Daudar Gora Book 2 page 64

 


Chapter: 64


Tunda aka shigo da Arshaan dakin kurkukun da ke makwaftaka da juna da na Miran Jasim sukema juna kallon kallo, duk da dai shi Jasim bai ko motsa da ga zaman takurewa waje dayan da yay ba, su dukansu dakin

babu yawaitar haske, sai dai ta dan hasken da ke lekowa sukan iya gain junansu. Sun kwashe awa guda a haka kafin Jasim ya mike cikin dan tangadi, dan baya cin abincin da ake bashi ga raunikan da ya jima kansa duk an masa tretiment dinsu. Jikin karfen da ya raba dakin nasu ya tsaya, sai kuma ya kece da wata irin dariya kamar wanda hauka ya kama. Cikin bacin rai da kunar zuciya Arshaan ke kallonsa, sai dai baice komai ba har yayi ya gama yay shiru dan kansa. "Oh!! Kai dama a tunaninka Jasim ne kawai ta karewa Arshaan? Lallai kai jaki ne bazan gaji da maimaita fada ba, why da ace uwarka na raye zuwa yanzu nayi imanin bakin cikin haihuwar wawa da tai irinka ne zai zama ajalinta. Kai anya ma kuwa bada cikinka ta shigo gidan nan namu b


"Jasimmmmm!!!!!!!".


    Arshaan ya fada cikin karaji da wani irin girgiza karfen tsakanin nasu kamar zai babbagesa,amma da yake a gine yake cikin kasa ko gezau shegen baiyi ba. Ka dan Jasim yay baya yana dage hannaye sama kamar wanda yay surrunder, sai kuma ya sake kwashewa da dariya kamar zai fadi ya sake dafe karfen yana fadin, "Shegen kaya ashe kasan abinda kake. To to naji uwarka anan ta haifeka, sai dai wlhy bazan daina tantama ba nikan kodan kasancewarka kasurgumin annamimi, butulu,sannan rago mai labewa a bayan mace domin kubutar da kai. Shin nawa ta siyeka ne har haka?"


     "Yanda aka sayo uwarka a gidan karuwai. Why da ga yau idan ka sake kuskuren zagin uwata, sai na maka lahanin da sai ruhin uwarka ya dawo duniya yana mai cikin garari Jasim.Wawa jaki kawai maybe ma uwar takace ta shigo mana da cikinka da ga wajen dan tsautsayi kawai. Ko an fada maka bamusan tarihin tushenta bane a gidan.


     "Amma kasan zan iva kasheka na binne gawarka a cikin kurkukun nan ko? Idan ka manta bari na tuna maka wanene Jasim in Abdul- majeed Aliy Qutb, domin ni a gareka sai dai kallo sai kuma hange daga nesa koda bakin cikina zai ajalinka. Ko an fada maka ban san kulle-kullen da ka jima kanayi a kaina bane?, Kana goyamun baya domin in mun kauda shi nima ka kaudani, sai dai kuma kayi kuskure, domin kafin kaga biri shi birin ya ganka dan hau. Da ido daya Jasim ke barci,sannan a tafin hannuna kake, zakuma ka tabbatar da hakan nan gaba jadan". Ya kare maganar yana wata yar iskar dariya cikin rangaji harya koma wajen zamansa ya sake zama rigija yana dariyar har lokacin.


      Shiru Miran Arshaan baice komai ba, sai dai yana tsaye kamar gunkin da aka ajiye dan tarihi idanunsa nabin Jasim din da kallo, da alama dai tattaro abin fada yake, ko kuma maganar Jasim din ce dai ke masa kaikawo dan bai taba tunanin yasan da wannan burin tattare da shi ba.







** BAYAN KWANAKI BIYAR **






Kwanaki biyar kenan da mika su Arshaan suma a makargama, Jasim kuwa sati guda. Sai dai kuma Tajwar Eshaan bai sake cewa komai ba game da su, hasalima a yau da ake saran ganin watan azumin ramadana ya dauka hutun fitowa fada har sai bayan salla. Tare da daura Sayeed Fayzul-haq akan komai dan zaije Umrah shi da iyalinsa kamar yanda ya sanar.Tabbas a wannan karon babu wasa a cikin al'amarin Tajwar Eshaan din, dan haka kowa ya shiga taitayinsa har su manyan masarautar. Duk da akwai abubuwan fada a bakinsu har game da karasa zaman shari'ar da aka fara amma sun gagara cewa komai har ya gama jawabin fara azumi da gamashi lafiya yay musu bankwana.


       A lokacin da Tajwar Eshaan ke can yana bankwana da jama'ar fada anan Iffah ce cikin babban bitalmanin kasar ruman bisa jagorancin babban dan Sayeed Khairul-Bashar mai suna Abdul-Shakhur in Khairul-Bashar tana bada umarnin ware kayan masarufi nau'i-nau'i domin dorasa a jagorancin rabawa talakawan kasa. Sai matasan masarautar da ta saka shi Abdul- Shakhur din ya samo har su hamsin da zasu jagoranci sauran jihohi da wanda za'a kai wasu kasashen da yaki ya samarwa yan gudun hijira da ma iftila' in rayuwa na talauci.


      Wannan al'amari ya matukar jjiga kunnen duk wanda ya samu labari a cikin masarautar, dan abinda bai taba faruwa bane, duk da duk azumi akan fitar da kayan masarufi a dan kai jihohi suma kuma ana da kasune ga Tajwar na jihohi bawai a wakilta wasu suyi aikin ba a cikin masarautar. Sannan a duk shekara tun ba hawan Tajwar Eshaan din Malikat Bushirat ce ke da wanna karfin ikon matsayinta na mahaifiya ga Shahan-shan. Sai kuma a yau labarin ya canja akaga Zawjata-almilk kan komai cikin kuma sauyi.


   


     Kamar yanda labarin ya isa kunnen kowa kuwa yaje ga Malikat Bushirat din da take zaman tsara yanda zatai fitar da wanna abinci bisa tsarawar uwa kamar kowace shekara. Ba kuma a bada abincin ma sai bakwai da azumi, sai kuma gashi yau ana gobe saka ran daukar azumi za'a fara rabon. Kayan da aka fitar kuma sun ninka wanda ita take sakawa a fitar sau dari. Dan duk wani abinci dake shekara ta uku a cikin bital mali Iffah tasa an fito da shi ana da kasa a hannun wakilan. Su kuma kasancewar matasa masu zafin nama da son dama su nuna tasu baiwar amma basu da wanna damar sun bata goyon baya dari bisa dari, duk da kasancewarta karama a shekaru kuma sun bata girmanta matsayin Zawjata-almilk, to kwarjini da cikar kamalar ta da barazana ma bazai bari ko kaso kawo mata wargi ka iya aikata hakan ba.


     Tsaf numfashin Malikat Bushirat ya dauke na wucin gadi lokacin da  Jazaa tazo mata da mummunan labari. Ta wani zuba idanunta kamar mai son gano gaskiyar maganar a jikinta. Kafin ta yunkura ta mike cikin wani irin zafin rai ta shiga bedroom din ta. Cikin kankanin lokaci ta canja shiri, tana kokarin fitowa Jasrah ta shigo dakin da sallama, dan tunda aka sallamota da ga asibiti nan sashen ta dawo take zaune, a kallo daya datai mata ta fahimci bacin rai dake tattare da ita. Itama yanzu take jin labarin komai a bakin hadiman sashin, dan haka ta biyota daki sanin yanzu yayar tata zata birkice. Ita mamaki take da yanda gaba daya yanzu wasu halayenta ke neman canjawa. Tunda ta dawo sashen kokarin ganin ta fahimtar da ita wacece Iffah take amma taki fahimtarta, gashi kuma yanzu Iffahn ta sake dangwalo wani al'amarin.


    "Akia Please kiyi hakuri, zuwanki wajen yarinyar nan a yanzu bashine mafita ba, sai dai maya zubar miki da mutuncinki. Ni a ganina nemanta ya kamata kiyi bayan tabar wajen sai muji dalilinta na zartar da hukuncin da kece ke zartar da shi, ko kuma ki tuntubi Abni kiji tunda dai bazatai komai bada saninsa ba".


"Bani hanya Jasrah".


Ta fada a zafafe kamar ma bataji mi Jasrahn ta fada ba. Cikin dakewa itama Jasrah tace,"Bazan barki ki fitaba gaskiya Akia, kiyi tunani abinda kike son aikatawa. Akia na miya canjaki haka? Bayan kuma a baya ba hakan kike ba. Karfa ki manta shekaru kusan hudu muna kuka akan matsalar dake zagaye da mu ta mutuwar matan Abni, amma a yanzu UBANGIJI ya kawo mana iyakar komai, a kanta komai ya canja har mutane suka fahimci makarkashiya ake masa sabanin da da shi kai tsaye kowa ke zargi. Kamata yay mu rungumi yarinyar nan muyi farin ciki da kasancewarta mata ga danmu bawai bore ga duk yunkurinta ba. Matsalarmu da ita dama can akan abinda muke zargin ta aikata ne, amma yanzu mun fahimci ba haka bane ba, to mizaisa bazamu manta komai ba mu maidata komai dinmu kodan farin cikin da yaronmu ke samu da ga gareta.


    Tassss! Kake jin saukar lafiyayyen mari a fuskar Jasrah, idanu kawai ta rumtse tana mai kauda kanta, yayinda Malikat Bushirat ke wani irin huci. Abune da bai taba faruwaba, dan ko sanda Jasrah a karama bata taba dukanta ba, shagwabata tai kamar yar data haifa ba kanwa ba, ta kyautata rayuwarta tai mata raino kamar Kwai a cikin cokali. Idanunta da sukai jazur ta bude, ta dan girgiza kai tana murmushi mai ciwo. "Zan iya amsar duk hukuncin da zakimun Akia dan ke uwa ce a gareni ba yar uwa kawai ba. Amma why bazan taba barinki ki zubar da mutuncinki ba". Tana gama fada ta zare key din kofar ta fice da sauri ta maida kofar ta kulle

gaba daya. Duk kiran sunanta da Malikat Bushirat keyi cikin karaji batako kulata ba tai shigewarta dakin dake matsayin nata a yanzun tana hawaye. Ita kam ta fara shiga rudani akan canjin halayen yar uwar tata, ta sara mike damunta a yanzu. Anya ba masu son cutar da Eshaan bane suka dawo kanta suka saka kiyayya a tsakaninta da yarinyar nan. Ita kam yanzu ta fahimci Iffah, tanajin kaunar yarinyar a ranta kamar tun a da can farko, matsalar data biyo baya ma a dalilin abinda suke tunanin ita ta aikatane. Amma yanzu kunyar haduwarsuma take ji. Dan bata san da bakin da zata fara rokonta gafara ba. Amma koba komai ALLAH ya sakama yarinyar tun ba'aje ko'ina ba, tunda gashi wanda ta yarda da shi fiye da kowa da komai yau shine kecin amanarta da matar dan uwansa, wannan wace irin mummunar kaddara ce. Hawaye masu zafi suka silalo mata, dan abune dake mata matukar kuna da zafi a zuciya tunda ya faru, ga kunyar fitama da takeyi dan ko hadimai shune suke mata akaikaice matsayin matar mai neman tsohuwar matar Shahan-shan……..✍️

No comments

Powered by Blogger.