Daudar Gora Book 2 page 74
…...……….Komai ya zama an yanka ta tashi, kashe ahalinta
ne kawai bata tashi mana ba, dan su kam an tabbatar mana sai dai was basu ba. Eshaan bai mutu ba, ita kuma ta samu nasarar barin kurkuku, sannan mun neman Barrister
Akeem daya jagoranci kashe mana iyayenta mun rasa. Tun daga lokacin komai ya rikice mana, wasan ya fara sauya salo. Koda muka tunkari Barbushi sai ya kwantar mana hankali da cewar ya samo wata mafitar. Zai kauda mana yarinyar cikin sauki, zai kuma kwantar da Eshaan ciwo da komai sai dai a masa. Dolene a lokacin a yarda daya da ga cikinmu ya zama Shahan-shan. Wannan shine dalilin samun kaimi da ga kowannenmu na ganin ya kuma kada dan uwansa kasa. Yayinda muka cigaba da kulla makirce-makirce ga Eshaan ciki hard kashe Sayeed Khairul-Bashar da haddasa zanga-zangar mutanen kasa, da tada bomb a cikin motar Barrister Abdallah Aas, da hada videon yanda yake kashe mutane da tsafi muka Bama matarsa da tunanin zata yada duniya ta gani, amma sai duk batai haka ba...Wata irin hayaniya ta tashin hankali ce ta tashi a kotun, musamman iyalan Sayeed Khairul-Bashar. Babban dansa yay wani irin daka tsalle sai gashi a gaban su Miran Arshaan din. Shaka ya hadasu ya kai musu, take yan uwansa suma suka iso. Da kyar aka kwaci Miran Arshaan da Miran Jasim a hannun yayan Sayeed Khairul-Bashar, dan sai da Shahan-shan ya tsawatar da kansa. Sai dai shima karfin hali kawai yake, duk da kuwa yasan abubuwa da yawa da Miran Arshaan din ya fada a yanzu ta dalilin bibiyarsu da ya rinkayi, akan su Bably kuwa randa Iffah tai masa rakon nan na ya binciko mata iyayenta a matsayin Ajmaal a ranar ya fara bibiyarsu har ya gano sune, shine kuma ya kubutar da Barrister Abdallah as da ga tashin waccan nakiyar da har yanzu mutane da yawa suke dauka ya mutu. Kisan Sayeed Khairul- Bashar ne kawai bai gama tabbatar da wanda yayisa ba sam sai yanzu da suka fada. Bayan kotun ta natsa da kyar, masu kuka nayi, masu tsine musu nayi Sayeed Hanifud-Din da gaba daya jikinsa yay sanyi ya dubi Miran Arshaan din da fadin, "Ita kuma Ameera Haifah minene alakarku kenan?"
Kallonta Miran Arshaan yay, ganin yanda ta kakkafesa da idanunta ya sashi sakin murmushi. "Duk abinda na lissafa maka anan harda ita a ciki, alakarmu ta fara kasancewa a tare ne bayan mutuwar Haysarn Akhi. Sai dai ita da Jasim tun kafin shigowarta masarautar nan suke tare. Dan ta kasance ma tarkar matarsa ce a yanda yake tarayya da ita a duk sanda ya yaso…
*Tsinanne kaima ai naga kana tarayyar da ita, kuma garama ni kafin tai aure ne, kaiko a cikin gidan nan tana matsayin matar Haysam din kake tarraya da it...
"Karya kake gatalalle, ban taba kusantar Haifah ba sai da Haysam ya rasu, ita kuma ta kawo min kanta da kanta bani a gayyato ta ba. Idan karya na mata gata nan ta misalta mana.......
Wani irin mahaukacin buga guduma Tajwar Eshaan yayi, sai da kowa ya zabura a cikin kotun har Miran Arshaan din da ya karbe Miran Jasim a fusace. Tabbas da ace idanunsa ba cikin gilashi suke ba babu abinda zai hana juyewarsu firgita kowa da ke a wajen. Sai dai fuskarsa fa tayi masifar sake tsukewa,
Sayeed Hanifud-Din da ya fahimci maganar ce baya bukatar a cigaba da yi, ya ce, "Kowa ya fahimta. Sai dai akwai abubuwan da bamuji da ga gareka ba,wanda kuma kowa yake ji a jikinsa kune kuka aikata din. Na farko ima Zawjata-almilk allura lokacin da take a kurkuku, sannan jefata a cikin ruwan shima".
"Tabbas allura mune, sai dai Bama allurar komai bace face ta sihiri da Barbushi ya bamu domin kame mata jiki ta kasa tsinana komai, dan haka mukai amfani da rigar da ke jikin Eshaan a randa ta bashi madara dan ta dauka shine, Haifah ce kuma tare da ni muka je mukai mata allurar a ranar. Amma jefata cikin ruwa wlhy bamu bane ba...."
"Karya kake kune Jasim, dan duk wanda ya aikata wadan can ayyukan to shine ya aikata wannan, kana son ka boyene domin kuwa al'amarin yayi iri daya da saka Miran Nayyar ruwa da akai shekarun da suka shude….
"Gaskiya ya fada basu bane ba!!".
Kusan a tare duk wanda ke'a cikin kotun ya dubi wanda yay maganar, yayinda Iffah ta mike a zabure dan wanna muryar ko'a mafarki bazata taba layance mata ba. Kaka kenan, dattijo ko muce tsoho mai ran karfe. Ya kara wani fes abinsa saboda canjin rayuwa da ya samu duk da jikin tsufarsa na nan tare da shi. A hankalin Tajwar Eshaan ya lumshe idanunsa da ke a cikin glasses, duk da shima dai abinda kakan ya fada ya girgiza mamakinsa, ga zuciyarsa dama a takure take da zancen su Miran Jasim na tabbatar da basu ke kashe masa mata ba kamar yanda Iffah ta taba fada masa..... Sayeed Hanifud-Din ne ya katse shirun idanunsa a kan Kaka ya furta,"Taya akai ka sani bawan ALLAH? Idan kuma har basu bane wanene?".
Kaka da ke fitowa da ga wajen zamansa ya tsaya gaban kotu yana mai sake jinjina kansa. "Tabbas kamar yanda na fada basu bane. Abinda kuma ya fada sun aikata iya shi din suka aikata sai wanda ALLAH ya barma kansa sani da su da suka aikata abinsu. Amma tabbas kamar yanda basu da alaka da kashe duk Zawjata-almilk da suka rasu, haka basu da alaka da kashe Miran Nayyar, itama kuma Zawjata- almilk Fhareedah basu ne suka sakata a cikin ruwa ba".
"To wanene?".
Murmushi kawai kaka yayi sai dai baice komai ba. Yayinda kowa ya zuba masa ido a cikin kotun. Malikat Haseenat son tuno inda tasan fuskar take. Malikat Bushirat kam zuciyarta wani irin mugu mugun harbawa take da masifar karfi kamar zata fito ta bakinta saboda abinda kakan ke fada. Sai dai zuciyarta kwantar mata da hankali take akan ta nutsu ko shi hadimin da ya aikata aikin bai isa ganita ba balle wannan shashashan tsohon da ke jiran ranar mutuwa….. Shirun kaka yasa Sayeed Hanifud-Din sake maimaita masa tambayar. Yanzu ma kaka murmushin ya saki mai sanyi sannan ya dago ya duba kowa da ke cikin kotun, idanunsa ne suka tsaya akan Iffah dake kallonsa tana jin kamar ta taso ta rungumesa. Murmushin ya sake sakar mata ya dauke idanunsa
"Ina rokon afuwa ga wanna kotu mai adalci akan kartsalandan da mai mata. Ban kasance anan dan sanar da wanda ya aikata abinda ake son ji ba, domin kowanene a wanna gidan yake kuma yana a cikin wannan waje sannan da kansa zai fallasa kansa a gabar da ya dace kowa ya sansa..."
"Tofa babbar magana, kotu zata so sanin miya kawoka baba?". Sayeed Hanifud-Din ya fada saboda inkiyar da Sayeed Tasadduq-Husain ya masa.
Gyara tsaiwa kaka yay da kyau, sannan ya ce, "Kamar yanda na fada a farko basu bane, tabbas basu din bane. Su kawai ALLAH ya jarbcesu ne ta hanyar bibiyar wata tushiya da suka zama sanadin samar da tsirranta a shekarun baya batare da sun
sani ba. Ta tafi ta sanadin su, sannan ta dawo ta sanadin su, duk da asali basu bane mafarin komai, dan suma a karan kansu suna aiki ne akan aikin daba nasu ba".
"Baba ka sake sanyani a rudani, ko zaka bayyana mana komai a bude dai-dai da fahimtar mu?".
"Mizai hana in har kotu ta bani dama?".
"Kotu ta baka dama, domin kana akan abinda take bukatar sani ne dan zartar da hukunci ga masu laifi, da yin adalci ga masu gaskiya".
"To Alhamdullah ". Kaka ya fada yana murmushi. Sai kuma ya maida dubansa ga su Miran Jasim da suke a rudanin son tuna inda suka san fuskar, dauke kai yay kamar bai gansu ba ya sake maidawa ga Sayeed Hanifud-Din. "Mune ahalin Zawjata-almilk Fhareedah. Mune kuma suka bada kwangilar halakawa, sai dai ALLAH ya kubutar damu tare da Barrister Abdallah Aas da ya dinga fafitikar taimkonmu tun sanda suka fara bibiyar mu". Ya karen maganar da nuna inda ya taso can karshen kotun.
A kusan tare Miran Arshaan da Miran Jasim suka zabura na tsabar kaduwa da gain Barrister Abdallah Aas da su Baby. Dai-dai kuma da zaburar Daneen Ammarah da idanunta suka sauka kan Babiy. Ba shekara ashirin ba, koda shekara dubu ashirin ce bata jin zata manta da wanna fuskar duk da ganin kwanaki goma sha uku kawai ta taba masa. An musu auren zalunci a wancan lokacin bada san ransu ba bada amincewarsu ba. Amma sun hade kai sunyi kuka tare, sunyi murmushin kuma a tare, sun kuma shaku a tare, sun kumaji radadin rabuwa da juna a tare, yayinda sukai kewar rashin juna a tare, Hankalin duk mutanen da ke a cikin kotun ya rarrabu, wasu akan Daneen Ammarah da ke nuna Baby cikin rawar lips alamar tana son magana ta kasa. Wasu akan su Miran dasim da suka rikice. Was akan su Ummu da ke fitowa:
"Zayyan!! Tabbas kai ne! Kai ne Zayyan ko bayan shekara ashirin sau ashirin ne bazan taba mantawa da kai ba!!!".
Wadan nan zantuka na Daneen Ammarah ne suka zaburar da kowa da kowa ido ya koma kanta har Babiy da kansa ke a duke bai san anai ba, sai dai zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri tunda ya shigo cikin masarautar dama a yau. Shima dai a karo na farko idanun nasa suka sauka akan Daneen Ammarah din, tsaf numfashinsa ya dauke, yay taga- taga zai fadi sai da Barrister Abdallah as da Hanash suka tarosa. Yan kananun magana ne suka fara tashi a kotun, yayinda Tajwar Eshaan ya kafe Iffah da idanu ta cikin eyeglasses dinsa, sosai jikinta ke tsuma itama kamar wadda take a rudani. Sai yaji ta bashi tausayi, wai a hakama bata san tushen al'amarin ba kenan. Ji yake kamar ya rufe ido ya gansa da ga shi sai ita kawal ya rungumeta dan sarar mata nutsuwa shima ko zai samu da ga radadin da zuciyarsa ke masa. Badan karya raba kan mutane ba da zai dage shari' ar nan ne har sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Amma sai ya hadiye komai kamar yanda ya saba dan shi a karan kansa so yake yaji ta inda aka fadi a ragaya, tunda dai gashi gwajinsu ya tabbatar da Daneen Ammarah matsayin mahaifiyar Iffah'r itama. Sannan yanayin Babiy da Mammyn mana yanzu ya sake bude komai a bayyane….✍️
Leave a Comment