Daudar Gora Book 2 page 27


 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (27)


.......... “Kallo nada matuƙar ƙayatarwa da ga nan ba?”.

   Ya faɗa a hankali cikin kunenta. Sosai tsigar jikinta ta yamutsa, dan haka cikin matse idanunta da jikinta da ke jingine da nasa ta ce, “Uhhm” acan ƙasan maƙoshi itama.

Murmushi ya sake saki da buɗe idanunsa, sai kuma a hankali ya ɗaura hannayensa kan nata da har yanzu ke'a kan ƙarfen. Itama buɗewar tai suka cigaba da kallon kaikawon mutane da mafi yawa suka kasance hadimai ne, sai daga can wajen masarautar kuma da kai kawon motoci yafi yawa. Yanda numfashinsa ke sauka a gefen wuyanta ba ƙaramin illata ta yake ba, tai dai jarumtar daurewa gudun kar aga gazawarta (Kun san dai mutuniyar tamu🥱😂). 

         Jin ruwan na cigaba da sauka kansu dan ya ɗan fara ƙarfi ya sashi sauke sassanyar ajiyar zuciya da lumshe idanunsa ya sake buɗewa, sai kuma ya miƙe da ƙyau ya ja hanunta da ke cikin nasa har yanzun, kamar jira suna shiga ɗaya daga cikin rumfunan wajen ruwan ya kece mai ƙarfi. Hanunnta da take mutsu-mutsun cirewa a cikin nasa ya saki, cike da basarwa ya kai zaune a ɗaya daga kujerun cikin rumfar. Zama yay irin na ƙasaita, ga fuskar nan tamau a tsuke kamar bashi ba. Batare da ya sake kallon inda take tsaye ba ya danna wani ɗan maɓalli ta gefensa sai ga abu na sakkowa a gefe-gefen rumfar, ruf ya rufesu suka koma kamar cikin ɗaki, dan yana gama sauka har ƙasa sai ga haske da ya ƙarama wajen ƙyau da ɗaukar hankali..

       Iffah bata ma san ta furta kalmar “Woow! Ya ALLAH”. Ba tsabar yanda abun yay matuƙar ƙayatar da ita. Sai kuma tai saurin ɗaura hanunnta kan baki tana ɗan satar kallon inda yake. Baima nuna yasan tanai ba, dan ya basar kamar ma bai san da zamanta wajen ba. Sai ma wani ƙara harɗe zamansa da yay yana lumshe idanunsa. Baki ta ɗan taɓe ta ɗauke kanta itama. Sosai ruwan ke sauka kamar ba ruwan farko ba, ga wani sanyi mai ratsa ɓargo duk da suna a rufe. Fara ƙudindine jiki Iffah tai tana ɗan yamutse fuska, sai dai duk da haka zuciyarta zungurarta take ta leƙa taga yanda ruwan ke zuba. Amma shakkar kasancewarsa a wajen ya hanata haka.

         “Sit”.

   Ya faɗa kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba. Da sauri ta buɗe idanunta da ke lumshe. Har yanzu yana a yanda yake. Kauda nata kan tai itama tana ɗan yamutse fuska. Sai kuma ta dubi kujerun, ji tai bazata iya musa masa ba, dan haka takai zaune tana ƙara ɗan matse jikinta dan sanyi takeji yana ratsata.

      Idanunsa ya ɗan buɗe a kanta sai kuma ya ɗauke. Cike da ƙasaita ya mike yana zare jacket ɗin jikinsa, ita dai kallonsa take ta ƙasan ido, jin ya zagaya bayanta ta maida kanta ta risinar. Sai kuma ta sake ɗagowa da sauri jin ya ɗora jacket ɗin a jikinta. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tare da dafe rigar data ɗan zame ta ce, “Thanks”.

      Bai ce mata komai ba sai da ya koma ya zauna inda ya tashi sannan ya sake dubanta fuska babu alamar wasa ya tsareta da idanunsa masu kaifi, kasa jurewa tai tai ƙasa da nata tana bin ash color ɗin jacket ɗin nasa mai ƙyalli da ƙamahinta ya mamayeta  da kallo. 

     “Waya faɗa miki an saka abubuwan nan? Su waye suka saka kuma?”.

     Batai tunanin zai tuhumeta da sauri haka ba, dan haka ta ɗan ɗago ta dubesa. Idanunsa na kanta har yanzu, ga fuskar nan babu alamar yasan miye murmushi ma. Nata tai saurin maidawa ƙasa ta sake risinarwa dan kallon ya matuƙar ratsata. Kamar mai raɗa a hankali ta furta “A mafarki na gani”. 

       Zaune ya tashi da ƙyau, Wani irin kallo yake mata tamkar idanunsa zasu faɗo. Jin kaifafan idanun nasa har yanzu a kanta ya sata saurin faɗin, “Da gaske a mafarki na gani, nima kuma banyi zaton abin zai tabbata ba, kawai dai zuciyata ce ta kasa nutsuwa akan lamarin. Dan duk sanda naita maimaita mafarki to daga baya sai abun kaga ya kasance a wasu lokutan”.

       (Ya arrahaman) ya faɗa a zuciyarsa dake faman bugawa da sauri-sauri. Kallo yake mata na kin ma rainamin hankali ko ke ba mutum bace halan, dan haka ya ƙara tsuke fuskar a zahiri. A ɗan kausashe ya furta “Who Are you Zawj? Miya kawoki gareni? Babu yanda za'ai wanda yay shirin kasheka ya dawo ya taimakeka kan yunƙurin wani mai ƙudiri irin nasa”.

         Yanzu kam ɗago idanunta tai ta ɗan kallesa dan tsabar shiga mamakin furucin nasa. Maidawa ta sake yi ta risinar tsigar jikinta na tashi saboda yanda kallon ya wani irin ratsata. Cikin wani irin sanyi da ɗan kaushi-kaushin muryar tunawa da ahalinta da suka tarwatse a dalilinsa bata san ya akai furucin ya fito ba ta ce, “FHAREEDAH BINT ZAYYAN!!”. Sai kuma tai shiru na wasu sakanni, kamar wadda aka tsikara ta ce, “Bani na kawo kaina gareka ba kai ne ka kawo kanka gareni Sultan. Mu huɗu iyayena suka haifa a duniya. “Hanash, Arfa, Fariha sai ni auta. A shekara ɗaya kafin yau gidanmu shine aljannarmu ta duniya, dan duk da muka kasance talakawa muna farin ciki irin wanda masu dukiya ba lallai sunayi ba. Cike muke da soyayyar juna, ƙauna, kulawa irin wadda ko tuntuɓe ɗayanmu yayi mu duka munajin ciwon a jikinmu ne. Duk wannan aljannar tamu ta sauya ne daga wani yammaci na ranar juma'a da bazamu taɓa mantawa ba. Ranar da zaran ƙaddara yay lilon da har Nina Arfa ta shiga a jerin ɗaya daga matanka.....” Hawayen da suka ciko mata ido suka sarƙeta ta kasa ƙara sawa. Wajen yay shiru sai saukar ajiyar zuciyarta a jajjere dana ruwan sama da ake ketawa tamkar ba ruwan farko ba, shikam yana zaune a harɗe baka isa iya tantance yanayinsa ba, a zahiri ma zakace idonsa a rufe suke, sai dai can ƙasa yake kallonta a wani irin yanayi da shi ya barma kansa sani.

      Hawayen da suka zubo mata ta share badan sun tsaya ba, ta cigaba da faɗin, “Komai ya rushe, komai ya canja, canjawar da har abada baya bazata dawo da shi ba. Na rasata, na rasa Fariha duk a dalilin aurenka, da ga ƙarshe na rasa Ummu da Babiy na rasa Hanash shima duk saboda kai fa. Komai ya ƙare, kamar ban taɓa mallakarsa ba, kamar ban taɓa zama mai ahali ba, kamar ma ban taɓa zama kowaba duk dai saboda kai fa. Inajin ciwo, ciwo matsananci mai ƙuna a kowane ɓargona da gunar jini na. Na kai gaɓar da bana baƙin ciki ko shakkar rasa numfashina nima a yanzu, dan abinda ya rage min kenan kuma bana jin yana da sauran amfani a gareni balle muhimmanci duk fa dai saboda kai. Nafi buƙatar na bisu nima, amma sai bayan na tabbatar da nunama duniya su waye su, wannan alwashi na ne duk da kasancewata mai rauni bazasu sha a banza ba sai dai mu rasa a tare ni da su duk da kasancewarsu a cikin ahali mafi girman daraja da kowa ke kallo a ƙasata....” nan ma kuka ya ƙara sarƙeta mai ƙarfi. 

     A yanzun ma bai iya ko motsi ba binta kawai ya ke da kallo zuciyarsa na wani irin zallo da bai taɓa fuskanta da ga gareta ba. Zamewa tai daga saman kujerar da take zaune a hankali ta durƙusa gabansa, kanta a risine hannayenta a haɗe 🙏. 

       “Ina roƙonka karka sakankance da ni, dan da gaske har yanzu zuciyata cike take da burin ɗaukar fansa. Ina kuma baka shawarar ka yanke min hukunci da gaggawa akan laifina kuma dai-dai da abinda na aikata, dan da gaske na shigo masarautar nan ne domin hukuntaka akan laifin da nake zargin kai kake aikata shi. Da shirin ɗaukar fansar jinin ƴan uwana na yarda da aurenka, da alƙawarin ɗan ɗana maka mutuwa kamar yanda na rasasu na shigo wannan masarautar. Kuma har yanzu ban gama tabbatar da babu hanunka a cikin ba. Ban kuma janye makamaina ba na son tabbatar da hakan. Sai dai ina rokonka kafin hukuncin ka sanar dani alaƙarka da Ajmaal dan ALLAH. Ka kuma janye kariyar da kake ƙoƙarin bani dan killaceni anan tamkar raunani ne. Burina fito-na-fito da su kamar yanda suka nuna min filin yaƙin na shirya. Na shirya tsaf da shirin bama kaina da kai kariya da ga duk wani sharrinsu koda daga baya kaima zan dawo na hukuntaka kamar yanda na shigo da ƙudirin yi duk da sun kasance jininka ne su ɗin”. Hannu ta sa ta share duk hawayenta tana sake miƙewa ta koma saman kujerar. “Kayi haƙuri da tsaurin idona haka nake. Koda ina so ko bana so haka zan cigaba da kasancewa domin hallayata ce wani yanayi bazai canja min ita ba, ita ɗin jinin jikina ce. Kallon cikin idonka na faɗa maka abinda yake gaskiyata bashi ke nufin baka da kima da daraja a idanuna ba. Kai ɗin shugabana ne, mai daraja da wata irin kimar da in wani mahaluki ya zageka a ƙetaran ƙasata ta ruman koda yafi ƙarfi na sai na daka tsalle wajen wanke fuskarsa da marin da sai na zubda haƙwaransa ƙasa a gaban duk wanda ya ke jin ya isar masa. Kayi a hankali Kanada maƙiya sosai kuma zagaye suke da kai tako ina, a cikinsu ma kuma har da ni nan da ke a gabanka yanzu Sultan. Duk ƙanƙantar maƙiyi kada kayi sakaci da shirinsa koda nice nan, dan allura ma da kake gani fa itama ƙarfece, idan har tsayawar numfashi a iya ƙirji baya nufin mutuwa kai tsaye to ka sani fa reza zata iya kisa irin na wuƙa har a gagara iya banbancewa jikin son a tabbatar. Dan haka kamar yanda na roƙeƙa kar sawayenka su wuce sashenka a yau, dan ALLAH kar kaje. Ina maka wannan roƙon ne a matsayin *_MATARKA_* ba shugaba da talakarsa ba, ba kuma ƙin fitar taka zai kareka da ga ƙaddarar ka bane ko hanasu cin nasara a kanka”........✍️



       *_Shahan-shan da gaske fa kayi takanka dan da alama aljanar gaskiya aka aura maka batare da ka farga ba🙆, to nidai ba ruwana kuzo broza ɗinku na cikin haɗari ƴan DAUƊAR GORA.... CONVERSETION 🏃🏃🤔._*



_Ga alakoro nan na raya gori😎😎_

No comments

Powered by Blogger.