Daudar Gora Book 2 page 24
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (24)
.....Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ido ta ɗan kallesa, babu shiri ta sake maidawa da sauri. Amma gudun kar yaga gazawar tata sai cewa tai, “Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Shahan-shan ɗin ƙasar ruman mana”. Ta bashi amsa tana ƙwaɓe fuska babu ko gargada a harshenta balle muryarta..
Mutuwar tsaye yay na mamaki, ya lumshe idanunsa a hankali, shi yau shi Eshaan ƙaramar yarinyar nan ke ambaton sunansa babu ko gargada a harshenta ko nuna shakkarsa balle akai ga tsoro a gabansa ido cikin ido. Abune da bai taɓa jinsa ba sai a bakin mahaifiyarsa ko kakarsa. Suma ɗin akan jima baiji sun ambata ɗin ba. (Kai wannan yarinya zata halaka shi)“Kada fa kace nayi rashin kunya kasa a ɓatar da ni ban gama cika burina ba, tunda ai dai kai ka tambayeni ko”. Ta faɗa tana mai langaɓar da kai idanunta na ɗan cikowa da ƙwalla na shagwaɓa da katse masa tunani da muryar nan tata mai ingiza bugun zuciyarsa kamar tasan mi yake tunani.
Komai baice mata ba, duk da yanda take kallonsa a kaikaice. Ya dai ɗan matsa gabanta yana cigaba da kallon ta kawai har tsawon wasu mintuna yanda tai kamar wata ƴar baby na bashi dariya a ƙasan zuciya. Sai kuma ya janye tare da ɗan matsawa da ga jikin nata da ya matso a zahiri babu ma alamar yasan minene murmushi. Aiko sai gata tana jan ajiyar zuciya. Basarwa yay kamar baijita ba.
“Miye burin naki?”.
Kalmar ta fito da ga harshensa a ɗan fisge tamkar wanda akaima dole. Batare da ta yarda ta kallesa ba ta ce, “Suna da yawa, muhimmai a cikinsu dai yanzu duk sun shafeka”.
Wani kallo da ke nuna alamar ni ɗin yay mata. Tako ɗaga masa kanta idanunta na ɗan cikowa da hawaye tana ƙiƙƙifatasu. A raunane kamar ba ita ba ta ce, “Ina son sanin halin da Iyayena ke ciki duk da an sanar min ka halaka su. Ina son sanin wanene Ajmaal?. Ina son idasa tabbatar da masu fuska biyun daular ruman wa duniya koda ni bazan iya wanke kaina ga kowa ba”.
Yanda yake kallonta kamar wata sabuwar halitta sai ka ɗauka idanun nasa sun kafe ne a kanta. A hankali ya ɗaga kafarsa yay ɗan taku ɗaya zuwa uku, a gabanta ya dakata gab-gab kamar zai haɗe jikinsu. Sai dai kuma baiyi hakan ba ya ɗan bar tazarar da bata wuce tsahon yatsa manuniya ba. Da sauri-sauri ƙirjinta ya hau dokawa ganin ya mata runfa, dan duk da kasancewar ta mai ɗan tsayi a gabansa ba komai bace duk da shima ba wani dogo bane na bala'i can, sai dai kuma dole a kira shi da dogon. Kamar yanda yake duban cikin idanunta haka itama ta ke dubansa, sai dai nata cike suke da ƙwalla ga tsumar da jikinta keyi ta kasa janyewa. Hannunsa ya dogare jikin lafiyayyar ƙofar mai tsananin ɗaukar ido, sai hakan ya sake bashi damar rufeta ruf har tana jin shaƙar numfashi ma na neman mata wahala tsabar yanda kwarjininsa ya cika mata ko'ina, har ji take kamar ma ɗakin ya musu kaɗanne.
Rasa abin cewa ya sashi ɗaura yatsunsa biyu kan haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau suna kallon juna, nasa ya sake lumshewa da sake buɗe wa a cikin natan cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara ya furta.
“Bayan kin cika waɗan nan sai me kuma?”.
Yanda yay maganar yana mai sake sarƙe kaifafan idanun nasa cikin nata da ke tara ƙwallar da bata san dalili ba ya sata shiga jujjuya masa kanta a hankali idanunta na sake cikowa da ƙwalla dan jin kusancin nasu take kamar wani dabaibayi da ya fi ma zamanta a kurkuku. Lips ɗinta ta motsa a hankali, cikin raɗa-raɗa muryarta na ɗan rawa ta furta, “Yi maka hukunci akan laifukanka”.
Da ƙyar ya iya haɗiye murmushin da ke ƙoƙarin yinƙuro masa. Sake matsar da fuskar tasa yay gab-gab da tata, hakan sai ya sake hauhawar bugun zuciyarta har yana iya jiyo yanda nunfashinta ke fita a sarƙe. Amma sai ya fuske abunsa ya cigaba da jujjuya nasa ƙwayoyin idon a nata cike da wani irin salon da ke neman fallasa sirrin da yake faman dannewa a ƙasan zuciyarsa.
“Bayan hukuncin da kikai min na son kasheni duk bai isa ba *_Niazmina_*?”.
Idanunta ta waro a matuƙar razane, tari mai ƙarfi ya sarƙeta, dan maganar tasa tazo mata a matuƙar bazata. Duk yanda yaso shanye dariyarsa a wannan karon hakan ya gagara har sai da lallausan murmushi ya suɓuce masa. Sai kawai ya jawota ya manna da jikinsa ya cigaba da yin abunsa dan ya kasa riƙewar..
(🥱Wato guy ɗin nan mugun ɗan latsi ne🚶🤭)
★Sosai take tarin har sai da ya janyeta suka koma bakin gado, shi dai murmushin sa kawai yake yana cigaba da shafa bayanta. Sai da ya ɗan lafa mata ya ɗauka tambulan ɗin ruwa da ke a side drawer ya tsiyaya kaɗan a ƙaramin cup. Ɗagota yay, batare da yayi magana ba ya ɗaura mata akan lips ɗinta. Da sauri ta shiga sha ƙwallar da ya cika idanunta da yay jajir na cigaba da sakkowa. Sai da ta shanye tas ya janye yana ƙara tsuke fuska kamar bashi ne ya gama murmushi ba yanzun. Ƙin yarda tai su haɗa ido, sai ma ta zame ta kwanta abunta ta juya masa baya. Shima komai bai sake ce mata ba yama miƙe.
“Dan ALLAH kada kaje zasu cutar da kai, dan sun saka abu a ƙasan kujerar zamanka”.
Shaƙaƙƙiyar muryarta da ke fita a dakushe saboda sarƙewar da tai ta sake ratsa dodon kunensa. Cak ya sake tsayawa tamkar wanda ake juyawa da remote, sai kuma ya ɗan waiwayo ya dubeta ganin abun nata serious ne. Tana a kwancen da take dai ta juyama ƙofar baya. Kallon kusan sakkani a shirin ya mata sai kuma ya juya ya cigaba da tafiyarsa batare da ya tanka ba. Idanu ta rumtse da ƙarfi jin ya fice a binsa.
Ranta a dagule cikin kamar bori-bori ta shiga kaima gadon ƙananun duka da tittirza ƙafafunta tana fadin, “Ni dai na faɗa ma gaskiya ai, duk abinda ya sameka kai ka sani mi ma ya shafe ni”.
(🥱Ato idan ya mutu bashi ya huta ba Iffah'r mu🤭🏃😜).
★Tsahon wasu mintuna bata iya ta tashi a kwancen da ya barta ba. Kokawa take da zuciyarta dake ingizata taje ta duba karfa ya fita ɗin. “In ma ya fita shi ya sani”. Ta faɗa a fili tana tura baki irin ko'a jikintan nam. Sai kuma can ƙasan zuciyarta ta ayyana mata (Idan ya mutu shikenan bazaki san gaskiyar rasa iyayenki da sanin waye Ajmaal ba fa kenan) zumbur ta miƙe kamar wadda aka tsikara, sauri-sauri ta fisgi mayafin abayarta ta yana a kai tana zira slippers. Ko sanda ta zauna a sashen bata san wannan ɗakin ba, amma ko gezau ta fito tana kalle-kalle. Da canki canka ta fito katafaren falon kamar wadda aka jeho.
Da sauri Sayeed Fayzul-haq da ke zaune a ƙasa gefen ƙafafunsa da wasu tarkace marasa ƙyan gani ya ɗago, shiko hamshaƙin ko motsi bai yi ba idanunsa na kan waya da ke hanunsa. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da ɗan galla masa hararar ƙasan ido, sai dai kuma can ƙasan zuciyarta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Dan tabbas tarkacen gaban nasu irin abubuwan da ta gani ne a mafarkinta kamar yanda kayan da ya sanya sukai dai-dai da wanda ta gani sanye jikinsa a mafarkin.
A ɗan daburce Sayeed Fayzul-haq ya sake maida kansa ya rissinar. Tunaninta ya katse cike da girmamawa ya ce, “ALLAH ya ƙarawa Zawjata-almilk lafiya da tsohon rai mai albarka. Barka da fitowa”.
Jin al'amarin tai wani gin-girin-gin ganin dattijon da shi kansa Tajwar Eshaan ɗin zai girmesa nesa ma ba kusa ba amma yana gaisheta da wani sinne kai na tsantsar girmamawa. Kai ita kam wannan mulkin mallaka na masu mulki baya burgeta. Tajwar Eshaan ɗin da har yanzu bai nuna yasan da zuwanta wajen ba ta ɗan saci kallo, sai kuma ta ɗauke a kasalance ta buɗe baki tana gaishe da Sayeed Fayzul-haq. Bawon ALLAH duk sai ya rikice, duk da kasancewarsa shaƙiƙin a zuri'ar gidan ina shi ina Zawjata-almilk ta gaidashi. Komai bata sake cewa ba ta juya ta koma hanyar da ta fito.
Da kallo ya bita ta ƙasan idon da tun ɗazun yake kallon nata dama. Harga ALLAH ta fara bashi tsoro. Dole yace tsoro, da farko ƙin ɗaukar abinda ta faɗa ɗin da muhimmanci yayi, amma sai zuciyarsa taƙi yarje masa hakan. Shine ya kira Sayeed Fayzul-haq akan a sallami shari'ar mutanen da ke jiransa sai nan da kwana biyu bisa wani uzirinsa. Cikin girmamawa Sayeed Fayzul-haq ɗin ke sanar masa ma ai ɗaya a ciki bai ƙara so ba har yanzu, dan sunama shirin tura dakaru nemosa ne kasancewar dama shine wanda ake ƙarar.
A dakatar kawai ya bada umarni ya yanke wayar. Bayan tabbatar da fitar kowa Sayeed ya sake kira ya sanar masa. Shine ya bada umarnin a duba masa kujerar zaman nasa da tace an saka abu. Sai gashi kuwa a cikin abinda baifi mintuna ashirin ba Sayeed Fayzul-haq ɗin ya iso da tarkacen da aka samu ɗin, daka gani kuma kasan kayan surkulle ne.......✍️
_Tofa kowa sai yay takansa aljanancin Iffah da alama ya fara bayyana yau ɗin nan😂🏃🏃🏃🏃_
Leave a Comment