Daudar Gora Book 2 page 19
K𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (19)
......<<★★ TA-ƘURYA ★★>>
_(Itace muke buƙata ta zama uwar Miran mai jiran gado, ki gaggauta, ki gaggauta tabbatar da ita cikin masarautar nan matsayin Zawjata-almilk daga nan zuwa mako huɗu. Inba haka ba kiyi kuka da kanki ta-ƙurya hahaha!!! hahaha! hhhhh!!!!)_
Zumbur ta miƙe daga ɗan barcin daya figeta, firgitattun kalaman uwa da tayi mata su a zahiri ne waccan ranar ke maimaita kansu yanzu a barcinta matsayin mafarki. Hannu takai ta yarce uban gumin da ya jiƙe mata goshi har yana zirarowa akan fuskarta. Tana a tsaka mai wuya, irin tsakan da bata taɓa shigaba a duk umarnin da uwa ta bata a baya. Maganar ƙulla auren nan bazai kasance ƙarami ba gareta a wannan karon, sakamakon zaman babu wanda ya yarda da ɗan uwansa da akeyi yanzu a masarautar ta ruman. Gaba ɗaya ta rasa ta inda zata ɓullowa al'amarin nan. Ji take komai ya sukurkurce mata, sai dai kuma bazata iya yarda da barin cikar burinta ba na tsawon shekaru da take ganin tazo gab da cimmawa. Dolene ma tai wani abu, sai dai salon zai banbanta dana baya koda kaɗanne, zatai irin ɓadda kamar data saba wajen ganin wannan auren ya ɗauru, dan ko zatai yawo tsirara bazata taɓa yarda Iffah ta zama Malikat ba, mai haihuwar magajin Shahan-shan never for ever hakan ta faru tana numfashi a doron duniya....
🥱To ta-ƙurya bara mu gani ko zaki iya, mudai ƴan kallo ne😉.
★★... ★.....
A hankali ta matse fuska sai kuma takai hannu kan shafaffen cikinta dake mata zafin yunwa. Rabonta da abinci tun yammacin jiya, dan ƙin cin abincin da aka kai mata da dare tai a kurkuku. Zamewa tai a hankali ta kwanta a gadon tana cigaba da matse fuska. Dubanta ta kai a karo na biyu kan kofin shayin da ya bata ta ɓalla masa harara kamar shi ya hanata abincin, sai kuma tai juyi ta maida fuskarta ɗayan side ɗin tana ƙara cure jikinta waje guda hanunnta na kan cikinta..
A hankali ya tura ƙofar ya shiga idanunsa da hankalinsa gaba ɗaya na kan wayar hanunsa mai shegen ƙyau da ɗaukar ido kamar wani glass. Ciki-ciki yay sallama a ƙasan maƙoshi, batare da nuna alamar tuna yabar wani a ɗakin ba ya nufi ƙyaƙyƙywar kujerar zamansa ta musamman ya kai zaune a ƙasaitance. Wani kalan zaman isa da izzar mulki yay har lokacin idonsa akan wayar da alamar serious abu yake yi. Sassanyan ƙamshin turarensa dake ratsa mata ƙofifin hanci ya sata buɗe idanunta sannu a hankali. Har sun canja kala alamar barci ya fara ɗaukarta. Juyowa tai sannu a hankali batare da tunanin shi ɗin bane da gaske, dan indai ƙamshin sa ne ya riga ya gama kama duk bedrooms ɗin da yake amfani da su tsabar yanda yake wanka da turare kamar ruwa. Akan ƙyaƙyƙyawar farar fuskarsa da hasken wayan ya ɗan haska baƙin sajen siɗik ɗin gashinsa na ƙyalli ta sauke, yanda akai masa gyaran fuskar da wani irin haɗaɗɗen style yay matuƙar ƙara masa ƙyau. Sai taji tana buƙatar cigaba da kallonsa kawai, wani abu data kasa banbancewa na tsikarar ƙasan zuciyarta.
A jikinsa yaji ana kallonsa, dan haka ya tsaya cak da ga sarrafa wayar da yake faman yi cike da ƙwarewa. Sai dai bai ɗago ba har tsawon kusan minti ɗaya. Sai da yay bala'in shammatarta a bazata ya ɗago nasa kaifafan idanun sai cikin nata dake tsaye ƙyam a kansa. Da wani irin sauri ta fisge kanta gefe cike da pretending ta riƙe ciki tana murƙususu ita a dole bata da lafiya ma. Idanun nasa ya kaɗa kamar wani mai zuƙota ta cikinsu, sai kuma ya yamutse fuska da sake tsuketa ya ɗauke kansa shima. Ci gaba yay da sarrafa wayarsa batare da ya sake kallonta ba, hakan ya bata damar sake satan kallonsa ta ƙasan ido tana sake ƙaƙaro kukan ƙaryanta. lips ɗinsa ya ɗan ciza kaɗan batare da ya bar abinda yake ba a hankali can ƙasan maƙoshi ya furta, “What happend?”.
Baki ta tura gaba kamar bazatace komai ba. Sai kuma cikin kuka-kuka da kai tsaye za'a kirashi na shagwaɓa tace, “Ni dai kayan cikina zasu naɗe, yunwa nakeji ga headache, ga ciwo jikina namun ko'ina da ina”. Ta ƙare maganar tana ƙara tura baki.
(Yarinyar nan ko...) Ya faɗa a cikin ransa idanunsa na wani binta da kallon slowly kamar mai zooming ɗin ta a cikinsu. Dan can ƙasa-ƙasa yake mata kallon da ita sam ta ɗauka hankalinsa na kan wayar ne baya ganinta saboda ganin yanda yake cigaba da sarrafa wayarsa bai dakata ba. Babu alamar zai sake tanka mata har tsawon kusan mintuna huɗu data cika tai fam da haushinsa. Tsabar son ƙular da shi sai ta fashe da sabon kuka ta shiga wani murƙususun tana kiran “Wayyo cikina Ummu yunwa zata halaka miki ni, nima kasheni zaiyi kamar yanda ya kashe ku. Abbiy ka shirya tarbana gani nan a hanya inda kuke. Ni wlhy garama a kasheni da wannan azaba da akemun, wayyo wo wo wo!!”.
Tamkar wani gunki haka ya cigaba da zuba mata ido yana kallon ikon God, shi kam bai taɓa ganin Fitinanniyar yarinya irin yarinyar nan ba a rayuwanshi. Sam batajin magana, ga shegen tsiwa kamar wata babyn roba mai battery. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa inda take ganin bata da alamar barin kunensa ya huta, yay tsaye a kanta kamar wanda aka dasa, sai wani binta yake da kallon ƙasaita. “Mike ciyon?” ya faɗa a fisge kamar ba shine ya tambayeta yanzun nan ta bashi amsa ba. Ɗan zabura tai da jinsa gab da ita dan batai zato ba, ta yunƙura da sauri zata tashi ya maidata. Sai kuma ya kai zaune gefenta har jinkinsu na gogar juna. Sake zaburar taso yi ya sake maidata yana tsatstsareta da mayun idanunsa masu kaifi. “Ni dai ya warke barshi” ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin ture hannunsa dake jikinta. Ko gezau baiyi ba, sai ma ɗorasa da yay saman kanta ya zare towel ɗin da ya naɗa mata tun ɗazun. Dogon gashinta mai alamar lema har yanzu dake faman ƙyalli ne ya bayyana, ya ɗan tsirama gashin ido na wasu sakkani kamar mai nazari, sai kuma ya janye yayo ƙasa da su kan fuskarta. Da sauri tai ƙoƙarin kauda fuskar, sai dai ya hana hakan ta hanyar taro fuskar tata cikin tafin hannunsa ya sarƙe idanunsa cikin idanunta ta ƙarfin tsiya. Wani irin tashi tsigar jikinta ta farayi, cikin rawar lips kamar zata saki kuka ta ce, “Nifa na warke nace”.
Idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta yana kusanta fuskarsu gab-gab da juna.
“Ban yarda ba”.
Ya faɗa cikin raɗa-raɗa yana hura mata iskar bakinsa mai ƙamshin banana akan fuskar. Zuƙa tai ta lumshe idanun tana kame jikinta da ke son fara rawa. Da ɗan rawar lips ɗin ta sake furta, “Da gaske nake ciwon ya daina”.
Yanda tai maganar a hankali cikin rauni kaɗan ya hana Shahan-shan sakin ihu, amma ya kanne cike da son nuna jarumta yana haɗe tsinin hancinsu waje guda. “Ni ban yarda ba, ki nuna na tausa miki bada zafi ba fa”.
Da ƙarfi numfashin Iffah ya fisga tsabar shiga ruɗani, sai da ƙyar ta jawoshi ya koma ƙirjinta, sai dai rawar jikinta ta fara bayyana kanta. Jin saukar tattausan hannunsa bisa lallausar fatan gefen cikinta zuwa ƙugu da ya matsa ya sata furta “Wayyo Ummuna”.
“Nima wayyo Ammie-na”.
Ya faɗa cikin kwaikwayon ƴar muryarta yana sake tura hanun saman shafaffen cikinta. Da sauri tasa hannu biyu ta riƙe hannun tana tura baki, hakan ya bama lips ɗinsu damar haɗewa, sai tai azamar son kauda fuskar amma ya hana hakan. A bazata taji saukar lips ɗin nasa kan nata. A tare suka buɗe idanun da suka lumshe, sai dai ita zazzaro nata tayi saɓanin shi da ya tsareta da nasa cikin kallon data kasa bama fassara. Da wani salo ya kaɗa nasa alamar ta rufe natan, kamar wata gaula ko wadda yake juyawa da remote kuwa ta rufesu ruf jinin jikinta na hautsina mata. Dole ta ƙanƙame hannunsa dake kan cikinta har yanzu da masifar ƙarfi dan bata da zaɓin daya wuce haka bayan shi.
Sai da yaso dan kansa ya janye lips ɗinsa suna mai sauke numfashi a jajjere kamar wanda sukai gudun gasa a ƙaton fili, cikin matuƙar dauriya ya kame nasa yanayin sai dai yaƙi yarda su haɗa ido sam. Itama ɗin dai ba kallon nasa take ba, hasalima bata da burin da ya wuce ta samu wajen ɓuya ko zata samu sassaucin halin da ya jefata na rashin tabbas. Tsahon wasu ƴan mintuna ɗakin ya cigaba da zama shiru, kafin shi ya katse hakan ta hanyar ɗagota gaba ɗayanta ya zaunar a kan gadon, hannunsa ya tura cikin gashinta, tai azamar rumtse idanunta da ƙarfi. Har yanzu akwai damshin da yake gudar mata shiga halin muran. A nutse ya miƙe tare da miƙar da ita, hannunta riƙe a cikin nasa suka isa gaban wadrub ɗin glass ɗin ɗakin nasa dake cike da kayan barci kawai. Ya ɗan danna wani maɓalli sai gata ta zuge ƙofa ta bayyana kanta. Saurin dubansa tai mamaki na barazanar halakata, shiko yay fuska abinsa kamarma bai ganta ba, sai ma janta da yay suka ƙarasa shiga. Ashe anan abun mamakin yake ba can ba, dan kuwa ɗakine babba zagaye da irin waccan wadrube na glass ɗin, kai kace wani shagon saida kaya ne mai zaman kansa. Duk wani nau'in sutura da kayan ado da yake sakama jikinsa ne anan, hatta da takalma sunada nasu sashen, agoguna masu ƙyau na diamond dasu azurfa dana manyan companys ne gasu nan ba'a magana. Bataji a ranta hakan mafarki bane ko bazai yiwu ba kasancewar sanin matsayinsa, Shahan-shan fa, ai ko abinda yafi haka ka gani bakayi mamaki ba. Shi dai ya fuske abinsa tamkar bai fahimceta ba, ya ƙarasa da ita gaban ƙaton mirror ɗin da ke ɗauke da nau'in kayan gyaran gashi kala-kala, ko mace albarka, saukar iskar ɗumin hair dryer ne ya maidota hayyacinta ta sauke nannauyan numfashi da ɗago idanunta ta dubi madubin.........✍️
Leave a Comment