Daudar Gora Book 1 page 39


_39_*

........A ɓangaren Iffah kam bayan sallamar Hadimanta data ƙudiri nutsuwa wajen fahimtarsu a tsanake itama ciki ta shige. Kamar yanda ta saba sai da ta gudanar da duk wani al'adan rayuwarta kafin barci

. Ta haye sabon katafaren gadon nata bakinta da addu'a. Manya-manyan littafan dake jere a bideside drawer ɗinta data kwaso a books room ta kalla cikin nazari har idonta ya sauka kan wanda ya kamata ta fara dubawa. Sai da taja lalausan bargon dake a saman gadon ta ɗan rufe kafafunta zuwa cinya ta gyara zamanta da ƙyau ta buɗe littafin da bismillah. A nutse kuma daki-daki ta fara nazartar littafin da ƙoƙarin dinga fahimtarsa yanda ya kamata da irin fahimtar dai-dai nata tunanin.

      Taja wani tsahon lokaci a nazartar littafin barci gwanin iya sata ya cigaba da rinjayar idanunta. Haka badan taso ba ta kife book ɗin a gefen ta zame ta kwanta tana hamma. Da ƙyar ta kammala haɗa addu'ar barci......


           ★★..... ★.....


      “Uwa komai ya rikicemun wlhy, narasa ina zan kama. Ki taimakeni kar yaƙin dana sha a baya ya zama wahalar banza akan cikar burina”.

    Ta-kurya ce mai maganar cikin tsananin tashin hankali da susucewa game da rashin mutuwar Iffah kamar na sauran matan baya”.

       Uwa dake hakimce duk tana saurarenta ta nisa tana mai girgiza kanta da sake tsuke mummunar fuskarta. “Ƴar shilar nan bata isa ja dani ba Ta-kurya, kin Sanni kin san aikina kin kuma san mizan iyayi. Ya kamata ki nutsu tsaf akan bayanin danai miki tun a baya. Tabbas mutuwarta zata iya zame mana mai wahala a lokacin da muke buƙata, shiyyasa naji takaicin suɓucewar waccan damar da muka samu a farko. Gashi kema sakacinki yasa har zuwa yanzu kin gagara kawo mana rigar dake sashen mai Babban ɗaki ko zamu iya kamo bakin wancan zaren dan zuwa yanzu na fahimci akwai masu irin manufarmu akan yarinyar kamar yanda na sanar miki. An kuma mana karan tsaye na kaita sashen Ajlaan ta hanyar ƙin bin dokokin kaita turakarsa, kin san kuma mu munbi matakanne wajen ɗana tarko akan waɗan ca har mukai na sara, sun shammacemu sun kaita ne, sai dai abinda basu sani ba hakan bazai taba tseratar da itaba a tarkonmu na gaba da kuma mutuwarta”

      “Uwa ba sakaci bane, a yanzu haka hadimar dana saka wannan aikin tana gab da kammala min shi. Ni yanzu tashin hankalina shine cikar lokacin kalmashe bakin zaren burina na biyu dake ƙara nisa. Har yanzu da buƙatar cikamakon aikin fa kafin na tsallaka na uku da shine cikar gaba ɗayan nasarata akan wannan yaƙin. Uwa ya kamata kiyi wani abu. Idan ita wannan yarinyar mutuwar tata bazai yuwu ba ta wannan silar inaga mu ajiye batunta gefe a haɗe wannan bakin zaren”.

        “Kema kinzo da magana mai ƙyau kam ta ƙurya. Kuma inaganin ya kamata cikin Zawjata-almilk biyu da suka rage ɗaya zata zama cikamakin ayyukanmu na biyu. Kinga sai mu haɗa aikinmu na uku dana ƴar shilar sudan can, amma duk da haka a kwana bakwai da zatai bazamu daina gwada sa'ar mu ba dai”.

     “Haka shine dai-dai uwa mai share kukan masu kuka. Madubin rayuwar duk wani mai buƙatar kallon ƙarshen ƙyawun nasararsa.”

     “Nasara takice Ta-kurya tunda har kina tare damu. Sai dai maganar yarinyar can dole ki haɗa da kirsa a yanzu kamar yanda kika saba wajen nasarar haɗa dukkan auren Ajlaan ta hanyar mai Babban ɗaki a yanda kika so. Ki kusanta kanki da yarinyar itama sosai”.

   “Indai wannan ne angama Uwa”.

“Na barki lafiya”.

Uwa ta faɗa tana mai ɓacema ganinta a sannu-sannu harta daina ganinta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke ranta duk babu daɗi. Dan zuciyarta kam ta fara ayyana mata ƙarfin ikon uwa ya fara sanyi. Dole ne ta nema sabon mai taimakonta duk da bazata taɓa mantawa da gudunmawar da uwa ta bata ba harta kawo wannan matsayin a wannan daula ta ruman da ayanzu take kamar mai juyata ta ƙarƙashin ƙasa da zahiri a yanda take so. Amma ga karamar yarinya da bata wuce kiyashin da take murjewa a ƙasan tsinin takalminta batare data sani ba tana neman zamewa rayuwarta wata ƙadangaren bakin tulu a gabar cikar babban burinta na ƙarshe......


         ★★★..... ★★.... ★....


   A ɗan firgice Iffah da kiran sallar asubahi ya farkar take kallon kanta da inda take a yanzu. Cikin shiga razani mai ban tsoro ta diro a gadon daya kasance saɓanin inda ta kwanta a daren na jiya. Kamar wadda ake ingizawa ta fice a ɗakin cikin sassarfa. Tabbas sashen Tajwar Eshaan ne dai take. “Taya haka zata kasance?”. Ta faɗa cikin bugun zuciya. Sai kuma ta fara tunanin kodai mafarki take yine. Hannu takai ta ɗan mari fuskarta. Sai dai babu abinda ya canja daga wanda idonta ke gane mata a yanzu. Dan lallai da gaske a sashen Shahan-shan ɗin dai take. 

      “Ya ALLAH mike faruwa da ni ne haka wai. Taya zan kwanta a sashen da ba wannan ba na kuma buɗe ido na gannni? Jiya an ɗaukeni daga ƙasa an maida saman gado na share, amma shine yau kuma za'a ɗakkoni daga wani sashe zuwa wani daban. Anya ba matsafan gidan nan ke son min wasa da hankali na ba?”.

    Wannan tunani na karshe ya sata saurin kama rigarta ta shinshina. Tabbas irin dai ƙamshin turaren jiya ne da karfinsa harya danne nata. “Ya Arrahaman” ta sake faɗa tana mai juyawa ta shiga kallon ɗakin da sauri. A kan tarin kayan turarruka da idonta ya sauka a kai ta nufa, ta buɗe gilashin da suke ciki kamar dai nacan ɗakin ta fara shinshinasu ɗaya bayan ɗaya. Sai dai abin mamaki babu wanda ƙamshinsa yay kama da wanda takeji a jikinta. (Dole ne ma na gano, kuma ta wannan ƙamshin insha ALLAH). Ta ayyana a zuciyarta cike da alwashin hakan. Alwala taje ta dauro jin makara na neman riskarta. Bayan ta idarne kuma ta sake nutsuwa wajen ƙarema ɗakin kallo yanda ya kamata. sai yanzu ma ta gane ba inda ta kwana a jiya bane wani ne daban. Sai dai shima wannan ɗin ya matuƙar haɗuwa fiye ma da wancan ɗin. Saɓanin wancan da tsarin komai na cikinsa ke fari anan kuwa komai blue ne, ga wani ƙamshi na fitina na tashi kamar dai wancan. Abu mafi ban mamaki nan ɗin dai duk da ya nuna ana tsaftaceshi a hargitse yake kamar anyi dambe a cikinsa. Ita kanta dama a shigarsa toilet har mamakin yanda taga kanta a birkice tai, dan tasan dai tsaf ta kwanta kuma bata buge-buge a barcin. Son yin salla a kan lokaci ya sakata bata maida hankali ba sai yanzu data idar ta samu nutsuwa. Tayi tunanin gyara ɗakin da fita binciken turaren nan na jikinta da alama ya tabbatar mata mai shi ke son wasa da tunaninta, sai dai wata zuciyarta ta bata shawarar ajiye waɗan nan batun ta sake kwanciya irin ta jiya tai likimo kozata samu bakin zaren ta hanyar shigowar wanda take zargin kamar jiya. Ta gamsu da hakan tako kwanta, sai dai tsahon kusan awa ɗaya babu wani wanda ya zo ɗakin, babu ma alamar wani ɗin zai zo harta tashi akan dole ta kimtsa ɗakin ta shiga wanka. Kayan data samu a lokacin gyaran ɗakin ta sanya babu ko ɗar a ranta. Tayi ƙyau sosai, ta kuma sake baza turarurrukansa a jikinta kamar jiya sannan ta fice a sannan kusan ƙarfe bakwai da rabi...


         Da ƙyar yau ma ta iya gano ɗakin data kwana a shekaran jiya, cikin Sa'a kuma ta samesa a buɗe. Shiga tai da sallama duk da bata zaton samun kowa a ciki. Tsaf yake kamar batai bidiri cikinsa ba jiya, an canja zanin gadon ga kamshi na tashi mai daɗi da sanyin ac. A yanda hadiman suka nuna sun ɗan yi shock da ganinta ya ɗan sakata a mamaki, amma sai ta dake babu alamar hakan gareta ta nufi ɗaya daga cikin kujerun falon tai zaman ƙasaita da ita kanta bata farga da yinsa. Hadiman da duk ganinta ya sakasu a firgici suka iso gabanta suka zube domin miƙa gaisuwa. Rayukansu kam cike da mamaki dan kowa dai yasan a jiya ba sashen ta kwana ba, tun fitar yamma da tai bata sake dawowa ba har suka rufe waje suka kwanta. Tun bayan idar da salla asuba kuma suka fito balle suce koda safen nan ta dawo. 

      A fisge ta amsa gaisuwarsu tana mai sauke manyan fararen idanunta akan ƙyaƙyƙywan tray ɗin dake ajiye a table ɗin gaban kujerar data zauna a jiya wadda koda ba'a faɗa mata matsayin kujerar ba tasan ta zaman Shahan-shan ce. Ɗan juyiwa tai ta dubi hadiman da har sun fara miƙewa. Ta jeho musu tambaya da faɗin, 

  “Wannan fa?”.

     Cikin sauri mai sanye da kayan kuku ta amsa da “Shayi na farko da Shugaba ke sha bayan gama motsa jiki”...

       “Kayan haɗin sa?”.

   Ta tambaya a takaice. Nanma da tsumar jiki ta lissafa mata. Iffah ta yamutsa fuska da sake harɗe ƙafafu. “A canja minsu da tatattun kayan itatuwa da ganyen koren shayi”.

    Cikin tsoro duk suka dubeta, ta sake tsuke fuska da musu alamar gargaɗi da hannunta. Kamar ƙyaftawar ido kukun ta ɓace a wajen. Cikin abinda bai fi mintuna goma sha biyu ba aka dawo da wani sabon haɗin shayin. Miƙewa Iffah tai da nuna hanya alamar ta kaita inda yake. Anan ma ba karamin tsoro bane ya bayyana a idanun hadimar har ma da sauran ƴan uwanta, amma tsayayyun idanunta masu ƙarfi fiye da girman shekarunta ya hana hadimar iya furtawa a baki. Kai tsaye hanyar dake acan gefe ta nufa, sai dai suna zuwa ta dubi Iffah a mariraice sai kuma ta duƙar da kai. 

      “Tsahon rai da amincin UBANGIJI su zama kariya ga Zawjata-almilk, wlhy bani da hurumin tsallake wannan iyakar”.

     (Kinyi mai wuyar) cewar Iffah a zuciya. A zahiri kam hannu ta miƙa ta amshi tray ɗin batare da tace uffan ba. Cikin rawar jiki hadimar ta buɗe mata ƙofar gilashin dake a wajen, Iffah ta ɗan tsirama steps na bene daya bayyana alamar shi zatabi kusan na sakan ashirin kafin ta maida ga hadimar da kanta ke duƙe, “Zaki iya komawa bakin aikinki”.

    Kamar dama umarnin take jira, cike da sassarfa tabar wajen ƙwaƙwalwarta fal mamakin wannan baiwa har zufa na taruwa a goshinta.


      ★Ba karamin sake jinjinama al'amarin wannan masarauta Iffah tai ba, dan tana ɗaura kafarta a step na farko na'ura ta fara shelanta kasancewarta a wajen. Abu mafi bata mamakin kalmar sunan da na'urar ta ambaceta da shi. Kafin ta sami damar wani waige-waige lifter data kwasota ta direta a wata ƙofar da hadimai biyu ke tsaye hannunsu riƙe da manyan bindugu. Tayi mamakin ganin yanda suka rissinar da kawuna sunka fara gaisheta. (Shin sun yarda da zancen na'urar ne? Kokuwa sun santa a matsayin Zawjata-almilk ɗin ne dama?).

    Da wannan tambayar da babu mai bata amsa ta cigaba da takawa a hankali kasancewar sun buɗe mata ƙofar wajen. Iska mai daɗi dake busawa ta sanyin safiya ta fara cin karo, ta zuƙa a hankali tana mai lumshe idanunta. Sai kuma ta buɗesu a sannu, a lokaci ɗaya bugawar zuciya da tsinkewar jini suka nema sarƙe numfashinta, neman daburcewa take sakamakon abinda tai tozali da shi. Babu shiri ta maida idanunta ta rumtse tana mai ambaton sunan ALLAH akan wannan mummunan gani da tai. To mummunan gani mana, dan tunda take a rayuwarta bata taɓa tozali da namiji a irin wannan yanayin da idonta ya gane mata ba.. Ji take kawai ta zura da gudu ta koma, sai dai hadiman dake bayanta fa? Wane irin kallo zasu mata bayan na'ura ta gama fallasata a garesu. Tabbas nuna gazawarta na nufin faɗuwarta, faɗuwarta a matakin farko kuwa na nufin rushewar gaba ɗaya nasararta.

    Da karfi taja numfashi mai kauri ta haɗiye, kamar zatai kuka ta sake buɗe idanun a hankali, sai dai koda wasa bata yarda ta kalla gaban nata ba.....


        Shigar ƙamshin turarensa da bayan shi babu wani mai irinsa da sautin takun takalman ƙafarta ya sashi juya sharɓeɓen takobin dake a hanunsa cike da gwanancewa ya karci ƙasa ya gocema Aamin nasa da suke wasan tare ya juyashi zuwa hannunsa na haggu saɓanin na dama sai gashi akan wuyan Iffah da numfashinta yay wata irin mummunan fisga.

    “Who are yo.....?”. 

   Yay yunƙurin faɗa cikin alamun bayyanar fushi mai haɗi da isa da ƙasaita, sai dai kalmar ta gagara ƙarasa fita a harshen nasa dalilin tozali da abinda bashi yay tsammanin gani ba. Tar-tar fuskokinsu suka bayyana akan takobin mai matuƙar ƙyalli da sheƙi da kai tsaye za'a iya kiranta faɗama jini na wuce........✍️

     

No comments

Powered by Blogger.