Daudar Gora Book 2 page 20

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (20)

.........Tar-tar take kallonsu a ciki yana busar mata da gashi a nutse fuskar kuma babu fara'a kota sisin kwabo. Kauda nata tai jikinta gaba ɗaya yay sanyi da al'amarinsa. Sotake tayi tunanin akansa dan ya gama birkita duk ginin da take kallonsa da shi a baya yau baki ɗaya, kaikawo kawai zuciyarta keyi. Ada zahirinsa take tunanin kallo, ashe ba haka bane, dan a yau ta kasa iya banbance zahirinsa na gaskiya. Ya rikita komai a lokacin daya kamata ace ta fahimci komai ɗin. Itafa gaskiya man kanta kawai ma ya tsiyaye tas..

      

    _(Nima dai nawa ya tsiyaye ƴar koran taki Iffah. Shahan-shan yazo da babbar bidi'a fa gaskiya🥱🤣)._

              


     ★★ MALIKAT BUSHIRAT ★★


   Tun fara faruwar al'amuran nan yau ne zuciyarta ta ɗan fara mata wasi-wasi, a karan kanta sai take ji tana son sanin wanene ya shugabanci yarinyar domin halaka mata gudan jininta. Dan tabbas akwai ƙamashin gaskiyar lauje cikin naɗi. Ba komai ya sata farga ba a yau sai kallon zancen ido data ga yana gudana tsakanin Malikat Ashwaq da Ameera Haifah a ɗazun sanda aka wuce da Iffah. Sai kuma kallon da taga shi kansa Tajwar Eshaan ɗin ya musu su dukansu kasancewar suna tsaye duk a waje guda ne. Ita ta haifesa, duk da bata rayu da shi na tsawon lokaci a zaman kwana da yini ba, tasan halin ɗanta ciki da bai, ta masa sanin da ko da ido yay magana tana fahimtarsa. Lallai kallon yana da manufa, manufa irin wadda ya kamata ace ta sani. Manufa irin wadda ya kamata ace ta farka daga nannauyan barcin dake neman tasiri a idanunta. Ta jima tana zargin Malikat Ashwaq a duk abinda ke faruwa ga tilon ɗanta, sai dai a yau zuciyarta na gaya mata akwai wasu bayan itan, a wasun kuwa har Mamma (Malikat Haseenat) bata cire a ciki ba, dan akwanakin nan take-taken tsohuwar na rikita mata yardar data mata a baya. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, gaba ɗaya ji take komai ya cinkushe mata, dole ne ma tana buƙatar yin nazari mai faɗi, ya kamata kuma ta gana da shi....

         

       ★ Zaune yake harɗe a ɗaya daga cikin lafiyayyun kujerun falon. Tun dawowarsa da ga sallar la'asar ya yada zango anan. Laptop ce a coffee table ɗin gaban kujerar da yake yana sarrafata sannu a hankali. Sai mug na shayi dake ta faman tururi ƙamshinsa mai daɗi daya gauraya dana turarensa na tashi sannu a hankali. Sosai siririn farin gilashin idonsa ya sake masa ƙyau. A yanda gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga screen ɗin computer ɗin zai tabbatar maka abu mai matukar muhimmanci yake yi. Dan sai lokaci-lokaci ya kan ɗan ɗauka mug ɗin ya kai bakinsa ya maida ya ajiye duk hankalinsa na kan abinda yake yin. Sayeed Fayzul-haq dake shigowa ya sake maimaita sallamarsa cikin nutsuwarsa, a hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa batare da ya ɗago ba. Sayeed ya ɗan ranƙwafa yana kai gaisuwa duk da basu jima da rabuwa ba. Kansa kawai ya jinjina masa alamar amsawar kenan.

      “ALLAH ya ƙara maka lafiya da nisan kwana. Malikat ke neman izinin ganinka idan bata shiga lokacin da bai dace da ita ba”.

         Shiru ya ɗan tsaya daga sarrafa system ɗin, sai dai kuma bai dagoba har shurewar wasu sakanni da suka zama mintoci biyu. Maida yatsunsa yay kan keyboard ɗin kamar bazai ce komai ba sai kuma ya motsa lips ɗin kamar an masa dole ya furta, “Zata iya shigowa”.

      “Malikat na godiya, ALLAH ya cigaba da kare mana kai adalin shugabanmu. ALLAH ya gafartama magabata”.

    Duk da addu'ar ƙarshe ta masa daɗi a cikin rai bai motsa ba balle ya amsa. Har cikin ransa yana masifar jin maɗaukakin daɗi a duk lokacin da wani yay ma mahaifansa da suka kwanta dama addu'a..


       ★Kallo yake mata irin na kewa da lumsassun idanunsa. Sai dai a zahirinsa baka isa fahimtar hakan ba kai tsaye. A hankali ya ɗan kauda idanunsa da ke binta da kallo yana rissinar da kansa dai-dai tana zama. Itama fuskarta da murmushi take dubansa saɓanin shi da tashi babu walwalar sosai. Sai dai ya motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Barka da yamma Ammie.”

      Murmushi ta sake saki da ke sake fidda ƙyawun da ALLAH ya mata. “Ina fatan kana lafiya Niger?”.

         Maimakon amsa gajeren murmushin da ita kawai keda lasisin ganinsa ya ɗan saki yana kauda kansa, sai kuma ya sake maidowa yana mai zuba mata idanunsan nan masu kaifi. Dan ita kanta data haifesa a duk sanda ya tsareta da su tana jin tasirinsu sosai tattare da ita. Nata ta janye cike da ƙasaita ta furta, “Ya jikin Ibnati?”.

      Kamar bazaice komai ba sai kuma a fisge ya amsata. “Alhamdullah”.

    “Thanks God. ALLAH ya ƙara lafiya”.

    A zuciyarsa ya amsa amin ɗin. Bata damu ba ta cigaba da faɗin, “Abubuwa da yawa da ke faruwa suna sake rikitamun kai, sai dai basu ne suka kawoni ba a yanzu. Yaya maganar shari'ar da aka fara?”.

         “Tana nan Ammie, za kuma a ƙarasata”. Ya faɗa a hankali cikin taushin harshe.

      Ajiyar zuciya ta ɗan sauke sai kuma ta ambaci sunansa. Dara-daran idanunsa ya sake saukewa a kanta da ƙyau. Itama kallonsa take cike da so da ƙauna. “Ina son tattaunawa da kai mai muhimmanci, sai dai ba'a nan ba Bin Haysam Abdul-majeed”.

      Idanunsa ya lumshe ya buɗe a hankali, sunan data kirasa na ratsashi matuƙa, cike da girmamawa a gareta ya furta, “Ki yanke duk lokacin da kike buƙata ni mai jiran umarninki ne a koda yaushe”.

    Ƙasaitaccen murmushi ta saki ƙaunarsa na sake ratsata. Cikin gyaɗa kai ta furta, “ALLAH ya cigaba da karemun kai, ya lulluɓeka da tarin albarka da rahamominsa marasa yankewa. Duk sanda na yanke zaka jini na barka lafiya”.

         Kansa ya ɗan rissinar alamar girmamawa, kafin ya furta, “A huta lafiya”.


★★..... ★....


       Bayan sallar magrib duk wani mai alaƙa da shari'ar ya kimtsa kansa a katafaren falon da akai wancan zaman farkon. Shine ƙarshen shigowa kamar a wancan zaman. Kan kowa rissine har ya zauna a inda aka tanada masa, tuni ƙamshinsa ya gama danne duk wani turare mai ƙarfi a wajen. Sai da ya gama binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya ta ƙasan ido na tsawon wasu mintuna kafin ya mula dan kansa yay gyaran murya. Dake nutsuwa kowa yay da maida hankalinsa garesa. Nan ma ya sake jan wasu mintuna biyun kafin ya ɗaura da faɗin,

       “Naso yanke hukunci a zaman ƙarshe na Shari'ar nan a yau, sai dai masu hannu a al'amarin sun nuna mana su basa buƙatar hakan. Bazan tambayi dan mi akai yunƙurin kasheta ba a karo na biyu, sai dai zan sanar da duk wanda ya aikata ya sake shiri akan wanda yake da a baya. Kamar yanda kuka kawo ƙarar neman hakkin yunƙurin kisan jininku da tayi, nima zan shigar da ƙarar neman hakkin kashe min mata da akayi. Kamar yanda nai alƙawarin nema muku haƙƙinku matsayina na shugaba, itama zan nema mata nata hakkin Insha ALLAHU a matsayina na shugaba bayan ta samu lafiya”.

       Kan babbar buta kenan, ai ba wanda suka shigar da ƙarar ba hatta masu goyon bayan Iffah kalaman Tajwar Eshaan ɗin sai da sukai musu tsawar saukar aradu na wucin gadi. A hankali Malikat Haseenat ta saki wani ƙayataccen ɓoyayyen murmushi, a zahiri kam ta katse suman zaunen da jama'ar wajen sukai ta hanyar faɗin, “Hukuncinka adalcine ga kowa koda son zuciya ta rufe idanun kowa. ALLAH ya ƙarama Zawjata-almilk lafiya, ya tona asirin wanda sukai mata wannan aikin koda a cikinmu ne”.

        “Shugaba ya amsa tare da godiya ga Uwar masu gida abin al'faharin ƴaƴan ƙwarai. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai albarka baya goya marayu”. Wannan kalamai sun fito ne da ga bakin Sayeed Fayzul-haq mai yawun faɗa da yawun Tajwar Eshaan kasancewar yanzu tamkar amintaccensa yake. Babu dai wanda ya motsa a zahiri, dan tamkar duk sun tafi suman wucin gadi ne, hakan yasa ya cigaba da faɗin, “Wannan kotu mai adalci ta bada umarnin sakin Zawjata-almilk da alƙawarin bata kariya har zuwa sanda za'a yanke mata hukuncin daya dace da ita. Ta kuma saki amintattun hadiman da har yanzu bata kama da laifin komai ba, zakuma su cigaba da aikinsu da ga yau. Ta bada dama ga duk mai ƙorafi akan wannan hukunci ya faɗa a zama na gaba”.

     Tabbas sun gama yarda cewar Tajwar Eshaan tsohon makirin kansa ne. Sannan hatsabibancin da suke jifansa da shi fa sun tabbatar da shi ɗin a tattare da shi yau. Rai ɓace kusan kowa ya fita a falon bayan fitarsa, kowa bakinsa fal da magana sai dai babu damar yinta anan kuma gudun abinda zaije ya dawo...


   ★★......


          Sam Iffah bata san wainar da ake toyawa ba, dan tun fita sallar la'asar da yay a ɗakin bayan ya tsareta ta ɗanci abincin da aka kawo bata sake ganinsa ba. Sai ma wani wahalallen zazzaɓi ne ya rufeta ruf. Da ƙyar ta iya tashi sallar magrib. Tayi ta a daddafe ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan rawar sanyi jikinta ke mata. Bata iya tashi sallar isha'i ba tana cikin bargo. Sosai jikin nata ya ɗauka matsanancin zafi ga ciwon kai ga sanyi tana ji. Tun bata damu da ƙin shigowar tasa ba har ta fara addu'ar hakan, a haka wani wahalallen barci ya ɗauketa.........✍️


No comments

Powered by Blogger.