Daudar Gora Book 1 page 50
*_Part 1 End_*
*_(50)_*
........Dire kofin da ke empty a hanun Tajwar Eshaan dai-dai da komawar Iffah daɓas zaune ƙasan lallausan kafet ɗin kamar wadda aka zarema dukkan numfashi. Ta
matse jikinta tana mai ƙoƙarin riƙe tsumar da takeyi tare da miƙewa zumut. Ya kafeta da ido lips ɗinsa na ɗan motsawa alamar son cewa wani abu amma jin kai da ƙasaita ya hanashi yin hakan. Sai kawai yay ƙoƙarin janyewa cike da basarwa amma hakan ya gagara. Shi kansa bai san yaya akai ba, bai san tayaya ba kawai ya samu kansa ne da riƙo hannunta. A tare suka rumtse ido bisa mabanbanta dalilai. Karan farko na fara tasirin dafin macizan da suka gama gauraye jininsa ya matsota a hankali garesa. Babu zato Iffah tajita saman jikinsa da ke fitar da wani irin sirrintaccen ƙamshi mai karya zuciya. Numfashinta ne ya fisga da ƙarfi kamar mai cutar Asthma, ta buɗe ido da sauri dan gaba ɗaya hankalinta ya dawo jikinta. Zumbur ta mike jikinta na wani irin kaɗawa ta fara jan ƙafafunta da baya-baya siraran hawaye da batasan na minene ba na rige-rigen sakkowa. Cikin son danne tashin hankalin dake cigaba da gauraye jijiyoyi da tsokar jikinsa ya ɗago idanunsa da launinsu har ya fara canjawa ya zuba mata, gab taci tuntuɓe da centre table, kaifin idanunsa da tasirin su gareta a wannan gaɓar ya sata zubewa gaba ɗayanta akan tebirin...Wata irin zufa ce ta fara keto masa a dukkan ƙofifin gashinsa, yayinda tun yana iya ganin Iffah a kusa da shi har ta fara masa nisa. (Tabbas a kwai matsala) ya ayyana a zuciyarsa yana mikewa da ƙyar. Da kallo ta bishi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu tamkar zata buntsiro ta bakinta. Ganin ya shige ta miƙe itama cikin sassarfa, harta nufi ƙofa ta dakata, tamkar an janyo idanunta suka sauka kan computer ɗinsa, janyewa tai dan burinta tabar sashen kawai amma sai zuciyarta ta dinga ingizata ga computer ɗin. Bayanta ta ɗan waw-wai-gawa irin dai na rashin gaskiya kafin ta koma da baya ta zauna a kujerar tasa ta dasama rubutun fuskar computer ɗin ido. A karan farko ƙirjinta yay wani irin masifar motsawa. Tsabar kaɗuwa batama san takai hannu ga computer ɗin ba har rawar jikinta na bayyana. Babu tantama saƙon data turama Ajmaal ne na karshe, kaɗan ya rage zuciyar Iffah ta ɓaro waje a wannan gaɓar, babu shiri ta fara sama dukkan saƙonin data tura masa ne babu ko ɗaya daya goge, kowanne kuma babu canji a date ɗin data tura ne. Ai babu shiri ta fito ta shiga settings ɗinsa na WhatsApp. A Profile ɗinsa, dp pic.. ɗinsa, da komai na dai Ajmaal ɗin data sani ne... “Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairin minha”. Iffah ta ambata a karon farko numfashinta na barazanar barin gangar jikinta, computer ɗin tai ƙoƙarin singumowa gaba ɗaya dan maidata cinyarta akai rashin sa'a ta danna abinda bata sani ba kamar ƙiftawar ido suuu ta shige cikin table ɗin. Ƙwaƙwalwarta neman bugawa tayi tsabar rikicewa, ta shiga leƙe-leƙe a wajen sai dai babu abinda ta gane. Babu shiri ta zabura hanyar da Tajwar Eshaan ya bi tana haɗa hanya.....
A ɓangaren Tajwar Eshaan kam da kyar ya iya kai kansa ɗaki, dan jefa kafar kawai yake batare da yasan inda yake takawa ba. A ƙasan lallausan carpet ɗin ɗakin ya zube yana mai jingina jikinsa da yay sharkaf da zufa jikin gado, duk wata addu'ar da tazo bakinsa ambata yake, a haka Iffah data gano ɗakin da ƙyar ta shigo a ɗimauce. Idanunsa dake a lumshe ya buɗe a hankali suka sauka a kanta. Dukkan ƙarfin halinsa da jarumta ya tattaro ya adana tashin hankalin da ke tattare da shi. A ɓangaren ta itama ruɗanin da take ciki ya bada gudunmawa wajen makantar da ita yanayinsa, cikin rawar harshe idanunta dake tsiyayar hawaye a kansa ta durƙushe ɗan nesa da shi.
“Dan ALLAH na roƙeka ka faɗamin wanene kai? Miye alaƙar ka da Ajmaal?!”.
Babu alamar zai tanka mata, sai dai idanunsa dake sake rinewa jajur na tsaye a kanta ƙyam. Tsahon wasu mintuna ya lumshe su da sake buɗe su a kanta yana cije lips ɗinsa. Ya kauda fuskarsa cike da ƙarfin hali, da son saisaita muryarsa, a maimakon ta samu amsar tambayarta sai saɓaninta ya fito da ga garesa.
“Ki canja madarar da kika bani da wadda ke akan dining. Hatta kofin da na sha daga cikinsa karki bari”. Ya ƙare faɗa a wahale cikin cije baki da rumtse idanunsa.
(Iffah ki nutsu karki tonama kanki asiri) zuciyarta ta ayyana mata. Idanunta ta rumtse da karfi tana gyaɗa kai kamar wadda ake faɗamawa a cikin kunne. Sai kuma ta shiga goge hawayen nata da maida kallonta garesa a yanayin son kare kai.
“Ni ba batun madara na tambaye ka ba. Wanene Ajmaal?!!!”. Ta faɗa a matuƙar tsawace.
Birkitattun idanunsa ya rumtse da ƙarfi dan sam baya son hayaniya, balle ma a irin wannan halin da yake ciki a yanzu. Ya buɗesu kanta shima a fusace har sai da kallon cikinsu ya sakata zabura. Shima cikin tsawar da fisgar numfashi ya ce, “Babu abinda zai amfanar da ke a jin amsoshin da kike buƙata a yanzu. Kije kiyi abinda nace!! Kije!!!!”.
Ba ƙaramin firgici Iffah ta shiga da yanayin nasa ba. A zabure kuwa ta miƙe, batama san taya ta nufi ƙofa ba ganin kanta kawai tai a falo, harta nufi ƙofar lifter ta dawo da baya, tambulan ɗin madarar ta ɗauka, ta nufi dining wajen wanke hannu ta juyeta, kofin ta ɗauraye jikinta nata ƙyarma, gaba ɗaya ta nema jarumtarta ta rasa, sai da ta tabbatar ya fita ta dawo kan dining ɗin inda aka shirya break fast, madarar dake a jiye a wani tambulan ta ɗaga ta juye a wanda ta wanke ɗin, ta sake komawa ta wanke wannan, sai kuma ta rasa ina zata ɓoyesa kamar yanda zuciyarta ke bata shawara. Da kyar ta samu nutsuwar samun wajen makalasa, ta dawo harta sake nufar hanyar fita ta sake dawowa da baya, kofin da ya sha madarar ne, shima ɗauka tai ta wanke ta zuba sabuwar madarar ta kauraya ta maida inda ya sha. Sake nufar ƙofa tayi sai kuma ta sake dawowa ta nufi ɗakin dai da ka ganta kasan tana a cikin halin ɗimuwa....
A ɓangaren Tajwar Eshaan kam tana fita tari ya sarkesa, jin saukar abu a tafin hannunsa da yake tare bakin ya sashi saurin kallon hannun. “Jini..” ya ambata a hankali saman lips, sai kuma ya saki wani irin wahalallen murmushi da mai da kansa ya kwantar jikin gadon yana ambaton “Sunci nasara, sun sami nasara ta dalilinki *_My Sohaa_*....” tari ya kuma sarƙesa a hankali, sai dai murmushin na nan maƙale a fuskarsa har yanzu, sai faman lumshe idanunsa da suka birkice yake yana ƙoƙarin buɗesu da ƙyar fuskar Iffah da hawayenta ne tsaye ƙyam a cikinsu. Ba mutuwa yake tsoro ba a yanzu, baya da ƙurar da zai barta a ciki, ya tabbatar itace zata sha wahala, wahala irin wadda ba ita yay mata tanadi ba. Hakanne ya zaburar da shi, yaja jikinsa da ke saki gaba ɗaya da ƙyar zuwa telephone..
Ana ɗagawa ya fara magana cikin son ɓoye yanayin da yake ciki. “Duk wani cctv footage na safiyar yau zuwa yanzu na sashe na ka kwashe sa, amana ko kai na haramta maka ganinsa ka ajiyesa gareni, idan kuma na rasa raina ka damƙashi ga Zawja Fareedah....”
Bai bada damar cewa komai ba ya yanke kiran, da ƙyar ya maida akalar wani zuwa Malikat Bushirat....
*_MALIKAT BUSHIRAT_*
Yanayin tashin hankalin da masarautar ke ciki koma a ace ƙasar baki ɗaya dan yau mutanen da suka fito zanga-zanga akan murabus ɗin Tajwar Eshaan sunfi na kullum yasa ko fita batayi. A kallo ɗaya zaka iya ƙirga damuwarta saman ƙyakykywar fuskarta data koɗe matuƙa a cikin kwanaki ukun nan. Tayi duk wani ƙoƙarin ta iya iyawa domin ganin gudan jininta amma al'amarin ya gagara. Kuka bata san iya adadin da tayi ba ba kuma ta san wanda zatayi a gaba ba, dan anzo gaɓar da ko'a mafarki bata taɓa sakata a lissafin ƙaddararta ba.....
Shigowar kira a landline ɗin ɗakin barcin nata ya sata zabura dan yazo mata ne a bazata, dole ta ambaceshi da bazata dan Tajwar Eshaan ne kawai ke da wannan hurumin. Har tuntuɓe taci amma bata damuba ta caɓi kan wayar tunkan ta karasa gareta da ƙyau. Rawar jikinta dana harshe na faruwa ne a lokaci guda, sai dai muryar data doki tsakkiyar dodon kunnenta ta saka numfashinta tsaiwar wucin gadi....
“Ammie!...”
Aka faɗa da ƙyar cikin kuma rawar harshe mai fidda sautin nakasashshiyar murya mai tabbatar da amon razani ga mai saurare.
“Saiful-malik!!...”
Ta ambata itama tare da fisgar numfashinta dake kaikawo a iya maƙoshinta zuwa cikin baki kawai. Shi bai sauka a huhu ba, bai kuma fita ta hanci ba. Bata ma san ta saki wayar ba ta fice...
“Ya ALLAH Akia!...”
Jasrah dake shigowa ta faɗa da sauri tana riƙo Malikat Bushirat da gaba ɗaya idonta ya rufe da ruɗani. Son ƙwacewa take tana ambaton “Eshaan.. Jasrah Eshaan.. Eshaan zasu kashe min shi”.
Sam Jasrah bata fahimci inda ƴar uwar tata ta dosa ba, dan haka tai saurin katseta da faɗin, “Na shiga uku Akia dan ALLAH nutsu kimin bayani, mi ya dakesa?”.
Ina Malikat Bushirat ta kasa amsata, dan numfashinta ma har ya fara fisga. Bata haɗa soyayyar Tajwar Eshaan da komai ba a duniya. Tana masa wani irin makahon so mai wahalar fahimta. Duk yanda Jasrah taso tanƙwarata ta kasa, sunan Eshaan kawai take ambata da son fisgewa ta fita. Bazai yiwu ta barta ta fita a haka ba, dan haka tai saurin danna ƙofar bedroom ɗin da ƙafa. Hankaɗata Malikat Bushirat tayi, duk da taji zafi dama gata ba wani ƙwarin jikin take ji ba amma haka ta daure ta murza key. Da ƙyar ta iya zarewa ta sake riƙo Malikat Bushirat tana mai fashewa da kuka. “Akia dan ALLAH ki sanar min, fitarki a haka ba itace mafita ba, idan ma akan masu zanga-zanga ɗin nan ne ki kwantar da hankalinki jami'an tsaro bazasu barsu su ɓalla koda gate na farko ba........”
“Jasrah ki fahimceni.....!!!”
Malikat Bushirat ta katseta cikin ƙaraji sai kuma ta fashe da kuka. Tabbas babu lafiya, ƴar uwarta a haka lallai akwai matsala. Har taune harshe take wajen ambaton, “Zan fahimceki faɗamin ko a taƙaice ne Akia dan ALLAH”.
Da ƙyar Malikat Bushirat ta sanar mata a dunƙule, nan fa hankalin Jasrah ya tashi itama babu shiri ta zabura ta buɗe ƙofar......
★★....
Suɓucewar kan wayar a hannun Tajwar Eshaan dai-dai da sake faɗowar Iffah ɗakin a birkice. Gaba ɗaya ma ta mance matsayinsa da nata, tai kansa babu alamar hankalinta na tare da gangar jikinta. Tana zubewa gabansa yana faɗowa jikinta hannunsa dafe da kansa yana ambaton “Ammie...” a hankali, ga wata irin zufar da tai masa sharkaf kai kace wanka yay a lokacin.
“Na shiga uku ni Fhareedah!”. Da Iffah ta faɗa cikin kuka ya saka shi ɗago idanunsa dake matukar jazur zattashin hankali. Akanta ya tsaidasu a wani irin bahagon yanayi, ya lumshesu da ƙyar ya sake buɗewa a kanta. Lips ɗinsa da suka koma jajur saɓanin pink a da suna motsa a hankali ya saki wani wahalallen murmushi da har Iffah ta koma ga ALLAH bazata taɓa mantawa ba, dan ya zauna a allon zuciyarta tamkar rubutu akan dutse. kafin idon nasa ya koma ya lumshe gaba ɗaya tattausan hanunsa na dama saƙale cikin nata da bata san sanda ya riƙo ba...........✍️
*_ALHAMDULLAHI!!🙏_*
Leave a Comment