya dubi Abu Zainab da ɗan murmushin ƙarfin hali a fuskarsa, “To Zakariyya kai ne ɗan gari, yanzu ta ina zamu fara kenan?”.

   Numfashi Abu Zainab ya furzar, tare da yin ɗan jimm alamar tunani, “E to Baba banace ba dai, dan al'amari nada wuya, saboda bamu da tabbacin waɗan nan jami'ai daga wane station suke. Amma ni yanzu a nawa shawaran ina ganin kamar mu nema gidan shi marigayi ɗin, tunda matarsa ita ta kawo jami'an tasan daga ina suke”.

     “Hakane, wannan ma shawara ce mai kyau, sai dai inda gizo ke saƙar kai koka san ina gidan Dawood ɗin yake? Dan ni dai rabona da shi ma kusan shekara biyar kenan tun suna tare da Muhammad Zayyan”.

         “Ito baba banace ba, dan kusan nima hakan dai take, amma bayan tashinsa daga anguwarmu nasan inda ya koma, sai dai bani da tabbacin ko har yanzu acan ɗin yake zaune tunda ba wani huɗɗa muke ba gaskiya, dama dalilin Abu Hanash ɗinne ake gaisawa sai kuma idan wani zama na anguwa ya haɗa kafin ya tashi kenan. Amma yanzu dai bara mu tafi can ɗin kawai rana ma nayi”.


       Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso anguwar, kasancewar ma ta cika ba kamar da ba da kyar suka iya samo gidan. Duk da jikinsu ya ɗanyi sanyi ganin ƙofar gidan babu alamar anyi wani abu daya shafi mutuwa Abu Zainab yay sallama har sau uku. Ana huɗun wani mutum ya fito. Cikin binsu da kallon rashin sani ya basu hannu suka gaisa. Abu Zainab da shima dai jikinsa yay sanyi ya ce, “Kayi haƙuri nasan baka sammu ba. Muma dai munzo nan ɗinne neman wani bawan ALLAH daya zauna anan shekara kusan huɗu haka baya. Sunansa Dawood, amma ana masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa ɗaya bashi kuma da yaro ko ɗaya”.

     “ALLAH sarki, gaskiya ban sanshi ba, dan nima dai ban wuce shekara biyu da tarewa anan ɗin ba. Na kuma sayi gidanne a hanun wani mutum Ibrahim Askari”.

    Abu Zainab zai sake magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai. Godiya sukai masa da sallama suka wuce.


      “Baba ban san miyasa ka dakatar dani ba. Dama zan tambayesa ne ko zai faɗa mana inda zamu samu shi Ibrahim Askari ɗinne”.

    Numfashi Kaka yaja ya fesar, “Dalilin da yasa na dakatar da kai kenan. Kasan shi al'amari irin wannan yana buƙatar kasan dawa zakai maganar abu na gaba. Inaji a jikina waɗanda suka haddasa tushen wannan matsalar dole suma zasu kasance suna bin bayanmu domin toshe duk wata hanyar da zamu iya bi. Dalili kuwa shine ina kallon lauje ne cikin naɗi akan al'amarin”.

        “Eh gaskiya hakane kuma Baba. To amma in har hakane mizai hana mu nema lauya, sai nake ganin cikin sauƙi shi zai iya binciko mana inda suke ma, kuma koma minene sai yazo cikin sauƙi tunda ana magana ne akan abinda ya shafi shari'a ko kuwa?”.

      “Itama wannan babbar shawara ce a mahangar hankali Zakariyya, sai dai shi lauyan ne matsala musanma irin mu wanda muke bukata. Mai gaskiya da amana”.

    “In dai dan wannan ne babu damuwa insha ALLAHU, akwai yayan matata data rasu, kwararren lauyane kuma mai nagarta da nasan zakaso aikinsa kuma zai taimakemu kasancewarsa babba. A yanzu dai nasan bazamu samesa a gidansa ba. Bara kawai muje ofishinsa”...


       ★★.....  ★...  ★★.....


    Kamar yanda Iffan ta nema alfarma a wajen Daneen Ammarah akan ɗakko mata akwatinta da aka kawo ta gidan dashi ya iso gareta. Taji matuƙar sanyi a ranta da farin ciki. Hadimar data kawo na fita ta buɗe akwatin ta shiga dubawa. Alhamdullah komai yana nan yanda yake, hatta takardar da malam Fawzan ya bata ɗinnan itama tana a inda ta ɓoye ta. Tana idar da sallar azhar littafin data sako a kayan nata kawai ta ɗauka da biro ta fara rubutu. Anutse take rubuta komai daya faru daki-daki tun daga barowarta gida har zuwa shigowarta cikin masarautar, abinda ya faru da ita dama wanda ke kan faruwa bayan warkewarta. Da zarar taji motsi koda ma Daneen Ammarah ne sai ta boye, a haka ta kwashe kaf yinin har zuwa dare tana abu ɗaya. Da daddare bayan kammala shirin barci maimakon kwanciya zaman karatun Alkur'ani tayi, koda Daneen Ammarah ta shigo ta sameta a hakan bata katseta ba. Tasa Hadimar dake biye da ita ajiye mata madarar da suka shigo da ita. Daga haka ta fice taja mata ƙofar da nufin ta dawo zuwa anjima, dan yanzu tana son zuwa ta duba Malikat Haseena ne da yai batajin daɗi.

      Iffah na ganin ta fice ta sauke ajiyar zuciya, addu'a tai ta rufe Alkur'anin ta mike, kofar taje ta sanyama key bayan ta leƙa babu kowa a corridor ɗin. Ta ɗan jingina da ƙofar tana mai ambaton “Alhamdullah” da sakin ɓoyayyen murmushi. Cikin sassarfa tabar jikin ƙofar zuwa ga akwatinta, ta buɗe tare da ɗakko wayar Arfa da takardar da Malam Fawzan ya bata. Number da aka rubuta ta kwashe a wayar, ta haye tsakkiyar gadon ta kwanta tare da jan lallausan bargon ta shige ciki har kanta sannan tai dailing number. Gaba ɗaya a kage take da zumuɗin a ɗauka. Dan haka take bin sautin shigar kiran da zuciyarta. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ɗin ba. Kira ta sake yi, nan ma dai shiru, bata gajiya ba ta cigaba da kira har fin sau goma kafin a ɗaga a karo kusan na goma sha biyar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tamkar wadda aka tsamo daga cikin ƙanƙara. Sai kuma tai saurin faɗin, “Assalamu alaikum”.

      “Wa'ake nema?”.

   Aka faɗa daga can maimakon amsa sallamar tata. Da lafiya lafiya ne sai tayi mitar ƙin amsa sallamar, amma sai tai saurin faɗin, “Sir Ajmaal”.

         “Wa'ake nema?”.

      Aka sake maimaita mata tambayar.

   Zuciyarta ta ɗan fara zabura amma sai ta danne ta sake maimaitawa itama. 

      “Sir Ajmaal”.

“Wa'ake nema?”.

Still aka sake faɗa kamar dai ba'ama jita ba.  

      Wayar ta janye a kunenta ta tashi zaune ta ɗauka takardar, number dai dake a jikice dai-dai batai mistake ba. Sake maida wayar tai kunne aranta tana faɗin (bara naga ƙarshen ku dai) ta sake amsawa da “Sir Ajmaal”.

    “Kin saɓa lamba”.

Aka bata amsa da yanke wayar lokaci guda batare da anjira cewar ta ba......


         

        ★★.....  ★...  ★★.....


  Kasancewar Abu Zainab suruki ga barrister cikin sauƙi suka samu ganinsa ta hanyar kiran waya. Har office yasa masinjansa daya fita yay musu iso ya shiga da su. Ganin lafiyayyen office ɗin nasa dama hukumar tasu ya sake tabbatar ma da Kaka babbane gaskiya. Sun gaisa cikin nuna sanayya shi da Abu Zainab. Ya kuma gaida Kaka da girmamawa kasancewar tsoho dama zai iya haifarsa. Basu saurari lemo da aka kawo musu ba Abu Zainab ya shiga masa bayani dalla-dalla. Sai da ya gama tsaf Barrister Abdallah dake rubuta wa ya ajiye biron yana jinjina kansa. Kaka ya fuskanta cikin son ƙarin bayani....

       “Baba kaima kasan shi Dawood ɗin kenan?”.

    “Tabbas na sanshi yaro. Hasalima ga gidan mahaifin shi Muhammad Zayyanu gana mahaifin Dawood. Sannan ta ɓangaren mahaifiyata ma munada alaƙar jini da mahaifin nasa. Shine kuma yay sanadin zuwan Muhammad Zayyanu garin nan, shi kuma Muhammad Zayyanu ya koya masa noman zuma daya gada ga mahaifinsa”.

         “Eh lallai sanayya ce babba kam. Sai dai kuma inaga ya kamata nasan miya rabasu? Dan yanzu hujjojin hanunmu sune zasu taimaka mana wajen kubutar da su saboda wannan case ne babba kuma da alama shiryayye”

      “To nidai kai tsaye banace ga abinda ya zama sanadin rabuwar kawunan nasu ba. Dan shi Muhammad Zayyanu mutum ne mai zurfin ciki da rashin kwaramniya. Amma dai lokacin da naga bana ganinsu tare na tambayesa ko akwai matsala? Shi da abokin nasa. Sai ya sanar min shi dai a saninsa bai masa komai ba ya janye daga jikinsa, ya kuma bisa ya bisa babu adadi danya faɗa masa amma yaƙi, daga karshe ma ya tattare kayansa da iyalinsa sukabar anguwar, bai kuma sake ganinsa ba har watanni sunja a lokacin. Na bashi shawarar ya ƙara nemansa dai, da muka sake haɗuwa na tambayesa sai yace ai yama bincika yabar gari. Iyakar abinda na sani kenan gaskiya”.

     “Shi kuma Dawood ɗin baka sake ganinsa ba kaima?”.

   “Eh to gaskiya ban sake ganinsa ba. Dan ko'a rasuwar mahaifinsa sai wai-wai mukaji yazo yay gaisuwa ya tafi kawai. Daga nan kuma dai bamu sake jin ɗuriyar tasa ba dan dama mahaifiyarsa bata raye tuni”.

       Barrister dake faman kaɗa kai ya sake ajiye bironsa. “Uhhm yanzu to inaga mataki na biyu shine musan wane station suke. Ko kuma inda ita matar tasa take”.

    Cikin damuwa Abu Zainab yace, “Munje inda muke tunanin samun nata bamu sameta ba. Sai dai an ambata mana sunan wanda ya saida gidan ga wanda ke ciki yanzu”.

       “Miye sunan”.

   “Ibrahim Askari”.

“Badamuwa kuje abunku, insha ALLAHU daga nan zuwa gobe za'a nema mana Ibrahim Askari ɗin. Suma kuma zan ɗan bincika ta hanyar jami'an dana sani a mabanbanta station na garin nan”.

      Sosai kaka ya dinga ma barrister godiya. Hakama Abu Zainab. Shi dai faɗa musu yake karsu damu. Aje a cigaba da addu'a komai zai zama labari insha ALLAHU......


         ★★..... ★★.... ★★.....


  Iffah kamar zatai kuka ta ƙara dailing number amma sai ma aka sanar mata switch up. Wani irin zafi da lugude ƙirjinta ya shiga yi, ta shiga neman number Malam Fawzan cikin rawar jiki tunda dai shine ya bata number..........✍️

     

No comments

Powered by Blogger.