Daudar Gora Book 1 page 34
*_34_*
........(Mi wannan mutumin ke ƙullawa?). Ta faɗa a zuciya batare data motsa ba. (Keda ke neman kusanci da shi dama miye matsalarki da koma mi yake nufi) wata zuciyarta ta sake ayyana mata. tamkar wadda aka zaburar sunan Arfa da Fariha ya fara amsa kuwwa a zuciyarta har tana jinsa yana tashi bisa sararin samaniya.
Kaifafan idanunsa masu nuna tsaurinsa ya zuba mata ganin ta basar da shi itama. Kusan mintuna uku babu alamar zata tankama zancen nasa har ya fara jin haushi. Ta taɓe baki da kauda kanta gefe, cike da dakewa ta furta, “Da gizago na tsorata ƙwarin gwiwata da bazan amincewa shigowa ramin zakin da ɗanyen nama shine abincinsa ba. Karka damu a kaina ranka ya daɗe, dan a wannan gaɓar *_cuta ce ta ɗakko cuta, ɓarawo ya ɗakko akwatin maciji”._*
Fuska ya ɗan motsa kamar zaiyi murmushi, sai kuma ya basar. “Bana haɗa ƙwanji da mage duk da kamaninta na yanayi da nawa matsayina na ZAKI har a hallaya. Ki kama kanki dan kina buƙatar rayuwa mai tsaho wajen moran ƙuruciyarki”.
Ya faɗa da muryarsa mai zurfi da ƙasaita yana miƙewa ya zagayeta ya wuce abinsa. Shiru bata motsa ba har ta gama jin ɓacewar sautin takunsa a wajen, ta ɗan cije bakinta “Zaki zako ka magantu fiye da haka”. Ta faɗa a fili cike da kwaikwayo salon maganarsa tana sakin wani lallausan murmushi da kai kofin shayi a bakinta, duk da zafinsa ta rumtse ido ta kwankwaɗe abinta sannan ta juya taima hadiman dake tsaye har yanzu kallo ɗaya ta ɗauke kanta batare da damuwar komai ba, dan tasan basuji komai ɗin ba da suka tattauna. A yanda suke maganar ma wani sai ya ɗauka wani zancen soyayya ne ya haɗasu. Komai batacema kowa ba itama ta miƙe tabar wajen, duk suka bita da kallon ƙasan ido kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.
A tafiyar tata tana ɗan kalle-kalle taci karo da camara, komai bataji a ranta ba, dan tayi tsammanin hakan tun farko, saboda babu yanda za'ai sashen mutum mai ƙarfin iko kamar Tajwar ace babu wani tsaro makamancin hakan koma fiye da hakan. Da ƙyar ta iya gane ɗakin data kwana. Tana shiga ta zube a kujera da sauke nauyayan numfashi, ɗakin da akaima gyara ɗan gaske tabi da idanu, sai taga ma kamar ba'a cikinsa ta kwana ba, ganin akwatin kayanta kawai ya tabbatar mata da shi ɗin ne. Tunani mai ƙarfin gaske ta faɗa kusan kashi uku zuwa huɗu musamman akan kawota da Malikat Haseena tayi, mi tsohuwar ke nufi da haka bayan su suka sanar mata an rasa matan baya ne a dalilin kawosu turakar Shahan-shan ɗin. Sai kuma akan Tajwar Eshaan ɗin, na farko waccan fuskar data gani a waje kafin shigowarta masarautar matsayin matarsa. Na biyu wannan fuskar ta yanzu da bata da banbanci da waccan ɗin, na uku hanyar da ya kamata ta cigaba da bi domin sanin ainahin wanene Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed a baɗini da zahirin rayuwa. Domin da gasken gaske tana a cikin ruɗani akan fuskokin nan biyu data gani a mabanbanta muhallai. Su ƴan biyu ne? Kokuwa shi ɗinne ke ɓadda kama yana fita?. Abu na uku kuma abinda ya faru a daren jiya da sai a yanzu yake bata matuƙar mamaki, tun a jiyan bawai ta ajiyesa a gefe bane dan bashi da muhimmanci ga haɗarin da tasan ta kawo kanta ciki, kawai dai bata san dalilin da yasa bataji ko ɗar ba a zuciyarta na tsoro, kuma har yanzu batajin tsoron sam, dama kuma tun asali bata da tsoron. Dan Iffah irin mutanen nan ne masu ƙesashiyar zuciya mai iya tunkarar komai koda yanada haɗari a garesu, tanada naci da zama kaifi ɗaya akan zimma da cimma buri duk da ƙarancin shekarunta. Na ƙarshe tattaunawarsu ta yanzu da shi da girman kalaman da yay amfani wajen jifanta da su. Ta ɗan murmusa da cije lips ɗinta tana mai lumshe idanu a hankali......
★★.... ★★.....
Zuwa yanzu tako ina maganar tsallakewar Iffah ce ke kaikawo a cikin masarautar. Kowa ya nutsu wajen tattauna abinda ke bakinsa da abokin maganarsa. Wasu jin daɗine game da hakan, wasu ko baƙin cikine a ransu, dan mutuwar Zawjata-almilk ɗin kamar wani makamine a hannayensu na dukan nasarar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ɗin. Tsallakewar Iffah kuma zai kasance kamar damar ƙalubalantarsa da suka riƙe ya kuɓuce musu kenan. Ita kuma yarinyar kimarta da nunawa duniya tafi ƙarfin masu ƙarfin zai yi tasiri a zukatan jama'a.....
★Komai dake faruwa yana isa da shiga a kunnen manyan masu faɗa aji ta bangaren iko da kusanci da Tajwar Eshaan ɗin. Wato Malikat Haseenat da Malikat Bushirat. Sai dai sunyi biris babu alamar zasu tofa nasu akan hakan bayan bayyanar farin cikinsu akan fuskokinsu daya gaza boyuwa ga kowa. Dan a dalilin wannan al'amari Malikat Bushirat har ƴafiya tayi ga wasu firsinoni dake a cikin kurkukun masarautar akan wasu laifuka nasu da basu kai sun kawo ba. A cikin sunne kuma aka sallami harda Diwa a dalilin bincike daya tabbatar da bata da hannu game da abinda ya faru ga Iffah a waccan ranar.
★A ɓangaren Malikat Haseenat kuwa maimakon bama abinda ke zuwama kunenta muhimmanci hankalinta ta maida wajen tantance hadiman da zasu koma aiki a karkashin Iffah ne bisa taimakon Daneen Ammarah da farin cikinta itama yake a bayyane. Dan itama dai har kyaututtuka na musamman yau ta bada ga hadimai tare da sakawa a tattaro mata dukkan malaman masarautar zuwa sashen Iffah da bukatar suyi saukar Alkur'ani mai girma. Ta kuma miƙe da karfin jikinta wajen shirya lunch na musamman ga Tajwar Eshaan da amarya Iffah Zawjata-almilk...
*_★BARRISTER★_*
Abubuwan da suka faru sun sakashi dakatawa a zahirance bisa shawarar Kaka. Sai dai yana cigaba da gudanar da wani binciken sirri dan yayma kansa alƙawarin binciko duk mai hannu akan wannan al'amarin nasu Babiy da ma inda aka ɓoye su.
Kamar yau ma tun jijjifin safiya ya fito daga gida. Kai tsaye hanyar jihar Hubab ya nufa inda bincikensa ya tabbatar masa nanne ainahin jihar da matar Abu Moosa ta fito. Jihar Hubab makwafciyar Dahab city ce (Daular ruman kenan) dan haka a cikin ƙanƙanin lokaci ya isa. Bai tsaya sanyaba ya ɗauka hanyar ainahin kauyensu kuma. Kasancewar anan ma hanyace shimfidaɗɗiya a kanƙanin lokaci ya isa. Da farko ya sha wahalar binciken inda gidansu yake, sai da yay dabarar nuna hotonta sannan.
Kusan mintuna goma bayan isar da saƙon tanada baƙo gareta ta fito cikin irin shigarsu. Tayi ɗan tsamm alamar shan jinin jikinta kafin ta ƙaraso a yanayin son basarwa. Barrister shi ya fara gaidata, tare da sanar mata sunansa. Lokaci ɗaya ruɗani ya bayyana akan fuskarta ta shiga waige-waige irin na rashin gaskiya da ƙoƙarin ja baya daga garesa...
“Bawan ALLAH ina baka shawara ka taimaki kanka ka bar ƙauyen nan, babu wani abu da zaka iya ji a gareni dan ban san komai ba”.
A fusace Barrister yay tsalle gabanta yana huci. “Baki san komai ba amma akaje da ke har gida aka kamasu. Karki sha mamakin bayan sanin inda kike har wasu abubuwa na sani a kanki Mss Farishta. Rashin bani haɗin kai kuma na nufin na tonasu kowa yasan ke ɗin wacece har ma da dalilin auren Dawood, sani kankine wannan babban koma baya ne a gareki kuma harma da zuri'arki”.
Yayu ta haɗiya masu kauri tana kallon Barrister, sai kuma ta sake wawwaigawa tabbacin dai akwai abinda take shakka. “Naji Barrister zan baka dukkan bayanan da kake buƙata, amma ina roƙonka kabar wajen nan, idan ma zai yuwu kauyen nan gaba ɗaya nake son ka bari. Wlhy na maka alkawarin zan zo na sameka na kuma faɗa maka komai da kake buƙata harma wanda baka sani ba”.
“Miyasa bazan sani ba a yanzu?”.
“Saboda zamanka anan yana da matuƙar haɗari”.
“Taya zan tabbatar da zaki zo ɗin?”.
“Na baka dama kabi duk hanyar da zata bibiyi al'amarina”.
Kafaɗarsa ya ɗan ɗage sama da faɗin, “Okay inaga bana bukatar hakan, kije kawai ni na san ta hanyar daya dace na bibiyekin. Amma yaushe ne zamu haɗun?”.
“Inasha ALLAH a daren yau ka sameni a ƙauyen Jumna”.
“Garin su Abu Hanash da Dawood kenan?”.
“Insha ALLAH”.
Tafiya yake zuciyarsa na faman masa kaikawo akan haɗuwar tasa da Farishta (matar Abu Moosa datazo har gida da ƴan sanda aka kama su Babiy. ALLAH yasa kun gane🥱). Duk da yasan zata iya ƙin aikata abinda ta faɗa na haɗuwar tasu a garin Jimna ya zaɓi barinta su haɗun can bisa lumana. A cikin Hubab ya tsaya yaci abinci tare da sallar azhar. Ya fito masallaci idanunsa suka sake sauka akan wata mota da tun fitowarsa ƙauyen su Farishta ya lura da ita tana biye da shi, sai dai duk da ya ganta suna tafiya kafaɗa da kafaɗa bai kawo komai a zuciyarsa ba. Janyewa yay cike da rashin bama abin muhimmanci ya shige motarsa da zummar zai cigaba da tafiya kawai yaga an zagaye motarsa da bindigu.......
★★★.... ★★.... ★...
A firgice ta farka a ɗan barcin daya figeta bayan ta idar da sallar azhar. Ta dafe kanta dake sara mata. Irin mafarkin da tai da dare ne dai babu banbanci. Huci ta furzar da faɗin, “Wace madara ce haka? Tabbas kodaga ina zata fito babu alkairi a cikinta tunda har mafarkin nan ya sake maimaita min kansa. Ya ALLAH”. Ta furta a fili zuciyarta duk babu daɗi, dan zuwa yanzu Iffah ta fahimci wani ɓoyayyen al'amari game da ita, tabbas in har zatai mafarki taita kuma maimaita irinsa sai wani abu ya biyo bayansa mai taɓa zuciya, ta gane hakanne a ɗan zamanta cikin masarautar nan, sai kuma auna abubuwan da suka faru a baya kafin yau ɗin. Sai dai tana ƙoƙarin ƙin gasktama kanta hakan dan kar zuciyarta ta shagala kan abinda zai sakata kaucema umarnin mahaliccinta kuma. Ga kanta jingim kamar yanda yakeyi a duk lokacin datai mafarki makamancin haka, sai zufa data jiƙeta sharkaf tamkar wadda tai wanka. Shigowar saƙo a wayarta da ke gefenta ya sakata tsurama wayar ido na kusan mintuna biyu, kamar wadda aka zaburar wani abu data shafa'a kuma sai ta jawo wayar. Data ta kunna a take tai downloading WhatsApp app..., Bayan ta kammala dai-daita komai tai searching number Sir Fawzan da zuciyarta ke ayyana mata ta fara nema, cikin rashin sa'a taga kusan kwana uku ma baya online ta hanyar lastsin ɗinsa. Duk da hakan bai mata daɗi ba batai wani yunƙurin kiransa ba ta maida akalarta kan number abokinsa Ajmaal. Cikin sa'a shikam dai yana online. Sallama tai masa a taƙaice ta tura, sai dai har kusan mintuna biyu babu reply (yana aiki) zuciyarta ta ayyana mata. Aminta da hakan ya sata cigaba da ajiye masa saƙo kawai a kan duk abinda ya sake faruwa bayan wanda ta tura masa ranar. Daga karshe ta aika masa da roƙon ya bincika mata iyayenta dan har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya dangane da su. Ta haɗa masa da adireshin gidansu, da faɗin (In har kaci amanata ko yaudarata na barka da mahaliccin rana da wata yay maka hukunci da alhakin dukkan al'amuran ƙasar ruman da zalincin mulkin wannan shaiɗanin dodo ke tafin hanunsa). Daga haka ta fito shima Sir Fawzan ɗin ta tura masa gajeran saƙo ta goge WhatsApp ɗin gaba ɗayansa ta ajiye wayar.
Da ɗan layin nauyin jikin dake tare da ita ta miƙe, tana ƙoƙarin shiga toilet taji kamar an gitta mata ta baya. Idanunta ta ɗan rumtse sai kuma ta waigo. Komai babu dai a zahiri dan haka ta kaɗa kanta kawai ta shige bakinta da addu'a....
Fitowarta kenan bayan ta watsa ruwa alerm ɗin ƙofar yay ƙara alamar ana knocking. Sai da ta zira doguwar rigar abaya data ɗakko cikin kayanta sannan ta ƙarasa ƙofar ta buɗe. Hadimar dake tsaye ta zube ƙasa cikin girmamawa tana kwasar gaisuwa. Amsa mata Iffah tai, zuciyarta babu daɗi akan yanda suke ƙasƙantar da kansu, ta amsa cikin sauƙin muryarta dake a sanyaye sakamakon mafarkin da duk ya sakar mata kasala..
“Wani abu ya faru ne?”.
Ta tare hadimar tunkan tace komai. Kai ta gyaɗa mata tana sake rissinar da kanta. “A gafarceni ya Zawjata-almilk. Dama abinci ne aka kawo daga sashen mai Babban ɗaki”.
Iffah tai ɗan jim tana hasashen wace kuma mai babban ɗaki? Kamar hadimar ta fahimta tai saurin mata fashin baƙi da “Malikat mai babban ɗaki”.
(Malikat Haseenat) shine abinda zuciyarta ta ayyana mata. Ta kaɗa kanta da faɗin, “Okay ba damuwa zan fito”. Daga haka ta maida ƙofar ta rufe. Ciki ta koma, sai dai maimakon zama sai ta koma kaikawo kamar mai Safa da marwa abubuwa masu yawa na faman mata kaikawo. Ta jima a haka sosai kafin ta sake kimtsa jikinta cikin wata tsadadiyar abaya mai adon stones dake ta ƙyalli da ɗaukar idanu. (Wannan yana cikin horon Daneen Ammarah data tabbatar mata koda wasa karta zauna da kazamar shiga ko fitowa da ga ɗaki a raguwar kwalliya. Dolene inhar zata bar cikin ɗakinta ta tabbatar komai na jikinta ya isa a kalleta da shi. A tsarin masarautar hakan ba fariyya bane mutunta kaine ga kowa. A kuma ɗan zaman Iffah cikinsu ta fahimci hakan sarai). A yanzu ma kamar ɗazun turarrukan sa ta baza har ƙamshinsu na rige-rigen fita kafin ita ta fita. Ta fito cikin takunta na nutsuwa da ƙasaita kamar wata budurwar macen ɗawisu (🥱😉lol)..........✍️
Leave a Comment