Daudar Gora Book 2 page 77
..………"' Tabbas hakane, yau kuma na kara tabbatarwa. Auran Ammarah da Zayyan abunne da bamu shirya masa ba, hakama samuwar wannan yarinya da rasata duk cikin tsarin UBANGIJN talikai ne. Baku aikata laifin komai a garemu ba face taimako. ALLAH kuma ya kaddara Zayyan matsayin miji ga Ammarah dan ya sanar damu abinda bamu da ilimin saninsa. Lallai jini ba karya bane ba. Dan tun a randa na fara ganin Fhareedah naji kaunarta mai karfi a raina, hakama mahaifiyarta. Komin kankantar al'amarin da ya shafeta Ammarah bata wasa da shi. Zuciyata ta fara rawa a kanta a lokacin da was al'amura nata ke kamanceceniya da Ammarah. Sai dai ban san ta ina zan kamo al'amarin ba balle na bashi fassarar da ya dace da shi. Dan ko'a randa mijinta yazomin da batun tambarin tawadar ALLAH dake jikinta irin na wannan zuri'a al'amarin ya jima yana mun kai kawo da kasa banbance makamar rikewa. Hakan yasa a cikin watan azumin nan dukkan addu'oina suka karkata ga al'amarinta. Sai gashi ya sake zuwa min da batun gwaji, yau kuma gashi kun tabbatar mana da komai ALLAH ya saka muku da alkairinsa, ya baku kariya fiye da wadda kuka zama sanadin bama wanna yarinya da ahalinmu bisa zartarwar UBANGIJINMU da ya sakaku zama sanadi. Yanda UBANGIJI ya hada jininmu a duniya, muna fatan ya hadamu a aljannarsa.Ina farin ciki matuka da kasancewar Fhareedah a cikin jikokina jinina, dan ita abar so ce ga kowa".
A tare duk aka amsa da Amin kowa na sharar kwalla. Kafin kuma rikici ya balle tsakanin Ummu da Mammy (Daneen Ammarah) akan Iffah. Ummu ta tabbatar har yanzu Iffah bata sauya ba kuma bazata taba sauyata matsayin wadda ta haifaba a zuciyarta ba. Tana mata kauna irin wadda takema su Hanash, dan haka bafa zata barma Daneen Ammarah ba. Itako ta marairaice mata akan tunda ta dana na shekara goma sha tara itama ta barta tai goma sha tara sai a koma yar sati-sati. (Iffah mai iyaye da yawa😂) Dariya Kaka da Mammah da lyyani da Hanash, Daneen Waheeda suka dinga yi musu. Shi dai Babiy kansa a kasa yana murmushi kawai, lokaci-lokaci yakan saci kallon Mammy din kamar yanda itama take satar kallonsa. Ummu duk tana lure da su, amma sai bataji komai na jin zafi a ranta ba sai ma tausayi da suke bata. Hakama Malikat Haseenat tana lure da su. Sallar la'asar ce ta tada zaman. Fuskar Iffah murmushi da hawaye sun kasa tsayawa. Ana dawowa da ga salla sashen Tajwar Eshaan suka nufa gaba dayansu bisa umarninsa. Kallon Iffah da duk tayi wani sukuku yake ta kasa ido zuciyarsa cike da tausayinta. Tun dazu hankalinsa na kanta, ko abinci bai iya ci ba sai madara kawai da ya dan sha kadan, yata tsammanin shigowarta amma shiru, dan haka ma yama Malikat Haseenat aiken son ganinsu gaba daya. Yau dai kam gasu Baby ga Shahan-shan a zahirancensa dan ko eyeglasses babu a idanunsa ma. Sun mika gaisuwar girmamawa a garesa yayinda shi kuma ya amsa musu da mutuntawa. Sun kara tattaunawa sosai inda shi babu wata kwana-kwana ya bukaci jin ta bakin Babiy da Mamy (Daneen Ammarah) akan maida musu aurensu. Diri-diri sukai su dukansu kamar wanda suka shiga rudani da maganar. Yayinda Kaka da Malikat Haseenat ke murmushi, hakama Hanash da Iffah kallon juna sukai sai kuma suka saki murmushi. Jin kowa ya kasa cewa komai Ummu da tai shiru kanta a kasa ta dago fuskarta da murmushi. Cike da nutsuwarta ta ce, "ALLAH ya karama adalin shugabanmu lafiya da tsohon rai mai albarka. Idan akai hakan tabbas zamu kasance a cikin farin ciki, dan an mutuntamu da karamci mafi girma da ba'a tabama wani a wannan kasa ta ruman ba. Nima zanso kasancewa da yar uwata kodan karta kwacemin yarinyata, why zan shiga wani hali". Ta juya ta kama hannun Baby dana Daneen Ammarah cikin roko tace, "Dan ALLAH karku bani kunya ku amince mu sake zama abu daya.
Karan farko Tajwar Eshaan ya saki wani dan murmushi mai ban mamaki, ji yake wata irin kimar Ummu da darajarta ta karu a ransa. Murmushinsa ya matukar birgesu, ya kuma sake sanyasu a farin ciki, sai dai kuma bai sake cewa komai ba.....
• MALIKAT BUSHIRAT*
Daga kotu da kyar ta iya fitowa zuwa mota, suna isa sashenta dakinta ta shige ta kulle kanta. Jiri take ji da wani irin mahaukacin ciwon kai ga bugun zuciyarta kara hauhawa yake. Shin mike shirin faruwa da ita ne haka, mike tunkaro rayuwarta. Danta Eshaan, Eshaan dai data sha wahala kafin samunsa ne yake auren yar Daneen Ammarah. Mai tambarin tawadar ALLAH a jiki, yarinyar da ke cikin lissafin ayyukansu. Mai tambari dai irin wanda Uwa ta shardanta mata a cikin sharudanta. Mike faruwa haka? Ta yaya hakan zai kasance? _(Ina tayaki murna da albishir din insha ALLAHU kafin mu dawo daga hutun in amarcinmu da iznin UBANGIJI zamu dawo da jikanki a wannan babbar garkuwar, dan haka kibar wahal da kanki akan sai Maleek ya auro wadda kike son ta haifa miki shi dole ko nisanta shakuwar iyayensa da zata zama sanadin samar da shi ta hanyar madara. Da ga kuma randa kika tabbatar da samuwarsa, ki fara irga kwanakin nadamarki da dana sani har zuwa ranar haihuwarsa. Hukunci da karfin ikon Iffah a saman naki, yanzun ne zai fara Mother in-law)_ kalaman Iffah suka shiga mata kaikawo da amsa kuwwa a cikin kunne kamar yanzu ne take fada mata su. _(Ammie na yarda ke Zakanya ce, sai dai ki sani duk karfin bajintarki da iya farauta a saman kowa watarana tsufa kan ¡ya sa ki rissina jikar bayanki ta zama sarauniya bisa karfin ikon naki, Ni bance nafi karfin kaddara ba, sai dai ki sani a tafin hannunna kike ke da komanki....)_. Kuka ta fashe da shi, cikin karaji ta furta "Bazai yiwu ba, bazan dauki faduwaba, wihy Uwa bazan dauka ba sai dai duk mu fadi tare, sai dai ai mutuwar kasko mu dukanmu baki daya" wani irin kuka ya sarketa, wasu kalaman Iffar ne suka sake shiga dawo mata…. _(Ammie wihy inada abubuwan ban mamaki da daga labulen sirrinki sau daya kawai sai ya hana wannan idanun naki barci.....)_ wani irin naushi ta kaina mirror din akin da sake kwala kiran sunan uwa_(…..……To wai nikam wane buri ne kike son cimmawa mai alaka da makiyi a tsakaninki da shi? Kin ko san da ace yasha ganyen shayin nan ko madarar nan illar da zatama rayuwarsa sai tafi wadda zatama tawa rayuwar? Sannan ke da kanki sai kin dawo kina kuka da dana sani. Idan ma wani ke baki wadan nan abubuwan matsayin wani kariya washi ko gurbata tawa rayuwar to tabbas ki farka. Ki farka why tunkan guri ya kure miki ki rasa kofofin fita a wannan masarautar.…)_ "Har abada! Har abadan abada bazan taba faduwa kasa ba, bazan rasa komai ba a lokacin da komai ya zama nawa ba....
"Dole ki rasa! Dole kirasa!! Dole kirasa ta-kurya!!Hahahahaha!!!!". Uwa ta fada cikin karaji da amsa kuwwar mummunar muryarta alokacin da take bayyana. A kallo daya zaka fahimci itama a birkice take. Dan idanun nata sun sake jajur, fuskarta ta sake muni matuka. Da wani irin karsashin wutar bala'i Malikat Bushirat ta fiskanceta, a yau babu wani tsoro ko shakku tare da ita balle girmamawar da ta saba ga uwar. Gabanta taje ta tsaya tana mai nuna ta da yatsa.
"Sai dai mu rasa gaba dayanmu, amma ba Malikat Bushirat kawai ba. Miyasa kika yaudareni?..
"Ke kika yaudari kanki, domin a yarjejeniyar mu akwai sharadin kin auren yarinyar data fito a wannan zuri'ar musamman mai tambarin na hakika".
"Amma da umarninki ta zama matar Saiful-malik, shin bokancin naki ya fara raunine ko dama ke din mayaudariyace kamar yanda yarinyar ta fada?!!!".
"Ki iya bakinki ta-kurya!!!".
*Bazan iyaba, nace bazan iyaba uwa. Wihy why, kinji na rantse, bazanyi asarar wahalata ba. Sai dai ni da ke duk muyi mutuwar kasko".
"Kece da danki zakuyi mutuwar kasko, kuma dole ki bamu jinin Ajlaan madadin sauran ayyukanmu da baki cika ba!!".
"Har abada, har gaban abada jinin Saiful-malik yafi karfinki azzalumar mushirika. Nima da kike gani hatsabibiyar kainace uwa, dan tun kafin ke gwanace a iyawata!!"
"Kin san da iyawar taki miya hanaki iyama kanki sai da taimakona. Butulu ke wacece, har wacece ke nace ta-kurya? Har mi kike takama da shi? In ce dai Ajlaan ne ko? Kuma mune muka samar miki da shi a lokacin da kike neman samuwarsa do rufe (Wa'alaikissalam 😭ALLAH ne kadai ke badawa da hanawa a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso. To ki rubuta ki ajiye mune zamu shafe babinsa da tarihinsa, kamar yanda muka shafe na ubansa da kakansa a doron duniya.Idan kin isa, Kin cika sunanki tsagera mu zuba!!!!"
Bat uwa ta bace a akin kamar tashin guguwa. Wani irin fashewa da kuka Malikat Bushirat tai cikin ihu da fisgo duk abinda ya tare mata gaba ta dinga ratsawa da kasa. Jikinta want rin jiljigar rawa yake na masifa, da ga karshe ma kawai sai ta yanke jiki ta fadi dan jini ya balle mata sosai saboda raunikan da ta jima kanta a dalilin fashe-fashe.….✍️
Leave a Comment