Daudar Gora Book 1 page 42


 *_42_*



.........Kasancewar Barrister Akeem ba baƙo bane na shigowa gidan masu hidima a gidan suka dinga gaidashi. Amsa musu Barrister Abdallah ya dingayi da fara'a da kuma muryar Barrister Akeem data zama yana

kwaikwaya a yanzu kamar yanda aka horar da shi. Ya iso katafaren falon da yaji komai na more rayuwar duniya, ga kamshi na tashi irin wanda aka san duk wani jinin ƙasar ruman da shi. Cikin girmamawa ya kai zaune fuskarsa da murmushi ya shiga gaida babban mutum ɗin dake zaune a falon cikin shigar kayan ƙasar na alfarma. 

     Da ƴar sakin fuska mutumin ya amsa masa da faɗin, “Barrister sai yau ake ganinka? Bayan kuma tun jiya nasa a sanar maka na dawo ƙasar”.

         “Amun afuwa ranka ya daɗe, an ɗan samu wani tazgarone daya riƙeni a dalilin zaman da Boss namu ya kira, nayi zaton zamu tashi akan lokaci harna iso nan ɗin sai hakan bata yiwu ba, ganin dare yayi kawai na wuce gidan dan nasan kana bukatar hutu”.

    “Hakane kam. Yaya aikin naku?”.

“Alhamdullh ranka ya daɗe munata bubbugawa”.

         Murmushi mutumin yayi, sai kuma ya ɗan gyara zamansa da zuƙar shisha ɗin hanunsa yana gyaɗa kai. Shiru ya biyo baya kasancewar ɗaya daga cikin masu masa hidima ya kawo ma Barrister shayi. Sai da ya kammala ya fice mutumin ya ajiye marikin shisha ɗin da fesar da uban hayaƙin daya tara a bakinsa.

   “Barrister dama ina maka wani neman gaggawa ne akan abokinka mai shegen taurin kai Barrister Abdallah Aas”.

       “Tofa oga ya ƙara yin wani laifi ne?”.

    “Kusan haka kam, dan akwai wani case na aminina dake a rufe sai ƙoƙarin ganin ya buɗosa yake yi. An masa gargaɗi kusan sau uku amma bai ji ba har sai da yajama kansa aka kauda shi kasan mutumin na ka da taurin kai”.

         “Kauda shi kuma ranka ya daɗe?”.

   Barrister ya faɗa cikin nuna rudanin as shine Barrister Akeem. Murmushi mutumin yayi irin nasu na manya yana ɗage kafaɗa alamar ko'a jikinsa. “To in basu kaudashi ba mi kake so suyi Barrister?. Yana da taurin kai ne gaskiya. Nasan dai kaji zancen tashin bomb ɗin can na jihar Hubab..?”

      “Yes Yes ranka ya daɗe, ai kowa ma dake ƙasar nan yaji wannan baƙon al'amari mai tada hankali tunda bai taɓa faruwa ba a wannan ƙasa tamu......”

    “To ga abokinka kam yaja ya faru, dan an tada wannan bomb ɗinne da shi kasancewar a cikin motarsa aka sakashi”.

    A matuƙar razane Barrister ya furta “What! Ranka ya daɗe abokin nawa?”.

        “Kaga kwantar min da hankalinka wannan ba wani abu bane. Sakamakonsa ya amsa a hannunsa. Kaga ko anan gaba masu shirin taurin kai irin nasa sai su kiyaye. Ba wannan ne abin damuwa bisa maƙasudin kiranka nan ba. Muna son ne ka maye gurbinsa a wancan case ɗin ne domin kwaso mana dukkan wasu bayanai da ya haɗa. Mun zaɓoka ne saboda kamaninku ɗaya, har yanzu kuma babu wanda yasan da shi bomb ɗin ya tashi. Kafin masu bincike su gama gano motarsa ce wadda bomb ɗin ya tashi a ciki muke bukatar ka kamla komai”.

       “Amma ranka ya daɗe......”

Hannu ya ɗaga masa da sauri. “Karkace komai Barrister, nasan zafin rasashi kakeji, ina maka ta'aziyyar hakan. Sai dai ka sani, wanda ya ɓatar da shi kaima zai iya ɓaddaka kai da duk a halinka wannan yafi shan shayi sauƙi a garesa. Dan haka ka kula. Akwai saƙo na kafin alkalami a motar ka mu yini lafiya🙏”.

       Hakan da yay na nufin ya sallamesa. Barrister Abdallah ya miƙe jiki a sanyaye. Gaba ɗaya tunaninsa ya rabu da zuciya da kwakwalwarsa. A yanzu kam ya gagara fahimtar komai gaskiya. Shin idan har waɗan nan ɗin sune mugaye a garesa, waɗan da kuma su yake bibiya a case ɗin su Babiy to sukuma waɗan da suka sakashi wannan aikin fa? Kenan fa kuɓutar da shi sukai a waccan ranar ko mi abinda sukai ɗin ke nufi? Ya ALLAH mike shirin faruwa da ni ni Abdallah?. 

      Ya tambayi kansa batare da yasan ina zai kama ba har ya ƙaraso jikin motarsa ya shiga. Da ƙyar ya iya tuƙin zuwa waje, yana hawa titi ɗan nesa da gidan aka dakatar da shi akan cewar yay parking ta cikin bluetooth ɗin kunnensa. Hakan ba karamin taimako bane a garesa, dan a yanda yake jinsa tabbas zai iya kife kansa a titin ma gaba ɗaya........


      

        ★★....  ★★.....


    

     Babu kowa a ɗakin sai wani irin ƙamshi mai matuƙar saka jiki kasala da sanyin ac. Iffah ta lumshe manyan idanunta tana ambaton sunan ALLAH da sake buɗesu. (Kai kai kai duniya fa na inda take) ta ayyana a zuciya tana dire tray ɗin hannunta saman wani ɗan table dake gaban ƙyaƙyƙyawar kukera ta hutawa. (Dama ce fa wannan) ta zabura dalilin wancan furucin da zuciyarta ta ayyana. “Tabbas dama ce kam”. Ta maimaita a fili tana ɗan waige-waige a nutse cikin hikima kuma ɗan gudun kar ya zam akwai camara a ɗakin kamar yanda aka bazasu ta waje ko'ina a sashen. Adai iya dubanta babu kamar sauran ɗakunan data kwana, dan haka ta cire takalmanta cikin sanɗa ta nufi ƙofar toilet da zuciyarta ke raya mata yana ciki. Tabbas yana cikin kuwa dan jin motsin ruwa. Ta daga hannayenta sama alamar Alhamdullah sannan ta baro wajen. Da ma'ajiyar turarrukan sa ta fara, sai da ta gama ɗagasu ɗaya bayan ɗaya ta shinshina. Sam babu alamar irin wancan, cikin damuwa ta maida ta rufe badan zuciyarta ta wankesa da zargiba har yanzu. Dan ta gama haƙƙaƙewa aljanun tsafinsa ya tura suka ɗakkota a daren na jiya dan ya cika burinsa. Amma ALLAH ya hanashi sa'a shiyyasama taga ɗakin kaca-kaca kamar anyi dambe a cikinsa. Da alama sun gusar mata da hankaline shiyyasama bataji sanda aka ɗakkotan daga can ɗin ba.

     Harta juya zata fita zuciyarta ta sake nata shawarar ta ɗan sake duddubawa ko zataga wani shaida da suke buƙata akansa. Cikin yanayin dai ɗan tsoro-tsoro na mara gaskiyar dake gudun a kamasa take ɗan buɗe-buɗen ta, sai dai abin mamaki idan ka cire turarrukan data gama dubawa, da wasu tarin books a cikin wata ƙyakykywan show glass, babu wani abu a ɗakin bayan kayan gado da na ƙawata adon ɗakin kuma. Sai kuma kayan barci kala-kala a cikin wani dogon gilashi shima alamar matsayin wadrub, sai dai kasancewar zallar gilashi komai ana gani fes dan duk rataye suke a jikin hanger ma.

     Iffah da gaba ɗaya kanta ya kulle na mamakin ina kayan da yake sakawa? Da takalma? Su agogo dama duk wani nau'in kayan da yake ado dasu fa?. Dan acan ma sauran ɗakunan da ta kwana iya irin abinda ke anan ɗin kawai ta gani. Lallai dole akwai abinda yake buƙatar tayi nazari a kansa kenan? (Minene to?) Zuciyarta ta ayyana mata tare da katse tunaninta sakamakon jin wani masifaffen kamshin shower gel da tsumammun turarrukan wanka ƴan asali da bata taɓa shaƙar irinsu ba.

       A ɗan firgice ta juyo, sai kuma ta sake juyawa da sauri tana mai rumtse idanunta da faɗin, “Wayyo ni Iffah” ta nufi ƙofar fita da matuƙar sassarfa tamkar zata kifa dan hatta da tsumar jikinta a bayyane take..

    

       Shiko da komai ya faru dominsa babu alamar hakan ya damesa. Dan ko kallon inda take baiba tunda ya fito. Babu ma alamar yasan da ita a ɗakin tattare da shi. Amma abin mamaki sai gashi ya zauna a kujerar da table ɗin ke tare da ita, wanda kuma anan ne Iffah ta ajiye shayin nasa. banbancin ɗanɗano da wanda ya saba sha kamar ɗazun ya sakashi yin tsamm da tsurama shiyin ido tamkar a cikinsa yake neman amsar sanin yaya hakan wai ke faruwa?. A zahiri ko babu wani abu a fuskarsa sai ma glowing da take irin na mai lafiyayyar fatar data jiƙu da hutu da jin daɗi. Yatsunsa biyu ya ɗan kai saman goshinsa ya murza kusan tsahon sakanni arba'in, kafin kuma ya janye yana mai ajiye kofin ya miƙe batare da ya sha ba. Ta can wajen gilashin da kayan barcinsa suke ya taka, hannunsa ya daura akan gilashin sai gashi gaba ɗayan drawer ɗin ta zuge a hankali ƙofa ta bayyana. Takawa yay ya shige, ta maida kanta ta zuge........


        (😏😏an wani rufe dan kar na gani, to Iffahn mu zata gano mana ai ehe🚶😞).


     ★★..... 


  Da gaske dai ɓatan Sayeed Khairul-Bashar ya tabbata a cikin masarauta. Dan Iya duk wani bincike babu wata alama ta yana a cikin gidan. Iyalansa sai kuka suke duk sun hargitsa masarautar. (Kamar yanda kukaji a baya Sayeed Khairul-Bashar Aami ne a wajen su Tajwar Haysam, Miran Arshaan, Miran Jasim da dai sauransu. Kaka kenan a wajen Tajwar Eshaan shi kuma. Sayeed Khairul-Bashar da Tajwar Abdul-majeed kakan Tajwar Eshaan ƴan uba ne suma. Kamar yanda a yanzu Tajwar Eshaan ke shan gwagwarmaya a hannun su Miran Jasim haka mahaifinsa Tajwar Haysam yasha wannan wahalar a hannun Aamin nasu irin su Sayeed Khairul-Bashar. Sai dai ko kusa basu ci galaba ba dan Tajwar Haysam ma dai kaifi ɗaya ne kuma tsayayyen mutum kamar yanda kuke ganin Tajwar Eshaan a yanzun. Wannan rashin nasarar tasu akan Tajwar Abdul-majeed da ɗansa Tajwar Haysam ce ta dawo kan Tajwar Eshaan a yanzu, sai dai kuma da alama bazai taɓa ya raga musu ba. A gefe kuma su Miran Jasim na amfani da wannan damar wajen dama garinsu akan Tajwar Eshaan... ALLAH ya sa kun gane ni dai ba ruwana🥱🚶)


        Duk bidirin da ake Tajwar Eshaan bai sani ba, dan yau ya fita fada ne a makare. Koda ya isa fada kuma aka kawo zancen da farko bai ɗauka abin na gaske bane, dan haka cikin halin ko'in kula irin nasa ya nuna musu maybe yayi fitar da kowa baya buƙatar ya sani ne. A bashi lokaci a gani. A cikin wasu ƴan majalissar tasa wasu sun gamsu da wannan jawabi, harma aka fiddashi waje dan hankulan mutane su kwanta. Sai dai a wani gefen kuma jawabin Shahan-shan ɗin tamkar samun wani makamine na dukansa da shi ga maƙiyansa na ɓoye dana zahiri, sai dai sun danne a yanzu basuce komai ba suna jiran lokaci........


     ★★..... BARRISTER ★★.....


    Ruɗanin da Barrister yake ciki ya wuce duk yanda mai hasashe zaiyi tunani. Gashi tunda suka maidashi gidan suka sake kullesa a ɗakin babu wanda ya waiwayesa har duhun magriba ya kawo, bayan idar da sallar isha'i ne aka kawo masa abinci. Dan haka ya fuskanci mai kawo abincin da alamar yar yanzu zuciyarsa ta kasa tsayawa waje ɗaya.

         “Dan ALLAH ina son magana da ogan ku Akhi. Ina da abubuwan tattaunawa da shi masu yawan gaske da muhimmanci”.

    Kamar bazai tanka masa ba sai kuma ya amsa shi da faɗin, “Boss baya nan, ganinsa kuma abune bamai sauƙi ba dan bana jin ma yana ƙasar. Karka damu idan yana buƙatar magana da kai zai zo da kansa basai ka nema hakan ba”. Daga haka yay ficewarsa. Jiki a sanyaye Barrister ya bisa da kallo harya maida ƙofar zai rufe yay saurin faɗin, “Na roƙeka kota wayane ka haɗamu, da gaske maganar da zanyi da shi nada matuƙar muhimmanci, da kuma buƙatar yinta da gaggawa”.

     Jimm saurayin yay yana kallon Barrister ɗin daga inda yake, sai kuma ya ɗan rausayar da kansa da faɗin, “Okay duk yanda mukai zan dawo”.

     “Nagode sosai”.

   


   Baifi mintuna biyar da fita ba sai gashi, har lokacin Barrister na zaune a inda ya barsa. Ya miƙa masa wayar hannunsa. Cikin jin daɗi Barrister ya amsa. Shi ya fara sallama da gaisuwa batare da la'akari daya girmi boss ɗin nasu ba. Amsa masa akai daga can a taƙaice, nan ma bai nuna ya damu ba cikin tashin hankali ya fara maganar dake cimasa rai..

         “Alhmdullah na cika umarninku, sai dai sakamakon dana samo ya matuƙar rikita tunani na. Dan wannan case ɗin case ɗin da nake yine, kuma a dalilinsa naje ƙauyen Lufana. Yanzu kuma sun bani aiki akan kaina, Ina cikin ruɗani sosai, dan na gagara fahimtar manufarku ku da su, shiyyasa gaba ɗaya ruɗani ya kasa barina na fahimci abinda ya dace na fahimta....”

     “Karka damu kanka da son sai ka fahimta Barrister. Kai dai kai musu aikin da suka buƙata, basu bayanai akan naka da case ɗin kawai”.

    “Idan nai haka zan saka rayuwar bayin ALLAH ne a haɗari, wlhy mutanen na mutanen kirki ne komai an shiryashi garesu ne bisa wata manufa. Ina matuƙar jin tausayinsu, an rabasu da ƴaƴansu har uku, an kuma biyo ta wata hanyar rusasu da shine nake son ma san dalili, yanzu kuma ace nine da hannuna zan miƙasu, idan nai hakan bazan taɓa yafema kaina ba”.

    “Baka da wani zaɓi bayan hakan Barrister. Idan kuma ka shirya rasa iyalanka ne fine”. Kitt aka yanke wayar. Barrister dake jin hajijiya na ɗan kwasarsa ya dafe bango da sauri yana mai ambaton sunan ALLAH domin neman ɗauki.........✍️

     

No comments

Powered by Blogger.