Daudar Gora Book 2 page 42
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (42)
.........Zubewa tai a ƙasan lallausan carpet ɗin wajen da ƙyau kamar wadda aka zarema dukkan kuzari. Duk da basu san mita kalla ba tai wannan irin zubewa zaune baki ɗaya duk sai suka saki dariya. Kaka yace “Rigimammiyar yarinya har yanzu ɗin baki yarda ba dai?”.
Kuka ta sake fashewa da shi a karon na biyu kamar wadda kaka yay ma allura. Idonta kan Laptop ɗin ƙuri tace, “Kaka! Babiy! Iyyani! Ummu! Hanash Akhi. Dama duk kuna raye? Kuna raye kukai nesa da ni?. Kuna raye nake kuka babu dare babu rana ba mai share mun? Miyisa haka? Why! Why Iyayena? Miyasa akacemin kun mutu har yanda aka kasheku aka nuna min......”
Wani irin kuka mai ratsa zuciya ya sake kufce mata. Idanunsa kawai ya lumshe yana ɗan matsesu da ƙarfi, dan har tsakkiyar zuciyarsa yake jin kukan. Ga wani abu na zaburo masa tun daga tsakkiyar kai har yatsan ƙafa. Jin zata ɓallo masa ruwa ya miƙe da ɗan sassarfa. A zahiri kam babu abinda mai kallo zai iya gani sai tarin nutsiwarsa da cikar kamala. Shiko shi kaɗai yasan sirrin dake tattare da baɗininsa. Sirrin da yake adanawa tsayin shekaru duk tsananin bamai iya ganosa akan fuskarsa. Da ga shi sai UBANGIJINSA. Sai amintaccen manomin ganyayyakin shayinsa da yake sha domin cigaba da binne raɗaɗin sirrin nasa. Jikin glass window ɗin ɗakin koma ace bango dan kamar da shi ne gaba ɗaya akai ginin sashen nasa ya ƙarasa. Huci yake faman firzarwa a jajjere, idanunsa da sukai wani irin kaɗawa launinsu ya canja nabin wajen masarautar dake ƙwanyar da haske tako ina da kallo. Babu yawan zirga-zirgan mutane, sai masu tsaro tako ina dake kaikawo kowanne da makami a hanunsa, dan tun abin nan na ƙarshe da ya ƙara faruwa da Iffah aka sake ninka tsaron gidan tako ina.
A ɓangaren Iffah kam kalamanta sun matuƙar karya zukatan su babiy, tuni suma sun fara share hawaye musamman Ummu da Iyyani. Kaka dai murmushi kawai yake da bin ƴar jikallen tasa da yake matuƙar so da kallo kawai. Haka ma Babiy ya kafeta da idanu zuciyarsa cike da tausayinta da so. Iffah'r sa jaruma ce, amma kuma mai rauni ce. Kura ce, ga tsoro ga ban tsoro. Murmushi ya saki a karo na farko shima, kafin a hankali ya katse koke-koken nasu. “To ya isa haka ko? Wani ya akai? mi akayi? Duk ya wuce Fhareedah kinji, kiyi haƙuri bamuyi nesa da ke ba dan son zuciyarmu. A duk motsinmu kina ranmu. Ƙaddara ce ta rabamu dake badan mun so haka ba. Amma ki gafarcemu kinji autan Babiy. ALLAH yay miki albarka, ya cigaba da baki kariya”.
Hawayenta ta shiga sharewa tana gyaɗa kai, haka take sam bata da gardama ko jayayya. Dan bata taso taga na sama da ita nayi ba. Sai da ta share hawayenta tas sannan ta sake kallonsu. Murmushi ta saki a yanzu kuma, cike da jin daɗin ganin sun canja mata gasu fas-fes da su. Gaishesu ta fara ɗaya bayan ɗaya, kowanne yana amsa mata cike da kulawa da ƙauna. Su kansu duk ta sauya musu, gani suke ta ƙara musu girma a ido, dan ma tasha wahala a kwanakin nan. Ga wani ƙyau na musamman ta ƙara da uban haske kamar mai yaron ciki. A ɗan marairaice ta ce, “Amma Kaka akace min duk an kashemin ku?”.
Dariya ya ɗanyi cike da dattakonsa. “Uhm uhm Iffatu duk gudun son tabbatar da ƙaddarar wani ga masu buri ai dole suyi haƙuri hukuncin ALLAH da zartarwarsa. A tunaninsu kam mun mutum, sai da wani bawan ALLAH damu kammu har yanzu bamu san waye ba ya tallafi rayuwarmu ya ƙuɓutar da mu..”
Da sauri Iffah ta kai dubanta inda Tajwar Eshaan ke tsaye har yanzu jikin window. Sai kuma ta sake maidowa ga su Kaka. “Har yanzu kuma baku san waye ba da gaske? To amma ya akai nake wannan video call ɗin da ku kuma?”.
A yanzu kam Babiy ne ya bata amsa. “Har yanzu bayan Barrister Abdallah ba mu san takamaimai wanda ya jagoranci fiddomu zuwa wannan ƙasar ta Saudiya ba. Waya kuma ance mana kawai zamuyi magana da ke ne. Mu harma mun fara tunanin ko kece”.
Idanunta ta waro da ƙyau, sai kuma ta sake kallon inda Tajwar Eshaan yake har yanzu, still dai yana tsayensa. “Ko kaɗan bani nace Babiy, hasalima ni an riga an sanarmin na rasaku. Shiyyasa a kullum nake cikin alhini da baƙin ciki.”
Kallon juna suka shigayi da mamaki, sai dai Kaka mutum mai hangen nesa ya ce, “K waya haɗamu da k?”. Baki ta buɗe zata bashi amsa, sai kuma ta sake kallon wajen window ɗin. Cikin sa'a yanzu kam ya juyo, ya wani tsatstsareta da kaifafan idanunsa. Kansa ya girgiza mata, da mata alamar zip a baki da yatsunsa biyu cike da gargaɗi. Jiki a sanyaye ta maida dubanta gasu Babiy, kanta ta ɗan girgiza musu ta ce, “Wani bawan ALLAH ne, asirrance ya kawo min nima ban gama tantance ainahinsa ba”.
Cike da gamsuwa suka shiga jinjina mata kawuna. Kaka kam dai murmushi kawai yayi ya basar. Da ga haka taci gaba da zaƙulo musu tambayoyi suna bata amsa ɗaya bayan ɗaya. Sun kwashe kusan awa biyu kamar ba kuɗi ake ci ba kafin yay mata nuni da sallama dan tuni ya baro window ɗin ya dawo inda ya tashi. Badan taso ba tai musu sallama. Suma ɗin dai da alama basu gaji da kasancewar da ita ba.
Yanda take ta sakin murmushi ya sashi kasa daina kallonta. Sai dai murmushin nata mugu-mugun birkita masa lissafi yake. Jiki a saɓule ya miƙe da nufin barin wajen yana rumtse ido da cije lips, a bazata, bazatar data nema kifo zuciyarsa ƙasa kawai yaji ta rungumeshi ta baya. Cak numfashinsa da duk wani abu mai motsi a jikinsa yay tsaiwar mutuwar wucin gadi. Iffah da gaba ɗaya farin ciki ya lulluɓe mata idanu tama rasa mizata masa yasan tana cikin shauƙi ga neman abokin da zai tayata wannan farin ciki batare data kawo komai a ranta ba ta rungumesa dan yau kallon Hanash take masa ba Shahan-shan ɗin ƙasar ruman ba. Kanta ta sake kwantarwa a faffaɗan gadon bayansa da baifi iyakarta rabi da kwata ɗin tsahonsa ba ta sake matse hannayenta data sakalo ta saman shafaffen cikinsa waje guda tai masa ƙamƙam tana murmushi mai bayyana haƙwara.
A hankali ta furta. “Jazakhallahu khairan Eshaan Akhi. Yanda ka faranta raina kaima ALLAH ya ninka maka farin cikinka na tsahon shekarun da zakai a duniya. ALLAH ya ƙara ɗaga darajarka ya baka kariya. ALLAH ya yafe maka kurakuranka ya baka ikon sauke nauyin daya ɗaura maka na jarabawar shugabanci. ALLAH ya jiƙan mahaifinka da kakaninka da duk wani makusancinka da baya numfashi. UBANGIJI ya biya maka buƙatinka harma wanda ka barma zuciyarka da wanda ma baka jisu a ranka ba har yanzu. ALLAH ya share maka hawayenka a duk lokacin da kaji son yinsu tun kafin su zubo....”
Rawa jikinsa ya farayi, numfashinsa na fisgar fita da gudu-gudu. Dan gaba ɗaya Iffah ta hargitso duk wani rauninsa na baɗini da ya ɗauki tsahon shekaru yana adanawa. Hannayenta da ke akan cikinsa ya zare a hankali cikin son dai-daita kansa, janyota yay ta dawo ta gabansa, kafin ta iya cewa wani abu ko samun damar kallon fuskarsa a wani irin slowly ya rungumeta gaba ɗayanta cikin jikinsa da gaba ɗaya ƙofifin gashi suka buɗe. Ɓat ta ɓace cikin jikinsa tsabar yanda ya fita girma da tsayi, tsam-tsam yay mata har sai da ta saki ƴar siririyar ƙara da masa ƙaramin dundu (ƙulli inji Katsina wa😀) a baya. Ko gezau baiyi ba, sai numfashi da yake ta saki a sarƙe, itako da taji matsan yayi yawa sai ta shiga mutsu-mutsun son ya saketa. Yo ina dalili wannan matsar kamar za'a ɓalla mata ƙashi. Ganin fa zai ɓaɓɓalatanne a shagwaɓe kamar zata fasa kukan ta ce, “Wayyo Eshaan Akhiiiiii!!”.
(Ya arrahaman) ya faɗa sauran notikan da suka rage suna aiki a jikinsa na ƙarasa kwancewa jin yanda ta fitar da kalmar Akhiiii ɗin. Ga wata irin hajijiya da ke juya masa ɗakin na neman zubar da shi ƙasa. Cak ya ɗagata da ga kan ƙasa. Da sauri ta ƙanƙamesa gabanta na faɗuwa jin yanda jikinsa ke wani irin tsuma kamar ba Shahan-shan da ta sani ba. “Am sorry” ya faɗa yana zubewa da su saman gadon da jawota jikinsa ya manne lips ɗinsu waje guda.
Wani irin salo yake mata mai matuƙar birkita tunani da susuta rai. Kamar ba shi ba, kamar ba Shahan-shan ɗin nan ba mai tsananin miskilanci da ƙasaitar mulki. Idanunsa ya matuƙar rufewa, babu yaren da yake fahimta sai yaren isar da saƙonsa ga Iffah. Sai da ya tabbatar ya gama lausasata da dukkan iyawarsa da shi kansa bai san ya iya ɗin ba. Lips ɗinta kam har wani irin zafi-zafi radaɗi-raɗaɗi suke tsabar yanda suka sha wahala a hannunsa. Yana sakin mata su baya taja tana mai jujjuya masa kanta. Da matuƙar tashin hankali da tsoron da ke bayyane cikin idanunta ta. Har numfashinta sarƙewa yake tsabar yanda ta tsorata da yanayinsa wajen furta “Please Eshaan Akhiii Please”.
“Bazan iya ba My Sohaa”.
Ya faɗa cikin wata irin sarƙaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa jinta tattare da shi ba. Ƙirjinta ne yay wata irin sake harbawa. Ta ɗan ƙara jan jikinta baya still tana jujjuya kanta. “Kai shugabane kamun adalci ban shirya hakan ba”.
“Gareki ni bawa ne, ke kaɗaice sirrin Eshaan bin Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb Fhareedah bint Zayyan”.
A cikin matuƙar tashin hankali ta sake ja baya tana girgiza masa kai dan idanunsa basu taɓa firgita rayuwarta irin yau ba, yau ɗin ma yanzun nan. Wani irin murmushi da ya nema ɗauke numfashinta ya sakar mata, tare da ɗora hannunsa saman zip ɗin gabar rigarsa ya zugesa zuwa ƙasa, ya ɗaga rigar kawai ya zare baki ɗaya. Ai a wani irin mahaukacin gigice Iffah ta fasa ƙara jikinta na karkarwa ta tusa kanta cikin filos ɗin gadon ta cure gaba ɗaya jikinta waje guda........✍️
_😬🚴Lamarin ya girmi ƴan shekaruna bara nayi nan._
Leave a Comment