Daudar Gora Book 2 page 15


 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (15)

........“Wlhy gaba ɗaya kaina ya kulle Akia, shin yarinyar nan wani ƙulli ne take son yi dan ta kuɓutar da kanta saboda tasan babban burin kowa sanin mai kashe matan Abni ne? ko kuwa gaskiya take faɗa? Idan gaskiya take faɗa taya akai tasani mu a tsahon shekaru muka gagara ganowa? Anya kuwa shigowar yarinyar nan cikin masarautar nan tun farko bada wata ƙullalliya ba?”.

    Shiru babu alamar Malikat Bushirat zatace wani abu, hakan bai damu Jasrah ba ta cigaba da faɗin, “Al'amarin Mammah ya cigaba da bani tsoro a wannan gaɓar. Anya ba akwai abinda take ɓoye mana ba daya kamata mu sani?”.

        A karo na farko Malikat Bushirat ta ɗago ta dubi Jasrah. Sai kuma ta miƙe cikin yanayin ƴar zabira. “Kamar mi kike tunani?”.

     “Abubuwa da yawa Akia. Ciki harda halayyarta ta yanzu dake bayyanar da ita a mara gaskiya. Zuciyata na rayamun abubuwa da yawa fiye da yanda kike zato. Abin tambayar anan miyasa take goyawa yarinyar nan baya? Miyasa take son bata kariya? Bayan gudan jininta ta shirya halakawa? Ki duba kiga yanda taƙi bamu goyon baya akan shari'ar nan ita da Ammarah. Yarinyar nan ita aka fara kaiwa sashen Abni, kuma ita ta kaita, batai ko ciwon kai ba aka kai wata daga baya ta rasa ranta. Mi hakan ke nufi? Kaɗan daga cikin zarge-zargena kenan”.

      Kai kawai Malikat Bushirat ke jinjinawa alamar gamsuwa da bayanin Jasrah, dan itama wannan tunanin ya jima yana mata kaikawo a zuciya. Taƙi fiddashi ne saboda tuna halayen Malikat Haseenat ɗin masu yawa kafin yau, amma yanzu kam zuciyarta na mata rawa akan a bubuwa da yawan gaske......


★★.... ★.....


       Barbushi dake kwasar dariya bayan gama sauraren Miran Jasim da Miran Arshaan ya tsagaita dan kansa ya tamke fuskar tamau kamar bashi ne yayi ba. “Ƙwarai kuna a tsaka mai wuya, tsakar da in har bakinta ya buɗe ta furta ƙarshenku yazo. Abu ɗaya zamuyi akanta, idan mun taki sa'a kun tsira. Idan akasin hakan ya kasance ku zargi kanku....”

         Komai basu iya sunce ba, dan zuciyarsu ta fara saka musu shakku akan gazawar Barbushi. Inba gazawa ba taya ƴar yarinya ƙarama zai dinga nuna kamar ta gagaresa. Bayan a da ya musu ayyuka manya da har a yanzu suke taka rawa da bazarsa. Ransu ɓace suka baro wajen nasa, zukatansu na matsanancin ƙuna, kowa kuma da abinda yake tattaunawa da ransa akan matakin ɗauka. Dan ko ana ha maza ha mata bazasu bar Iffah ta cigaba da numfashi ba a wannan gaɓar. Kai hatta da uban gayyar za'ai ƙurun-ƙus a wuce wajen dan sun gaji da gafara sa basuga ƙaho ba. In ba hakaba yarinyar nan zata ɓallo musu aiki....


       ★★... TA-ƘURYA ★★...


      Tun zaman shari'ar nan ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ta rasa makamar kamawa. A lissafi bayan boka Ruƙuƙi ta ziyarci manyan bokaye a ƙalla huɗu amma amsa guda suke bata bazasu iya mata aiki ba ta koma ga UWA. Tsabar takaici har kuka tayi, kuka irin wanda ake kira kuka data ɗauka tsahon shekarun da bazata iya tuna sanda tayi makamancin sa ba ma. Jin tsanar Iffah take fiye da komai yanzu a duniya. A kwanaki biyun nan da suka gabata bayan zaman shari'a ta yanke shawarar gwada kasheta amma duk hanyar da tabi sai ta sameta a toshe. Wannan ne ya sake ƙona mata rai da sake jin raɗaɗi mafi girma.

       (Ki ajiye komai ki sake komawa ga uwa, karki bari wahalarki ta wuce a banza) shawarar aminiyarta ta sake dawo mata a karo na babu adadi. Jagwab takai zaune, cikin don danne hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tace, “Mike shirin faruwa da ni ne haka? Shirin dana ɗauka shekaru kusan arba'in inayi ne wata mitsitsiyar halitta zata zama sanadin rushemin, micece ita? Mi take takama da shi?” hawayen da take dannewar suka zubo saboda radaɗin da take ji. Bata da sauran zaɓi a yanzu face sake nemo UWA. Zumbur ta miƙe tamkar wadda aka tsikara. Ta lalubo kayan surkullen da take kiranyen uwa da su, da ƙyar ta gano robar da hayaƙi ke ciki ta bulbula a burner, take ɗakin ya harmutse har baka iya ganin komai, ita kanta numfashinta har wani fisgar yake tsabar ƙarfin hayaƙin. Idanunta ta rumtse tare da zubewa bisa gwiwunta ta fara hurwa na kiranye cikin yaren surkulle. Amma tsahon lokaci babu alamar uwa, har hayaƙin ya Kore, bata gajiya ba ta cigaba tana mai sake ninka rauninta (Wa'iyazubillah). 

       Ta share tsahon awa guda tana abu ɗaya babu uwa babu alamar ta. Sai ranta ya ƙara sosuwa, ta dunƙule kanta waje ɗaya tana mai jin hawaye nason zubo mata. Amma ta hana hakan saboda taurin zuciya. Har karfe biyu na dare da masarautar ta nitsa bakajin motsin komai alamar anyi barci, in ma da wanda bai barcinba ya kasance a killace ƙarƙashin inuwar karamin motsi. Waya ta ɗauka tai danne-danne ta kai kunne, a bugu ɗaya aka amsa mata. Kafin ace komai da ga can cikin bada umarni ta furta, “Ki sashi ya jirani a garden”. Daga haka ta yanke kiran. A gurguje tai shiri cikin ɓadda kama ta fice, bazaka taɓa ɗauka mace bace, ta canja kammani cikin kayan jami'an dake aiki bada tsaro a masarautar. Dan haka babu wanda ya maida hankali kanta harta isa babban garden ɗin masarautar dake a ɓangaren kudanci. Wajen nada ƙarancin haske, sai kukan tsuntsaye da ake kiwo jefi-jefi. Da sauri ya fito da ga maboyarsa, ya zube a gabanta yana miƙa gaisuwa. Nuni tai masa ya miƙe batare da ta amsa masa ba. Mikewar yay, kansa a rissine, dan haramunne a garesa kallonta. 

     Sai da ta gama ƙare masa kallo sama da ƙasa ta mika masa anvelope ɗin hannunta. “Daga daren yau zuwa safiyar gobe ina buƙatar jin kuka, ina buƙatar naji kukan mutuwar Zawjata-almilk. Idan aka samu kuskure kuwa kukan mutuwarka ahalinka zasuyi. A jefata a babban ruwan swimming pool na garden ɗin gabashi”.

         “Umarninki shine abin jirana da cikawa”. Ya faɗa da sauri cikin matuƙar girmamawa. Bata sake tankawa ba ta juya tabar wajen. Sai da ta ɓacema ganinsa ya iya ɗago kansa dake a risine yana sakin nannauyar ajiyar zuciya. Ba yau ya fara mata aiki ba, sai dai a shi kansa har yanzu bazai iya sanin ainahin wacece ba. Dan a koda yaushe cikin ɓadda kama take bashi umarni ko ta saka amintacciyar ta ta bashi, sai dai a duk lokacin da ita ta bashi da kanta ya san ba aiki bane ƙarami. Anvelope ɗin ya buɗe, ya wani zaro idanu da ganin makudan kuɗin da ke ciki miƙaƙƙu sababbi ƙal sai ƙamshin sabunta suke. Fuskarsa washe da murmushi ya sumbaci kuɗin, ransa fes da samunsu. Duk da dai yasan bazai cisu a banza ba, dan wannan aikin bazai taɓa zama mai sauƙi ba a garesa kasancewar matsanancin tsaron da kurkukun da Zawjata-almilk ke ciki, amma kodan waɗan nan taurarin dolene ya cika umarni.......


     ★★......


   Ya kai mintuna goma yana kallon yanda masu tsaron kurkukun ke kaiwa da komowa, kowanne kuma da makami tare da shi. Ga haske ƙal tamkar rana dan ko allura ka yar ka duka ka ɗauka abinka batare da ka nema ba. Bugawar ƙaton agogon masarautar da ake iya gani tako wace kusurwar daular ta ruman ya sashi jan numfashi a sarƙe. Karfe uku dai-dai kenan, awa ɗaya garesa kacal na kammala wannan aikin. Dan huɗu nayi zaka fara jin motsin hadimai na tashi domin fara ayyukansu, musamman masu share-share da goge-goge. Zaman ɗammarar ƙugunsa ya gyara da ƙyau, hakama hular kansa kalar kayan jikinsa na ainahin amintattun jami'an dake cikin sashen Tajwar Eshaan. Ya ƙara saita kansa da ƙyau cikin dakewa ya tunkaresu hannunsa ɗauke da babbar jaka. Duk da sanin matsayin masu waɗan nan kayan a gidan gaba ɗaya sukai masa ca. Bai nuna razana ba duk da zuciyarsa na faman dukan dari-ɗari ne. Cikin sake matse kansa ya sara musu alamar girmamawa yana mai miƙa musu I'd card ɗinsa. 

     “Umarnine da ga shugaba, zan sada kayan nan ga Zawjata-almilk domin sakasu a gobe idan zata fita, na kwashe na dattin dake tare da ita”.

           Kallonsa suke kawai suna sake kallon katin domin tantance shi ɗinne a hoton kokuwa. Sai dai hoton ya ɗanyi duhu, duk da kuma hasken wajen dai rana bazata taɓa zama ɗaya da hasken lantarki ba. A dake ya sake faɗin, “Ba tantancewar kaɗai ake buƙata ba. Ya kamata ku kira sashen shugaba domin tabbatarwa, wannan shine cikar aikin masu tsaro”.

      Kalamansa sun ɗanyi tasiri garesu, sai dai duk da haka wani ya tubure akan sai ya fara zuwa ya tabbatar bawai kiran waya ba. Dan ko ƙuda an tabbatar musu su kasance masu himma wajen hanashi gittawa zuwa inda Iffah take sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Tsabar ƙarfin hali na hadimin nan, babu ko nuna gezau ya bada goyon baya. Hakan ya ƙara saka sauran jin sun yarda da shi, sai dai wancan ɗin babu alamar hakan. Sai ma tabbatar musu da yay su cigaba da tsaresa zaije ya dawo”.

       Tsahon mintuna goma da tafiyarsa sai gashi ya dawo, batare da yace komai ba yay masa nuni da ya shiga. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ya saki da ɗan kashe ido wa jami'in da a yanzu yake ta faman sinne kai kamar wani munafuki. Sauran basu damuba dan su dama sun aminta tun dazun, dan haka ya wuce hankali kwance.


      Tana tsaka da ɓarawon barcin da ya sace ta bayan ta idar da sallar da take tsaiwar yi duk dare domin miƙa kukanta ga UBANGIJI taji kamar numfashinta na fita a fisge, firgigit ta farka da ƙoƙarin kai hannunta saman hancinta, sai dai aikin gama ya gama dan ya riga ya shaƙa mata abinda ke cikin handkherciff ɗin. Duk yanda taso sake yunƙurawa hakan ya gagara sai ma jikinta dake saki baki ɗaya. Daga haka bata sake sanin inda kanta yake ba.

       Jikinsa na ɗan ɓari ya sakata a babbar jakar hanun nasa tare da zuge zip ɗin. Bai tsaya ɓata lokaci ba ya saɓeta kasancewarsa ƙaƙƙarfan mutum babu alamar da zai tabbatar maka mutum ya ɗakko. Gashi dama Iffah ta rame sosai duk da dama ba wata mai jiki bace can. Sai dai kuma duk da hakan ƙarfin haline kawai irin na masu busashshiyar zuciya dan sumar da itan da yay jikinta duk ya saki ta sake nauyi. Sai da yay musu sallama da sanar da su ya kwaso kayan dattin wajenta ne bisa umarnin Tajwar Eshaan sannan ya wuce.........✍️


       Hummm

No comments

Powered by Blogger.