Daudar Gora Book 1 page 49
*_49_*
.........Tunda al'amarin nan ya faru babu wanda zai ce yaji koda motsinsa a masarautar hatta hadiman dake zagaye da sashen nasa. Har masu dafa abinci da amintacen hadiminsa dakan iya ganinsa ko kai masa saƙo ma ba ganin nasa suke ba.
Abinci kuwa yanda suka shirya haka suke kwashesa. Amma hakan baisa sun gajiya ba kasancewar aikinsu ne. Yau ma kamar kullum sun tsaftato ko'ina sun kuma bajesa da ƙamshi mai taɓa kuzarin mai shaƙa. Bayan an haɗa abincinsa da duk a kwanakin nan yanda ake shiryashi haka suke zuwa su kwashe duk suka koma hawa na uku da shine dai wajen zamansu, sai amintacen hadiminsa da kawai ke da lasisin zama a hawa na karshen ne yay zaman gadin abincin gudun samun matsala duk da babu wani mahaluki a zahiri daya isa ketowa har nan ya saka wani abin cutarwa da ake tsoro.Kusan ƙarfe takwas abinda hadimin bai zaton gani ko tsammani ba yay matuƙar kidimashi. Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ne da suka kwashe kusan kwanaki takwas batare da sanyashi a idonsu ba ke tunkaro falon cikin takun ƙasaita da izza. Cikin rawar jiki da ruɗani hadimin ya zube a ƙasa bakinsa har rawa yake wajen miƙa gaisuwa. Kamar yanda ya saba kai kawai ya ɗan jinjina batare da damuwa da hadimin ya gani ko bai gani ba ya gittashi ya wuce. Hadimin ya ɗan lumshe ido da zuƙar daddaɗan kamshin shugaban nasa yana mai sauke ajiyar zuciya a ƙasan maƙoshi.
Tajwar Eshaan da baima san yanayi ba a hankali ya kai zaune cikin kujera ya harɗe ƙafafu cikin salon zama irin na sarakan da suka isa. Sai a lokacin hadimin ya zaburo ya sake zubewa gabansa.
“Ya shugabana ko ana bukatar shayi?”.
Kansa kawai ya ɗan jinjina alamar eh yana kauda fuskar sa gefe. Da sauri hadimin da ke satar kallonsa ta gefen ido ya miƙe, haɗaɗɗen daning table ɗin mai cike da kayan breakfast ya nufa, cikin abinda baifi mintuna biyu ba ya dawo ɗauke da ƙaramin tray da butar shayi a samansa. A ɗan tebirin gaban kukerar da yake zaune ya ajiye. Ya tsiyaya shayin a ƙaramin kofin. Baya yaja sosai kansa a ƙasa cikin ƙanƙan da kai yace, “An kammala ya shugabana”.
Baiyi magana ba, bai kuma motsa ba har bayan wasu mintunan biyu. Bayan ya kai shayin bakinsa kusan sau biyu ya ɗan dubi hadimin dake tsaye kai a risine ya sake kauda kai. Maganace a bakinsa, amma sai da ya sake jan wasu sakkani kafin ya furta ta a fisge.
“Mike faruwa a daular ruman?”.
Tambaya mafi rikitarwa, mamaki, al'ajabi harma da ruɗaki ga duk wanda ya jita a bakin da ba'ayi tunani ko tsammani ba ce ta riski hadimin. Falon ya shiga waw-wai-gawa cikin tsumar jiki. Tabbas shine dai akaima tambayar ba wani ba. Sai duk ya sake ruɗewa ba shiri ya zube ƙasa akan guyawunsa. “Kariyar UBANGIJI da ingantacciyar lafiya su kasance ga shugabana, abubuwa da yawa sun faru marasa daɗin faɗi da sauraren ji. Sai dai ban san wanne ake bukatar na isar ba”.
Tamkar ma bashine ya buƙaci jin ba, tsahon wasu mintuna da zasu iya kai huɗu ya sake amsawa ciki-ciki.
“Komai”.
Kai hadimin ya jinjina yana mai sake ƙan-ƙan da kai, ya fara zayyano komai tiryan-tiryan tun daga randa aka ɗauke Iffah sashen har zuwa yau ɗin nan da yake gabansa. Ya kare da faɗin, “Idan na faɗi abinda ba shi shugabana ke buƙatar ji ba ina mai neman afuwa”.
Idan gunki ya motsa bayan ƙare abinda ya buƙaci ji to ya motsa. Hadimin dama dai baya tsammanin samun sharhi ko tambaya ko fashin baƙi daga abinda ya faɗa, dan haka yaja bakinsa yay shiru yana ɗan satar kallonsa ta gefen ido. Ba yau ya fara ganin Tajwar Eshaan ɗin ya danna wani abu a gefen kujerar da yake zama computer ta bayyana ba kamar yanda yayi a yanzu, sai dai a iya hasashensa da dube-dube idan yana gyaran saman ya kasa gano komai......
★★... KAUYEN JUMNA ★★
Hukuncin da kaka ya yanke, sakamakon tashin hankalin da suka kwana a ciki shi da Ummu da Iyyani tun da sassafe suka fito da nufin komawa gidan Babiy na daular ruman gaba ɗayansu. Kaka ya gama shirya tunkarar kowa gaba-da-gaba a yanzu, dan haka babu ko ɗar tattare da shi. Saurayin nan na kwanaki dake ƙoƙarin shigowa layin gidansu yay saurin taka birki idanunsa a kansu. Tabbatar da su ɗinne dai ke tafe a ƙafa ya sashi ɗaukar wayarsa da sauri-sauri ya latso wata lamba. Sai da tana gab da tsinkewa aka ɗaga, da ƙyar ya iya haɗa haruffan sallama bai jira an amsa masa ba ya ɗora da faɗin, “Oga abin mamaki gasu nan suna fitowa da alama ma garin zasu bari”.
“Woow interesting”.
Aka faɗa daga can cikin nuna ci da birgewa. Sai kuma aka ɗora da faɗin, “Maza ka juya ka koma kan ainahin hanya kafin su isa. Ka tabbatar nan da mintunan da basu wuce hamsin ba na gansu a gabana”.
“An gama boss”.
Saurayin ya faɗa da tsantsar girmamawa. Sam su Kaka dake tafiya hankalinsu bai kai kan motarba saboda Ummu dake tafiya a wahale, idan ma ta taka ɗaya biyu sai sun tsaya ta huta kafin su cigaba. Yayi jira na kusan mintuna goma sha ɗaya kafin su iso inda tuni ya iso shi yay fakin. Da sauri ya fito daga lungun daya laɓe hanunsa riƙe da leda yana ɗan cillawa yana ƴar wakarsa. Kamar wani shiri sai ko idon Kaka dake ma Ummu nasiha ta daure su ƙarasa akan wannan saurayi. Yay ɗan jimm alamar shan jinin jiki, sai kuma ganin yanda saurayin ya gittasu babu alamar ya gansa ya sashi zabura.
“Ƴan samari na ce ba...?”
Kamar saurayin bazai kula ba sai kuma ya juyo a ɗan yatsine yana faɗin, “Kace mi....?” sai kuma ya ƙi ƙarasawa da nuna alamar shock kamar gaske. “Ya ALLAHU wa nake gaji haka kamar Baba?”. Kaka ya sauke ajiyar zuciya da jin shakkunsa gaba ɗaya ya gudu yay ɗan murmushi. “Kaga ja'iri ni ne ɗin dai, yaushe haka a gari babu labari?”. Kai a sunkuye saurayin ya shafa ƙeya yana murmushi. “Afuwa kaka uziri ne ya ciyoni har nai ƙudirin shallakeku a karo na biyu batare dana leƙa ba. Yanzu haka ma nan jirana ake saƙo na amsa anan ɗin fatana na kai Dahab (Daular ruman) kafin cikar awa ɗaya da rabi”.
Cikin jin daɗi Kaka yace, “Kai Alhamdullah da wannan zance. Ka ganmu muma can ɗin muka nufa a she da rabon ba sai mun sha wahala ba na jiran mota ma”.
Saurayin ya ɗago irin da mamakin nan, irin sai yanzu ya lura da su iyyanin nan. Gaishesu ya fara da ban haƙurin bai lura da su ba ne wai. Iyyani ta amsa masa da kulawa tana faɗin babu komai.
“Idan hakane Baba ai ku shiga kawai mu wuce, gaisuwar ma a karasata a hanya”.
“Af, e to kaima kayi zance na gaskiya. Amma ai zamu dakushe maka uzrinka”.
“Ai babu komai baba, sahun giwa ya isa take na raƙumi”.
Fuskokinsu ɗauke da murmushi duk suka shiga, Iyyani da Ummu a baya. Kaka ya shiga ta gefensa. Sai da ya tabbatar sun hau hanya ya gyara zaman norse mask ɗin fuskarsa da ƙyau, handkherciff ɗin gefensa ya matsar jikin ac kamar zai goge ya danna ac'n motar ya ƙure. A take ya busa tare abinda ke jikin handkherciff ɗin gasu Iyyani da kaka suka shaƙa har suna sakin ajiyar zukata kusan a jere. Kashewa yay da sauri yana faɗin, “Af kajini da karambani zansa Baba mura”.
Nauyin da kawunansu ya fara musu ya hanasu damar magana duk suka dafe kai kusan a tare, kaka ne ke ƙarfin halin cewa wani abu amma ya kasa, su Ummu kam tuni sunyi luuu jikin kujera alamar barci ya bugar da su. Kakan ma yay luuu a tasa kujerar. Nannauyan numfashi saurayin ya sauke da ɗan juyawa ya dubesu ta mirror. Tabbatar da sun suma yanda yake buƙata ya sashi janye Norse mask ɗin fuskasa da sakin murmushi ya latse wayarsa. Ana ɗagawa bai jira komai ba ya furta, “Done! boss”.
“Proud of you”.
Aka bashi amsa a taƙaice da ga can da latse wayar......
(Ta faru ta ƙare🤦😱)
★★.... ★★.... ★★.....
Tajwar Eshaan da bai sake bi takan hadimin ba kam hankalinsa gaba ɗaya ya tattara ne ga computer ɗin gabansa a yanda yake harɗe. Cikin nutsuwa yake sarrafata a take saƙonnin da yake buƙatar gani suka bayyana kansu. Hannu ya kai ya sake daidaita gilashin idanunsa da ɗan yamutsa fuska ganin dogon text message ɗin daya buɗo... Dai-dai nan takunta da ƙyamshin sassanyan turarenta ya fara rige-rigen isowa hancinsa tun kafin bayyanarta. Wani irin harbawa daya tilastashi ɗaga ƙwayoyin idanunsa kaɗan ta cikin gilashin yay sai ko suka sauka akanta. Sanye take cikin shirinta da baza'a kirasa mai matuƙar ƙawa ba, ba kuma mai ƙasƙantarwa ba. Babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta, ƙamshin turarenta ma a yau ƙasa-ƙasa ake iya jinsa. A zahiri zaka ɗauka yanayin da masarautar ke cikine ya sata kasancewa haka, sai dai a haƙiƙanin gaskiya komai a sukurkurce yake gareta. Duk wanda ya san alwashinta akan Tajwar Eshaan zai kalla wannan lokaci ne matsayin na farinciki a gareta domin ta kusanto hanyar cikar nasararta, sai dai zuciyarta danƙare take da wani irin ruɗani da ƙunci. Amma ta kasa dakatar da kanta, komai yana sarrafa kansa tare da ita ne tamkar wadda ake sarrafawa da na'urar remote. Yanda ta ɗanyi turus kamar wadda ta firgita da ganinsa ne ya sashi maida idanun nasa ƙasa cike da basarwa ga screen ɗin computer ɗin kai kace baima san da ko motsinta ba a wajen.
Da ƙyar Iffah ta iya jan numfashi, yayinda bugun da zuciyarta ke faman yi tsananinsa ya ƙara hauhawa. Sai dai mi, bata iya jin zata dakata duk da wani irin rauni da kasala dake cigaba da mamayeta. Tamkar wata hawainiya haka ta cigaba da takowa da sanɗa har inda yake, ta ɗan rissino ta gabansa ta dire tambulan ɗin hannunta a tebirin gaban nasa batare da tayi magana ba.
Amintaccen hadimin nasa da al'amarin ya zame masa kamar wani sabon abu, yay saurin dawowa hayyacinsa cikin rawar harshe ya fara miƙa gaisuwa gareta. Hannu kawai ta iya ɗaga masa a kasalance dai-dai tana kaiwa a kujerar dake gefen Tajwar Eshaan zaune. Dole ya miƙe da sauri ya fice a falon, dan cigaba da zamansa haramunne. Iffah dake jin kamar ta fasa kuka a dai-dai wannan gaɓar ta ɗaga idanunta da girmansu a yau gaba ɗaya ya shanye da ƙyar ta saukesu akan Shahan-shan da yay tamkar bai san da wani mahaluki mai numfashi a falon ba bayan shi.
“Bar... ka da sa.. fi... ya”.
Ta faɗa a rarrabe tamkar mai koyon magana. Da gaske yau ƴan izzar ne a kasan, dan haka bai nuna alamar yaji ba, dan bai ko motsa ba balle ɗauke ido akan abinda ke gabansa har kusan tsahon mintuna biyu kafin ya ɗaga mata hannu da ƙyar ya cigaba da abinda ke gabansa. A ƙalla da a ainahin Iffahr ta take salon nasa zai soke ta, bakuma zata iya haƙuri ba sai ta maida murtani. Amma abin mamaki sai ta miƙe jiki a saɓule ta nufi daning babu jimawa ta dawo da glass cup. Da kallon ƙasan ido ya bita zuciyarsa da jijiyoyin jikinsa na wani irin tsitstsinkewa tamkar suna masa ishara da abinda ke tinkarosa. A karo na farko takai durƙushe gabansa, tare da buɗe tambulan ɗin data shigo da shi mai ɗauke da tatacciyar madara dake gauraye da dafin macizai daban-daban har kala biyar. Jikinta rawa yake, har shi kansa sai da ya lura da hakan ta kallon gefen ido da yake mata. Madarar da bata wuce rabin kofi ba ta miƙa masa tana mai rumtse idanunta wasu hawaye da ƙarfinsu ya zame mata nauyi a ƙirji na gangarowa da gudun tsiya bisa ƙyakykyawar fuskarta.
Cak ya tsaya daga abinda ya keyi, duk da bai juyo gaba ɗayansa yana kallonta ba, hankalinsa kaf ya koma gareta. Kusan a tare zuciyarsa da jininsa ke tsitstsinkewa. Bashi da bukatar shan madara a wannan gaɓar dan a nasa tsarin da rana ko dare kawai yake shan madara. Sauran lokuta shayi ne mafi rinjaye da ruwa. Amma a yanzu duk da bahagon yanayin da yake jin jikinsa, da wanda yaga yarinyar a ciki sai ya kasa nuna bazai sha ba, tamkar shima ana ingizashi da remote ɗinne ya kai tattausan hannunsa saman nata a karo na biyu. Zabura tayi kamar wadda ke son dawowa hayyacinta sai kuma ta koma laƙwas tare da buɗe idanunta da sukai jazur ta sauke a kansa. Kallon cikin ido sukai ma juna na kusan tsahon minti ɗaya cirr batare da ɗaya su ya motsa ba abinda bai taɓa faruwa da su ba. Shi ya fara janye nasa a kasalance tare da hanunsa da ya zaro kofin daga cikin nata...
A yanzun ma firgigit tayi tamkar wadda ta farka a barci harda ɗan zabura ta kai hannu kamar zata riƙo kofin sai dai abin mamaki shi har ya kaisa kan baki...........✍️
(🤦Da zaka iya jina daga tawa duniyar da nace karka sha😭).
Leave a Comment