Daudar Gora Book 2 page 56
Book 2 Chapter: 56
."Haba Waheeda ina kika shiga kekuwa haka kinsa zuciyata na neman karasa harbawa a tsaye".
Da yar raha-raha da ga can Daneen Waheeda ta ce, "Oh oh Kinga kwantar da hankalinki nabar wayar ne a daki why ina sashen surukinki. Halan wani masifar shegiyar can ta sake jangwalowa?".
"Uhhm ai wannan karon ba ita ta jangwalo ba ita aka jangwalowa. Ni Ashwaq naga abinda zai kasheni a wannan masarautar yau da raina. Wai kin san kuwa madarar da aka shayar da dakinki wai Miran Jasim ne ya samar da ita".
"What!"
Daneen Waheeda ta fada cikin zabura da ga fasa zaman da tai niyyar yi da ga can. "Wait! Wait wait Ashwaq wai nikam mi kike son fada minne haka. Jasim Akhi namu kike nufi yake shirin kashe Eshaan din komi? Ni Wihy gaba daya ma kin rikitamin lissafi".
"Bake lissafinki ke a rikice ba, ai kowa ma yau a masarautar nan lissafinsa a rikice yake wallahi.
Tiryan-tiryan ta kwashe komai na zaman kotu a yau ta fada mata kamar yanda ta saba kai mata gulmar duk wani motsin yan masarautar musamman Malikat Bushirat. Wani irin irin tashin hankali Daneen Waheeda ta shiga tana zungura manya-manyan zagi dan ita dama can mace ce masifaffiya mai zafin tsiya. A wani lokutan akance tafi kowa gado mahaifinsu a kaf yayan Tajwar Abdul-majeed. Daga can ta ce, "Gobe ki tsumayi zuwana RUMAN yar uwa wannan dambarwar ba'ayita babu ni kusa ba. Amma karki fadama kosu Mammah. Shin yaya bakar dagarki tayi ne za'a kashe mata tilon dan gwal din ta da take hura muku hanci".
"Uhm-iuhm ai labarin kam dai babu dadin ji, amma tunda kince kina tafe ke dai kwantar min da hankalinki sai kin iso kawai".
"Okay bara kiga naje na fara shiri ma tun yanzu. Amma da mutuniyarki zan taho dan wannan karon kam inaga sai na nunama Eshaan kwanji akan Iftihal dan ko yaki ko yaso sai ya aureta tunda dai matan sun daina mutuwar".
"Ina tare da ke dari bisa dari kuwa. ALLAH ya kawo ku lafiya".
Da ga haka sukai sallama Malikat Ashwag na faman sakin murmushi, dan itafa ranta fari kal da abinda ya faru a yau din.
(Ina fatan kun gane matsayin Daneen Waheeda dai. Itace kanwa ga Daneen Ammarah da Tajwar Haysam mahaifin Tajwar Eshaar ta uku ga Malikat Haseenat da mukace tana aure acan yankin larabawa. Kawace sosai ga Malikat Ashwaq, kuma yar uwa, dan kusan ma itace tai ruwa tai tsaki wajen gain Malikat Ashwag din ta auri Tajwar Haysam duk da shima dai ya sota a karan kansa. Tare sukai karatu dan haka akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu da har take tayata kishin Malikat Bushirat. A duk sanda ta sami wani sabon labari musamman akan koma bayan Malikat Bushirat sauri take taga ta sanar ma Daneen Waheeda. Shiyyasa a randa hadimanta sukazo mata da bayanin Malikat Bushirat taje wajen Malikat Haseenat akan kara auren Tajwar Eshaan tai azamar kiranta ta sanar mata dan tasan babban burin Daneen Waheeda din shine hada auren babbar diyarta da Tajwar Eshaan da suke kusan sa'anni. Ta matukar mutuwa a kansa amma shi ko kallo bata ishesa ba. Hakan yasa ita Daneen Waheeda din taso a hada auren amma Malikat Bushirat taki bada hadin kai. Dan ta fahimci so Daneen Waheeda keyi Tajwar Eshaan ya auri yarta su koma juya akalarsa data mulkin kasar ruman din. Ga kuma sharadin da UWA ta gindaya mata na karta yarda Tajwar Eshaan ya auri wata da ga cikin zuri'ar masarautar sam. Yin hakan gagarumin abune da zai rusa komai da yake komai a hanunsu. @) ALLAH yasa kun gane)
Dan daburcewa uwa taso yi, dan bata so akazo wannan gabar da wuri haka batare data Karmala shirinta ba. Anya kuwa batayi babban sakaci akan ta-kurya ba. Itama fa itace tsanin cikar nata burin data dauki tsawon shekaru tana bi matakala-matalaka domin maida murtani ga ahalin wanna masarauta baki daya.…... Ganin irin kallon da ta-kurya ke mata ne ya sata hadiye komai ta dai-daita yanayinta. Fuskarta ta sake tsukewa da gyara zaman kasaitarta. "Ta-kurya ban boye miki domin wani dalili ba, sai dan kareki da ga shagala kan al'amarin sa, amma ki sani na jima biye da Jasim da hana makircinsa tasiri kan Ajlaan. Shin bakiyi mamaki ba ne yau? Bakiyi mamakin faruwar abinda ya faru din ba ne? To bari na kaiki inda baki sani ba. Nice nan da kaina na budewa Jasim aiki yau, kuma na fara ne tun a randa ya kai kayan asiri fadar Ajlaan. Ban miki maganar bane ba dan ina son sai an kai karshe. Kuma duk abinda ya farun yau a kotu nima ina tare da ku".
Wata irin wawuyar ajiyar zuciya Malikat Bushirat ta sauke. Gaba daya sai taji abinda ya tsaya matan a makoshi ya fada a cikin cikinta.Dari bisa dari ta yarda da zancen uwa, dan bata taba mata karya ba (hummmm). Fuskarta dauke da murmushi ta sake gurfana a gabanta. "Yanzu kam na fahimta, na fahimci komai uwa. Dama ni nasan bazaki bari na fadì ba. Amma naso ace kin sanar min tuni, da sai na daidaita rayuwa jasim,sai na kafa tarihi akansa irin wanda harara wani bazai sake kwatantawa ga Saiful- malik dina ba a wanna masarautar"
Wani irin shegen dariya uwa ta kwashe da shi."K yar halak ce ta-kurya, shiyyasa nake sonki fiye da duk wanda ya kasance a karkashin baiwata. Na miki alkawarin bazaki sake yin kuka ba, zan cigaba da tsaya miki fiye da tsayawar da nai miki a baya. Zan cigaba da kare Ajlaan fiye da kariyar da kike tunanin yana da (Wa"iyazubillah. Ya rabba ka tsaremu da aikata shirka koda a cikin duhun jahilci ne @ A). Zan baki mamaki, tabbas zan baki mamaki ta-kurya".
"A kullum cikin bani mamaki kike ai uwa, shiyyasa bazan gaji da fada ba, bazan gaji da maimaitawa ba ke ta dabance a cikin daban".
"Hhahahahahaha!!!!!!!".
Uwa ta kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya har ta-kuryar najin sautinta cikin iska, kai kace gaba daya masarautar koma kasar ruman dinne baki daya zasu jita.
(Uhm uhm da alamafa akwai wani kulli tare da Uwa, ko minene shi@? Muje dai zuwa sannu sannu ai bata hana zuwan sai dai a dade ba'a je ba🏃♀️🥱)
A wani bala' in firgice ta farka da ga barcin da ya figeta bayan idar da sallar azhar. Kanta dake wani irin sara mata ta dafe tana ambaton sunan ALLAH. Ta kai tsahon minti uku a haka kafin ta mike daga saman sallayar da anan barcin ya kwasheta. Gaba daya jikinta tsuma yake, yayinda zuciyarta ke mata tariyar mafarkin nata dalla-dalla. Jin jiri na neman zubdata kasa tai saurin zubewa bakin gado tana sake dafe kai. A hankali ta furta, "Uwa!! Wacece ita? Ta ina zan fara bincike saninta",. Kantane ya sake sara mata, tunda take mafarke-mafarkenta bata taba mai nauyi irin wannan ba. Duk da bataga fuskar wadda ke zaune a kujerar karfen nan ba zagaye da wasu irin munanan halittu taji a ranta dole ta kasance abar toro. Sai kuma gain Malikat Bushirat da tai a gabanta dirkushe, shin minene hadin Malikat din da wadan nan munanan hallitun? Tajwar Eshaan a gefe daddaure da wasu irin igiyoyi wuta, sai dai shima bata ganin fuskarsa amma tana iya jin yanda yake ambaton sunayen ALLAH radam.
"What's wrong..
Dagowa tai da sauri dan sam bata san da shigowarsa cikin dakin ba, hasalima bata san ya dawo ba. Idanunta data kafeshi da su ta dan janye tana kara tsarkake sunan UBANGIJI mahaliccin wannan bawa. Komai nasa mai kyau ne da birgewa. Hatta kayan zaman gida dan ya saka badan kwalliya ba sai su fidda cikar kamalarsa da zati.
"Kaina ke ciwo".
Ta fada kanta a kasa dan kallon nan nasa na kasa-kasa da ke daburta mata lissafi bata son shi. (Aljanun sunzo kenan) ya fada a zuciyarsa yana wani dan yamutsa fuska. A zahiri kam baice komai ba ya dai cigaba da kallonta. Kusan minti daya sannan ya motsa da cigaba da takawa a hankali cike da kasaitar nan tasa. A gabanta yaja ya tsaya, tare da zare hannunsa dake cikin aljihun wandon jeans dinsa ya mika mata. Idanunta ta dago ta kalli hannun da ke fari tas da shi, ga jini nata kaikawo a tafin kamar ba namiji ba. Idanunsa ya dan lumshe da budewa a lokaci guda yana gyada mata kai alamar ta daura nata. Kamar mai jin tsoron hakan ta dago natan ta dora a cikin nasan. Sake lumshe idanun vavi kamar wani wanda maganadisu va taba.
din akwai wani kenan. To miyasa ta boye? Bashi da mai basa amsa baya kuma bukatar sonji gareta yanzu dan ransa duk babu dadi yake ji. Itama da kanta ta fahimci hakan, dan fuskarsa a tsuke take fiye da sanda suka fita kotun. Sai duk take jin kuma babu dadi. Dan haka kawai take jin tausayinsa. Idan har zai shiga damuwa saboda halin wancan karen uncle din nasa, yaya zai kasance kuma a randa zai san mahaifiyarsada kanta ke halaka masa matan aurensa da duniya ke kallonsa a mai halakasu tsahon shekaru. Kai kai wannan al'amarin fa na taba mata zuciya why sosai matuka. Ajiyar zuciya ta dan sauke a hankali, sai kuma ta kai hanunta saman lallausan gashin sajen fuskarsa ta shafa. Murya can ciki ta ce, "Kayi hakuri? Ka amsa da hannu biyu jarabawace. Badan UBANGIJI baya sonka ba ya jarabeka da su. Shi kansa mulkin ma da kake kai ai jarabawa ce. Kai numfashinmu ma kansa jarabawace a garemu, dan UBANGIJI ya azurtamu da shine domin yaga zamu kasance masu bin dokokinsa ne ko kuwa masu bijire masa".
Idanunsa da ke lumshe tun sanda ta daura hanunta saman fuskarsa ya bude a hankali,sunyi zajur fiye da yanda ya shigo da su a dan birkice. Hannun ya kamo yana kallonta, cikin tsananin kasala ya daura lips dinsa a tsakkiyar tafin ya sumbata. Sai da ta matse jikinta tsabar vanda lininta vAv wata irin vamuitsawa har cikin fara son kwatar kanta. Sai dai kuma babu hanyar samun wanna damar da ga jarum Shin yaya lafiyar giwa da ma. Balle kuma ita da kanta ta balle likin.
Duk yanda taso tuna masa dinkin dake a tare da ita babu alamar yana ma iya jinta balle fahimta. Burinsa kawai yake kokarin cimmawa a cikin rufewar idanu..
(* Tsun-tsun da ya ja ruwa (?))
***
Da karfi, karfin karfi yake buga kansa a bangon dakin kurkukun mai tsananin duhu da ta iya karamin windown kawai ake iya gain dan ziririn haske. Gaba daya zuciyarsa ta bushe, zafi
yakeji a cikinta mai tsananin tururi dake kona zuciya. Shi shi Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb ne wata karamar yar iskar yarinya yar cikin cikinsa tai sanadin kawowa cikin kurkuku. Shi Arshaan da ya koya sanin kansa a wajensa zai yima cin amana? Shi hadiminsa da ya dauka tsahon shekaru yana kyautatama zaici amanarsa a gaban makiyansa. Wace irin wannan, mai tsananin duhuwa da babu lissafinta a cikin duka lissafe-lissafensa. Ta yaya shi Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb zai yi irin wannan faduwar bakar tasan a gaban karfin ikon dan makiyansa kuma makiyinsa.
Cigaba da buga kan yake da karfinsa yana ihu mai tsananin karaji da ya saka masu tsaron dakun kurkukun nasa da Tajwar Eshaan ya bada umarnin bama tsar mai tsananin tsauri tsora. Cikin karfin hali daya a cikinsu ya dan leko, ta dan hasken da ya hasko da ga karamin windown ya hango fuskar Miran Jasim da tai wani irin jage-jage da jini dan ya fasa goshinsa. A zabire yay baya yana zazzaro idanu. Yan uwansa ya sanarma, babu bata lokaci sukai kiran shugaban jami'ai suka sanar masa dai-dai da yanke jikin Miran Jasim da jini ke rinjayarsa va fadi kasa....
Rungumeta yay tsam-tsam a cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Jin kukanta yake har tsakkiyar zuciyarsa. Dan kuka take sosai five a daren shekara jiya kasancewar yau fami yay akan ciwo.
"Ni ka kaini wajensu Ummu".
Ta fada cikin kuka. Yanda tai magana tana sake barke masa da kuka ga hawaye shabe-shabe harda su majina ya sa yaji dariya na yunkuro masa. Kamar ba yanzu ta gama iyayi a kotu ba,dan duk abinda ta dingama Miran Jasim akan idonsa ne tsaf. Amma jiba yanzu a dan abinda bai taka kara ya karya ba ta koma abin tausayi.Ya fahimci sai ya dage matukar dagewa akan dorata a irin layin da yake bukata ta hau inba hakaba ragguwa za'ai, bakinne kawai cike da zance da tsiwa. Bashi da burin sake wani auren bayan ita, dan haka dolene ta shirya karbarsa a duk sanda yazo. Murmushin da ke neman kufce masan ya hadiye da kyar da saka hannu yana goge mata fuskar data kwabe da hawaye. Cikin dadisashiyar muryarsa data kara komawa can kasan makoshi a fusge ya furta, "Am sorry bazan kara ba".
"Why zaka kara, ranar ba sai da kace bazaka sake ba amma yau ka kara, ni bazan sake zama a sashen na a kasheni kwana na bai kare ba". Ta kara barke ma sa da kukan tabara.
Yanzu kam kasa rike dariyar yayi, dole ya Murmusa har jerarrun fararen hakwaransa masu è da siririyar wushirya na bayyana Bashi da zabin da ya wuce sake rungumeta a jkinsa tsam-tsam yay murmushinsa iya san ransa. (Shi kam wannan Fitinanniyar yarinya ALLAH ya bashi, kuma yana so da kaunar abinsa fiye da zaton mai hasashe). A zuciyarsa yake maganar yana bata sumbata masu kyau a wuya. Kafin ya mike ya dagata cak zuwa bathroom. Idanunta ta rumtse sosai da kankamesa ita a dole karya gammata jiki kar kuma ta gansa itama.
Gashi yay mata mai kyau bayan ya duba yau baiyi barna ba dan ciwukan wancan ranar ma sun warke sai abinda ba'a rasa ba, taimaka mata yay tai wanka, hawaye kuwa da ya ga ba dainawa zatai ba bai sake ce mata komai ba kansu. Da zasu fito cewa tai ita why bazata iya ba sai dai ya dauke ta. Baice komai ba, illa murmushi da yay a zuciyarsa ya dauke ta cak suka fito tana faman tura masa karamin bakinta.Ga idanu sunyi luhu-luhu na kukan da tasha.
"Idan baki bar turamin bakin nan ba zan maimaita ni babu ruwana". Ya fada yana tsane mata laimar ruwan kanta da towel. Narai-narai tai da fuska zata sake masa kuka ya daura yatsansa saman bakinta ya ce, "Shilli!! Harda kuka ma". Babu shiri ta hadiye abunta da maida bakin da sauri.Murmushi ya saki ya cigaba,Da tsane mata mata gashin…. kiran da ya shigo ta sashi dakatawa su duka suka dubi wayar, kamar bazai daga ba dan har tana gab da tsinkewa sai kuma ya kai hannu ya dauka batare daya matsa da ga gabanta ba ko dauke towel din da ga kanta.
Cikin girmamawa shugaban jami'ai ya shiga gaishesa da ga can, a takaice ya amsa masa murya a dake kamar bashine ke hidimtawa yar yarinya ba. Da ga can shugaban jami'ai ya kara nutsuwa sannan yay masa bayanin abinda ke faruwa. Shiru kamar bazaice komai ba kafin ya nisa a dan fisge da maganar nan tasa kasa-kasa ya ce, "Doctor Afif ya je ya dubasa a cikin kurkukun". Daga haka ya yanke kiran.
Kallonsa Iffah tai da jajayen idanunta, gaba daya ya sauya kamar bashi ba ya koma mata Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da ta fara gani a sashen Mammah. Muryarta a dashe saboda kukan da tasha ta ce, "Miya faru?".Kamar bazai kulata ba yana cigaba da goge mata kan tsahon minti biyu kafin ya motsa lips da kyar ya furta "Jasim"……………✍️
Leave a Comment