Daudar Gora Book 1 page 8

 


*_8_*



..........Zaune takai a kujerar dake duban tasa tana mai kallon agogon hanunanta. Ya saki murmushi cikin kafeta da idanu. “Daga zuwa sai duba agogo?”. 

    “Hakan dolene Sir, domin ko lokacin islamiyya zan cinye anan. Kaga kenan sai da tsantseni”.

         “Okay”.

Ya faɗa yana gyara zamansa. “Ba buƙatar maimaita abinda ya faru baya, na gaba kawai yanzu shine zanyi iya ƙoƙarin ganin na haɗu da abokin nawa koda ta waya ne, kin san aikin nan nasu yana hanasu samun isashen lokaci matuƙa kasancewarsu manya dake tare da babbar kafar yaɗa labarai mai aiki da kamar duniya gaba ɗaya. Ke yanzu a gareki miye shirinki?”.

    Kafaɗa Iffah ta ɗan ɗage cikin jan iska da hurowa. “Kusan dukan shirina a kammale yake, burina kawai nasamu yin hira da African Aye👁️‍🗨”.             “Indai hakane haɗuwa da abokina kawai ya rage mana, fatana dai bayan ni kar wanda yasan wannan hatta a gidanku, inba hakaba zamu iya shiga haɗarin da har burin rayuwarmu ma bazai cikaba bayan wannan. Nikuma zanyi duk yanda zanyi insha ALLAHU wajen hana wannan sirrin fita daga gareni....”

      “Shi abokinka ɗin fa?”.

“Baki da matsala da shi domin shi aikinsa ne”.

     Kai ta jinjina masa fuskata cike da murmushi. Sai kuma ta rissinar da idanunta alamar jin kunyarsa saboda kallon daya kafeta da shi. Kunyar nada nasaba da tuna yanda ta dinga wancakalar da shi da manufarsa a sanda yake malaminta. Sai gashi shine na farko data fara tunkara da matsalata a yanzu duk da kuwa tana kallonta a kan matsalar data shafi kowa na ƙasar Ruman ne. Sautin murmushinsa ya sakata ɗagowa ta ɗan kallesa, sai kuma ta sake kauda kanta gefe itama tana murmushin.

    “Hummm!”

Ya faɗa yana miƙewa. Itama miƙewar tayi batare data yarda sun sake haɗa ido ba. “Kije gida zamuyi waya”. 

           “Nagode sir, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka”.

      Jin sautin murmushinsa ya tabbatar mata jin daɗinsa, amma sai tai gaba da sassarfa tunkan ya sake cewa komai........


★__________________★


         *_DAULAR RUMAN (MASARAUTA)_*


            Katafaren ɗaki mai ɗauke da ƙayatattun kayan more rayuwa, kwance take bisa lafiyayyen gado da dukkan nau'in shimfiɗunsa suka kasance na alfarma. Sautin dariyar dake tashi cikin kunnuwanta tamkar mafarki ya sata buɗe idanu, cikin tsumar jiki ta ture lallausan bargon da take ciki, tamkar walƙiya ta dire ƙasan lafiyayyen kafet ɗin dake malale gaban gadon tai kneel down tamkar mai neman gafara, kanta a risine alamar nuna tsantsar girmamawa.....

      Tamkar shirin film ko labaran almara tsohuwa tukuf sanye cikin jajayen kaya ta bayyana bisa baƙar kujerar ƙarfe mai ɗauke da adon gold a cikin ɗakin. Baƙace matuƙa mai tsananin muni da jajayen idanu, yanda ta zauna ƙafa a harɗe kai ka ɗauka itace Shahanshan ɗin.....

        “Lafiya da tsahon rai su ƙara kasancewa a rayuwar *_Uwa_* mai share kukan masu kuka”. Hamshaƙiyar matar ta faɗa cikin tsantsar girmamawa ga tsohuwar dake harɗe saman kujerar tata tamkar sarauniyar ingila.

      Cike da isa da ƙasaita tsohuwar taja wani kakkauran numfashi da sake faɗaɗa girman ƙofofin hancinta ta hanyar hurashi, ƙara harɗe ƙafafunta tai tana mai motsa yatsun hanunta, idanunta jajaye kafe akan matar. Cike da isa da ƙasaita mai ɗauke da rashin daɗin muryarta ta tsufa ta fara magana. “Ta-ƙurya kin kusa cin nasara wajen cika sharaɗi na biyu akan alƙawarinmu. Na tayaki murna, saura sharaɗinki na ƙarshe, mafi wahala a cikinsu”.

         Ƙasa ta ƙarayi da kanta cike da girmamawa a gareta, da dukkan ƙarfin zuciyarta ta furta, “Kece madubin nasarata Uwa!, duk inda akaga naje da jagorancinki na isa. Yanda na cika na farko shima na biyu zan cika sa, nayi alƙawarin cika na ƙarshe ma fiye da yanda kike tsammani.....”

       Jajayen idanunta masu kama da garwashin wutar gidan biredi ta ɗago tana kallon ƙyaƙyƙyawar kuma hamshaƙiyar matar dake gurfane a gabanta. Ta ƙyalƙyale da wata dariya mara daɗin saurare ga kunen kowa, sai kuma ta gimtse tamkar ba ita tayi ba tana zaro manyan jajayen idanunta kamar na dodanni. “Ta-ƙurya nasan zaki iya, sai dai akwai wani babban ƙalubale dake tunkaro cikar nasararki ta biyu, kuma gab yake da cimmawa, idan baki gaggauta datsesa ba, zakiyi biyu babu”.

     A razane ta ɗago tana kallonta cikeda bushewar zuciya, sai kuma ta maida kanta da sauri ta rissinar “A gafarceni Uwa, a kawar da ko miye mai son yima cikar burina kutse. Na rantse da ALLAH daya halicceni, koda cikin yankin ahalina ne bana buƙatar numfashinsa Uwa!!”.

     Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi sai kuma ta gimtse fuska. Kanta ta shiga girgiza mata da dukkan isa. “Ta-ƙurya wannan karon akwai banbanci da koyaushe, dama na taɓa faɗa miki bayan cikar nasararki ta farko akwai ƙalubale dana gani akan cikar ta biyu, sai dai ba'a buɗe mun komaiba a wancan lokacin, alamar haka na nuna ƙarfin taurarin mai yunƙurin, amma a daren jiya dana tsananta bincike akan mafarkinki na gano wani yanki da ƙyar. Ƴar shilar suda na ƙoƙarin yin cara irin ta gawurtattun zakaru a kunnen bututu da taimakon wata zuciya mai son kusantar tata.”

     “A taimakeni a kawar mun dasu gaba ɗayansu Uwa. Ko a bani damar kawar da su da kaina”.    

    “Hhhhhhh!!!! Ƙaddarar ƴar shilar bata mutuwa bace cikin sauƙi. Tana kuma da ƙarfin taurarin da zata iya cin nasarar dusashe naki”.

        Bugawar da ƙirjinta yayi ta zata zuciyarta ce zata fito ta bakinta dan tsabar razana. Ta kafeta da idanu cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara. Sai kuma tai saurin maida kanta ƙasa ta rissinar tana faɗin, “A gafarceni Uwa”.

     Wani irin kakkauran numfashi mai cike da gargaɗi tsohuwar taja, cike da ƙasaita tana yamutse mummunar fuskarta ta cigaba da faɗin, “Zamu iya samun mafita sai dai akwai ruɗani a cikinta. Har zuwa yanzu kuma ban samu buɗewar ruɗanin ba kai tsaye. Dan haka kina da zaɓi biyu. Kodai ki ƙara yin duk yanda zakiyi igiya ta ƙullu tsakanin Malik-alMuluk da wannan ƴar shila muyi duk yanda zamuyi tazama cikamakin aikinmu na biyu, ko kuma ki barta ta cimma burinta.......”       

           Idanunta da suka kaɗa jajur tai ƙoƙarin ɗagowa, sai dai ta maidasu da sauri zuwa ƙasa. “Uwa amma kin faɗamin na cinye jarabawa ta biyu da zarar ya aura cika makin matansa shine matakan nasarata, yanzu haka akwai su su biyu da suka rage ɗauke da aurensa a kansu, zasu miƙasu garesa a karshen watannin nan kamar yanda na samu tabbaci. Taya zamu shigo da wata bayan aikin ya cika. A yanzu ya rage kawai samun cikar burina na ƙarshe ne a kansa. Miye dalilin shigowar wannan yarinyar abinda bai shafeta ba? Mizai hana ai mata wani hukuncin daya dace da ita?...”

      Hannu ta ɗaga mata cikin tarar numfashi da ƴar hasala-hasala, da kakkausar murya tana mai nunata da ɗanyatsa “Amma har yanzu ban sanar dake wadda ta dace ba, kuma damun san cutarwace na umarninmu gareki bazamu ce ta shigo ba”. 

    “Hakane Uwa, a gafarce ni. Sai dai Mahaifiyar Zak.......”.

Ta faɗa da alamun shiga tashin hankali mai girma, amma kallon da Uwa ta watso amata ya hanata ƙarasawa.

         Bata tanka mata ba, sai dai yanayinta ya nuna a hasale take, dan cikin kaushin murya da zunzurutun jin zafi ta kaɗa ƙahon hanunta mai kama da kwarkwaron gidan dodon koɗi. A take haske ya gilma, sai ga farar takarda a hanunta. “Ƴar shila burinta shine ɗaukar fansa, domin biyu a cikin masu ɗakin Malik-alMuluk da suka shuɗe jininta ne. Burinta shine bin kadin jininsu ta hanyar bayyanama duniya ko kawar da shi. Bayyanawar tata kafin cikar burinki faɗuwarki ne, a yanzu haka kuma ta haɗu da mai taimaka matan harma sun gama magana”.

      Sosai zuciyarta ta ƙara harzuƙowa. Amma sai batace komai ba saboda ganin Uwa a hasale take da ita. Cikin yin ƙara ƙasa da kai  tace, “Da ace bayan cikar burina ne kauɗi da ƙudirin ɗaukar fansar wannan yarinya ya shigo haske ne ga cikar burina. Dan zata ƙarasamin aikin ƙarshe da zanyi. Amma tunda ta shigo a tsakkiyar labarina dolene ta fuskanci hukuncin daya dace da ita. Idan ita bazata mutun ba shi a kawar min da shi mana Uwa”. 

      “Hakan mai sauƙi ne, sai dai shima babu buƙatar mutuwarsa, dan zai iya mana amfani a gaba. Sannan shi rabata da shi shine mafi ƙololuwar hukuncinsa. Dan haka daga nan zuwa safiyar kowace juma'a ta ƙarshen shekarar nan ki tabbatar an zarga igiya tsakaninta da Malik-alMuluk, a dakatar da kai masa matan da suka rage a kaita garesa bayan tarewa, dan da ita zamu cigaba da amfani har samuwar cikar burinmu ga kowa!!.”

      Da sauri ta ɗago kai jin muryar nayin nesa da ita, sai dai kafin ta iya furta wani abu Uwa ta ɓace daga ɗakin tamkar guntun girgijen hadari a tsakkiyar fararen gizagizai. Zumbur ta miƙe tana mai dafe kanta dake sara mata, wani irin tuƙuƙi da ƙaiƙayin mai zafafa ruhi zuciyarta ke mata. Sai dai sanin wacece Uwa ya sata jin ɗan sassauci kaɗan, amma ruɗani mai ɗauke da abubuwa masu matuƙar yawan gaske da fassarasu a ɗauka shekara dubu bisa dubu ba'a kammala ba na neman danne wancan ƙwarin gwiwar. Taya ruhin ƴaƴan sarakunan ƙasar Ruman basu bata matsala ba sai ƴar talakawa ƙasƙantattu? Dolene yarinyar nan ta ɗanɗana kuɗarta na hukuncin shiga gonar daba tata ba ƙwarai da gaske, sai tayi wasa da ita a tsakkiyar titi wasa irin na ɓera a hanun mage, dan ko ita Malikat bata isaba.....


      (Tofa masu karatu, ita kuma wannan wacece ita? Iffah fa ta taro match ɗin da babu players. Kumuje zuwa dai muga yaya wasan zai kaya🚴🏼...)


         ★__________________★


      *_IFFAH_*


           A ɗan firgice ta buɗe idanunta tare da tura hannu ƙarƙashin filon data tada kai ta sake danne wayar dake faman ɓurari cike da tsoron kar Ummu ta jiyo, dan tasan Babiy da Hanash basa gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai matuƙar ƙarfi da zaro wayar, cikin rawar jiki ta dannata a silent. Tamkar jira kiran ya sake shigowa kuwa. Idanunta masu matuƙar girma da haske ta waro sosai ganin mai kiran, ai batama bari tayi ring na biyu ba taa ɗaga tare da kaiwa kunnenta tana direwa a gadon. 

    “Kina jina?”.

Aka faɗa daga can. Kanta ta jinjina masa tamkar tana gabansa dai-dai tana leƙawa tsakar gidansu. Daga can gefen da Babiy ke kiwon tsuntsaye ta hango Ummu, dan haka ta sauke ajiyar numfashi da fara magana cikin raɗa. 

     “Ina jinka Sir! Ta samu ne?”.

“Babu lokacin dogon magana Iffah, kiyi ƙoƙari daga nan zuwa awa ɗaya ki sameni, dan kuwa mun tsinta dami a kala Ajmal ya shigo Ruman, kuma a yanzu haka mun gama magana da shi sai dai ban sanar masa ainahin zancen ba, ya kuma buƙaci haɗuwa dake.....”

     “Ya ALLAH! Alhmdllhi. Naji daɗi matuƙa wlhy Sir. Insha ALLAHU duk yanda zanyi kuwa zan fito ka saurare ni”.

         “Okay”.

     Kawai ya faɗa yana mai yanke wayar. Itama shiri ta shiga faman yi a gaggauce, tare da tattare takardun dukkan bayanai data tattara waje ɗaya. Bakinta ɗauke da addu'ar samun nasarar amincewar Ummu abisa ƙaryar data shirya akan fitar ta  fito. Daga inda Ummu take tako zubomata ido na alamar tuhuma. Gareta ta ƙarasa cikin danne komai da karsashin data aro. “Ummu kiran gaggawa na samu daga Ikram. Inaga dai abinda muka jima muna jirane ya fito”.

          “Amma Iffah....”

    “Ummu dan ALLAH kar kice a'a”. Iffah tai saurin tarar numfashinta cike da marairaicewa. “Ni ba hanaki zanyiba, sai dai wannan yawan fitar taki a kwanakin nan bana zuwa makaranta ba ya fara damuna Iffah. Shin kin manta halin da muka shiga da wanda zamu iya shiga a yanzu? Ina jin tsoro wlhy, matuƙar tsoro a duk sanda kika fita koda makaranta ne”.

     Sosai tausayin Ummu ya sake mamaye zuciyar Iffah, ta haɗiye hawayen da suka taru mata a ido tana ƙaƙaro murmushi. “Insha ALLAHU Ummu babu abinda zai faru, wanda ya farun ma a baya bazamu taɓa mu yafe ba. Fita ta kuma ta daina baki tsoro, tunda kinga duk sanda zan fitan ina suturta dukkan jikina”.

    “Shike nan ALLAH ya tsareki, dan ALLAH kiyi maza ki dawo kafin Abbin ku ya dawo gidan nan ko ɗan uwanki”.

     “Insha ALLAHU Ummuna”. Iffah ta faɗa tana rungumeta. Shafa kanta Ummu tai tana murmushin ƙarfin hali itama, dan ba wani zuciyarta ta samu nutsuwa bane ita dai, ta bartane kawai saboda tace fitar ta shafi karatunta. Amma zata cigaba da rakata da addu'a harta dawo.........✍


No comments

Powered by Blogger.