Daudar Gora Book 2 page 63

 


Chapter: 63


A bangaren Iffah kam itama dai wanka tai ta gyara jikinta, yunwa ta hanata cigaba da zaman dakin ta fito neman abinci. A irin wannan lokacin. Babu kowa a falon sai daddadan kamshi da sanyin ac mai ratsa

bargon jiki, mamaki ya kamata, duk da dan sanyi-sany in garin na hadarin dake tasowa dan fitina sai an kunna na'urar sanyaya waje, baki ta tabe abinta ta nufi dining room din da glass ne kawai ya gitta tsakaninsa da falon dan komai a tsare yake.


Shayi tai kokarin fara sha dan shi take bukata, wani irin masifar sarawa kanta yay lokacin da hanunta ke sauka kan abinda aka zuba shayin. Janye hannun tayi da sauri ta kurama flaks din shayin ido, sake kai hannu tai a karo na biyu, nan ma kanta ya kara sarawa al'amarin kamar wata almara. Sake janyewar dai tayi tana kaiwa zaune jagwab idonta akan flaks din dai. Ta kwashe mintuna uku tana kallon sa sannan ta sake daurawa a karo na uku, yanzu kam duk da abinda takeji a jikinta na azaba bata cireba tsahon wasu mintuna. Idanunta sunyi jazur cikin kankanin lokaci, gaba daya kamanninta sun canja kamar ba Iffah'r ba. A wani irin fusace ta mike dauke da tray din da flaks din ke kai zuwa kitchen.


Taku take cikin nutsuwarta da kasaita ki tarwada ko budurwar hawainiya.

Kwarjininta da cikar kamalarta kan shafe karancin shekarunta musamman dan tana a cikin irin wannan yanayin. Kasancewarta a kitchen ba karamin rudani bane ga ma'aikatan cikinsa. Hannu kawai take daga musu da ga gaisuwar da suke mikowa gwiyawunsu kan kasa. Kwalayen gayen shayi uku da daya daga cikinsu ke kokarin fitarwa ta zubama idanunta da sukai jazur.


"Wannan fa?".


Cikin sauri suka bata amsa da "Ganyen shayin shugabane".


"Daga ina ya fito?".


"Wanda ke kawowa a koda yaushe".


        '"Ina bukatar ganinsa daga nan zuwa awa biyu".Daga haka tai gaba tana kokarin hada sabon shayi da kanta. Sunyi kokarin ganin sun amsheta amma ta hana hakan, cikin kankanin lokaci ta kammala ta fice batare data sake bi takan kowa ba. Dai-dai kuma da fitowar Tajwar Eshaan cikin shiga mai sauki ta zaman gida alamar bazai fita ko'ina ba. Har yanzu fuskar cidin-cidin take babu alamar yasan minene murmushi. A sanyaye Iffah ta karasa cikin dining room din kamar yanda shima can din ya nufa kamar bai ganta ba.Kama kanta tai itama suka kai Zaune a tare tana dan satar kallonsa tai ta Kasan ido ganin ya kai hanunsa kan jug mar dauke da madara. Ta zubama madarar ido itama, wani irin kallo takema jug din na kurilla,sai kuma cikin dauke kai da cije lips muryarta a sanyaye da girmamawa ta ce, "Shi wannan madaran illane ga duk wanda ya sha shi, barinsa a inda aka gansa shi yafi alkairi".


     Shiru kamar bai jita ba, sai kuma ya waiwayo a hankali ya dubeta, fuska ta shagwabe tare da marairaiceta ta jinjina masa kai. "Dan ALLAH karka sha akwai matsala tare da madaran".


      (Ya arrahaman wai yarinyar nan mutum ce kuwa?) ya fada a zuciyarsa kaifafan idanunsa a kanta. A hankali ta daura hanunta kan nasa ta zare jug din madarar ta ajiye gefe. Shayin ta hada masa, tare da ajiyewa gabansa tana fadin "Zakaji dadin wanna shayin fiyema da madaran".


   Nan ma shiru babu alamar zaice wani abu, ya kumaki daukar shayin. Sai ma gani tai ya yunkura zai mike cike da izzar nan tasa ya taka zuwa kofar barin dining room din, Iffah ta bisa da kallo ta gefen ido zuciyarta na wata irin tafasa itama. Sai dai girmansa da kimarsa bazai barta ta nuna ba koda a fuska. Kanta kawai ta dukar, da karfi ta matse idanunta da cije lips dinta shima da karfi. Kadan ya dawo da jikinsa baya alamar dama bai fice daga dining room din ba ya kafeta da kallo.A karon farko ya saki kasaitaccen murmushin da ganinsa a fuskarsa ba karamin yaki bane. Dawo wa yay a hankali ya zauna ya dauka shayin ya fara sha. Sosai kam ya masa dadi, amma babu alamar hakan a fiskarsa. Itako ta dauke kanta gefe tama daina kallonsa. Cak taji anyi sama da ita batare da tasan sanda ya gama shan shayin ba ma.Wutsil-wutsil ta farayi da kafafu tana tura baki, bai kulata ba har sai da ya kaita bedroom ya dire a gado….





😏 Yau dai bazan dauki rahoton ba.







* *







Cikin kankanin lokaci zartar da umarnin Tajwar Eshaan na rufe su Arshaan da Ameera Haifah ya zagaye masarautar. Nan fa aka fara yan kananun maganganu kamar yanda al'adar take.Yayinda kowa ke tambayar kansa mi yakai Haifah sashen Miran Arshaan din sanin babu wata alaka tsakaninsu ta zahiri face matar yayansa. Anya kuwa babu wani abu a kasa shr Tajwar Eshaan din ya shinshino dan kasancewar tasu tare kam dole akwai wani al'amari mai girma na boye. Wasu ma dai tuni suka fara fassara al'amarin da cewar akwai dai abinda suke aikatawa. In ba hakaba minene ya kaisu haduwa a irin tsohon daren nan ba mata ba, ba kanwa ba, ba uwa ba ko wata shakikiya, kuma har takaisa da neman kasheta irin haka. Labarin ya fara zama gaskiya lokacin da Jasrah ta farfado. Cikin kuka take sanarma Mammah da take dubata tare da Malikat Bushirat cewar dama ta taba zargin Haifah a wani lokaci da tai kiransa tsakar dare, ranar ta samu damar ganin kiranne dalilin manta wayarsa da yay ya fita wani kiran ujila da batasan wayayi masa ba. Tana dagawa Haifah ta yanke kiran, sai dai ta riga taji muryata, koda ta dauki number ta kira da wayarta ba'a daga ba, washe gari ta bada a mata bincike kan number din aka tabbatar mata bata akan waya. Taci gaba da saka masa ido akan hakan amma ba'a sake kuskuren kiran ba,sai dai a wasu lokuta takanji kamshin wani irin turare na mace wanda shine taji a daren jiya Haifah nayi. Ta rushe da kuka mai cin rai da zuciya. Babu abinda Malikat Bushirat keyi sai cika da batsewa, tana matukar son Jasrah a rayuwarta, sannan ga Haifah da ke matsayin kishiya da ma akwai burbushin wani abu a kasan rai na kishin zama da miji daya da sukai,duk da ita shaida ce mijinsu bai taba son Haifah k harva bata taba zama mai wata power a cikin masarautar ba shi yasa tuni bata a cikin jerin wanda suke a gabanta itama, duk da tayi aiki a kanta kamar su Malikat Ashwaq, dan acewar uwa ba'a sakaci da makiyi komai kankantarsa.


        Ta tabbata Jasim da Haifah neman juna suke a bakin kowa bisa zancen Jasrah, sai abinda Tajwar Eshaan din yayi yay matukar burge ahalin

masarautar har wasu na saka masa albarka da rage jin zafinsa a zukatansu. Oho shi baima san duk anai ba, dan yana can tare da yar shilarsa suna hutawarsu. Shirunsa kuma na nufin bazai fitoba yau gaba daya kenan.







****










Kamar yanda Iffah ta bada umarnin gain mai kawo kayan shayin Shahan-shan an isar da sakonta. Bayan sallar la'asar tana tsaka da nazarin littafi aka sanar mata zuwansa ta hanyar wayar landline. Bataso katsewar karatun nata ba, sai dai kuma haduwa da mutumin nada nada matukar amfani dan haka ta tashi ta kimts dazun ta riga ta gama tsara shirinta yanda ya dace, dan sun tattauna da Daneen Ammarah ta kuma bata shawara duk da a farkon bayanin Iffah din jimm tayi na rashin fahimtar manufar hakan. Sai da Iffah tai mata bayani dalla-dalla dai-dai da yanda ta tsara sannan ta gamsu ta Kuma bata goyon baya dari bisa dari.


     Hurumin duk wani bako a sashen Shahan-shan iyakarsa falon farko ne, wanda har va tsallake zuwa na biyu ya kai babban bako kam na musamman, balle na uku kuma da a tarihi ma bayan masu hidima Malikat Haseenat da Malikat Bushirat ne kawai suka taba iya tsallake wannan hurumin sai ko Daneen Ammarah da tai dalilin Iffah, dan Tajwar Eshaan fa bai zauna a sashen da mahaifinsa ya rayu ba. Shi da kansa mahaifin nasa yasa akai masa wannan ginin tunkan ya dawo kasar ruman. Hakan yasa har yanzu babu wani mahaluki daya san sirrikan tsarin wannan sashe sai mai shi din.


     A kowane falo Iffah na samun gaisuwar girmamawa, dan ta stairs ta biyo ko'a jikinta duk da wahalar hakan, yayinda amintattun Hadiman Tajwar Eshaan da'a ka'ida basa sakkowa ko falo na biyu sai da dalili ke biye da ita. Dattijon mutum da alamu suka nuna shima din dai wani babbane dan babu wata kazamar shiga tattare da shi vav saurin mikewa domin girmamawa ga zawjata-almilk din. Iffah takai zaune tana satar kallonsa ta gefen ido batare da kowa zal iya lura da hakan ba. Rissinawa yay domin gaisheta ta daga masa hannu kawai da masa nun da wajen zama.


     "Godiya nake ranki ya dade".


Ya fada cikin kankan da kai yana kaiwa zaunen".


     Sai da taja kamar minti biyu falon shiru kafin ta nisa. "Na bukaci ganinka nan ne bisa wani dalili da bai gaza biyu ba. Na farko daga yau na dakatar da kawo duk wani ganyen shayi da sunan Maleek a gidan nan. Na biyu akwai aikin da zakamin".


     Hankali tashe ya dan dubeta sai kuma ya rissinar da kansa. "Ranki ya dade ki gafarceni, wani abu ya faru ne?".


   "Komai bai faru ba. An samu sauyin sabon tsarine kawai. Shin kozan iya sanin sunayen abubuwa da ake hada kayan shayin Maleek?"


     "Sosai kuwa ranki ya dade, mi kike bukatar sani?"


"Komai"


    Ta bashi amsa a takaice. Da sauri ya bude jakkar gefensa ya zaro wani littafi. Da sauri daya daga cikin hadiman ta amso ta kawo mata bayan ta kai har kasa. 


A dake Iffah ta amsa babu alamar wani dar tattare da ita ta fara duba littafin Kavance dan babba.


    Duk da yasan babu wani abu na cutarwa a ciki tunda a sirrance kuma aka bashi ganyen shayin da ya aiko jiya da dare a tsorace yake, dan harga ALLAH gizagon wannan baiwa da kwarjininta ya cika masa ido matuka har yana jinsa a takure cikin falon ma. Da din dadawa kuma wannan shine karo na farko da akai masa irin wanna kiran ma sabanin da da sai ya hada wani samfur na sabon ganyen shayi yakan zo ya gabatar kozai birge Shahan-shan.


     Kusan mintuna biyar Iffah nabin littafin daki- daki har kusan tsakkiyar, dan gajerun bayanai ne akan yanda ake hada ganyayyakin da sunayensu. Rufewa tai tare da dan dagowa ta dubesa. "Uhm komai dake anan kam bashi da wani aibu, sai dai sabaninsa daga yanzu muna bukatar fresh ganyayyakin ne. Kuma za'a dinga noma su ne a cikin masarautar nan".


"Yanda kike so haka za'ayi ranki ya dade". Ya fada cikin tashin hankali a bayyane. Iffah da tai kamar bata fahimcesa ba ta mike, "Ka hada duk abinda ya dace a turamin, idan na kammala da nawa shirin zan nemeka".


"Godiya nake ya Zawjata-almilk. ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai amfani".


   Hannu kawai ta daga mai tai wucewarta,hadiman da al'ajabi ya sandarar a tsaye suka

take mata baya da sauri….✍️







(Wato wannan yarinyar ko? Humm 🥱😂


No comments

Powered by Blogger.